← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 95

Sashe 87

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ƙyar aka tarwtsa tarin matasan nan, tana zaune ta ƙurawa fuskarsa ido, ƴan sanda suka ɗauki statement ɗin abun da ya faru.

Jauhar sai addu'a take yi, tana fatan Allah ya sa ya farfaÉ—o.

Ta riƙe hannunsa, tana shafawa a hankali ta ce "Allah ya shirya mini kai, ya baka lafiya master, inuwarka ce kawai nake tsaye a ciki nake saka ran samun farin ciki, dan Allah ka daina zuwa ana cutar mini da kai"

Idonsa a rufe, ya É—aga hannunsa a hankali, ya shafi fuskarta sannan ya buÉ—e idon a hankali ya kalleta sai dai bai yi magana ba.

"Sannu master, an yi maka É—inki a bayanka, akwai abun da yake yi maka ciwo ne?" Ya girgiza kai almar a'a.

Ta shafi sumar kansa ta ce "Allah ya baka lafiya"

Juyi yayi a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, muryarsa ƙasa-ƙasa ya ce "Idan kina kuka ciwon ƙara zafi yake yi" ta goge hawayenta ta ce "To na daina, amma idan aka ji maka ciwo, zuciyata ce take kuka ba na so master".
A hankali yake matsa hannunta, yana jin wata nutsuwa ta mussaman, da sassaucin zafin da zuciyar sa take yi masa.

Zuwa magariba, ya miƙe ya ce sai sun tafi gida, Jami'an tsaro suka ce za su tafi da shi, sakamakon tayar da tarzoma a unguwa.

Walid ya ce "Saboda hauka ake yi, master ku ware gida, ni ku tafi da ni mu muka je muka tayar da tarzomar"

Ana fito da Al'amin, guduma ma ya taso, da sauri, Al'amin daga shi sai dogon wando, suka tari napep suka tafi gida.

A wurin maman halimatu jauhar ta karɓi mukulli, ta buɗe musu gidan suka shiga.

Ta saka yayi wanka, yayi alwala ya rama sallolin da ake bin sa, ta kawo masa abinci ya ci.

"Master" ya kalleta "Dan Allah ka fita daga shirgin madakin nan, ba shi da imani, kar ya hallaka ka dan Allah"

"Sai dai É—aya yayi ajalin É—aya ko ni ko shi, shari'ata da shi, Allah ne kawai zai rabata"

Cikin rauni ta ce "Ina haÉ—aka da girman zatin Allah"

"Shhhh, ki daina haÉ—a ni da Allah, kin san nauyin abun da aya aikata mini?"

"Ban sani ba, amma ina da yaƙinin koma me zaka yi masa, ba zaka huce ba, ka yi haƙuri ka bar wa Allah mana, idan wani abun ya same ka ya zan yi ne? Yanzu kalli halin da ka sakamu a ciki, na san yanzu haka a cikin pain ka ke, ciwon a jikinka yake, amma a zuciyata nake jin raɗaɗin, haba master, haba dan Allah" tayi maganar wasu zafafan hawaye na gangarowa daga cikin idanunta.

Ya miƙa hannunsa ɗaya da ba a side ɗin ciwon yake ba, ya janyota jikinsa, ba ta musa ba ko yi masa gardama, ta kwanta sosai ta cigaba da kukan, tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa sosai, kasancewar babu riga a jikin sa.

"Ba zan ɓoye miki ba, ban taɓa tunanin zan yi wata alaƙa da wata 'ya mace ba, saboda ina yi musu kallon azzalumai, ke ki ka fara canza tunanina".

Al'amin Ibrahim shi ne cikakken sunan Al'amin, mahaifinsa haifaffen garin kano ne, gidansu gidan yawa ne, baban Al'amin shikaÉ—ai ne a wurin mahafiyarsa, sai tarin 'yan uba da galibinsu mata ne.
Yayi karatu daga primary zuwa sakandare har yayi diploma, sai dai aikin yi ya gagara samuwa, akwai abokinsa sammani da suka yi karatu tare, tare suke yawon neman aiki, ya ja shi garin su tofa, aka samo musu gona, suka fara noma.
A can ya haɗu da Zahra'u, ya ce yayi mata, da fari tsokanarta yake yi, saboda kwalliyar da take yi ta 'yan ƙauye ce take bashi dariya, daga baya soyayya ta ƙullu a tsakaninsu.

Abu kamar wasa, har ta kai ga aure, duk da bashi da wata ƙwaƙƙwarar sana'a, sai kame-kame.

Sun sha gwagwarmayar rayuwa tare, sun yi faÉ—i tashi, sun yi fama da yanayin rayuwa, kafin Allah ya buÉ—a masa ya fara samu.
Lokacin da suke cikin wahala babu mai taimakonsa, daga shi sai ita suke wahalar su, ta samu ciki a lokacin ta haifi ɗan ta na fari, aka saka masa Abubakar Assidiƙ, sai lokacin da Allah ya fara buɗa masa, 'yan uwansa suka saka musu ido, da surutun yana zaƙewa da yawa a kanta.

Komai ya samu ita, ya tashi daga tsakiyar cikin garin kano, ya koma gwauron dutse yayi mata gida mai kyau.

'yan uwansa suka fara tsangwamar ta, da cewa ta shanye musu ɗan uwa, Ibrahim ya mayar da ita makaranta ya samo mata admission a FCE, ta ke karantar English islamic. Kasancewar ta mace kyauta, da fara'a da sakin fuska ga mutane, ya sanya take da masoya sosai. Sai dai duk da kyautarta, da son mutane dangin mijinta ba sa ƙaunarta.

A can gwauron dutsen, ta haɗu da wata mata rahila, maƙwabciyarta ce, tana yawan zuwa ta kawo mata complain a kan mijinta ba ya kula da ita da yaranta, hakan ya sanya tausayin rahila ɗarsuwa a zuciyar Zahra'au, kusan kullum cikin yi wa rahila aike take, na abun da zata kula da yaranta, kuɗi, sutura, abinci kayan masarufi, saboda Ibrahim yana sakar mata sosai baya yi mata iyaka da komai.
Tana NCE 2, Sadik ya shekara biyar, ta samu ciki, tayi ta fama ga laulayi ga karatu, rahila take barwa Abubakar ta tafi makaranta, ƙarshen wata, take biyanta da kuɗi mai kauri saboda ita ma ta samu.

Ta haifi ɗanta na biyu, aka saka masa Muhammad Al'amin, saboda haihuwar maza da take yi, dangin miji, suka ƙara yi mata caaa wai tana ta haifar maza, dan ta kwashe komai na gado idan ya mutu.

Ayshercool
08081012143

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

    Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

    Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

    Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

     Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955

Ya saki Sadik a ƙasa bayan ya caka masa almakashin, cikin tsananin tashin hankali, Al'amin ya yi kukan kura ya danƙi ɗan daban, amma wani daga cikin yaransa, ya lallaɓa ya sake maka masa gora a baya, ya gantsare yana wani irin ihu, suka yi gaba suka bar su.

Ya din ga dukan gate ɗin gidan, yana ƙwalawa Abbu kira, ya koma kan Sadik, ya rungumo shi, yana jijjiga shi.

Sai da garin yayi shiru, sai kururuwar Al'amin yana kiran Yaya.

Maƙwabcinsu ya fito, na kusa da shi ma ya fito, aka din ga buga gidan su Al'amin, har aka tafi nemo mota, sannan Abbu ya buɗe. Sai dai ya shiga tashin hankali, ganin Sadik a kwance kamar mara rai.

Cikin tashin hankali Abbu ya tafi kici-kicin fito da mota, Al'amin ya zuciya ya É—auki Sadik a kafaÉ—arsa, kawai yayi gaba.

Da ƙyar aka riƙe shi, aka saka Sadik a mota.

Al'amin sai zubar da hawaye yake yi, ya na kiran "Yaya ka buÉ—e idonka ka kalleni, ka tsaya yanzu zamu je asibiti"

"A galabaice, Sadik ya motsa ya riƙa hannun Al'amin, sai kuma hannunsa ya saki. ko da suka je Asibiti, aka tabattar musu da Sadik ya koma ga Allah.

Al'amin ya durƙusa a kan gawar, ya din ga rusa kuka, kukan da ko lokacin da umminsu ta mutu bai yi shi ba, maƙwabta na ta rarrashin Al'amin.

Cikin kuka Abbu ya ce "Al'amin komai ya samu É—a na kai ne sila, ka sa nayi rashin É—a mai biyayya"

"A'a Alhaji Ibrahim, kar ka sake ka É—orawa Al'amin laifi, kai ne babban mai laifi, kana sane sarai unguwar nan babu kwanciyar hankali, ka bar su a waje, da ka buÉ—e musu sun shiga gida, koman dare ai da haka ba ta faru ba".

A daren aka yi wa Sadik sutura, Al'amin gani yake yi kamar a mafarki, awannin da suka gabata suna tare amma a yanzu wai babu Sadik. Kodayeke Abbu yana da gaskiya shi ne sila, da bai ce zai bar gidan yayi tafiyarsa ba, da haka baya faru ba, dan kuwa Sadik ba ya yawon dare.

Har jami'an tsaro sai da suka zo suka É—auki bayanan abun da suka faru, sai dai Al'amin ya kasa magana.

Sadik ya tara É—imbin mutane, yara da manya matasa da dattawa wurin sallatar gawarsa, kasancewar sa mutumin kirki.

Al'amin ya ji ina ma shi aka kashe, Sadik ya rayu, yayan nasa guda ɗaya tal da yake saukewa duk wata damuwarsa ya ɗauka babu ƙosawa ko gazawa, an kashe masa shi.

Alhaji sammani, ya yi wa Ibrahim tatas, a kan yadda ya koma soko a kan gidansa, tare da ci wa Rahila mutunci tsaf, a kan abubuwan da take aikatawa.
Ƙarshe ta shiga ta fita, ta raba abotar da aka yi shekaru ana ginata, suka rabu dutse a hannun riga, suka yi uwar watsi.

Depression ya nemi ya kama Al'amin, babu wand yake ta tasa, gashi yanayin halayarsa idan ba wanda ya sanshi ya saba zama da shi ba, ba kowa zai iya masa ba, saboda miskili ne, ga nuƙufurci, ba zai taɓa cewa wani ga damuwarsa ba, shi ba abokai ba, haka ya din ga ragaita a layi, raɗaɗin mutuwar Sadik taƙi barinsa.

Ya tafi wurin 'yan sanda ya tambayi, ko sun kama wanda ya kashe yayansa, suka ce masa bincike suke yi a kai, dan har a lokacin ba su tabattar da wanda yayi kisan kan ba, kuma a ranar ba Sadik kawai aka kashe ba.

Al'amin ya koma gida, yayi ta addu'a Allah ya sa a kama wanda ya kashe masa Sadik, duk da dare ne, amma a ko ina ya ga wanda ya kashe shi zai gane, dan kuwa ƙofar gidan su akwai security light.

Duk bayan kwana biyu sai Al'amin yaje, tun suna sauararsa har suka fara korarsa.
Chapter 87 · 0% Book details