Sashe 64
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta ce 'm"Jauhar kin kyauta, wato miji daÉ—i, ki ka kasa zuwa ki duba É—an uwanki, ya kusa mutuwa"
Cikin tashin hankali jauhar ta ce "Subhanallah, mama ban sani ba ba shi da lafiya ne?"
"Ina fa, ya dawo daga aiki, aka samu wasu suka sassare shi".
Abun ya É—agawa jauhar hankali, ta ce musu ba ta sani ba.
Al'amin yana can wurin su Walid, kansa yana yi masa ciwo, ga yana jin yanayin jikinsa kamar zazzaɓi yana son kama shi.
Yana jin wayarsa na ta vibrating yayi banza.
"Viper wayarka fa ta cika mini kunne, dan Allah ka É—aga"
"Ƙyale ni, kamar zazzaɓi ne zai kama ni"
"To ka kashe wayar mana".
"Ba zan kashe ba"
"Ka duba mana ko beb É—in ka ce take nemanka, yarinyar nan ta na kula mana da kai yasin".
Viper yayi tsaki, ya sake gyara kwanciyar sa.
Walid ya miƙa hannu, ya ɗauki wayar ya ɗaga ya ce "Ya aka yi?"
"Ka gaya wa uban gidanka, na ga cikarsa ta shigo mana arear, duk da kashedin da na yi kar ta sake zuwa, tun da ya kwasheta. Yayi ganganci mafi girma da muni, tun tun da ya bari ta shigo, ya zo ya É—auki gawarta a dabata!.
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Walid ya kalli Al'amin, ya lumshe idanunsa, wasu irin jijiyoyi suka fito raÉ—a-raÉ—a a goshinsa.
Yayi shiru ya ƙi ko motsawa.
"Mai zamani, ba ka ji me ya ce ba ne, matarka fa yake maganar ka je ka É—auki gawarta"
"Na aiketa ne?"
"Ban gane ka aiketa ba? Kai kut....." Ya É—ura masa ashar.
"Idan da gaske ya kasheta fa?"
Al'amin ya tashi zaune, ya É—auki wayarsa, ya danna ya kira wata lamba.
"Yeah maza"
Ya ce "Ina aikin da na saku?"
"Ai ta gama ta tafi ma"
Ya ce "Ba tafiya a ta yi ba, gidansu ta tafi, ba ka kira ni ka gaya mini ba. Wancan garan ya ce in je in É—auki gawarta a dabarsa, wallahi ya kashe 'yar mutane sai na kasheka kai ma"
"Haba maza, cewa ka yi mu saka ido, ta shiga ta gama abun da take yi ta tafi, kuma min bi ta ba ta sani ba, ta gama ta tafi ba ka ce mu bi ta mu ga ina zata tafi ba"
"Wallahi liti ka bari muka haɗu sai na saka maka ƙarfe, ka ji na rantse. Ya ajjye wayar ya yinƙura, Walid ya ce "Ina zaka je, ka ce ba ka jin daɗi, ka zauna bari ni na je"
"In zauna sai ya kasheta, sannan zan je?" Yayi maganar a zafafe.
Walid ya bi shi da kallo, yana son gano haƙiƙanin in da ya dosa, amma bai gane ba, Al'amin ya sake birkicewa ya ce "Ya kasheta ko ya bar ta da rai, ba shi ne a gabana ba, tun da ba ni na gayyato ta rayuwata ba, abu mafi muni shi ne ace madaki ya kuma yi mini illa, idan haka ta kasance, kan mai uwa da wabi, zan ɗauki matakin da ya dace".
Ya fita da sauri, Walid ya bi bayansa, bai ma san ina ne gidan na su ba, sai da walid ya yi masa jagora, yaran madaki suna ganin Al'amin ya shigo musu unguwa da rana tsaka, amma aka rasa mai tunkararsa, dan ba su fiye galaba a kansa ba, sai sun yi masa taron dangi.
Suna tafe a hanya, liti ya kira Walid ya ce masa "Ka ce ya kwantar da hankalinsa, na yi waya tana lafiya tana cikin gidan su, zamu fito da ita lafiya in sha Allah"
Walid yana gaya wa Viper, ya ce "Ka ce masa bana so" ya yi maganar yana ƙara sauri.
Jauhar kuwa na can, har ta ɗora musu girki, sai zungurarta suke yi, su ji a wani hali take ciki a gidanta, da irin zaman da take yi da Al'amin, amma ta dinga waskewa, taƙi gaya musu komai.
Hafsa har da tambayarta, wai wuri É—aya suke kwana?.
Jauhar ta kwashe da dariya ta ce "To zai kwana a waje ne yana da mata?".
Surayya ta ce "Iyee zama da maÉ—aukin kanwa, wato har bakinki ma ya buÉ—e haka?"
Jauhar ta yi dariya ta ce "Kai Anty surayya tambayata fa tayi, bari na ƙarasa na je gida ma na yi girki, kar ya dawo".
A tunaninsu za su ga jauhar cikin mawuyacin hali, amma sam ba su ga alamar hakan ba.
Ta shiga suka gaisa da anty lubabatu,ta din ga murna yadda ta ga jauhar, babu alamar wahala a tare da ita, ta aika 'ya'yan anty lubabatu su je gidan kakannin su, su karɓo mata shirin dutse a wurin ƙanwar anty lubabatu. Da yake duk a unguwar ne.
Anty lubabtu har da harhaɗawa jauhar 'yan kayan gyaran aure na mata, ita dai ba ta ce komai ba, ta karɓa ta ce ta gode.
Da ta fito daga gidan, ta lura da wasu matasa da ba ta san suwaye ba, a layin amma ba ta damu ba ta shige gida.
Walida ta tare ta ta ce "Me Anty lubabatun ta baki?" Suka karɓi ledar hannunta, suka ga kayan mata da turarukan wuta da humra masu kyau da ƙamshi.
Suka din ga yi mata dariya cikin izgilanci surayya ta ce "Wai nan ba ki yadda ba ke matar aure ko jauhar? Dan Allah ya ki ke yi ke kuwa da shi, ga 'yan shaye-shaye da ƙazanta, kuma har kiss ku ke yi?"
Jauhar ta yi wani irin murmushi ta ce "Yaya surayya kenan"
"Gaya mana man"
"To ni me zan ce? Annabi ya hana faÉ—a, sirrinmu ne ai"
Surayya ta ce "Lallai, yau na ga illar ƙani ya rigaka aure, ni ki ke gaya wa baƙar magana jauhar?
"A'a ki yi haƙuri, ba baƙar magana ba ce"
Ta karɓe kayanta, ta saka a jakarta, ta cigaba da aikinta.
Ta zauna tana yanka salak, sai mita take yi ba ta haÉ—u da yaya saifu ba, kuma baba ma baya nan"
Tijjani ya fito yana É—an tattakawa, ta din ga yi masa sannu.
Tun da ya shigo layin yake ganin yaran madaki tsilla-tsilla, alla-alla yake yi ya ƙarasa ya tabattar da abun da madaki ya faɗa gaske ne ko akasin haka, idan gaske ne bai san iya adadin haukan da zai yi masa ba.
Walid ya ce "Ga gidan nan" dai-dai lokacin ɗan gidan anty lubabatu ya zo zai shiga gidan su jauhar, hannunsa riƙe da ledar viva, an zubo mata dutsen shiri da kayan yi kala-kala, babar anty lubabatu ta ce a bata kyauta a matsayin jari, shi ne gudunmawarta na biki.
"Kai shiga nan gidan ka ce.... Sai kuma ya yi shiru dan ya manta sunanta, sai Fatima yake iya tunawa.
Walid ya ce "Ka faÉ—a masa sunan"
Tsaki yayi ya ce "Na manta sunan, sunan wani iri ne dai haka kamar Angela"
Walid ya ce "Amma kuwa ka yi asara"
Al'amin ya ce "Ka ce 'yar madara ta zo in ji Master"
Walid na son yin magana, ya maze ya ce "Na san ƙarya fa madaki dama yake yi bai kasheta ba".
Yaron ya shiga ya fara ba ta saƙon hajiya kakarsa, na bata kyautar dutse, ta karɓa tana murna da godiya, sannan ya ce "Wani a waje ya ce wai 'yar madara ta zo" take gaban Jauhar ya faɗi.
Walida ta ce "Wace wata 'yar madara, babu ita a gidan nan, in ji wa ya ce maka?"
Yaron ya ce "Wai in ji Master "
Jauhar ta ce "Na shiga uku, master ne, ban gaya masa zan zo nan ba, waye ya gaya masa?".
Ta ce "Bari na É—aukko jakata"
Anty ta fito ta ce "wannan aikin kuma wa zai ƙarasa shi? Ai sai yayi haƙuri ta gama, kai je ka ka ce masa aiki take yi, ya dawo an jima"
BuÉ—e baki jauhar ta yi ta ce "A'a anty kar ya gaya masa haka, kaga haidar ka ce masa...
Anty ta katse ta ta ce "Fita ka je ka gaya masa haka, waye shi ba gidan sirikansa ba ne ba".
Gaban Jauhar ya tsananta faÉ—uwa, ba ta san me hakan ka iya haifarwa ba.
Mama ma fitowa ta yi ta ce "Ba zaki zauna ki cigaba da aikin ba"
Viper kuwa wani marurun takaici ne ya ƙule masa a wuya, jin irin saƙon da aka aiko masa da shi, kamar shi za a aikowa da wannan banzar maganar. kawai ya sai kai zai shiga gidan, walid ya riƙe shi ya ce "Mai zamani gidan sirikanka ne fa, dan Allah kar yi wani abu mara daɗi, ka zubar mata da mutunci"
"Tun da suka zaɓi su aura mini ita, sai na tabattar musu da maganata ce gaba da ta su a yanzu" kawai ya saka kai cikin gidan.
Cak ta tsaya, jikinta yana tsuma, ganinsa ya shigo yana wannan takun nasa, ya ƙureta da ido, tun kafin ya ƙaraso.
Tsit suka yi suna kallon ikon Allah, ya ƙaraso, ta wutsiyar ido ya kalli yaya tijjani da ke zaune a kan farar kujera, ya sauke idonsa a kan mama, su surayya sannan Anty Zakiyya ta ƙarshe.
Yana ganinta ya ƙara tabattar da Rahila ce ta saka aka yi masa aure, bai ga alamar akwai mahaifiyar jauhar a cikin su ba.
Ya kalli Jauhar ya ce "Ni na aiko ki zo ki ka ce mini ba zaki zo ba?"
Ta ce "Dan Allah Master ka yi haƙuri"
"Shut up!" Yayi maganar cikin ƙaraji, tare da ball da bokitin da aka kawo markaɗe, da kwanon salak ɗin duk suka tarwatse a wurin, ta zabura ta ƙanƙame jikinta. Ai ba ita ba, har sauran matan gidan da 'yan matan.
Tijjani kuwa É—imaucewa yayi, dan kuwa ba zai manta muryar nan ba, duk da yana tantama amma kamar muryar wanda suka yi ma aika-aika.
"Dama mun yi da ke zaki zo nan? Kin zata ƙarya suke yi da suka ce za su saraki idan suka kuma ganinki a unguwar nan?" Ɗago ido ta yi cikin tsoro tana kallonsa.
Ganin yadda duk ta rikice ya sanya ya saki muryarsa ya ce "Zo ki wuce mu tafi"
Ta ce "Bari na É—akko hijjabina"