Sashe 32
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nabila ta kaɗa kai ta ce "Kusan watana guda zuwa na biyu ma, kawai ina fafutukar yaya zan ganshi, na san dama zaki ƙaryata ni, ban gaya miki ba ma balle ki hana ni ko ki yi mini masifa. Amma cikin ikon Allah, viper ya bar mini shaidar da zai tabattar da ya ganni"
Cikin rashin fahimta, sumayya ta ce "Kamar yaya?"
Nabila ta É—aga rigarta, sai ga plasta a gefen cikinta, ta saka hannu ta cire plastan, sai ga rauni a wurin.
Sumayya ta waro ido, tare da rufe baki, ta ce "Na shiga uku, Nabila kin haukace ne? Wai dama da gaske ki ke?"
Ta saki rigar ta ce "Ai kafin yayi mini haka, rannan karnuka sun kusa yin watanda ta. Sunayya gayen nan ya wuce duk yadda nake tunani, ashe faɗar sunansa ne a baki kawai mai sauƙi, wallahi idanunsa sun kusa sakani fitsari a wando, sumayya yaya zan kwatanta miki yadda yake ne ki gane abun da na gani? Kwarjininsa ya wuce duk yadda zan kwatanta miki, wallahi da ya shaƙe ni, na ɗauka mutuwa na yi"
"Har shaƙe ki yayi, kin ga Nabila ki rufa mana asiri, amma yaya aka yi ki ka samu in da yake?"
"Na gaya miki kusan watanni biyu kenan ina nemansa, na san idan na gaya miki, hana ni zaki yi, duk ba wannan ne ya dame ni ba, yayi alwashin idan ya sake ganin fuskata, sai ya kashe ni, kuma mummunar kasada na kuma tafkawa Sumayya".
"Ta me kuma?!
"Wayarsa na sato, kan na taho!".
Alhamdilillah, duka duka a nan mu ka kawo ƙarshen free pages, mu kasance a cikin paid pages, domin jin ainihin gundarin labarin *ƘARFE A WUTA*.
₦500 ne kacal ta wannan account ɗin, masu so ta private special group 1k zasu saka a wannan account ɗin.
0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Ayshercool.
08081012143
🔞
*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*
*Ina masu buƙatar sayen nagartattun kayan magungunan mata, wanda babu cuta ko algus a ciki, ku yi joining link ɗin nan, domin samun nagartattun magungunan mata*
https://chat.whatsapp.com/BLqFsnlyNf0B483RhoWq8v
Tsoro Nabila ta fara ba wa Sumayya, "Are you serious? Nabila da ya kashe ki fa, ko kuma idan ya biyo ki fa? Meyasa ba kya tausayawa rayuwarki ne?"
"Wallahi nima na yi tunanin hakan, amma ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, ai bai san in da nake ba, yadda zan ba wa DSP wayar nake tunani, ba tare da ya yi mini faɗa a kan dalilin da ya sa na yi ba, ko tuhumata"
Ta ciro ƙaramar waya mai madannai, ta miƙawa sumayya, sumayya ta karɓa tana salallami, da sarawa sheɗancin Nabila.
Nabila ta ce "Wayar babu caji, sai na je gida zan sakata a caji" tayi maganar tana karɓar wayar, ta sakata a aljihun ƙaramin wandonta na ciki.
Ta sauka daga kan gadon, ta ce "Bari na shiga banÉ—aki na fito, na baki labari" ta sauka ta shiga banÉ—akin da yake cikin É—akin.
Sumayya tayi ƙuri da ido tana kallon ƙofar da Nabila ta shiga, tana tunanin yadda abubuwa masu karo da juna suka sakata a tsakiya.
Wayarta ce ta fara ringing a cikin jakarta, ta ɗaukko taga baƙuwar lamba, ta ɗaga tayi sallama.
Muryar namiji ce ya ce "Ya ku ka yi da ita?"
Sumayya ta ce "Ita wa?"
"Wurin wa ki ka je?" Aka tambayeta.
Ta basar ta ce "Wa ke magana?"
"Ya zama dole fa ki yi aikin da aka saka ki, ko kina so ko ba kya so, a in da taken nan idan aka so za a iya kasheta, ko a saceta ayi abun da ake so ta yi, yin abun da aka saka ki ne kawai zai tseratar da rayuwar ta. Ta haÉ—u da shi ko kuwa?"
ta sunkuyar da kai ta ce "Wai dan Allah a tunaninka, tayaya mutumin da ƴan sanda ba su kama ba, ita ta haɗu da shi? Ƙarya kawai take yi dan ta raina mini hankali, Nabila tana da yawan wasa wasu lokutan, amma ƙarya take yi"
Nabila ce ta fito daga banÉ—aki, ta ce "Da wani garan ake waya? Ko kin yi sabon kamu ne?"
Sumayya ta katse wayar ta ce "Ba wani sabon kamu"
"Sumy, ciwon nan na cikina ne yake yi mini zafi fa"
Sumayya ta ce "Ai Allah ya ƙara, ni dama shegen duka ya yi miki, ya kakarya ki "
"Ta Allah ba taki ba muguwa, wallahi sumayya da dukana yayi, zai iya kashe ni, kin ga ƙirarsa kuwa, kin ga tsawonsa?. Kin ga a yadda ya din ga kallona, na kasa gane wane irin kallo yake yi mini"
Ta kashingiÉ—e kanta tana gwadawa Sumayya irin kallon da yake yi mata.
"Wallahi sumayya ban taɓa ganin ido mai ban tsoron nasa ba, kin ji muryarsa, daga cikin ƙirjinsa yake fitar da ita, abun tsoro, ya ci sunansa viper".
Wayar sumayya ta fara vibrating, ta tashi tsaye ta ce "Ina zuwa"
Ta fita waje ta É—aga wayar ta ce "Ya aka yi kuma?"
"Idan har ba ta haÉ—u da shi ba, meye dalilinta na gaya miki ta haÉ—u da shi?"
Kamar sumayya za ta yi kuka ta ce "Yayanta É—an sanda ne, na gaya muku, a bakinsa da kafafen watsa labarai kawai take jin sunansa" katse wayar aka yi, ba tare da an sake ce mata komai ba.
Ta koma É—akin da Nabila take, sai dai abun mamaki taga Nabilan kamar matacciya.
Da sauri ta ƙarasa ta taɓa ta, ta ga bacci kawai take yi, daga fitarta zuwa yanzu bai ci ace har ta yi wannan baccin ba.
Message aka turo mata "Idan ki ka bamu bayanin da yake saɓanin gaskiya, abun zai wuce haka, ya zama dole ki bi duk wani umarni da zamu baki, muna bibiyarku daga ke har ita"
Sumayya ta ajiye wayar, ta dafe kanta tana salati.
Tsaye yake ƙyam a kan ƙololuwar dutsen, yana kallon yadda rana ta doshi faɗuwa, gari ya fara duhu sosai, a hankali ya ɗago hannunsa, ya kalli inhaler da take hannunsa, seretide inhaler ya din ga jujjuyata, yana sauke ajiyar zuciya.
"Boss" ya ji muryar Walid a bayansa.
Ya zagaya gabansa ya ce "Ka saukko haka dan Allah, magana nake son mu yi"
"Bana buƙata kowace iri ce"
"Na san na yi maka laifi, amma ka yi haƙuri, zan nemota duk in da take, kuma zan dawo maka da wayarka ina mai baka haƙuri"
Ko motsawa bai yi ba, balle walid ya saka ran zai yi magana, daga bisani ya goya hannayensa a bayansa, ya cigaba da kallon rana.
"Amma me ka ke tunani game da yarinyar nan? Anya babu wani abu a ƙasa da yakamata mu sani?"
A hankali ya juyo, ya dafa kafaɗar Walid, ya matsa da ƙarfi ya ce "Hakan bai dame ni ba, koma wacece, Ma'aruf , madaki, da kuma wannan yarinyar da ka kawo, sai na tabattar da na kashe su gaba ɗaya, ko ta halin ƙaƙa".
"A'a master, mace ce, wataƙila sakata aka yi, dan Allah ka yi haƙuri, zan yi maka bincike a kanta "
"Idan ka kuma gaya mini wannan sunan, zan hankaÉ—aka daga kan dutsen nan"
Walid ya yi murmushi ya ce "Baka girmama sunan ne viper, idan har ka damu har haka, yakamata ka bawa kanka da lafiyarka kulawa, ta haka ne zaka yi abun da ka ke so, yanzu ka taimaka ka sakar mini kafaÉ—ata, wallahi kamar na karye"
Ƙurawa walid ido yayi, Walid ya sunkuyar da kansa, ya san ya tunzuro zuciyar Viper, sakar masa kafaɗarsa ya wuce shi, ya fara sauka daga kan dutsen.
Har bayan azahar Nabila ba ta farka ba, su kansu ma'aikatan asibitin, sun yi mamakin irin baccin da Nabila take yi.
Hankalin sumayya kuwa yayi mummunan tashi, ganin Nabila ba ta farka ba.
Bayan la'asar sai ga Abba, tare da Salim, wanda ƙani ne ga Nasir.
A É—akin da Nabila take suka tarar da Sumayya.
Sumayya ta gaishe su, Abba ya amsa ya ce "Sumayya ke ce a wurinta?"
Ta jinjina kai ta ce "Eh Abba"
"Ai ni ce mini tayi, ba wani abun damuwa bane, ana gama yi mata abun da za ayi mata, za ta koma gida, sai da na koma na tarar ba ta dawo ba"
Sumayya ta ce "Eh, ai ta samu bacci ma".
Idonsa ya sauka a kan gefen rigarta, da take a huje ga jini, cikin mamaki ya ce "Ya nake ganin jini a jikinta?"
Da sauri Sumayya ta ce "amm, dama wai faÉ—uwa suka a adaidaita sahu, shi ne ta ji rauni"
"Amma ni bata gaya mini haka ba ai" yayi maganar cikin matsananciyar damuwa.
Wata irin miƙa Nabila ta yi, tare da yin salati, duk suka yi kanta suna yi mata sannu.
Suka din ga jera mata sannu, suna yi mata ya jiki.
Sumayya ta kirawo likkta, ya zo ya ƙara duba Nabila, yayi rubuce-rubuce a file ɗin ta, ya sallame ta.
Abba ya din ga yi mata faÉ—an meyasa ba ta gaya masa ta faÉ—i a adaidaita sahu ba, ta nunawa likitoci ciwon da ta ji.
Sumayya ta kalleta, suka haÉ—a ido, sai ta fahimta, dan haka ta ce "Ai ba wani ciwo bane Abba, mu tafi gida na gaji".
"Kin tabattar babu wani abu da yake yi miki ciwo?"
Ta jinjina kai alamar eh, suka fito zuwa motar Abba, suka tafi tare da sumayya, su ajiyeta a gida.
Sumayya ta kalli Nabila ta ce "Wai ya aka yi É—azu daga fita ta, ki ka fara bacci, kusan awa huÉ—u ki na bacci?"
Nabila ta É—an yi shiru tana tunani, ta ce "Wani likita ne ya shigo yayi mini allura"
"Ba Nurse ba, likita da kansa?"
Nabila ta jinjina kai alamar eh, Sumayya ta yi shiru ba ta ce komai ba, a zuciyarta, take jinjina tsagwaron rashin imanin honorable Indabo, kenan idan ba ta yi abun da suke so ba, za su kashe Nabila kenan.
Gabanta ya faÉ—i, ta kalli Nabila da ta kashingiÉ—a, tana ta lumshe ido, alamar baccin bai isheta ba.
Tunani take da wa zata tattauna wannan maganar ne? ko wurin hukuma ta kai, ba ta da shaida ta zahiri, kuma ta san babu wani mataki da za a iya É—auka a kai.