Sashe 82
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kalleshi tana dariya, ya kalleta ya ce "Ki ka sake ki ka yi magana ni da ke ne".
Jauhar ta ce "A'a ni ban ce komai ba" tayi maganar tana cigaba da dariya.
Tana ta aikinta an kusa shan ruwa ya ce "Anya kina azumin nan kuwa?"
Ta ce "Ina yi mana"
"Gani nayi yau sha bakwai ga wata, ba kya azumi"
Ta kalleshi ta ce "To meye da sha bakwai ga watan?"
Al'amin ya ce "Period ki ke yi, dan banaba kya azumi" zaro ido tayi cikin mamaki, yaya aka yi ya san tana period, cikin jin kunya, ta ce "Ni ba abun da nake yi, ba wanann date É—in bane"
Kawai ya gyaɗa kai, ya ce "Ai da ki ka gama cin ƙosan a kitchen ki ka cika cikinki, ba ki goge bakinki ba, kuma lemon da ki ka sha ma cup ɗaya kin sha naki, tun da ba azumi ki ke yi ba, sai iya yi mini dariya" ai kamar ƙasa ta tsage ta nutse, ba ta sanin ya ake yi, yake sanin ta aikata wasu abubuwan ta hau goge baki ta ce "Sa ido ba kyau, azumi ka ke yi kar ka zobe ladanka, ko a kwashe ladan naka a bani"
Yayi murmushi bai ce komai ba.
A wurin shan ruwa faÉ—a suka yi ta yi, wai ba zata cika kofi da kunu ba, ba tayi azumi ba, kamar sako da sakuwa.
"Wai master, dan ban yi azumi ba ai ni na girka, sai ka barbaÉ—awa duniya ban yi azumi ba? Haba master"
Ya ce "Eh ai ba yi ki ka yi ba, dan haka nawa sai ya fi naki yawa, ƙara mini"
Ta tura baki ta ce "Aikuwa da gobe in Allah ya kaimu sai dai ka karɓo kunun sadaka, da ƙosai ka ci, ba zan yi girki ba, tun da ni ba na azumi, ko ka girka abunka".
Ya ce "Eh dan dai girki, ba wuya zan iya, ƙosan nan ma rago shi nan, gandiya ƙatuwa da ke ba kya azumi"
"Bani da lafiya ne" haka suka yi shan ruwan, ya din ga jin kamar bai taɓa shan ruwa da nustuwa irin wannan ba.
Ita kanta tsokanar da yake yi mata daÉ—i take ji, bayan sallar isha'i ya zauna a falo, ya É—auka zata yi masa surutun da ta saba, sai dai hankalinta ba ya kansa, yana kan magenta da take cewa boti, tana bashi abinci tana shafa shi, haushi ya ishe shi, shi gashi ba iya hirar yayi ba, balle shi ya fara, kawai ya tashi ya tafi É—akinsa. Bayansa ta bi da kallo kawai ta yi murmushi ta ce "Master kenan, hukuma sai da rarrashi".
Bakwai ga watan azumi ya kama ranar da za su bi Indabo campaign, tun dare ya haÉ—a yaransa da wurin da za su haÉ—u su tafi.
Da sassafe bayan Jauhar ta tashe shi yayi sahur, ta idar da sallar asuba ta kwanta bacci, ya silale ya fice.
Wunin ranar ba ta ganshi ba, ba ta damu ba sai da ta ga an kusa shan ruwa, ta din ga kiran wayarsa, amma ba ta shiga, sai hankalinta ya fara tashi, dan ta san duk in da ya je da an kusa shan ruwa yake tahowa gida.
Al'amin kuwa bayan sun dawo daga campaign, an yi sare-sare sun yi shaye-shaye, an yi wa indabo aikinsa yadda yakamata, Al'amin ya sallammi yaransa, shi kuma Indabo ya ce ya bishi gida, da shi da wasu 'yan jami'iyya su sha ruwa a gidansa, ya sanya an shirya abun shan ruwa.
Al'amin ya ce sai dai su tafi tare da walid.
Ƙaton falo ne na musamman, mai ɗauke da haɗaɗɗem dining, kayan abinci aka kawo, na ƙasaita aka din ga jerewa a kan dining ɗin nan, cikin fulasai na alfarma.
Walid ya ce "Mu na cin albarkacinka mai zamani, wannan sabga haka?"
Al'amin ya bari, aka gama jere abinci, ana ta rawar jiki a fara ci ayi buÉ—e baki, ya tashi, ya bubbuÉ—e fulasan.
Wani irin farfesu aka yi na kajin gidan gona, ƙosassu, ga flask ɗin dankali dana ƙwai abincin ma har da na almubazzaranci.
Al'amin ya ja flask ɗin kaji, ya janyo na dankali, ya haɗe kan kayan shayi madarar gwangwani da milo, ya kalli Walid ya ce "Dafe mini wannan mu ɓace".
Indabo ya ce "Ina zaka tafi kuma, za a ci abinci?"
"Gida" ya bashi amsa.
"To kuma na ga kana harhaÉ—e kan kwanukan abincin, ya zaka yi da su ga mutane za su ci?"
Kai tsaye ya ce " 'yar madara zan kaiwa"
"A'a ya mage zata yi da wannan uban abinci haka?"
Walid ya ce "Ba mage ba ce, madam za a kaiwa"
Indabo ya ce "Haba mai zamani, sai ka ce a É—ibar mata, amma yaya za ayi mutane na zaune abincin mutum sha biyu duk ka kwashe rabi?".
"Ba zai yiwu da ni da na saka rayuwata a hatsari, da wanda ku ka tsaya a cikin rumfa hankali kwance, ka yi mana sallama iri É—aya ba, ai kana da kuÉ—i a dafa musu wani. Ka san son zuciya ba halina bane, a baya ban yi ba ba zan fara yanzu ba. Ba zan ci wannan abincin ita ba ta ci ba, kuma ai ga wasu nau'in abincin nan ku ci. Walid É—aukko kwandon kayan marmarin nan ma"
Indabo ya ce "To fulasan fa? Ka tsaya sai a juye maka a leda, na madam ne wannan"
"Madam ba ta fi madam ba, sadaki bai fi sadaki ba. Ina fatan ka fahimci lissafin? kuma kuna da kuɗin sayen wasu, ko ba yanzu ba idan kun ci zaɓe zaku samu, dan haka har fulasan mun cinye" Indabo yana ji yana gani, Al'amin ya yarfa shi a gaban jama'a, suka kwashe abinci suka tafi.
Jauhar ban da ruwa babu abun da ta sha, har bayan sallar isha'i sai yawo take yi a cikin unguwar tana nemansa, hankalinta a tashe. Ta gaji ta dawo gida da nufin ta kira Walid.
Kawai ta dawo ta tarar da shi.
"Master ina ka tafi, hankalina ya tashi tun safe rabonka da gida, ba ka gaya mini ina zaka je ba, gaba É—aya tun da aka sha ruwa na kasa cin komai, ban san ina ka ke ba".
"To kukan zaki yi?"
"Baka gaya mini ina zaka je ba, hankalina gaba ɗaya ya ƙi kwanciya haba master dan Allah"
"Ohh murya kamar tsuntsuwa, yenyenyen, ki din ga buÉ—e baki ki yi magana sosai" kawai tayi shiru cike da takaici, idonta kawai ya kalla, ya san hankalinta a tashe yake.
Ƙeyata ya tura, zuwa ɗakinsa kawai ta tarar da jeren kwanuka, haɗaɗɗun fulasai, da uban kayan marmari.
Tayi saroro tana kallon kayan.
"Zo ki zuba mana mu ci, ba kayan wani bane, mun je campaign ne muka dawo aka shirya shan ruwa, na ce a gida zan ci na taho da shi".
A É—an tsorace ta ce "Master duk wannan kuma?"
"Eh kwaso kwanuka"
Iya kajin sai da suka tsorata ta, dan sun kusa goma, fulasai ne na alfarmar gaske.
Ta ce "Ai ba zamu iya cinyewa ba".
"Gasu nan dai, ki yi abun da ya dace".
Duk son Jauhar da nama, sai da ya isheta, ta bawa maƙwabta, ta zuba wani ya kira guduma a waya, ya ce masa ya zo ya karɓa.
Hatta magenta, sai da ya ƙoshi da ciye-ciye.
Haka kurum ya din ga jin annashuwa a ransa, ganin ta ci ta ƙoshi, har abun ya gundureta.
Bayan jera masa godiya da ta gama yi, kamar yadda ta saba, tare da addu'oi, ta ce "Master Alfarma zan nema a wurinka dan Allah"
"Ina jinki"
Ta saka hannu ta karɓi wayarsa ta ce "Dan Allah kar ka ce mini a'a, ko ba zaka yi ba".
"To kar ki tambayi abun da ba zan iya ba".
"Zaka iya mai babban suna, kaga naman nan yayi mana yawa, duk da an babbayar dan Allah sonake na ƙara gyara shi, ayi miya gobe in Allah ya kaimu, mu je yi wa su baba sannu da shan ruwa"
A take ya tsuke fuska, ya ƙi magana.
"Dan Allah Master, na neman albarka mu je mu gaishe su"
"Wai ke wace iri ce ne? Tun da muka yi aure, bayan su hajiya, kin ga wani ya zo gidan nan daga ɓangarena? Ko Abbun kin ga ya zo? Dama maraba suke nema da ni, har gara mahaifinki ma ya zo"
Jauhar ta ce "Kar ka ce haka, dama ba su yakamata su zo ba, mu yakamata mu je, ai su iyaye ba a fushi da su, kai fa ka yi wa wani faÉ—a a kan haka, bai kamata kai ace ka aikata haka ba, dan Allah ka yarda mu je" An kai ruwa rana sosai tsakaninta da shi, kafin ya amince.
Washegari suka shirya, bayan azahar suka fara zuwa gidan su Al'amin.
Suka fara zuwa gidan su Al'amin, suka yi sa'a Abbu yana nan, sai dai rahila tayi mamakin ganin Al'amin, yayi wani shar da shi, sai ƙamshin turare yake yi kayansa sun sha guga.
Ashe Abbu zuwansa gidan su biyu, ba ya samun kowa, a gidan, gashi Al'amin ya wanke ƙafarsa ya daina zuwa gidan.
Abbu baki ya kasa rufuwa, mamaki yake ganin Al'amin, a nutse da shi ya sako 'yar matarsa a gaba gwanin sha'awa, sai dai sai cika yake yi yana batsewa yana wani basarwa.
Dan tun da suka gaisa da Abbu, bai sake cewa komai ba, jauhar ce take bashi amsa idan yayi magana.
Rahila ma sai zuba take ta ce "Ikon Allah, anya ba a canzo wani Aminun ba, kun yi kyau abunku kun ƙara ƙiba, an ce kin yi rashin lafiya kwanaki, To na san dai ba zai wuce laulayi ba, Allah ya raba lafiya"
Al'amin ya ce "Amin, tashi mu tafi rana tana yi" kawai ta girgiza kai jin Al'amin ya amsa, idan ma haka ne ai kamata yayi, yayi shiru kawai.
Rahila ta sake cewa "To sai ayi ta kula da ita, ka san masu ciki sai ana lallaɓa su, ban da hantara da abun da zai ɓata mata rai, kuma ba zama zaka yi ba, ciki tun yana ƙarami ake fara sayayyar kayan jariri".