← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 95

Sashe 10

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba dole na santa ba, a wurinki na santa ai"

"Ashe matar nan tsinanniya ce"

Da sauri sumayya ta ce "A'uzubillahi, me yayi zafi, mentor É—in taki?"

Nabila ta ce "Zilwajahiani ce, abun da muke ji a kanta daban, yadda take daban. Yau muka haÉ—u a kotu, kin san ina cikin team É—in barrister Bashir, tare muka je court yau.
Bayan an fito, jiki na tsuma na bita, ƴan jarida sun baibayeta, na yi mata magana kin ga wulaƙantaccen kallon da tayi mini? Ba shi ne ya dame ni ba, duk da uniform ne a jikina, na cire girman kai na gabatar mata da kaina, a matsayin lawyer mai koyi da ita, amma still ban isheta kallon kirki ba. Abunka da zuciya da abun da take so, na matsa tare da miƙa mata wayata, a kan ta bani lambarta, sai ce mini ta yi ba za ta bayar ba, kar na isheta da kira. Na ce mata bakomai, a matsayina na mai koyi da ita, kuma mai ƙaunarta, dan Allah ko mintuna uku ta bani, na daɗe ina burin haɗuwa da ita. Ina son ta bani shawara a matsayina na lawyer mai tasowa, kuma ta bani tips da zan bi, na zama kamarta a rayuwa, dan ina son ta da irin ayyukan da take yi. Ta ƙare mini kallon baki isa ba, sannan ta ce 'Ki zama kamar ni kuma? Taka matsayin da na taka? Never! Don't even give a try, ba zaki taɓa zama ba, and leave my way please, ina da abun yi"
Haka fa ta ce mini, a gaban mutane da masu yi mini dariya, da masu yi mini Allah ya ƙara wai neman suna da gidin zama ne ya janyo mini, wasu kuma su ka bani haƙuri wai haka halinta yake. Sumayya yau na tozarta, an wulaƙanta ni, duk yadda nake ganin ina da class, soyayya ta rufe mini ido, saboda ina ƙaunar matar nan fisabilillahi, wallahi da ƙyar na ƙarasa chamber, nan da nan na fara jiri, numfashina ya fara sama, kin ga dariyar da aka yi mini, wallahi na muzanta fiye da tunaninki"

Sumayya ta ce "Nabila jikina yayi sanyi, ban taɓa zaton matar nan za ta aikata haka ba, wai meyasa mu mata, galibin mu ƴan baƙin ciki ne? Wato ba zaki zama kamarta ba, sai ka ce wayo da dabararta ne suka ba ta matsayin da take kai".

"Wallahi sumayya, ko zan rasa raina, ko da kasada, sai na tabattar da na yi suna nima, sai dai idan Allah ya ƙaddara na mutu. Amma ina roƙon Allah, in sha Allah tana raye, sai na ɗaukaka fiye da tunaninta, kuma bibiyarta zan din ga yi, da bibiyar duk wani abu da ya shafe ta, sai na rama abun da ta yi mini. I will do a background check on her"

"Ke fa baki iya ɗaukar abubuwa da sauƙi ba, ki ƙyaleta mana kanta ta yi wa, ni na ce me?, abun da nima ake yi mini, ni kusan kullum ake yi mini, ke yau ne kawai, kuma arfa matsayi na duniya ba na kiyama ba"

Nabila ta girgiza kai ta ce "Wannan ke ki ka ga zaki iya, kuma ƙaramar alhaki ce ta wurin aikinku, wannan kuwa dizgin da ta yi mini, in sha Allah rabbi, sai na rama shi, dole na ajiye shirme, na mayar da hankali a kan aikina, ko dan fansar nan, kut wallahi matar nan ta gama cuta ta, kuma ba zan huce ba har sai na rama wallahi. Rakani titi in tafi gida" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tashi tsaye.

Sumayya ta danƙota ta ce "Nabila ki din ga sanyawa zuciyarki salama mana, kin fiye zafin rai, ki bi komai a hankali, kalli yadda ki ka kusa kashe kanki a banza. Idan Allah ya yi nufin ɗaukakaki fiye da ita, ita ɗin banza ta hana, dan Allah ki manta da ita, ki cigaba da rayuwarki".

Ta kalli sumayya cikin takaici ta ce "Lallai ma sumayya, dan ba ki ga abun da ta yi mini ba, a gaban mutane har da masu yi mini dariya. Ni gaba ɗaya ma ji na yi ban yarda da ita ba, abun da ake faɗa a kanta daban, abun da na gani yau a kanta daban, akwai wani abu a ƙasa, and i will run a background check on her, for the first place ma, wacece ita? Idan ta kama har bunkuren zan je mahaifarta, meyasa abun da ake faɗa a kanta daban, ita kuma halinta daban".

Sumayya ta ce "Na shiga uku, Nabila" kafin ta yi magana, Nabila ta yi waje, ta tarar da umman sumayya na salla, ta ce Umma na tafi, ta fice daga gidan.

Sosai abun da ya faru ya tsayewa Nabila,da ta tuno abun sai wani irin takaici yakamata.

Yau ba kowa ya san ma ta koma gida ba, dan yau babu surutu da hayaniya.

Abu kamar wasa, har dare Nabila ta kasa walwala, ko fitowa daga ɗaki taƙi yi, gani take kowa yana kallonta zai gane an dizgata yau, duk iyayin na ta da jan ajin.
Nabila irin mutanen nan ce masu saka abu a ran su, dan haka ko ta yi niyyar manta abun da ya faru, sai ta kasa.

Ta ɗaukko wayarta, ta kunna data, ta tarar da messages ɗin sumayya, ta na ta yi mata faɗan ta yi haƙuri ta manta da abun da ya faru.

Nabila ta yi mata reply da "You are not serious, ki saka ido ki yi kallo"

Social media ta hau, ta shiga searching ɗin sunan barrister Naja'atu Bunkure, nan da nan sai ga hotunanta, da wasu daga cikin ayyukanta na jin ƙai, sai dai ba ta samu wani cikakken bayani da take son samu a kanta ba.

Tsaki ta yi, bayan tuna yadda take mutuwar son matar nan a baya, har hotonta take sakawa a dp ɗin ta, saboda yadda take ƙaunarta, amma lokaci ɗaya a yanzu ji take yi, ba ta da wani maƙiyi idan ba ita ba.

Har sha biyu da rabi na dare, ba ta samu cikakken abun da take son sani ba, sai ma zarge-zarge da suka din ga É—arsuwa a ranta game da matar.

Saukkowa ta yi daga kan gadonta, ta fice daga É—akin, fita tayi can babban falo, ta nufi kitchen ta samu abun da za ta ci, dan yunwa take ji sosai.

Fridge ta buÉ—e, ta samu ruwa mai sanyin gaske, da coc ta fito falo tana sha.

Hasken fitila ta hango a baranda, ba a kashe ƙwan wurin ba, ga abba kullum sai yayi magana a kan rashin kashe kayan wuta, kafin a kwanta bacci.

Wurin ta nufa, da niyyar ta kashe ƙwan, ta na zuwa ta leƙa, ta hango nasir a kan kujera, yana ta danna system.

Ta window ta je ta zura hannu, tana taɓa masa kunne. Caraf! Ya riƙe hannun ba tare da ya ɗago ba.

Tayi dariya ta ce "Shi ne ba ka tsorata ba"

"Me ki ke tunanin zai razana É—an sanda?"

Ta ce "Ai dai É—an sanda mutum ne, kuma na san ka ji tsoro mazewa ka yi"

Yayi murmushi ya ce "Tsoro sai lauyoyi"

Ta buɗe ƙofa ta fita ta zagaya in da yake ta ja kujera ta zauna sannan ta ce "Duk tsoron lauya bai kai ɗan sanda ba"

Ya É—ago ya kalleta, sanye cikin kayan bacci pink, masu bargo kanta ko É—an kwali babu, tayi parking É—in gashinta"

Murmusawa yayi ya ce "Ke kin san babu tsoro ga wanda yake riƙe makami, yayi yaƙi da ɓarna"

"Hmm, yi dai a hankali, dan harshe ya fi makami dafi, kar lauyoyi su baka mamaki watarana"

"Ina aiki kin zo zaki dame ni, ina nawa aikin, ina kallabinki?"

"Yana É—aki" tayi maganar tana lashe murfin jarkar lemon hannunta.

"Kalli abun da ki ke yi kamar ƴar ƙauye, sai an yi magana ki fara ke barrister ce, ke degree holder " yayi maganar yana mayar da hankali a kan system.

Ta numfasa ta ce "Wai aikin me ka ke yi ne?"

"Wani aiki ne mai wahala, wanda nasara a kansa, na iya sawa na samu cigaba a aikina".

Nabila ta ce "Haba dai, to Allah ya taimaka"

"Amin" ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

Shiri ya wanzu na wani É—an lokaci, sannan ta ce "DSP"

"Na'am barrister"

"Sannu da aiki" ya É—ago ya kalleta ya ce "Kin isheni fa, za ki tashi ki bar wurin nan"

"Yi haƙuri, na daina magana"

Ya cigaba da aikinsa, ta na shan lemonta, tana jin yadda iska ke kaÉ—ata.

Duk abun nan, Abba ta É—akinsa ya na hango su, sai dai ba ya jin me suke cewa.

Can ta sake cewa "DSP"

A hasale ya ce "Ke! Meye ne? Tashi ki je ki kwanta dare yayi"

"Ni na kasa bacci, raina ne a ɓace".

"Ai dama kullum cikin ɓacin rai ki ke, tun da ke a rayuwarki ta duniya, baki da haƙuri tashi ki bani wuri"

Ta marairaice ta ce "To ka tsaya ka ji me aka yi mini mana, dan Allah kafin na tafi, ka gaya mini me zan yi, wanda zai saka na yi suna, kowa ya sanni" tayi maganar very serious.

Cikin gatse ya ce "Ki nemo in da Aminu Viper yake, ki taimaka mini na kama shi, kin ga sai ki yi suna, ni na samu cigaba a aiki"

Ta fuskance shi sosai ta ce "Waye shi, a ina yake? Kamar na taɓa jin sunansa"

Ya kalleta ya ce "Shi nake ta aiki a kansa, galibin aikin ta'addancin da ƴan daba suke yi, a wasu shiyyoyin da saka hannunsa, yaransa ne. An ce lallai na kamo shi, tun da yankin da ake ɓarnar ƙarƙashin kulawata yake akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison"

"Dan Allah idan na nemo maka shi, zan yi suna, kowa ya sanni?"

Kallon baki da hankali yayi mata, ya cigaba da abun da yake yi.

"Ka ga riba biyu kenan, na yi suna, kuma ka samu cigaba a wurin aiki, yes! Amma na ji ka ce akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison how? Kun tabattar da hakan ko kuwa? Ka bani hints mana, laifin me ya yi a ka kai shi prison É—in?".
Chapter 10 · 0% Book details