← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 95

Sashe 47

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da Baba ya sanar da wanda za su karɓi kuɗin Jauhar ɗin tare, sun yi mamaki, suka din ga tambayar sa, meyafaru da waccan saka ranar, ya ce musu matsala aka samu.

Dubu É—ari uku da hamsin, aka kai kuÉ—in komai da komai, har da lefe da sadaki da kuÉ—in aure, wai bayan sati biyu za a É—aura aure.

Mama ta fito tsakar gida ta din ga rangaɗa guɗa, suna Allah ya sa za su gani, gaba ɗaya sai jauhar ta zama confused, wane irin abu ne haka? Alhaji mu'azzam ne ya dawo? Ko kuma yaya aka yi, aka kuma karɓar wani kuɗin. ta ji ana zancen wani Al'amin shi kuma daga ina? Ta tambayi kanta.
Sai dai tsananin kunya, da kawaicin jauhar, bai sanya ta yi magana ko ta tambaya ba.

Su surayya suka din ga yi mata dariya, wai ta ga samu ta ga rashi, from grace to grass.

Duk wani shirin auren, Mama ce take yi, ita ke karɓar kuɗin a hannun Baba wani abun ta saya mata mai kyau, wani akasin haka, masu kyan ma tana saya ne, saboda kar a yi mata gori, ta riƙe yarinya shekara goma sha shida za a shiga sha bakwai, amma ba ta yi mata abun kirki ba.

Aminu kuwa tun kan a kai kuɗin, yayi ɓatan dabo, dan rigimarsa ba ta ciwo shi ya zo gidan ba, dan haka tilas Abbu ya fara bin dabar da yake zama, da duk in da ya san zai ganshi, amma babu shi babu labarin sa, haka ya din ga bayar da cigiyarsa, kamar wani kuɗi, kowa ya tambaya sai ya ce masa bai ganshi ba.

Rahila ta ce masa ya cigaba da shirin sa, duk in da ya tafi ma zai dawo.

A gidan su jauhar kuwa, hankalinta ne ya tashi, da ta ji Anty na yi mata iƙirarin wai nan da sati biyu za a ɗaura mata aure, da angonta Al'amin.

Saifu ya kasa jurewa, ya samu Baba ya tambaye shi, wai meke faruwa da auren jauhar ne?.

Baba ya ce "Eh, nan da sati biyu za ayi"

"Amma na ga kamar sau biyu aka kawo kuÉ—in, wancan an ce Alhaji mu'azzam, yanzu kuma an ce Al'amin wanne ne gaskiyar lamarin ne?"

Baba ya ce "Maman ka da Antynku, ne suka yanke shawarar a aura mata wani, wancan za a iya samun matsala, ta ɓangaren zakiyya ma aka kawo wannan ɗin" cike da takaici yake kallon Baba ya ce "wace irin matsala kuma Baba? Meyasa wanda aka kawo ɗin ba za a haɗa shi da wata ba, sai jauhar? A ina yake, kuma menene sana'rsa? Yazo ya ganta ta ganshi, yayi mata?"

Baba ya sunkuyar da kai tare da girgizawa ya ce "No, amma na san ba za su zaɓi abun da zai cutar da ita ba, kuma jauhar yarinya ce mai biyayya"

Takaici ya ishi Saifu, ya tsani yadda matan gidan suke shirya wa Baba abun da suke yayi, kuma yayi babu musu mussaman a kan jauhar.

Kawai ya tashi ya fita tsakar gida, ya tarar da ita, tana ta uban wanke-wanke, gefe ta jiƙa kayan wankin uniform ɗin ƙanan yaran gidan.

Ya ja kujera ya zauna a kusa da ita ya ce "Waliyiyya, wai saura sati biyu aurenki?"

Tayi yaƙe ta ce "Haka na ji, amma dai Baba bai gaya mini ba".

"Wanda zaki aura ɗin kin taɓa ganinsa ne? Ki na son sa?".

Ta sunkuyar da kai tana murmushi ta ce "Ko ban ganshi ba, tun da an ce su mama ne suka zaɓa mini shi, kuma Baba ya amince na san ba zai cutar da ni ba"

"Baki taɓa ganinsa ba kenan?" Sai ta kasa amsa masa, ta cigaba da durza tukunyar hannunta cikin ƙarfin hali.

Can kuma ta ce "Dan Allah yaya, ka roƙi baba, ya ce masa dan Allah ina son ƙarasa makarantata, ko WAEC na yi"

Saifu ya girgiza kai ya ce "Ki kwantar da hankalinki, na san juriya kawai ki ke yi, amma in sha Allah, ba zaki ji kunya ba jauhar".

Mama ce ta fito ta ce "Kai saifu, uban me ka ke gaya mata, hure mata kunne zaka yi?"

Ya tashi tsaye ya ce "Ko na hure mata kunne, ba zai huru ba, kawai ina tausayin sauran ƴan matan ne, saboda komai nisan jifa ƙasa zai dawo"

Ta ce "Saifu ni ka ke gaya wa haka? Me ka ke nufi?"

"Mama kin san fa me nake nufi sarai, Allah ya haramta zalunci a kan kansa, babu wanda zai yi ya tsira wallahi" ya ƙarasa maganar yana ficewa.

Cike da takaici da son hucewa, mama ta rarumi takalmi, ta jefi jauhar da shi a fuska, aikuwa ya tsokane mata ido.

Ta zauna ta din ga mutsutsuka idon, sai da idon yayi taruwar jini.

Ƴan unguwar su jauhar sai ganin invitation suka yi na bikin jauhar, suka din ga zuwa gulma da jin ba'asi, wane irin aure ne haka faka-faka ko lefe ba a nuna musu ba, da yake ba su san ma zancen kawo kuɗin auren farko ba.

Mama da zakiyya, suka din ga cewa saboda ayi a rufa mata asiri, ake son ayi gaggawa a aurar da ita, sadakarta aka bayar babu ko kayan lefe.

Saboda cin fuska a gabanta, suke faɗar hakan. A gabansu sai ta jure, tayi kamar ba ta ji ba, idan ta ɓuya kuma sai tayi ta kuka.

Al'amin kuwa, honorable Indabo ne ya saka aka kai shi asibiti ta ƙarfin tsiya, saboda ciwon ƙafarsa an sake fama masa lokacin da ya tayar da rigima a wurin campaign, a haka yake lanjarata, ya tafi nasa wuri, saboda soyake Aminun ya warware sosai, kafin lokacin zaɓe kuma, yadda zai yi masa aikinsa yadda yakamata.

Yana shiga arearsu, aka sanar da shi cewa, babansa yana ta yawon nemansa, mamaki ya kama shi, dan idan zai kwana nawa bai ganshi ba, babu ruwansa da in da yake, dan haka cikin gaggawa ya nufi gidan, domin jin dalilin neman nasa.

Sai dai da ya je ya tarar da Abbun yana shirin fita.

"Kai baka iya sallama bane Al'amin, sai dai mutum ya ga ka bayyana kamar wani shaiÉ—ani?"

"To meye marbarsa da shaiɗanin?" Tayi maganar ƙasa-ƙasa.

Sarai ya ji ta, amma ya yi shiru, ya samu wuri ya zauna ya miƙe ƙafarsa ya ce "An ce kana nema na"

"Ba an ce bane, nemanka nake yi, ka dawo daga gantalin kenan? Kodaye ba yau ka fara ba, ka buÉ—e kunnenka da kyau ka saurare ni"

Yayi shiru bai ce komai ba.

"Daga nan ba kasuwa zani ba, Abba ne zai je ya buɗe shago, gidanka na chiranci, na gado zan je, za ayi masa wasu ƴan gyare-gyare, ba ni da kuɗi sosai a hannuna, za a yi masa abun da ya sauwwaƙa, kai ka ƙarasa gyarawa daga baya".

Ya yi shiru yana wasa da zobensa, kamar yadda ya zame masa É—abi'a, idan ba ya son yin magana.

Abbu ya cigaba da cewa "KuÉ—in aure na kai maka, next week za a É—aura maka aure"

Lanƙwashe ƙafarsa ɗaya yayi, ya koma wasa da yastun ƙafarsa, yana kallon wani wurin daban.

Rahila ta ce "Taɓɗijan, lallai gagare".

Abbu ya ce "Al'amin da kai nake fa"

Ya É—ago idonsa ya kalli Abbu ya ce "Wai ni ko wa?"

"A'a da ubanka nake ba kai ba, ni da waye a wurin nan?"

Al'amin ya ce "Ni fa yau ban sha komai ba, garau nake balle ace a buge nake ban ji dai-dai ba, wannan kawai zance ne, ni da ake cewa gagarrare haihuwar asara, wa zai bani wani aure? Ni bana buƙata, idan kuma ba haka ba, duk abun da ya biyo baya ba ruwana idan na kashe yarinya, ko na yi mata illa, kar a zo ana yi mini ƙanan maganganu, ba na so bana buƙata".

Ya yinƙura zai fice, Abbu ya riƙe shi ya ce "Umarni nake baka, ba shawararka ko ra'ayinka nake nema ba, dole ne wannan, aurenka wani satin, na kai kuɗin aure da komai, dole ka nutsu ka shiga hankalinka, idan ka illata musu ƴa ko kasheta kuma, zan sallamawa duniya kai, wannan shi ne hukuncin da na yanke"

A fusace ya ce "Meyasa zaka yanke wa rayuwata hukunci, ba tare da amincewata ba bayan ka daɗe da sallamawa duniya rayuwar tawa? Ka yi hakan ne saboda farincikin matarka ko? Ta daina ganina na gusa na bar mata gidan nan ita da iyalinta. Da zan iya wallahi garin zan bar muku na ɓacewa ganinku ku samu cikakken kwanciyar hankali kamar yadda ku ke buƙata, amma ba zan iya ba.
Ka sani ina ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, da gaske zan iya kashe ƴar mutane, ko na illata ta, sai dai ba na fatan na fi haka lalacewa, idan ka yi mini baki, zan ƙara lalacewa ne zan bi umarninka, amma duk abun da na yi mata da ni da kai zamu ɗauki nauyin zunubin. Saboda ni babu mata a tsarin rayuwata, miyagun halittu da babu Allah a ransu, bana fatan raɓar su, saboda yadda tasirin kaidinsu ya kassara rayuwata, kassarawar da ba za ta gyaru ba, mace ɗaya da nake wa kallon rayuwata, uwata kenan na rasata a yanzu babu wata mace mai sauran kima da mutunci a idona, nayi alƙawarin nesanta kaina da mata, nesantawa mai nisa ta har abada, amma ka karya mini alwashi, ta hanyar janyo mace rayuwata, ina sake nanata maka, duk abun da ya biyo baya, tare zamu ɗauki nauyin zunubin".

Ya saka hannu, ya cire hannun Abbu da ya riƙe masa riga, ya saka kai ya fice.

Har ya bar gidan, babu wanda ya sake magana, daga ita har Abbu.

Gaba ɗaya aka hana jauhar fita daga gida, ana ta shirin biki, ita kuma tana rama kamar ana tsotseta, duk ta fiƙe sai farar fata da idanuwa.

Maƙwabciyar su ta din ga cewa "Gaskiya mama ban so a aurar da jauhar yanzu ba, na so a bari maƙerin budurci ya gama ƙere mana ita, wannan kyawun da gidan wani hamshaƙin ya dace"

Anty ta ce "Wannan ma hamshaƙin ne".

A gida mama ta saka su surayya sa walida, suka dinga kwaɓe-kwaɓe suna murzawa jauhar da sunan gyaran jiki.
Chapter 47 · 0% Book details