← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 95

Sashe 69

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce "Subhanallah" ya zauna yana faɗin "Yarinyar kirki, tuba nake yi yakamata ace na zo gidan naku, tafiya ta kama ni ne, ina ga yau kwanana huɗu da dawowa, kuma ina maganarku sosai wallahi, dan Allah ki yi haƙuri"

"A'a babu komai, ai mu ne masu laifi, tuntuni yakamata ace mun zo, ban san gidan nan ba ne shiyasa shi kuma bai kawo ni ba"

Rahila ta ce "Hmm, dama ya za ayi ya kawo ki, ai ko za a shekara sai idan rashin mutuncin sa ne ya kawo shi" yanayin maganganun da rahila tayi, ya tabattar mata da ba ita ce mahaifiyar Al'amin ba.

Abbu ya ce "Ina fatan dai ba wata matsala, ba yayi miki wani abu na rashin kyautatawa?"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Ba ya yi mini sai dai.." sai kuma ta yi shiru.

Rahila ta yi farat ta ce "Sai dai me, ki faÉ—a ba wani abu, ai mu duk iyayenku ne".

"Ƴan sanda ne suka zo mana cikin dare, suka kama shi suka tafi da shi, naje na kuma zuwa anƙi sakinsa, wai suna zarginsa da ta'amalli da hodar iblis".

Rahila ta ce "Taɓ! Ki ce shi likkafa ce ta cigaba a harkar shaye-shayen har ya kai wannan matakin?"

Jauhar ta ce "A'a ba ya amfani da ita, wani ne ya kawo ya ce a ajiye masa, ban san kowaye ba, su kuma suka zo amma wallahi ba shi da laifi, shi ne na ce bari na zo, dan Allah baba ko da hanyar da za a bi a sako shi, ba ma shi da lafiya wallahi, da na je dukansa suke yi, jikinsa duk shaidar duka" ta ƙarasa maganar tana kuka, duk yadda ta so riƙe hawayen amma abu ya gagara.

Rahila ta ce "Au dama shi ne dalilin zuwan naki? Sai da matsala ta afku ki ka nemi gidan ubansa, in dai wannan ne ya saba, kina zaune 'yan iskan da suke bashi goyon bayan yin rashin mutunci za su saka a sake shi".

Abbu ya ce "Ya isa haka rahila" ya kalli Jauhar ya ce "Ki daina kuka yarinyar kirki, case da ya haɗa da irin wannan case ne babba ba ƙarami ba, Al'amin ba ya jin magana ko kaɗan".

"Wallahi baba ba shi ya kawo su ba, ban taɓa ganinsa da ita ba".

"Idan ma yana ta'amalli da ita, ba gaya miki zai yi ba ai"

Abbu ya ce "Ki kwantar da hankalinki, idan da wata matsala ki koma gidanku, zuwa lokacin da komai zai daidaita, zan je na ga abun yi"

"Abbu ka san cocaine kuwa? Wallahi ka je suka fuskanci belinsa ka ke son yi, za su iya haɗawa da kai, ka dai koma gefe ka taya su da addu'a, duk masifar da ya janyo ta ƙare masa a kansa idan yana da rabo ya fito, idan babu ya ƙarata a can".

Kalaman rahila suka yi wa jauhar zafi da nauyi, ba shiri ta tashi ta ce "To bari na tafi sai anjima".

Rahila ta ce "Ki je gida ki yi ta addu'a, idan babu dama ki koma gida, amma shigar mahaifinsa wannan case É—in ba mafita bane ba, kina zaune za a sako shi".

Abbu ya ce "Ki yi haƙuri kin ji, zai fito in sha Allah, zan san abun yi"

"Ka daina saka mata rai da zaka yi wani abu fa, haka kurum wani abu ya sameka gani ga 'ya'ya ka barmu"

Bayan tafiyar jauhar, Abbu ya ce "Rahila, anya ban yi wauta ba da na biye miki aka aura wa yarinyar mutane Al'amin ba, kalli yadda take cikin tashin hankali da damuwa fa".

"Wannan yarinyar fa da ka ke gani, ba a bar tausayi ba ce ba, ko ka manta kangarewa iyayenta ta yi suka nemi maraba da ita?"

"Duk da haka rahila, ni fa tantama nake yi a kan maganar nan, gaskiya ina ga zan jagoranci raba auren nan, Al'amin ba zai yi hankali ba"

"Abbu ina ruwanka, dan Allah ka bar maganar yaran nan"

Jauhar kuwa bayan ta fita, ba tare da tunanin komai ba, ta nufi unguwar su, ta je ta samu baba, ko da wani abu da zai iya taimaka mata, ba tare da tuna haɗarin da hakan ka iya haifarwa ba, kodayeke wanda yake cikin ruwa ko takobi ka miƙa masa kamawa zai yi.

Ayshercool
08081012143

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955

Sosai take sauri, tare da fatan Allah ya sa baba yana nan.

Sai dai tayi iya ƙoƙarinta wurin daidaita nutsuwarta, kafin ta ƙarasa gidan.

Yamma ta fara yi, yaran gidan sun dawo, sun yi kaca-kaca da shi, duk sun zubar da kayan makarantar su ko ina, ga uban wanke-wanke da aka rasa mai zaman kawar da shi daga wurin.

'yan ƙananan yaran gidan ne suka fara murnar ga jauhar, ɗakin mama ta shiga suka gaisa, ta kalleta ta ce "Lafiya na ganki yanzu? Wani abun ne?"

Jauhar ta ce "Lafiya ƙalau wurin baba na zo".

"In ce ko dai lafiya, kuma ya san kin zo? Ki tashi ki tafi kar ki saka makakken mijinki ya zo yayi mana tijara da tashin hankali"

Anty ce ta leƙo falon ta ce "Jauhar ashe abun da ya faru kenan?"

Jauhar ta kalleta ta ce "Anty dama kina nan ina wuni?"

"Lafiya ƙalau, ashe kuma kama mijinki aka yi da hodar iblis, abu bai yi daɗi ba".

Dammm! Ƙirjin jauhar ya buga, yaya aka yi anty ta san wannan zancen, mama ta ce "Kamar yaya?"

"Yanzu muka yi waya da rahila, ta ce bata daÉ—e da barin gidan ba, ta je musu wai an kama shi".

Wani abu É—aci ya tsaye wa jauhar, kamar ta fashe da kuka, ta ce "Ba ya ta'amalli da hodar iblis, rigima ce kawai ta haÉ—a su da wasu, shi ne dai na je na sanar musu, kar ya zamana ba su sani ba"

"Dan ubanki ni zaki yi wa ƙarya dan ki kare mijinki, ai rahila ba zata yi miki ƙarya ba"

Walida ta ce "Taɓ, Allah ya kiyashemu taɓewa, hodar iblis abun ba arziki ai na zata a sara suka kawai ya tsaya ashe babban kai ne"

Duk yadda ta so ta riƙe hawayenta ta kasa, ta fashe da kuka, suka din ga aibata Al'amin, gashi ba ta tarar da baba a gida ba, babu alamar za su tausaya mata, ko su rarrasheta, kawai ta tashi ta ɗauki jakarta tana kuka, ta fice.

Hafsa ta ce "Allah sarki jauhara da tuni ana china ko gidan Alhaji mu'azzam ana shan A.C" suka din ga dariya.

Ta kwashi ƙafa ta nufi gida, tare da ƙudirce wa ranta da yardar Allah, babu abin da zai saka ta sake zuwa gidan nan da matsalarta, ƙarshen ƙiyayya da tsana dai ana nuna mata a gidan nan.

Kamar daga sama ta ji an buga mata tsawa "Ke bamu hana ki shigowa unguwar nan ba?"

Sai a lokacin ta tuna abun da ya faru, cikin tsoro ta kalli mai yi mata tsawar, sai dai ta kasa magana, ta bishi da ido.

"Ba magana nake yi ba"

"Nawa ubanka ya bayar aka shimfiÉ—a unguwar da za a hanata shigowa mahaifarta?" Ta ji wata muryar daban.

Ta kalli matashin yaron, guduma kenan É—an gidan mai unguwa, da su Walid suka bawa ragamar kula da gidan Al'amin da shige da ficen jauhar, har ta je gidan su Al'amin ta taho nasu gidan yana biye da ita.

Saroro ta yi tana kallonsa, dan ba ta san shi ba.

"Waye kai? Meya kawo ka unguwar nan?"

Guduma ya nuna masa Jauhar, ya ce "Wannan, wallahi kana taɓa ta zamu ɓalla ƙarfe a wurin nan, mu rabu salin alin" ɗayan ya ja da baya ya basu hanya, guduma ya ce wa jauhar "Mu je"

Ita dai ba ta iya yi masa magana ba, ta cigaba da tafiya ita yanzu gaba É—aya hankalinta da lissafinta yana kan halin da take ciki a yanzu.

Misalin ƙarfe uku da rabi na dare, jirginsu ya sauka malam Aminu Kano international airport, direba ya zo ɗaukarsa.

Duk da a gajiye yake, saboda doguwar tafiyar da ya yi, hankalinsa da lissafin sa yana kan, ya ƙarasa gida garin Allah ya waye, ya je ya ji ba'asin dalilin fasa aurensa da yarinyar da ya ƙallafa rai a kanta, kullum cikin tunanin ta yake, kuma tun da aka ce, an fasa bashi ita, ya ji ya ƙara ƙaunarta, ta shiga ransa fiye da yadda yake tunani.

***
Kwanaki kaɗan ya rage jauhar ta fara jarrabawa, amma ba ta iya karanta komai, ga uniform ɗin ta, ga litattafanta sai dai ba ta da nutsuwar da za ta yi karatu, duk ta ƙare tayi rama ga rashin abinci dama damuwar da take ciki ba ta barinta ta ci abincin.

Walid sai da yayi mata faÉ—a a kan zuwanta gidansu ba tare da saninsu ba, tare da jaddada mata mugunta da gaba mai tsanani da take tsakaninsa da Al'amin.

Tana kwance a falo, maman halimatu ta shigo gidan, ta tarar da ita a kwance cikin damuwa ta ce "Jauhar, rayuwa za ta yiwu a haka kuwa? Yanzu da mutuwa yayi ba dole ki yi haƙuri ba, kin addabi kanki, kamar ko abinci ma fa ba kya ci" kamar ta soso mata wurin da yake yi mata ƙaiƙayi, ta hau rera kuka, ta zauna ta rungume ta ta din ga rarrashinta.

Ta ce "Sako hijjabinki mu je gidana, kya ɗan sake ki sha iska, zaman kaɗaicin nan ba abun da zai amfana miki sai ɓacin rai"

Haka ta bi maman halimatu, dan ba ta da wani zaɓi face hakan, ta zuba mata abinci ta bata, sai dai ta cakala ta bar shi ta ce ta ƙoshi.
Chapter 69 · 0% Book details