← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 95

Sashe 28

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta fara shiga wurin aiki, ta gabatar da ayyukanta na ranar, sannan ta fara harhaÉ—a kayan aikin da za ta yi amfani da su.
Gaba ɗaya jikinta babu ƙwari, sai tsananin tsoro da fargaba.

Murtala ne yake ta kwantar mata da hankali, tare da nuna mata, hakan ma wani cigaba ne, ta sani ko daga program É—in su daidaita da honorable É—in.

Jin sa kawai take yi, tare da murmushin yaƙe.

Har bakin motar gidan radiyon da za a kai ta a ciki, yana ƙarfafa mata gwiwa, "Sumayya, abun da zan gaya miki shi ne, ki san iyakar ki a kan program ɗin nan, iya tambayoyin da aka rubuta miki, ki yi masa su zaki yi masa, kar ki ƙetare su ki jawo wa kanki matsala, ƴan siyasar nan ba kowa ne mai imani a cikin su ba"

"In sha Allah uncle murtala zan kiyaye, na gode sosai"

Ta shiga motar ta zauna, direban ya ja suka tafi.

Nabila kuwa tana office tare da barrister Habib, dan yanzu ya saukko ya fara yaba mata, tana ƙoƙari, ya fuskanci kawai shiririta ce take damunta a kan aikin, da rashin mayar da hankali.
Tana yi tana kallon agogo, kar ta saɓa lokacin da a ka bata.

"Barrister" ta kira shi, ya É—ago yana sauraren ta.

"Ban sani ba ko kana jin radiyo"

Ya ce "Ina ji mana, meyafaru?"

"Cases da dama, idan suka faru mussaman na masu ƙaramin ƙarfi, sai in ga barrister bunkure ta tsayawa mutane, wai ita ba dan kuɗi take aikin ba, dan barrister ce da ba kowa yake iya ɗauka ba, amma tana tsayawa marasa ƙarfi, ko kuɗi ne suka yi mata yawa?"

Barrister Habib ya girgiza kai ya ce "Ke dai kawai ayi sha'ani"

"Ka san wani abu kuwa? Akwai wani case da wata mata, ta je gidan radiyon su sumayya, ta kai koken an yi wa ƴar ta fyaɗe, an dawo mata da ita daga gidan aiki, ta je gidan da yarinyar take aiki, an hana su shiga, ta kai wurin ƴan sanda, amma ana ta yi mata yawo da hankali, wai yaron ɗan manya ne. To na ji an ce ta shiga case ɗin, amma haryanzu babu wani update, ka san da na so na jarraba sa'a ta, nima na shiga case ɗin ayi da ni, na tausayawa matar da yarinyar, amma na san ana babbakar giwa, wa zai ji ƙaurin zomo, na san ba za ta saurare ni ba ma".

Barrister Habib ya tattara hankalinsa a kan Nabila ya ce "Nabila"

"Na'am"

"Just be yourself, ke dai ki kalli mutum a riga kawai, Naja'atu kura ce da fatar akuya, ba wata abar burgewa ba ce, da zaka yi koyi da ita ba. Yarinyar ƴan siyasa ce, babu wani taimakawa masu ƙaramin ƙarfi, ta fake da wannan ne, dan sunanta ya ƙara fitowa, kuma ya rinjayi ɓarnar da take aikatawa, ai mun yi karatu da ita tare, ƙwalluwar shegiya ce, ke abun bai baki mamaki ba, ace kowace shari'a idan ta tsaya maka, zaka yi nasara, ace komai kai ka ke nasara akwai ayar tambaya ai, dan haka ki yi ta kanki kawai.
Duk da mu ma ɗin wasu lokutan, muna take gaskiya, amma yanayin aiki ne ya zo da haka, kuma nata ya ƙazanta".

Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Biri yayi kama da mutum"

Nabila a zuciyarta ta ce "Idan haka ne, ba gaba da gaba yakamata na yi da ke ba, tona miki asiri zan yi"

Habib ya ce "Ya dai?"

"Nothing sir, jikina ne yayi sanyi kawai na gode sosai da bayaninka"

Ba tare da neman iznin kowa ba, ta É—auki jakarta ta fita.

A in da ta tsaya shekaranjiya, nan ta je ta sake tsayawa, tana fatan Allah ya sa ba jirgata za su yi ba.

Ta shafe a ƙalla awa guda a wurin, har ta sare zata tafi, matashin da ya kai mata waya, liti yayi mata magana da ita, ta gani a gabanta.

Bai ce mata uffan ba, ya miƙa mata wata takarda.

Sunan wata unguwa ne a jiki,da dai-dai wurin da zata je ta tsaya, saboda tsabar wauta da rashin hankali, ta yi masa godiya ta tari abun hawa ta nuna masa takardar.

Mai baburin ya gaya mata kuÉ—insa, babu neman ragi, ta afka ciki ta ce su tafi.

Lissafin da take ma a zuciyarta, na mamakin yadda Naja'atu tayi mata kallon ƙasƙanci ne, ta wulaƙanta ta alhalin ma ba wata mutuniyar arziki ba ce.
Babban abun da ta fuskanta, ƙasar nan ba zaka taɓa samun wasu damarmaki ba, har sai ka taka wani babban matsayi na musamman, ka shahara sai dai hanyoyin bi a shahara ɗin ne, ko da kasada ko ka kauce hanya.

Ta yi wa kanta alƙawarin, dole za ta bibiyi case ɗin yarinyar nan, ba naja'atu ba, ko a hannun ƙaramar hukumar bunkuren case ɗin yake, sai ta bibiya, ai da ƙananan kasada ake babba, ga kuma babban target ɗin ta, Viper, ta san idan aka kama shi, dole a sara mata, ta shiga cikin mata da suka kafa tarihi.
Da wannan gurguntaccen tunani na Nabila, mai cike da wauta da rashin lissafi, suka cigaba da tafiya can ta ce "Malam, wai haryanzu ba a zo ba?"

"Ba ki taɓa zuwa unguwar ba ne?"

Ta ce "Eh, sai yau zan fara"

Ya ce "saura kaÉ—an in sha Allah"

Sai dai gabanta ya fara faÉ—uwa, tun bayan da ta ga sun bar cikin mutane, sun fita wajen gari. Dai-dai wani gidan gona ya ajiyeta, wurin duk shuke-shuke, da alama akwai mutane a daf da wurin, amma sai an yi tafiya kan a tarar da in da suke. Shi kansa titin wurin, babu ababen hawa da suke kaiwa suna komowa a wurin.

Sai rukunin manya manyan kamfanunnuka a wurin, na shinkafa da na taki, wurin shiru sai ƙarar injinan da masana'antun ke amfani da su.

Sai da ta sallami mai a daidaita sahun, sannan ta fara tunanin, to ina ma za ta nufa?

Tsayawa ta yi, tana waige-waige, kawai ta hango wani mutum ya tunkarota, nan ta fara ja da baya, tana tunanin ko zurawa za ta yi da gudu.

"Mu je" ya ce mata a kausashe.

Ta turje ta ce "Ina?"

"Ba ke ce baƙuwar Viper ba, mu je"

A raunane cike da tsoro ta ce "A'a, ka kirawo shi mu yi magana a nan, ni dama kaya nake son saya a wurinsa"

Cikin mamaki ya kalleta ya ce "Wani irin kaya?"

"Wanda yake sayarwa" tayi maganar a tsorace tana kallon Walid.

Ya gyaÉ—a kai ya ce "Baki san waye shi ba amma? Kin yi kasada nafi muni, wuce muje kafin na saraki biyu a wurin nan"

Cikin rawar jiki ta ce "Dan Allah ka yi mini rai, ni ka kirawo shi nan kawai".

"Wallahi zan saɓa ki a ka, wuce mu je"

Salati Nabila ta din ga yi, dan tun da ta yo dakon kasadar nan, sai yanzu ta ga zunzurutun wautar da ta aikata.

Ya sakata a gaba, suka nausa bayan kamfanunukan.

A can gidan honorable kuwa, yana da office a cikin gidan sa, in da yake ganawa da mutane na mussaman.
Hankalin sumayya ya É—an kwanta, bayan da ta ga mutane na shiga suna fita a gidan, da alama ba shikaÉ—ai ne a gidan ba, kuma gidansa ne da yake zaune da iyalinsa.

A harabar gidan aka dakatar da wanda suka rako sumayya, aka ce itakaÉ—ai za ta shiga.

Wani security yayi mata jagora, zuwa wani sashe na gidan, ya kaita wani falo, ya ce ta jira a nan, ta samu wuri ta zauna, a kan kujera, tana zaune a falon office É—in, tana É—an kalle-kalle, tana jira kamar yadda aka umarceta.

Cikin office É—in kuma, Barrister Naja'atu ce suke magana da honorable.

"Ni fa na yi iya ƙoƙarina, amma da alama mutanen nan, su na da taurin kai, juyin duniya sun ƙi saduda, sai iƙrarin a karɓar musu hakkinsu suke yi, ina ga kawai a ɗauki matakin da ya dace a kan ta".

Indabo ya ce "Lallai dama haryanzu akwai masu ƙi faɗi a talakawa?"

"Akwai su fa, ku kuna gefe, mune muke shiga cikinsu da rufe bakunanansu a kan ɓarnar da ku ke aikatawa, sai dai kan mage ya fara wayewa, babban abun damuwar sun gaya mini an tabattar musu tana da ciki"

Yayi saurin É—aga kai ya kalleta "Ciki kuma? Sau nawa yayi mata fyaÉ—en ne?"

Ta ɗage kafaɗa ta ce "Wannan kuma shi za ka tambaya, ba zan iya cigaba da ɓata lokacina a kan wannan kucakan mutanen ba, ina da abubuwa masu muhimmanci kawai ayi abun da ya dace".

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Abdul, ban san lokacin da zai yi hankali ba, ina tsoron lokacin zaɓe, a samu wani ya fito da miyagun halayensa, in the next couple of years, sonake ya samu ref, ko deputy governor a tsayar da shi takara, saboda yarjejeniyar da muka yi, da jam'iyya kenan kafin na yarda na zauna a cikinta, amma al'amarin sa kullum ƙara lalacewa yake yi"

Barrister Naja'atu ta ce "To, gara dai ka san abun yi"

"Anyway, shikenan, ki tura mini address ɗin su ita yarinyar, za ayi abun da aka saba" ta miƙe tsaye ta ce "No problem"

Ta buɗe ƙofar office ɗin ta fito, kallo ɗaya sumayya ta yi mata, ta gane ta, saboda yadda Nabila take ɗora hotonta a status ɗin ta a baya.

Cikin son tabattar da abun da Nabila ta gaya mata, a kanta, ya sanya  ta tashi da sauri tana murmushi ta ce "Barrister Naja'atu Bunkure, baya goya marayu, dama zan ganki ido da ido?" Sumayya ta yi maganar tana murmushi.

Kamar ta ga kashi, ta yatsuna fuska ta ce "Sannu".

Sumayya ta maze ta ce "Na tsinci dami a kala yau, ni Æ´ar jarida ce, a cikin ayyukan da ki ke gudanarwa, zan so yi miki tambaya É—aya zuwa biyu, na san masu sauraronmu, za su ji daÉ—in hakan, kasancewar ki abar so da koyi ga al'ummar mu, mussaman mata. Dan akwai sister na, die hard fan É—in ki ce, ita ma lawyer ce.

Cikin fusata Naja'atu ta ce "Ke saurara mana, daga ganina sai tsare ni ki hau zuba dan kina Æ´ar jarida, who permits you to do that?"
Chapter 28 · 0% Book details