Sashe 33
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***
Yana kwance a kan gadonsa yana kaɗa ƙafa, hannunsa ɗaya yana riƙe da waya, ɗaya kuma kan shisha, yana ta fesar da hayaƙi.
"Hello" sautin muryar mace ya fito daga cikin wayar.
Ya ce "Hello, how far?"
Ta amsa da "Ya aka yi?"
"Mun yi magana da tsoho, ashe kin gano in da yarinyar nan take?"
"Eh, na gano, sai dai sun ce ba za su karɓi kuɗi ba, hakkinsu suke nema, dan haka sai ka san yadda zaka yi"
Yayi murmushi ya ce "Ki san yadda za ki yi dai, ai kin san dolenki ki ɓoye laifin nan ma, kamar yadda ki ka saba".
Cikin takaici ta ce "Ka ce dole?"
"Ƙwarai dole, idan asirinmu ya tonu ai kema naki ya tonu, yanzu wane matakin ki ka ɗauka?".
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Yadda na lura, takamaimai, ba su san waye kai ba, daga ita bar babarta, dan haka zan je gidan ita Antyn taka, a bamu adress ɗin maigadin da suka kaita Asibiti lokacin da abun ya faru, duk da Yallaɓai ya gaya mini, an sallame shi daga aiki, amma dole za mu yi framing ɗin sa da laifin, in case wani zai tayar da maganar, sai mu ce mai laifin ya shiga hannu, abun da nake ƙoƙarin yi kenan"
Ya kwashe da wata irin dariya ya ce "DaÉ—i na da ke akwai brain, anyway ina ne gidan su yarinyar, she needs to learn a lesson, da ita da babarta da É—an jaridar da ya saka zancen".
Da sauri ta ce "Kar ka kuskura, ba zaka ɓata mini aiki ba, na gaya maka ba su san kai waye ba, idan kuma ka yi wani yinƙuri, da ya samar da wata ɓaraka babu ruwana a ciki na gaya maka"
Abdul ya ce "Na ji, ina son ganin yarinyar ne kawai"
"Abdul, ina da abubuwan yi da yawa a gabana"
"Naja'atu, kar ki katse mini waya, ki bani adress É—in yarinyar".
Kashe wayar ta yi, tare da jan tsaki, ta cigaba da rubuce-rubucenta.
Nabila sai wajen sha É—aya saura na dare, sannan ta É—an dawo dai-dai, sai a lokacin ta samu ta yi wanka, a cikin É—akinta ta tsaya tana kallon cikinta, da ciwonta, da haryanzu yake yi mata zafi.
A haka ta lallaɓa, tayi shafe-shafen skin routine ɗin ta, ta fita kitchen ta haɗo tea, ta dafa indomie, ta koma ɗakinta, ta saka wayar Viper a caji.
Ta É—auki wayarta ta tarar da tarin missed calls É—in Nasir, ta kira shi ta saka wayar a hansfree, tare da kashingiÉ—a.
Ya É—aga tare da yin sallama, ta amsa masa a hankali.
"Arfa ko ki neme ni, ki ji ya na sauka ko?"
A shagwaɓe ta ce "Am sorry, i got a little accident ne, a asibiti na wuni"
A É—an rikice ya ce "Subhanallah, garin yaya meyafaru?"
"Don't mind, akwai labari ne"
"Wane irin labari? Amma dai kina lafiya ko?"
Tayi murmushi ta ce "Gashi muna magana da kai, lafiya ƙalau nake, ka ce Viper daga prison aka sake shi ko? Laifin me yayi aka kama shi?"
Nasir ya ce "Ohhh my God, meyasa ki ka damu da lamarin nan ne har haka Arfa?"
"Ni ka amsa mini Please"
Ya ce "Yeah, amma ya shiga prsion, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, shigarsa na ƙarshe ne, ya ɗan daɗe, kuma da alama laifin da ya yi babba ne, sai dai ba wannan ne a gabana ba, kama shi nake son yi.
Akwai jami'anmu suna yawo a farin kaya, suna neman bayanai a kansa"
"Ka daina wahalar da kanka, na samo maka abubuwan da za su sauƙaƙa maka komai"
Ƙasa-ƙasa yayi da murya ya ce "What do you mean? Ba na son wasa fa".
ÆŠan shiru ta yi, ta tabattar idan ta gaya masa gaskiya a yanzu, ba gwaninta za ta yi masa ba, dan muddin ta gaya masa ta san in da yake, zai ce ta je wurin Æ´an daba, zaneta zai yi, kuma sai ya gaya wa Abba ta shiga uku.
Dan haka ta ce "Da gaske nake, na je wurin wata client ɗin mu, a unguwar da yake, na samo labari, yana da yaransa da suke ƙananan dilallan tabar wiwi, amma ba su san in da yake ba, wai akwai wani guda ɗaya a tal'udu, yana sayar da katin waya bayan magariba, amma ƙwayoyi yake sayarwa, ya san in da yake".
Ya ce "Look arfa, ba na son wasa, daga zuwa unguwar wurin client, har ki ka samu wannan rahotannin?"
"Haba DSP, kar ka manta ni ma fa ma'aikaciya ce, wallahi ba ƙarya nake yi ba, daga majiya mai ƙarfi na ji labarin, na je wurin kuma na ga mutumin yana zaman sayar da katin wayar, idan baka yarda ba, idan ka dawo da kanka ka bincika"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "No, ba sai na dawo ba, zan aika a bincika mini, ina fatan baki gaya wa kowa ba?"
"No, babu wanda na gayawa"
Nasir ya ce "Good, amma kar ki kuskura ki yi wani abu, da zaki saka kanki a cikin hatsari kin ji ko?"
Nabila ta ce "To, idan ka dawo zan baka wani abu mai muhimmancin da zai taimaka maka, amma sai idan zaka yi mini alƙawarin ba zaka dake ni ba, ko ka yi mini faɗa" tayi maganar tana kallon wayar Viper.
"Menene abun?"
"Sai ka dawo tukuna zan gaya maka, take care"
"Shikenan, Allah ya kaimu na dawo É—in, ki kwanta ki huta"
"Ok bye-bye" ta kashe wayar ta ajiye, ta É—auki ta Viper, da ta yi caji, ta kunna ta.
Ta kai wayar hancinta ta sinsuna, ga warin sigari tana yi, ga ƙamshin turare.
Ta fara shige-shige a wayar.
Cikin call log É—in sa ta duba, ga lambobi nan, sai dai duk kiransa ake yi ba ya kira, sai jerin private number da ake kiransa da ita.
Ta duba cikin messages É—in sa, babu komai a ciki, sai dai a cikin drafts É—in sa, yayi saving É—in wasu kwanakin wata.
Tayi shiru tana tunanin yadda ta É—aukko wayar ta sa, lokacin da take tattare kayan jakarta, da ta buÉ—e idonta ta gansu a tarwatse, ta ga wayar a gefe, ta haÉ—a da ita tana sane.
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani laifi ka yi aka kama ka, sannan aka sake ka, ba bisa ƙa'ida ba? Shi yafi cancanta ma in mayar da hankali in binciko, yadda ana kama ka, zan yi raising case ɗin nima, a hukunta waɗanda suka sake ka" tayi maganar tana sake mayar da wayar ta sa caji.
"Ko ban ce na san in da ka ke ba, wayarka zata bawa jami'an tsaron damar nuna in da ka ke".
Ta mayar da kwanukan kitchen, ta dawo ɗakin ta rufe ƙofarta ta kashe fitila za ta kwanta, sai dai tana kashe fitilar, sai ta ga kamar Viper ne a tsaye a gabanta, saura ƙiris ta kurma ihu, ta kunna fitilar tana zazzare ido, tana cigaba da ƙarewa ɗakin kallo, zuciyarta na saƙa mata ko ya biyo ta.
Da ƙyar ta nufi gadonta ta kwanta, gabanta na faɗuwa, ba tare da ta kashe fitilar ba.
Zumbur ta kuma tashi zaune, ta É—auki wayar ta sa, ta sakata a cikin wardrobe É—in ta, ta rufe ta ta dawo ta kwanta tana rarraba ido.
Sai dai fa fafur ta kasa bacci, tsoro ya baibayeta, mussaman idan ta tuna ya ce idan suka sake haɗuwa sai ya kashe ta, sai yanzu ma ta fara tunanin da yaya zata miƙa wayar nan ga DSP Nasir, dan dolen dole sai ya tuhume ta, to idan ya tuhume ta wace amsar za ta bashi? Yaya aka yi wayar ɗan daba ta zo wurinta?.
Sai kuma ta koma tunanin, yaya iyayensa suke ji, sun haifi É—a ya zame wa mutane masifa a gari?.
Tsananin zurfin da tayi a cikin tunani, ya sanya, wani ɓarawon bacci, ya yi awon gaba da ita, sai dai baccin bai je ko ina ba, ta din ga jin numfashi a fuskarta.
A hankali ta buɗe idanunta, jin saukar numfashi a fuskarta, sai dai me, tayi tozali da fuskar Viper, ya kafeta da manyan idanunsa da suka yi jawur, dogon karan hancinsa yana taɓa nata, ko ƙiftawa ba ya yi.
A firgice ta yi ihu, ta faÉ—o daga kan gadon, jikinta na wata irin kyarma, tana jejjera numfashi, sai dai ta buge wurin ciwonta, dan har ya fara zubar da jini.
Sai da ta ɗago ta sake kallon gadon, sannan ta ga ashe filo ne yake taɓa mata hanci, sai ta ga kamar Viper.
Ta rintse idanunta tana addu'a, tare da dafe gefen cikinta da yake ta yi mata zafi.
Æangaren sumayya ma hakan take, dan kasa bacci tayi, dan ita kwanciyar ma gagararta ta yi, tayi dana sanin sha'awar fara aikin jarida, wace irin masifa ce haka tana zaman zamanta, ana neman mayar da ita Æ´ar ta'adda, saboda an fi Æ™arfin ta.
Alwala ta yi, ta tayar da salla, ta din ga addu'a, tana fatan Ubangiji Allah ya tsare su daga sharrin honorable Indabo, mussaman Nabila da ba ta san wainar da ake toyawa ba, gashi a yau kawai an yi wasa da rayuwarta, ba tare da ta san hakan ba, nan gaba ba ta san me za su yi mata ba, kuma ta san muddin ta gaya wa Nabila, akwai ƙura dan za ta iya aikata abun da zai sanadin su rasa rayuwarsu gaba ɗaya.
Sai dai tana ta tunanin wace hanya Nabila ta bi ta ga Viper, tun da ta ce sun haɗu to lallai sun haɗu ɗin, hatsabibancin Nabila da taurin kanta, har tsoro yake ba ta. Tun da ta ƙududi aniyar yin sunan nan, idan ba wuƙa ta gani a maƙogwaronta ba, babu lallai ta haƙura.
Honorable Ma'aruf ne a tsaye yana ta zazzagawa Abdul masifa kamar zai ari baki, shi kuma sai cika yake yana batsewa yana harare-harare.