← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 95

Sashe 61

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina gida, ni wallahi yarinyar nan ta fara takura mini, komai kuka, duk ta tashi hankalinta, iyayenta ba su yi mata adalci ba, ni fa ba zata hana ni rayuwata yadda nake so ba".

Walid ya ƙyalƙyale da dariya ya ce "Mai dogon zamani, da uban waye ya damu da ka ji koma menene mana, tana da tausayi ne kawai da alama, ka dai daina yi mata muzurai da zare ido kawai"

Yayi tsaki ya ce "Ka saka liti ya nemo mini suwaye yaran nan"

"Shikenan, zamu faso gobe in ga jikin naka, sai da safe". Ya ajiye wayar ya kalli fuskarta, tana ta bacci a zaune.

Hannunsa É—aya ya saka, ya janyota ta kwanta a kan katifar, shi kuma ya jingina da bango ya cigaba da bacci.

Kasancewar ba salla za ta yi ba period take yi ya sanya, tana ji ana kiran sallar asuba, ta cigaba da baccinta, sam ta manta a ina take.

Ƙaurin da ya isheta ne, ya sanya ta fara tari, tayi juyi ta buɗe ido, da fuskarsa ta fara tozali, yana busa sigari. Ta tashi tana kallon ɗakin, sai yanzu ta tuna ta shigo tana yi masa fifita.

Ta hau soshe-soshen cizon sauro.

Ƙura masa ido ta yi, ya kawar da kansa gefe.

A raunane ta ce "Master"

Idonsa ya É—ago ya kalleta.

"Dan Allah ka daina, ba na so zuciyata ba ta yi mini daɗi, kuma zaka cutar da kanka, kalli yadda ka je aka yi maka rauni, ka zubar da jini, haba master manya ba sa haka" tsuke bakinsa yayi yana sakin hayaƙin, a ƙoƙarin sa na hana maganganun ta yin tasiri a zuciyarsa.

Ta girgiza kai ta ce "Shikenan, ya jikin?".

Yayi mata banza, ya cigaba da busa sigari.

"Dan Allah ko ba zaka daina ba, ka rage mana, lafiyar ka fa".

"Ke, ki koma in da ki ka fito mana, ko na É—aure ki na ce ki zauna ne? Tashi ki bar mini É—aki".

Ta gyaɗa kai ta ce "Abun har da gori, Allah ya baka haƙuri" ta miƙe idonta fal hawaye.

Tana kitchen tana aikin karin kumallo, aka buga ƙofa, ta saka hijjabi ta buɗe ƙofar, ta ga walid d wasu matsa su biyu, suka gaisa suka ce mata, wurin mak dogon zamani suk zo.

Ta haÉ—e rai ta ce "Sunan shi Al'amin, bari na yi masa magana".

Tana shiga ta tarar da shi a falo ya fito.

Ta ce "Ka zauna sai su shigo su ganka, amma ka ga da rauni a jikinka" tayi maganar tana sunkuyar da kai, tana jiran ya gaya mata baƙar magana.

Idonta ya É—an yi ja, saboda kukan da ta yi.

Ya nemi wuri ya zauna, ba tayi tunanin zai yadda da hakan ba.

Ta je ta leƙa ta ce musu su shigo.

A falo suka tarar da shi, gida sai ƙamshi yake yi, gashi dai ba wani haɗaɗen gida ba, amma ta gyare gidan tsaf.

Suka zauna a falo, Walid ya ce "Maza wallahi ka more, mu ma Allah ya tsamo mu, dan Allah ji wani ƙamshi kamar a gidan masu kuɗi".

"Duba ni ka zo yi, ko munafunci ka zo yi?"

Walid ya ce "Duka, amma dai ya jikin? Kut ka sha ɗinki kamar ƙwarya, za su ci ubansu yaran nan, kan yamma an gano su in sha Allah".

Suna ta zuba, tana jiyo shi yana saka baki sama-sama, da ita ce dai ba zai yi hira ba, amma yana magana.

Tayi sallama suka amsa, ta zo ta ajiye musu kofuna, da cokula da flask ɗin shayi, ta koma ta kawo jallof ɗin taliya a faranti, sai ƙamshi take yi.

Liti ya ce "Allahu Akbar, sannu amarya, wannan hidima haka? Ai da mun sani tuntuni mun zo" Al'amin kallonta yake yi, da jinjinawa ƙarfin halinta, har ta ƙar sanwa, ta yi girki da su.

Suka kewaye, suka din ga cin taliyar nan, liti ya ce "Kalarta kalar girkinta, abincinta mai daɗi, ita kuma 'yar beauty, wallahi maza ka more, ga gida mai ƙamshi"

Ji yayi ya kasa haÉ—iye abincin, maimakon ya ji daÉ—in yabon suka yi mata, sai ya tsuke fuska ya tsame hannunsa daga kwanon abincin.

Har suka gama santin, bai sake cewa komai ba, Walid kuma yana ankare da shi, dan haka da gayya, ya cigaba da kunna shi, suka gama abun da za su yi, suka fita tsakar gida suka din ga yi mata godiya.

Walid ya ce "Wai ba zaka fito ka raka mu ba?"

Tayi farat ta ce "A'a ba shi da lafiya ai"

Walid ya ce "Au, to Allah ya baku haƙuri, Allah ya ƙara afuwa ya bar ƙauna".

Bayan fitarsu ta kwashe kwanukan, ta wanke, tana ta aikinta, yana kan doguwar kujera a kwance, sai dai ba ta kula shi ba.

Kusan kwanaki uku, jikin master yayi kyau, ba shi da ƙan jiki, ba zai sha magani ba sai ya ga dama, dressing kuwa cewa yayi ba ya so.

A kwanakin nan jauhar na jin ciwon kai, da ciwon jiki, sai dai ba ta wani damu ba.

Duk yadda ta so hana master fita, da 'yan dabaru sai da ya saka ƙafa ya fice, ya tafi nasa garari.

Cin abinci ne yake dawo shi, ko sau É—aya bai tambayi yadda take samun yin cefane ba, sai da ya zo ya ci.

Tun da ya dawo gidan ya ji shiru bai ji motsinta ba, kuma bai ga abinci ba, sama da awa guda, saɓanin da, da ya shigo za ta fito.

Kasa kwanciya hankalinsa yayi, ya nufi É—akinta.

A kwance take a kan gadonta, amma bai tabattar da idonta biyu ko bacci take yi ba.

Ya ƙarasa gaban gadon, sai dai ya manta sunanta, Fatima zahra kuma yayi masa nauyin da ba zai iya faɗa a bakinsa ba.

Ayshercool
08081012143

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Dukan gefen katifar da take kai yayi, amma ba ta motsa ba, ya zura kai ya leƙa fuskarta, ya ga bacci take yi. Duk da bai saba zuwa ya tarar da ita tana bacci ba.

Ficewa ya yi, ya bar É—akin, shi babban takaicin sa, rashin samun abun da zai ci.

Jauhar kuwa, tun dare ta kwana ta na fama da matsanancin ciwon mara, ga ulcer ta tayar mata, sai gudawa take fama da tashin zuciya, ta samu ya lafa mata, ta kwanta ta hau bacci ga gidan yau babu abun da za ta dafa, É—an kuÉ—in hannunta sam ba su da yawa.

Ƙarshe dai buredi ya fita ya samo, ya dawo ya zauna a falo yana ci.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ga kiran indabo ne, kallon wayar ya cigaba da yi, yana cin buredinsa, sai da ta kusa katsewa ya É—aga ya saka a kunnensa, yayi shiru.

"Aminu"

"Mmm"

"Na dawo, kai nake jira, haryanzu ba ka zo ba"

"Zan zo"

"Yaushe kenan? Haba kai kuwa dan Allah, ba ka san kiran me nake yi maka ba fa"

Al'amin ya ce "Na ce zan zo ai"

"To shikenan, Allah ya kawo ka"

Ya ajiye wayar, gaba É—aya haushin buredin da yake ci ma yake ji, sam ba ya yi masa daÉ—i, har aka yi kiran la'asar, ba ta fito ba.

Ya tashi yayi salla, ya fito falo ya sake zama, sai ga ta ta fito tana É—an yamutsa fuska. Fuskar duk ta É—an É—aga tayi jawur.

Ta zo ta nemi wuri ta kwanta, ba tare da ta ce masa komai ba.

"Wai yau ba abinci ne?" Yayi maganar yana wani basarwa.

Maimakon ta ce masa babu abun da za ta dafa ne, sai ta ce masa "Ba na jin daÉ—i ne"

Ya taɓe baki, ya tashi ya saka takalmansa ya fice daga gidan, fitarsa ba kaɗan, ta ji horn da tsayuwar mota a ƙofar gidan, mintuna kaɗan ta ji ana bugun gate, ta saka hijjabi ta je ta buɗe.

Baba ta gani a tsaye, cikin matsananciyar murna ta ce "Baba" yayi murmushi ta ba shi hanya ya shigo.

Suka isa har falonta, ya samu wuri ya zauna ta ce "Baba meyasa baka kuma zuwa ba?" Tayi maganar hawaye na cika mata ido.

Wani irin matsanancin tausayinta ya kama shi, har ya ji kamar shi ma ya yi kukan, amma ya danne ya ce "To ba gani na zo ba, Waliyiyya 'yar baba"

"Baba babu wanda ya zo mini, sai yaya saifu da Anty lubabatu, kowa yaƙi zuwa in da nake, wai ba za su zo ba, mijina ɗan daba ne, kuma ba abun da zai yi musu, ba ruwan shi da su.

Baba ya ce "Waliyiyya, ki daina saka irin wannan abubuwan a ranki, kar su dameki, ki yi haƙuri ke mai haƙuri ce, amma ki ƙara. Ya gidan ya mijin naki?"

Cikin jin kunya ta ce "Yana nan lafiya, yanzun nan ya fita"

"Jauhar, ina fatan dai babu wata matsala dai ko?" Ta girgiza kai ta ce "Babu".

Turus yayi ganin takalma a ƙofar falo, amma ya ƙarasa ya shiga, ba tare da ya yi sallama ba.

Kallo ɗaya ya yi wa mutumin, ya ga yana yanayi da jauhar ya ƙarasa cikin falon, hannunsa riƙe da baƙar leda.

Durƙusawa yayi har ƙasa ya ce wa Baba "Ina wuni" hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa jauhar ba, dan tun da ta ji motsin shigowar sa, take fatan Allah ya sa kar ya yi wa baba wani abun na rashin ɗa'a.

Baba ya ƙare masa kallo, kai ba ka ve mara ji bane ba, dan a cikin nutsuwarsa yake, ya ce "Lafiya ƙalau malam Aminu, yau dai Allah ya yi mun haɗu, ya gidan ya iyalin naka"

Ya amsa da "Lafiya ƙalau".

"To masha Allah, Ubangiji Allah ya yi muku albarka, ayi ta haƙuri, ka san ita rayuwar aure, zama da mace sai haƙuri, dole za ku saɓawa juna, ayi ta haƙuri. Ba yabon kai ba, na san Waliyiyya yarinyar kirki ce, amma duk da haka na san dole wataran a saɓa Allah ya yi muku albarka"

Ya amsa da Amin, ya tashi ya bar wurin ya tafi É—akinsa.

Ta ce "Baba bari na dafa maka abinci"  ta faɗi hakan, dan kar baba ya fahimta wani abu.
Chapter 61 · 0% Book details