← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 95

Sashe 13

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake hayayyaƙowa Nabila yayi, amma cikin dakiya da taurin kai, take mayar masa da martani.

Da ƙyar aka rarrashi police ɗin, dan cewa yayi sai sun tafi da ita station, wataƙila ma ƴar ƙunar baƙin wake ce, ko ta na da alaƙa da masu laifin.

Nabila ta ce "Ni za ka yi wa sharri, ki in ƙunar baƙin waken zan kai, zan tsaya saurarku ne, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba".

Ana ta ƙoƙarin sasanta magana, amma Nabila ta ƙi yin shiru.

Ta ciro wayarta, ta kira Nasir sai huci take yi.

Yana É—agawa ta ce "Yaya, ya ake ciki ne? Akwai wani labari ne?"

Ya ce "No, wallahi arfa kin ganni, na zagaya station uku a yankin, duk ba a kai su ba, amma wata majiya ta tabattar mini da sakinsu aka yi, just recently"

"Sakin su kuma? Saboda me?"

"Ban sani ba, a kan abun da nake ƙoƙarin yin bincike kenan"

"Ka hanzarta ka taho asibitin cikin gari, akwai waÉ—anda aka kwantar, police sun hana shiga sun hana fita, an hana kowa shiga, ko da kuwa kusa da É—akin. Har da Æ´an jarida ma an hana su"

Cikin sauri ya ce "Ok shikenan, gani nan in sha Allah, hankalina bai kai kan in zo asibiti ba ma na duba ko akwai abun da zai taimaka mini, amma gani nan stay safe"

Ta amsa da "Ok"

Ta ajiye Wayar a jakarta, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ƴan sandan suka saka mata ido, dan kar ta yi wani mummunan yinƙuri, dan ba su san manufarta na dagewa a kan son shiga wurin ba.

Babu tsammanni aka fito da matasan, wasu É—auke da raunuka, wanda ba za su iya tafiya ba, an turo su a kan gado, an nufi hanyar barin emergency da su.

Nabila ta nufe su cikin sauri, amma Æ´an sanda suka tare ta.

Ta kalli ɗaya ta ce "Yallaɓai ina za a kai su? Na ga wasu a mugun yanayi, ya za a bar asibiti da su?"

Babu wanda ya kula Nabila, aka saka matasan a cikin ambulance, har da iyayen wasu daga cikin matasan jami'an tsaron suka hana su bin su, suka rufe ambulance É—in, su kuma su ka hau ta su motar ta Æ´an sanda, suka bar harabar asibitin.

Ƴan jaridar da suka yi ƙoƙarin bin su ma, aka dakatar da su, aka hana su ƙarasawa ma in da motar take har suka tafi.

Tsayawa ta yi kamar wata shashasha, tana mamakin yadda abubuwa suke tafiya, kamar a film.

Motar DSP Nasir ce ta shigo cikin harabar asibitin, yayi parking ya fito, yana ƙoƙarin kiran Nabila a waya,ya tambayi tana ina.

Da sauri ta ƙarasa in da yake, tana kallonsa, amma ta kasa magana.

Ya ce "Yaya dai? A wane ɓangaren suke, kin samu ganin na su kuwa?"

Nan ta kwashe duk abun da ya faru, ta gaya masa.

Cikin asibitin ya shiga, tana biye da shi, ya tambayi office É—in incharge na A&E É—in, ya gabatar masa da kansa, tare da yi masa tambayoyi, a kan dalilin da ya sa, aka sallami mutane da raunuka a jikinsu. Amma ya tabbattar masa da cewa, babu wanda yayi musu wani cikakken bayani, kawai Æ´an sanda sun kawo musu yaran jina-jina tun a daren jiya, sun ba su kulawar da ta dace, daga bisani Æ´an sandan suka ce asibiti za su canza musu, aka tafi da su.

Nabila ta yi shiru, sannan ta ce "Akwai wata a ƙasa yaya Nasir, ko waye wannan Aminun, ya na da wanda su ke sponsiring ɗin sa. Shi an kasa kama shi, amma ya na saka yaran mutane ta'addanci, you need to put more effort, and i will hundred percent support you, everyone is equal before the law, dole a nemo shi a hukunta shi"

Ayshercool
08081012143
[7/20, 2:02 PM] null: *ƘARFE A WUTA*

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g.

6

Nasir ya ce "Sannu da ƙoƙari arfanmu, amma ki daina saka kanki a risk kin ji ko? Zan cigaba da ƙoƙarina in sha Allah sai na yi sanadin kawo ƙarshen ta'addanci da harkar daba a garin nan, domin kuwa yana ci mini tuwo a ƙwarya nima, but for now mu je na kai ki wurin aikinki"

Nabila ta ce "DSP, dan Allah idan ka gano wani abu na rashin gaskiya, ko waye yake da hannu a ciki, ka tona masa asiri. Dan ina ga sumy zan yi wa magana, su faɗi abun da ya faru a gidan rediyo, an saki waɗanda aka kama, kuma wanda aka ji wa rauni ma, an hana kowa zuwa wurinsu, daga bisani kuma jami'an tsaro sun kwashe su daga asibiti, babu wanda ya san in da aka kai su, wannan wane irin abu ne?" tayi maganar cikin haƙiƙancewa.

Yayi murmushi ya ce "Kar ki soma, ki na wasa da hukuma arfa, yanzu sai ki kwana a ciki ke, yanzu dai mu je mota" haka ya tasa ta a gaba zuwa mota, suna tafe tana mita.

"Wallahi yaya na fara sarewa da lamarin ƙasar nan, anya kuwa gyaran ake so ayi da gaske, ta yaya za ace an gagara kama mutum ɗaya? Ana yekuwar ana nemansa, amma kuma ana kare laifukan da yake aikatawa, ni na kasa gane kan wannan lamarin.
Ni fa muddin na gano wani abu na rashin gaskiya, sai na yi magana"

"No Arfa, ba huruminki bane ba, ba kuma aikinki ba ne ba, kar ki kuskura ki saka kanki a hatsari, ƴa mace ce ke lamarin ƙasar nan ya wuce tunaninki, ba abu ne mai sauƙi kamar yadda ki ke hangensa ba"

Ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce "Yaya garin nan yana kan gaba a garuruwan da ake ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, duk al'ummar da matasanta suka lalace da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi ba ta da gobe mai kyau, matasanmu su ne tushen al'umma mai kyau"

Nasir ya ce "Na fuskanci abun da ki ke nufi, but is still not your field"

Tayi shiru ta mayar da hankalinta kan titi, tana ta tufka da warwara a zuciyarta.

Ko da ya kai ta wurin aiki, ta sauka suka yi sallama, ta shiga tana shiga office É—in ta, sumayya ta fara kira.

Sumayya ta É—aga ta ce "Kin gama fushin ne?"

"Ke ware ba wannan ba, matsoraciya da ba ki je ba ni na je, na samo labari, ina ga bayyana labarin ka iya janyo hankalin manya a cikin lamarin"

Sumayy ta gyara zama ta ce "Labarin me?" Nabila ta gaya mata komai, yadda yaran da aka kama suka yi ɓatan dabo, da yadda aka fice da na asibiti ba tare da sanin ina aka kai su ba.

Sumayya ta ce "Nabila lallai wannan magana ce babba, bari zan yi magana da MD na ji mai zai ce, gaskiya yakamata a zurfafa bincike a kan lamarin nan".

Cikin zaƙuwa ta ce "Dan Allah sumayya ki ƙoƙarta, ayi a sanar, a ji mai hukuma za ta ce a kan haka, ko kin san shi kansa Aminu Viper ana zargin ko dai guduwa yayi daga gidan yari, ko kuma sakinsa aka yi ba bisa ƙa'ida ba, shiyasa ake tsananta nemansa yanzu"

"Ke ya aka yi ki ka sani?"

"Yaya ne ya gaya mini, akwai lauje cikin naÉ—i a lamuran mutumin, mutum kamar wani sheÉ—ani".

Sumayya ta yi shiru sannan ta ce "Bari, yadda mu ka yi da su zan gaya miki, amma maganar nan ta É—auki hankalina sosai"

"To shikenan, ina saurarenki, yadda ake ciki, ki sanar mini" suka yi sallama.

Haka kurum zuciyar Nabila ta cigaba da azalzalar ta a kan lallai tana son sanin wanene wannan Aminun, akwai yiwuwar ta samu gagarumar nasara idan aka ce da saka hannunta wurin kama shi, shahararta ita zai ba ta damar yin gaba da gaba da Naja'atu Bunkure.

Sai kuma ta tambayi kanta, for the first place, laifin me ya yi aka kai shi prison, har ake tunanin ya fita ba bisa ƙa'ida ba?.

"Akwai ayar tambaya a kan abubuwa da dama" ta yi maganar a fili.
***
Ƙurawa wayar gabansa ido yayi, yadda take ta vibration kamar ta tashi, a wannan karon ma private number ce, lambar da ko ta halin ƙaƙa yake fatan ganin ko waye mai ita ya bayyana a gare shi.

ÆŠan mama da ke kusa da shi ne, ya É—aga wayar ya sanyata a hansfree, ya tura masa gaban sa.

Daga cikin wayar aka ce "Manya gatan wasa, ko ka  tsorata ne ya sanya ka gagara ɗaukar wayata?"

Yayi shiru bai ce komai ba.

"Idan za ka kwana dubu kana ɓarna, zan kwana dubu ina goge ta, ina ɓatar da sahunka. Ka na ta cigaba da aikata ɓarna, saboda kana son lallai sai ka san waye ni ko?"

"Wanene kai?" Yayi maganar a É—an hasale.

Mutumin yayi murmushi ya ce "Mutum, mai zuciya cike da muradai kamar ka. Ƴan kwanakin nan ka fi mayar da hankali a kan sanin wanene ni, fiye da abun da yake damun zuciyarka. Ka bi a hankali kar garin kallon ruwa kwaɗo ya yi maka ƙafa, kar ka saki reshe ka kama ganye, ya kai wannan maciji mai hatsarin gaske"

Al-amin ya numfasa ya ce "Ni ba karen farauta bane ba, da za ka din ga wasa da ni, tamkar ɗan kwiwiyon da ka raina, ka yi a hankali da ni, ƙarfe nake cikin wuta, na fi ƙarfin ɗauka da hannu"

Ya sake murmusawa ya ce "Ka huta mutumina, ka samu abun da zai ɗebe maka kewa, ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, ba za su taɓa rabaka da damuwa ba, matuƙar ba ka yi abun da zuciyarka ke gaya maka ba, haryanzu ka na da sauran ƙuruciyarka, zaka iya amfanar da al'ummarka"

Kafin Aminu yayi magana, mutumin ya katse wayar.

"Amma Yallaɓai, kana ganin wannan abun da muke yi shi ne dai-dai? Akwai abubuwa da yawa da yakamata ace mun mayar da hankali a kai, ba bawa ɗan daba kariya ba"

Ya ajiye jaridar hannunsa ya ce "Kalle ni da kyau, ba na abun da babu manufa a kansa, dan haka kawai ka saka ido"

Waya ce ta fara ringing, ya ɗaga sannan ya miƙo masa.

Ya karɓi wayar tare da yin sallama.

"Wa'alaikum Salam, barka dai ya ƙoƙari?"
Chapter 13 · 0% Book details