← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 95

Sashe 75

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ka shirya mini mijina, Allah ka sa ya daina abun da yake yi. Ya Allah, Allah ka sa ya shiryu.
Allah na san ba zaka kunyata ni ba, Allahumma inni as'alukal jannata wa na uzubika mina narr. Rabbana hablana min azwajina, wa zuriyyatuna ƙurattu a'ayunun waja'alna lil muttaƙina imama. Rabbigfir ummi wa abi, warahamhuma, kama rabba ya ni sagira" ta ƙarasa tana shafar fuskarta, da tafukan hannayenta, hakan ya tabattar masa da addu'aoin ta ne na salla, take maimaitawa.

Ya lulluɓeta, ya tashi ya sake fita, sai dai abubuwa daban-daban suna ta cigaba da kai komo a zuciyarsa, ya ji ƙwarai yana son sanin wacece yake zaune da ita a matsayin mata, shi dai ya san ba shi da nagartar da uban kirki zai bashi auren 'ya, idan ba da wata a ƙasa ba.

Cikin gari ya sake ninkawa ya tafi, bai zarce ko ina ba sai gidansu, ya tarar har sun rufe ƙofa.

Bugawa ya fara yi iya ƙarfinsa, Abba ya zo ya buɗe, yana ganin Al'amin ya ruga da gudu ya koma, saboda yana bala'in tsoronsa.

Ba tare da ya kula kowa ba, ya shiga kitchen, ya dudduba babu komai sun cinye abincin.

Rahila ta fito, ta ce "Kai Aminu lafiya ka zo mana a wannan daren? Yaushe aka sako ka?"

"Shahida" ya ƙwala mata kira, kasancewar ya hangota a falo.

Cikin hanzari, ta fito ta ce "Gani yaya"

Yayi mata alama ta shiga kitchen, ta shiga ya bi bayanta, ya ce "Dafa mini shayi cikin flask É—in nan" yayi maganar yana nuna mata flask É—in shayinsu, family size.

"Wai Aminu me ka ke yi haka, dan me zaka sakata girki a wannan tsohon daren?"

Bai kulata ba, ya kwaso ƙwai ya zube mata ya ce "Ki soya mini wannan ma".

Rahila ta koma bedroom ta taso Abbu ta ce "Ta so, ga ɗanka can ya zo a wannan tsohon daren, kar ya yi mana ɓarna".

Abbu ya taso ya fito, dan ya fara bacci ma.

Ya fito yana faÉ—in "Kai Al'amin lafiya, ka zo mana a daren nan? Ina matar taka ina gidan naka?".

Shahida ta ce "Abbu ka koma ka kwanta, ba wani abu, girki kawai ya ce na yi masa".

"Kuma a daren nan, ina matar ta sa?".

Abbu yana ta ɓaɓatu, Amma Al'amin bai kula shi ba, sai ma ɗaukko ledar viva, ya buɗe fridge ya kwashe lemon ɓawo ya zuba a ciki, kankana da sauran abubuwan da ya gani a ciki har da su madarar ruwa.

"Ka yi masa magana, wannan kayan da yake É—iba ina zai kai su?".

Al'amin ya kalli rahila ya ce "Da kuka aura mini 'yar mutane, ai kun san bani da abun yi, in bari yunwa ta kasheta ko na fara satar kayan mutane ne na kula da ita? Ba ta da lafiya dan haka dole na fito na nemi abun da zan kai mata ta ci".

"Da can kai da me ka ke riƙe kanka, ba sai ka nema ba, kuma saboda lalacewa da abun kunya, daga gidanku ne za a ciyar maka da mata?

Al'amin ya waiwayo a fusace, ya nunata da yatsa ya ce "Ki kiyayi lokacin da haƙurina zai ƙare a kanki"

Shahida ta ce "Yaya gashi na gama, ka ga akwai su maggi ma a nan, tayi maganar tana buÉ—e drower tana É—aukkowa. Ta buÉ—e wata ta É—ebo su taliya da macaroni ta ce "Ka haÉ—a da su"ya girgiza kai ya ce "Ban da wannan, wannan sun isa"

Ta sake cewa "Yaushe zan zo gidanka, ina son kan na koma school na zo muku ziyara, tun da ba ma nan aka yi bikinka, samu zo mu dubata"

A taƙaice ya ce "Sai kin zo".

Ta ce "Wannan ɗin sun isa, ko kuna buƙatar wani abun?"

Ya ce "A'a, sun isa. zo ki rufe muku gidan" ya ƙarasa maganar yana kwasar kayan, ya nufi hanyar ficewa.

"Al'amin" Abbu ya kira sunansa, ya tsya cak bai waiwayo ba.

"A tunanin auren nan da aka yi maka nutsuwa zaka yi, ka daina wasu abubuwan da ka ke aikatawa, amma abu ya ci tura, ka sanya 'yar mutane a tasku da tashin hankali, meya kai ka ta'amalli da hodar iblis?.
Lokaci yayi da yakamata ka daina wasu abubuwan, ko dan kare mutuncinka da na iyalinka. Ko dan ka ga ka sameta a ɓagas ka ke nema ka wahalar da rayuwarta"

"Kaga Abbu dan Allah ka daina jan maganar nan, ya tafi kawai su je can su ƙarata, dama ai ba ji take ba ita ma, daidai da ita ne"

Wani abu mai nauyi ya haÉ—iye, ya saka kai ya fice, ba tare da ya sake cewa uffan ba.

Bayan ya tafi, Shaida ta ce "Mama dan Allah ki daina tayar da hankalinki a kan yaya, idan yana wannan abubuwan ki zuba masa ido, tun da ba kullum yake zuwa ya yi ba. Abu ɗaya kawai yake buƙata yayi iko da kayan mahaifinsa a matsayin sa na ɗa, kamar yadda muke yi, kin san fa ke da shi, ba kwa jituwa ki din ga kawar da kai a wasu abubuwan da yake yi, yana ɗaga miki ƙafa fa kar yayi miki wata illar".

Abbu ajiyar zuciya ya yi, maganganun shahida gaskiya ne, amma shi babban takaicin sa, Al'amin ba ɗan da za a haɗu a rufawa kai asiri bane ba, miyagun halayensa ya sanya ba ya son ya zo ko in da yake. Gaba ɗaya auren da aka yi masa bai sanya ya nutsu ba, kodayeke da sauƙi tun da ya san ya fito ya nemi abun da zai bawa 'yar mutane.

Ya koma É—akinsa, Rahila ta bi bayansa, Amira ta ce "Ohh yau ni nake ganin tsiya, yanzu fa sai a ce ciki ne da ita ko?"

Shahida ta ce "Ba abun mamaki bane"

"Taɓ, a wannan muzuran da tashin hankalin nass har ta ɗau ciki, iko sai Allah"

Al'amin ya sake ninkawa, ya koma gida ya shiga É—akinta, ya tarar tana ta baccinta, kamar ya tashe ta, sai ya fasa, ya koma É—akinsa ya kwanta.

Bai farka ba, sai wajen tara na safe, a gaggauce ya yi sallar asuba, ya fito falo, ba ta nan ya shiga É—akinta, tana kwance ta takure wuri É—aya.

"Kin tashi?" Ta jinjina masa kai almar eh.

"To taso ki karya ki sha magani"

Ta ce "To, bari na yi wanka nayi brush"

A hankali ta lallaɓa jikinta, ta shiga ta yi wanka, ta canza kaya ta fito falon.

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Ina kwana?"

"Lafiya ƙalau, bari na kawo miki abinci"
Kitchen ya je ya ɗaukko kofi, da shayin da ya zo da shi a flsk, da uban ƙwan da ya saka shahida ta soya masa.

Ya ajiye mata a kausashe ya ce "Gashi nan ki karya, ki sha magungunan da suka baki. Saura ki ƙi ci wani ciwon ya kuma kama ki"

Ta na fara ci ta ji ta ƙoshi, amai ma take ji.

"Wai ba kya so ne ki ke jagwalgwalawa?"

Ta ce "Na ƙoshi ne"

"A ɗan abun da ki ka ci ne har kin ƙoshi" ya taɓe baki, ya miƙa mata magungunan ta karɓa ta sha.

Ya bata wayarsa ya ce "Saka mini lambarki, idan da wani abuk sai ki kira ni fita zan yi"

Kallonsa tayi da mamakin yana sane ko wulaƙanci ne, ya sanya yake tambayarta lambar waya.

"Bani da waya" ta amsa kanta a ƙasa.

Ya mayar da wayarsa aljihunsa ya ce "Shikenan, maganar da nayi miki, ki yi tunani a kai, a ɓangarena ni ina ganin hakan shi ne mafita kawai, amma ki yi tunani abun da ki ka yanke, ki sanar da ni".

Dummm ƙirjinta ya buga, kenan haryanzu yana kan bakansa? Ba ta ce masa uffan ba, ya fice.

Rasa abun yi tayi, duk da ba ta da tsarki, tayi alwala ta zauna ta kalli gabas, tayi ta addu'a a kan lamarin rayuwarta.

Can wurin su Walid ya tafi, in da suke zama su yi shaye-shaye, su naÉ—a wiwi.

Walid ya kalli Al'amin ya ce "Maza lafiya kuwa? Yanayinka ya nuna kamar akwai damuwa".

Banza ya yi wa walid, dan haka shi ma ya share shi, ya cigaba da aikin gabansa.

Sai kuma can ya ce "Mai laya"

"Na kiyayi mai zamani, ya aka yi?"

"Dama yara matasa suna hawan jini ne, ba sai tsofaffi ba?"

Ya ce "Eh to, na ji an ce akwai wanda ake haifar su da shi ma, amma hawan jini a matasa, maybe damuwa ce ko gado".

Ya jinjina kai.

Liti ya ce "Maza ko kai hawan jinin ke damu? Kana da 'yar madara, ai ba zaka yi hawan jini ba"

Tsuke fuska ya yi, jin liti ya kira jauhar da 'yar madara.

Gidansu Al'amin, Abbu ya shirya zai fita ya kalli rahila ya ce "Yakamta idan an janye yajin aikin nan, ku je ku duba matar yaron nan"

Rahila ta ce "Taɓ haka kurum, su dai yaran su je ni in je ya illata ni a banza? Su dai su je"

Abbu ya ciro kuÉ—i a aljihunsa ya ce "Amira, ga kuÉ—i nan ku hau mota, ga dubu biyar ku saya mata fruit ku kai mata, na ji an ce zuwa jibi in Allah ya kaimu, za a janye yajin aikin, sai ku je ku duba jikin nata, kafin na samu na je nima"

Ta amsa da to Abbu. Sai dai bayan fitarsa Amira ta ce "Na samu na saka data, dan ba za ta ci 5k É—in nan ba".

Shahida ta ce "Wallahi kuwa da sai na gaya masa, ai ba haka ake yi ba" haka suka cigaba da faÉ—an su na sakonni.

Jikinta ya ɗan yi sauƙi, sai dai ba ta daina ciwon kai ba, ga damuwar abun da Al'amin ya sake nanata mata, kenan yana nan a kan bakansa na rabuwa da ita.

Kusan kwanaki biyu, ba ta bari su zauna wuri É—aya, saboda kar ya sake tayar mata da maganar.

Ya gama karyawa, yana kallonta tana ta shirin dutsenta, karyawar ma ba ta yi ba, kamar yayi magana kawai ya shareta, ya tashi ya fita.

Su halimatu suka shigo, suka tayata aikace-aikace, sannan suka koma gidansu.

Tana falo tana karatunta tana shirin dutse, aka yi sallama a tsakar gida.
Chapter 75 · 0% Book details