← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 95

Sashe 7

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu neman izni, ta afka ciki ta ce "Sannu bawan Allah, ka yi haƙuri Allah ya baka lafiya, ka daure"

Duk sauka waiwayo su na kallonta, har da ma'aikatan, mutumin ya ce "Na gode sosai"

Ta ƙara matsawa ta ce "Amma hatsari ka yi ne? Kodayeke wannan ai yankan makami ne ba hatsari ba"

Ya ce "A'a wani É—an daba ne, ya sare ni jiya cikin dare, dama hukuma ta daÉ—e ta na neman sa"

Sumayya ta gyara tsayuwarta ta ce "Subhanallah, bawan Allah a wace unguwa ce haka? Ko rigima ku ka yi da shi ne?" Ƙanin malam lawan da yake tsaye a wurin, a fusace ya kalli sumayya ya ce "Dalla malama fita, mutum yana fama da kansa, kin zo ki na yi masa wasu surutan banza"

Ta ce "A'a Allah ya baka haƙuri, ka sani ko akwai wani taimako da zan iya yi masa. Kalli saran da aka yi masa fa, idan ba za ka damu ba, zan naɗi muryarka, mu saka a radio, ko Allah zai saka, hukuma su bi maka haƙƙinka, barin su da ake yi suna cin bulus ya sanya suke cigaba da ɓarna".

Malam lawan ya ce "Ke rufawa kanki asiri, hatsabibanci da ta'addanci yaron, ya wuce tunanin ki"

Sumayya ta zaro wayarta, za ta yi magana, sai ga wasu mutane guda biyu sun shigo da wani kaki a jikinsu, da ba ta san na menene ba, suka mayar da ƙofar ɗakin suka rufe.

Malam lawan ya kalle su, ba su ne Æ´an sandan da aka kirawo suka tsaya masa, likitoci suka zo kansa ba ne.

Sumayya ta yi tsilli-tsilli da ido,  ɗaya ya ƙirga mutanen da suke cikin ɗakin, da likita ɗaya, nurse ɗaya, sai ƙanin malam lawan da sumayya. Dan duk maƙwabtan da suka kawo shi, sun tafi wurin sana'oin su. ya ce "Ku biyar ne a ɗakin nan, idan ka sake mu ka ji labarin sunan wanda ya yi maka wannan raunin, to za ka maye gurbinsa da ya bari na gidan yari, dan haka ka ja bakinka ka yi shiru".

Sumayya ta ce"Ban gane ba Yallaɓai, mutum mai laifi kuma ace kar a faɗi waye? Ba ka ga irin illar da aka yi masa ba ne, ga karaya ga rauni, da ya kashe shi fa?"

Ya ba ta amsa da "Da ya kashe shi, bakinki zai iya sakawa, ki É—auki hukuncin da za ayi masa na kisan" daga nan suka juya suka fice.

Mamaki ya mamaye sumayya, ta ce "Kai kuwa bawan Allah, waye wannan shi kuwa, da har jami'an tsaro masu kaki, za su hana bayyana laifinsa, ana sane aka ƙi kama shi kenan?"

Malam lawan ya ce "Ba zaki ja mini masifa ba, ki fita ki bar wurin nan, na ji da masifa É—aya, bayan É—inkin nan a karye nake wallahi"

Cikin tsananin naci, da son samun rahoto, ta kwantar da murya za ta lallaɓa shi, ta samu labari, amma da likitan da ƙaninsa suka koreta daga ɗakin.

Fitowa ta yi, tana ta mamakin abun da ya faru, yaya za ayi hukuma ta bawa mai laifi kariya, wane irin abu ne haka?.

Ba ƙaramar makara ta yi ba, amma tunanin abun da ya faru, ya fi ɗaure mata kai.

***
Sannu a hankali yake yi wa kansa allura, yana yi yana fatan samun abun da yake so, a hankali ya gama É—urawa jijiyarsa ruwan allurar da yake fari tas a cikin sirinji, bayan ya kammala tsaf ya fara jin kansa yana yi masa nauyi.

Take idanunsa suka yi mitsi-mitsi, ya soma lanƙwasa kansa, yana jin idanunsa kamar za su fito waje, suna yi masa yaji, a haka ya kunna sigari, ya kashingiɗa, ya na bawa sama hayaƙi,yana jin yadda jikinsa ke son bijirewa aikin allurar.

Wayarsa ce ta fara vibrating, ya miƙa hannu, ya ɗaukkota ya duba, yana zaton ko a cikin yaransa ne, sai dai ya ga private number ce.

Har zai ƙi ɗagawa, sai kuma ya ɗaga ya saka a kunnensa, amma bai yi magana ba.

Daga cikin wayar aka ce, "Meyasa ba ka gajiya da neman magana ne? A wannan karon ma sai da ka saka na yi abun da na goge ɓarnar da ka yi, yakamata ka nutsu Aminu"

Ya saki hayaƙi, tare da ɗan kaɗe tokar da sigarin ta tara, sannan ya ce "Waye kai? Sannan waye ya saka?"
Mutumin yayi dariya, ya ce "Mutum mai ba ka kariya, domin cimma nasa muradin, yakamata ka sauƙaƙa mini aiki, ka daina aikata abubuwan da za su din ga barin trace a kan ka".

"Ka yi muguwar kasadar ƙoƙarin cimma burinka da mutum irina, kar ka manta viper ake yi mini laƙabi da shi, macijin da ya fi kowanne hatsari, idan ka bari na sare ka, ka gama yawo" yana gama maganar ya cillar da wayar, ya ɓata fusaka kamar ya fashe da kuka.

Cikin fusata ya ce "Ni again? wani ya kuma amfani da ni? Impossible zan watsa dafina a in da ya dace da in da bai dace ba, sai na tabattar da danganawa ga kunyar ƙarshe, ko da kuwa za ayi mutuwar kasko" ya yinƙura da nufin ya tashi tsaye, amma ya kasa sarrafa gangar jikinsa, hakan ya tilasta masa komawa ya nemi wuri ya kwanta.

Duk da irin faÉ—an da sumayya ta sha a wurin aiki a kan makara, bai dame ta ba, jikinta sai tsuma yake saboda ta zo da rahotanni masu muhimmanci da É—aukar da hankali.

Ofishin head of news ta je, ta shiga da sallama.

Matar ta ɗago ta amsa mata da ƙyar, ta ƙarewa sumayya kallo, ta ce "Yanzu ne lokacin shigowa aiki ko? Gaba ɗaya yaran yanzu ba kwa ɗaukar aiki da muhimmanci, kodayeke karatun ma ba wani na kirki ku ka yi ba, duk da satar amsa ku ke gamawa. Ki shiga hankalinki kafin na kai maganar nan wurin MD"

Sumayya ta risuna ta ce "Afuwan anty, in sha Allah ba zan sake ba, na samu wasu rahotanni ne masu muhimmanci, da ya san na tsaya a hanya, shiyasa na makara na kawo miki a tantance ne ko za a saka su a news"

A yamutse matar ta ce "Na menene" cikin farinciki da jin ƙwarin gwiwar ta yi abun arziki ta fara da gaya mata abun da ya faru a asibiti.

Amma matar sai cewa ta yi"Amma ba ki da hankali ko? Ta yaya zamu saka wannan shirmen a news?"

"Anty ai a rahotanni, ko a janyo hankalin hukuma.... "Dalla yi mini shiru, business mu ke yi a nan mu, ke fa iyayinki da rawar kanki yayi miki yawa sumayya. Meye hujjarmu idan aka tsutsiye mu, cewar hukuma na ɓoye mai laifi?"

Sumayya ta ce "Wallahi a gabana aka yi, mutumin yana nan a emergency"

"Kin ga idan ba ki da abun faÉ—a, fita ina da abun yi"

Sumayya ta yi iya ƙoƙarin ta, ta danne abun da yake taso mata na fushi ta ce "To shikenan, sai kuma akwai abun da na gani, ina kan hanyar tahowa nan, a nan wajen gari, an tsinci gawar yaro an cire masa wasu sassan jikinsa".

"Almara kenan, wa zai yadda da wannan zancen?"

"Ba zance ba ne ba, na yi recoding É—in maganar wasu daga mutanen da suka fara cin karo da abun".

"Sumayya, ba irin wannan labaran mu ke buƙata ba dan Allah, je ki su murtala sun fita neman rahotanni, ki din ga kawo sensitive abubuwa"

Summaya ji tayi wata irin ashar na kai komo a wuyanta, da take ƙoƙarin narkawa matar nan, ta rasa abun da ta yi mata, haka kurum ta tsane ta. Ta yi ta kyararta ba ta son ta ga tayi wani abu na cigaba.

Sumayya ta fice daga office É—in kamar ta yi kuka, ta koma reception ta nemi wuri ta zauna.

Ba uwar da ta tsinana a aikin yau, tun da head of news department ta yi mata wulaƙanci.

Kasancewar a makare ta je, ya sanya lokaci yayi gudu, Lawisa, wato head of news É—in, ta din ga shiga tana fita, ta na kaiwa tana komowa, idan ta kalli in da Sumayya take sai ta haÉ—e rai.

Wannan karon bayan ta fita, a tare suka shigo da managern director, sai karairaya take yi masa, tun da ya shigo ma'aikatan suke ta gaishe shi.

Ban da sumayya da ɓacin rai ya saka ta cika ta batse.

Sai da yayi gyaran murya ya ce "Wannan ba sabuwar staff É—in mu ba ce? Ya na ganki a nan? Wane department aka kai ta ne?"

Lawisa ta yi caraf ta ce "Sir ba ta da ƙwarewar aiki ne haryanzu, ana ɗan nunnuna mata aiki ne, kafin ta gama gogewa".

Ya ce "Ok, babu laifi" sumayya kamar ta kwaÉ—awa lawisa mari, a fusakarta da ta sha uban bleaching, duk tayi taruwar jini.

Ta daure ga gaida MD, sannan suka wuce gaba.

Tsaki Sumayya ta ja, tana duba wayarta.

Sai dai jin sallamar Nabila a reception ya sanya ta É—ago da sauri tare da amsa mata.

"Ya na ganki a nan?"

Nabila ta ce "Ke baki iya karrama baƙo ba ko?" Ta tsaya suka gaisa da admin ɗin da ke reception, sannan ta ƙarasa kusa da Sumayya ta zauna.

"Arfa, ya na ganki yanzu ne? Lokacin tashi daga aiki bai yi ba?"

"Kema ya na ganki a nan kamar mara galihu, ke baki da office É—in da zaki zauna ne? Ki zo chambermu ki ga ofishin da aka bani hajiya, kamar wata sarauniya"

Sumayya ta ce "Eh ofishin da baki damu da aiki ba ko, sai sun dawo da ke gadin chamber tukuna".

Nabila ta yi dariya ta ce "Kin san wani abu, wai nan aikena aka yi, zan je na lallaɓa na zo da wata mata, ko in tattauna da ita, sannan in je shagari firm, zan haɗu da wani lawyer, kuma ni wallahi kaina ciwo yake yi"

Sumayya ta kalleta ta ce "Ba zaki ba kenan?"

"Ai faɗa ma ɓata baki ne, sumayya wurin nan naku mai kyau, tashi ki rakani na zaga" duk da ran sumayya babu daɗi, amma ganin Nabila ya sanya ta jin sanyi a zuciyarta.

Suka shiga zazzagawa, ta kaita news room, sai dai su na buÉ—ewa suka tarar da MD da lawisa a ciki, suna aiki.
Chapter 7 · 0% Book details