← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 95

Sashe 94

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Afuwan Hafsat, wallahi madam ce nayi  ta faman rarrashinta, taƙi yin shiru kin san kishi babu daɗi, shiyasa na zauna da safen nan ma da ƙyar na fito, duk a cikin damuwa ta ke, yanzu haka kanta ciwo yake saboda kuka, ina ga da kaina zan fita nema mata magani"

Tamkar hafsa ta zabga masa mari haka ta kalleshi ta ce "Ni bana buƙatar kulawarka kenan sai ita?"

Ya ce "No ba haka bane ba? Ai ke sabuwa ce, sai ta fiki shiga damuwa, bari na je na sayo mata maganin na kai mata, na yi ordern abinci, idan ban dawo da wuri ba ki karya kawai.

Abu kamar wasa, har wurin kwanaki uku, bai saurari hafsa ba, wai uwargidansa ba ta da lafiya, har ma ya É—auki fushi da ita, wai ba ta je ta yi mata sannu ba, ta É—auki waya tana kuka ta sanar da Anty, Hankalin Anty ya tashi, ta ce ta je ta dubata É—in, za su sake shiri su ma.

Baya nan hafsa ta shiga duba ta,  ta ce "Na ji an ce baki da lafiya, na zo duba ki"

Ta ce "Ko ɗaya, lafiyata ras, kawai ina ƙoƙarin nuna miki ƙarfin ikon da nake da shi a cikin gidana da irin gangancin da ki ka aikata na shigo mini gida"

Hafsa ta ce "Shigowar ai ita ce mai wuyar, tun da an ce hanawa ki ke yi, ni kuma na yi nasara na shigo, mu zuba da ni dake".

"Lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka, ga fili ga mai doki".

Har hafsa ta kwana bakwai a gidan nan, ba su haɗa shimfiɗa da Alhaji mu'zzam ba, duk ɗokin amarcin da take yi, komai ya fita daga kanta, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ƙiri-ƙiri yake nuna mata shi ta matarsa yake yi ba ita ba, saɓanin abun da ya nuna mata a waje.

Jauhar kuwa ta cigaba da yi wa master magiyar, ya taimaka ya bari ta je gidan hafsa tun da an yi bikin, kuma ta na son ta je gida ta gaida baba, ta bashi gudunmawar biki.

"Ni fa nayi miki alƙawarin zuwa gidan yayrki, amma amarya ce, ya zaki je musu gida sati ɗaya da biki?"

Cikin rashin fahimta ta ce "To ba a zuwa?"

"Eh, idan sun shirya samun zuriya su, ai ba za so ki dame su ba, idan lokaci yayi zan kai ki".

Anty da Rahila suka cigaba da yawon bin bokaye, ƙauye-ƙauye, dan su sake kama Alhaji mu'azzam, kuma ya saurari hafsa.

Komai na buƙata gashi nan a zube, amma miji ya gagareta sai dai ta ganshi daga nesa.

Tayi iya ƙoƙarinta, duk wanda ya zo, ba ta bari ya fuskanci tana cikin damuwa, ta baka abinci ka ci ka sha, idan zaka tafi ta baka na mota mai yawa, tayi ta hura hanci, saboda tana cikin gida na alfarma ga motoci a parking lot.

Jauhar ta gaji da yi wa Al'amin magiya, ta ƙyale shi, dan kansa ya ce ta shirya, shi zai kaita gidan hafsan, su gaisa ya dawo da ita.

Ta din ga murna tana yi masa godiya, amma ta ce "Dan Allah master a sakawa baburin nan salansar sa, idan muka fita fa saboda ƙarar da yake yi, sai kowa ya waiwayo ya kallemu".

Ya ce "Ni fa na fi son abuna a haka"

Ta kwantar da murya ta ce "Na sani, amma a taimaka mini, ko so kake kowa sai ya É—aga kai ya kalli babyn robar taka?"

"Zan duba"

"Yauwwa master na"

Yayi murmushi ya ce "Naki, waye ya baki?"

Ta ce "Allah ne ya bani, kuma na karɓa hannu bibbiyu ina yi masa godiya"

Ta kira hafsa a waya, hafsa ta ɗaga da ƙyar tana cika tana batsewa, Jauhar ta ce "Anty hafsa ina wuni, ina ta kiranki ba kya ɗagawa"

"Bana kusa ne, shiyasa"

"Adress É—in gidan zaki bani, gobe in Allah ya kaimu zan zo in sha Allah"

Kamar hafsa ta ce mata ba ta so, b tare da la'akari da su ba su taɓa taka gidan jauhar ba, amma sai ta ga ya dace jauhar ta zo ta ga daular da take ciki, dan haka ta bata adress ɗin.

Bayan ta gama wayar, ta ce "Master ta bani adress É—in, babu wuya ma gane gidan nata. Zo mu yi kallo a wayata" ta yi maganar tana zama a kusa da shi.

"Ni kallon nan gajiyar da ni yake yi"

Ta ce "Ahh haba dai, ko kaÉ—an nan, yana da kyau ka samu abubuwan da za su din ga É—ebe maka kewa"

Al'amin ya ce "To zaɓi ɗaya, ko dai ki sauke wannan abun, ko kuma a haƙura da kallon" yayi maganar yana nuna boti, da yayi ɗare-ɗare a kan cinyar jauhar.

Jauhar ta kwashe da dariya ta ce "Boti master ya ce ka tashi daga cinyar matarsa" kwanciya magen ya ƙara yi, yana lafewa.

"Ban taɓa ganin abun da ya raina ni ba, kamar ke da magen nan ba"

Jauhar ta din ga dariya, ita yadda ba sa ga maciji da botin ma dariya yake bata.

Ta zauna a kusa da shi, tayi connecting da mp, ta saka musu film.

Ta kalleshi ta ce "Ka ji ko? Baby ake cewa mace, kai baka yi mini irin wannan kalar soyayyar, sai zare mini ido da sakani kuka"

Yayi murmushi bai ce mata komai ba, sai dai ta ji ya saka hannayensa ya riƙe nata. Mintuna goma da ta ɗaga kai ta ga yayi bacci. Ta zuba masa ido yana bacci, a ranta ta cigaba da yi masa addu'a.

Ta kashe wayar ta ce "Master ka tashi ka je ka kwanta tun da kallon ne ba ka so"
Yayi shiru bai motsa ba. "Master"

"Mmm" ya amsa ba tare da ya buÉ—e idonsa ba.

"Mu je na yi maka addu'a ka kwanta"

Ya ce "ÆŠauke ni, na gaji"

Ta ce "Na É—auke ka, ai kuwa da sai dai wata ba ni ba, aikin me ka yi ka gaji har haka?"

"Ƙasa muka kwashe tifa biyar, ban sha komai ba kuma na yi aikin, ni da su Walid"

Jikinta a sanyaye ta ce "Har tifa biyar master. Baka gaya mini ba sannu, amma dai sun biya ku ko?"

Ya tashi zaune ya ce "Eh, har na kai wa mai solar kuÉ—in, ya zo ya saka miki solar, ya kawo miki fankar solar zafi ya fara yawa kuma ba wuta".

"Solar kuma master? Da mun sai kayan abinci, zafi lokaci ne zai wuce, solar fa da tsada".

"An ce masu asma, ba sa son zafi" ya yi maganar yana tashi tsaye, tashi ta yi ita ma, sai ta rasa me za ta ce masa, ya nufi ɗakinsa, ta rasa ta ina yakamata ta fara ma. Akwai abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace yana yi da kuɗi, da solar da ya saya, kamata yayi ace ya sai musu kayan abinci, ya ɗinka sutura da ko ɗan takalmi ne mai kyau na kwalliya. Duk in da ya kwashi taklminsa soso haka yake ƙarawa gaba da su, kayansa ma ita ta ware masu kyan ta kai ɗakinta, sai idan za shi wani wuri na musamman ko juma'a ta bashi ya saka. Sai dai ta san bai kyautu, ta nuna ba ta ji daɗin abun da yayi ba, domin ko ba komai, yayi ne dan ya kyautata mata.

Ya nemi wuri ya kwanta, ta zauna a kan katifar, ta É—ora hannunta a kansa, tare da karanto masa addu'oin kwanciya bacci.

Abun da jauhar ba ta sani ba, bayan ciyar da shi da ta din ga yi farkon auren su, Addu'ar da ya ji tana yi masa cikin magagin ciwo, tayi matukar tasiri a zuciyarsa, Addu'a ce da idan ba uwa ba, ba kowa zai yi maka ba. Addu'oin da take yi masa idan yayi mata wani abu na kyautatawa ma, ba ƙaramin daɗi yake ji ba. Ga uwa uba kirarin da take yi masa wasu lokutan, da suke fasa masa kai. Duk wani abu da zai yi baya manta tarin alkhairin ta.

"Allah ya saka maka da alkhairi, ya buɗa arzikin ka, ya wadata mu da halal ya nesanta mu da haramun. Na gode sosai da sosai Allah ya biya ka da gidan aljanna, ya jiƙan iyayenmu"

Idonsa a lumshe ya ce "Amin 'yar aljanna, addu'ar ta yi daÉ—i" tayi murmushi ta tashi.

Washegari da wuri ta shirya, tana ta murna za ta je gidan hafsa, ta wanke laifinta na rashin zuwa biki.

Shi kuma ya ce zai kaita, amma ya din ga yanƙwanata.

Ba su fita ba sai sha É—aya saura, tiryan-tiryan, har gidan hafsa.

Gida ne babba na gaske, Al'amin ya ce "Ba daÉ—ewa zaki yi ba, da wuri zan dawo mu tafi"

"To Allah ya dawo da kai lafiya, take care".

Ya ce "To, ki shiga, sai na tafi"

"Saboda kar in gudu?"

"Idan kin gudu ma zaki dawo" yayi maganar yana tayar da babur É—in sa.

Juahar ta shiga har falon Hafsat, ta din ga bata haƙuri na rashin zuwanta bikin nan ta ce "Kin san halik maza wasu lokutan sai a hankali, babu yadda ban yi ba, amma ya hana, ba shi da lafiya lokacin" Hafsa sai ɗan fizgar kai take yi, wai ita dole ga matar mai kuɗi.

Har la'asar tana gidan hafsa, bayan ta gama shan ƙamshin, ta saki jiki kuma suka hau hira, da yake ita ce sakuwar jauhar, daga ita sai jauhar.

Ta din ga koɗa mata irin son da Alhaji mu'zzam yake yi mata, dan ta tura mata haushi. Jauhar kuwa ko a jikinta, ta ce "Wallahi yaya hafsa idan Allah ya baka miji mai sonka tsakani da Allah, duk wani ƙalubale mai sauƙi ne"

Ta ce "Aikuwa shiyasa nake tausyinki, aure ba soyayya, ga miji sai a hankali"

Jauhar ta ce "Aikuwa ke da ki ka yi na soyayyar ma, ba ki fi ni samun kulawa ba, da farko a tsorace nake da shi, tun da muka saba Alhamdilillah"

"Taɓ, haryanzu yana safarar cocaine ɗin?"

Duk da jauhar ta ji haushin maganar ta ce "Da safarar cocaine yake, ai mun girmi zaman Kano sai Abuja"

Al'amin ya kira jauhar, ya ce ya zo ta fito su tafi.
Chapter 94 · 0% Book details