Sashe 70
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Halimatu ta zauna kusa da ita ta ce "Anty jauhar dan Allah ki daina kuka, zaki yi rashin lafiya " tayi maganar tana goge mata hawaye. Akwai shaƙuwa sosai a tsakanin jauhar da yaran layin, wasu ma ko iyayen su ba ta sani ba, amma su tana hulɗa da su, ta yi wa matan kitso, ta koya musu karatu idan tana da abinci ta ba su, ko 'yar alewa ko abun kusa da baka, shiyasa suna son taruwa a gidan idan master baya nan, sai dai rashin walwala da ba ta yi yanzu ya sanya duk suka watse suka daina zuwa.
Baban su halimatu ya dawo, dama juahar na tsakar gida, ta gaishe shi ya amsa sama-sama, ya shige falo, ya fara ƙwalawa salamatu kira.
"Baban halimatu sannu da zuwa "
"Me matar mutumin nan take yi mini a gida? Haka kurum da tsinannen kwashe-kwashenki, ki janyo mana masifa muna zaman lafiya"
Cikin takaici ta ce "Haba dan Allah, menene a ciki, tana zaune ita kaÉ—ai cikin damuwa shiyasa na ce ta shigo, amma ka san haka kurum ba mai shige-shige ba ce ba".
"Ke ki ka sakata a damuwar da zaki cirota, ambulance uwar taimako "
Jauhar na jin su sama-sama, ta tashi ta É—auki mukullin gidanta, ta fice ta koma gida.
Jauhar ta kama addu'a iya yin ta, su liti fafur sun ƙi gaya mata kotun da ake yi wa Al'amin shari'a, kuma suka ƙi gaya mata prison ɗin da yake.
Baba yana karyawa da safe, ya ga kiran waya da baƙuwar lamba, ya ɗaga ya ɗan yi gyaran murya yayi sallma.
"Wa'alaikum Salam, barka da safiya baba".
"Yauwwa barka dai, da wa nake magana?"
"Alhaji mu'azzam ne baba, ina ƙofar gida na zo, na ce Allah ya sa ba ka fita ba".
Jikin baba yayi sanyi, ya ce "Ahh ina nan ban fita ba tukuna, ashe ka dawo"
"Eh baba na dawo"
"To gani nan"
Ya miƙe zai fita, mama ta ce "Ina zaka kuma kai da waye?"
"Baƙo" ya bata amsa a taƙaice.
Ya fita tsakar gida, hafsa ta shirya za ta tafi makaranta ya ce "Ke haryanzu baki tafi makarantar ba me ki ke yi?"
"Ba ni da lectures ne da wuri, shiyasa yanzu zan tafi"
"To Allah ya tsare" ta amsa da amin.
Baba ya fito suka gaisa, ya ce "Malam mu'azzam ka dawo ashe?"
Cikin girmamawa ya ce "Eh baba, na sameku lafiya?"
"Alhamdilillah"
"Masha Allah, baba tun ina china na samu wani labari, hankalina duk bai kwanta ba, na yi iya ƙoƙarina wurin dawowa, baba ko wani laifin na yi ka hana ni auren jauhar?"
Baba ya girgiza kai ya ce "Wallahi ko ɗaya, kawai dai ka san matar wani ba ta auren mijin wata, Allah bai ƙaddara aurenku ba, ina mai baka haƙuri, na yi maka laifi ban kyauta ba, da kuɗin aurenka a hannuna na aurar da ita, amma ka yi haƙuri dan Allah"
A razane ya kalli Baba ya ce "Aure aka yi mata?" Baba ya jinjina masa kai a sanyaye ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
Hafsa kuwa har ta sako kai za ta fita, ta hango Alhaji mu'azzam, ta koma cikin gidan da gudu, ta samu mahaifiyarta a É—aki ta ce "Anty, saurayin nan na jauhar ne ya zo, Alhaji mu'azzam gashi can da baba a waje"
A sukwane ta tashi ta ce "Haba dai?"
"Wallahi da gaske nake"
"To maza É—auko kayayyakin nan ki yi amfani da su ki fita kafin ya tafi"
Can kuwa Baba sai haƙuri yake bashi, yana yi masa nasiha, dan shi bai san ma an yi mata aure ba sai yanzu, gaba ɗaya ya shiga damuwa, aƙalla zai bawa jauhar shekara ashirin da wani abu, ya girmeta nesa ba kusa ba, sai dai ta shiga ransa sosai da sosai, duk da ya sha yinƙurin ƙara aure a baya, amma matarsa tana hanawa, bai taɓa shiga damuwa na rashin wata ba sai jauhar, kamar ya zubar da hawaye haka yake ji.
Jiki a sanyaye ya ce "Shikenan baba babu damuwa, na gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya basu zaman lafiya da zuriya É—ayyiba".
Baba ya amsa da "Amin"
Suka yi sallama, ya shiga motarsa amma ya kasa tuƙin, ya kifa kansa a sitiring motar, yayi shiru ya ji gaba ɗaya duniyar tayi masa wani iri, babu irin zargin da bai kawo a ransa ba, na dalilin hana shi auren jauhar.
"Malam ya dai" da sauri ya É—ago kansa ya ce "Jauhar"
"Ba ita ba ce, yayarta ce, tun É—azu na ganka a nan baka tafi ba, lafiya?"
"Yauwwa Alhamdilillah, dan Allah in tambayeki mana?"
"Ok, Allah ya sa na sani" tayi maganar tana sake gyara tsayuwarta cikin iyayi.
"Ko kin san dalilin da ya saka aka fasa bani aurenta, tun da kin ce ke yayarta ce"
"Eh to, rashin ji ta fara yi, baba ya yanke shawarar aurar da ita kawai, tun da baka nan"
Alhaji mu'azzam ya ce "Wani irin rashin ji?"
"A tunaninka wane rashin ji mace za ta yi, a aurar da ita babu shiri?"
Cikin matsanancin mamaki ya ce "Jauhar É—in?"
Hafsa ta ce "Ita fa, ko dan kana ganinta a haka? Dama ba sonka take yi ba, akwai wani saurayinta ɗan daba, da ta ƙallafa rai a kansa, ta fara rashin ji, kawai baba ya aurar da ita, ai ka ga ba zai gaya maka haka ba" yayi shiru yana kallon hafsa, kawai ya ji maganganun nata ba su shige shi ba, ya gyaɗa kai ya ce "Shikenan, Allah ya basu zaman lafiya"
Ta ce "Amin, dan Allah ko zaka sauke ni a hanya, school zan tafi ko a titi ne sai na sauka na samu abun hawa?"
Ya ce "Bakomai bisimillah"
Jauhar ta idar da sallar la'asar, ta ga kiran walid a wayar Viper, ta tashi ta ɗaga da sauri, suka gaisa, ya ce "Wani tunani na yi, akwai uban gidansa da muke yi wa aiki, ɗan majalisa ne, sai dai Viper ne kawai yake iya samunsa kai tsaye, na ce ko wurin P.A ɗin sa zamu je, ki gaya masa dan ni ba shiri muke yi da shi, na taɓa marinsa idan mu ka je da ke wataƙila su saurareki".
Cikin É—oki ta ce "To shikenan, Allah ya sa dai su fito da shi É—in" ya amsa mata da amin.
Hafsa kuwa cike da salo da kisisina, da tasirin sihiri, sai da ta karɓi lambar Alhaji mu'azzam, har bakin department ɗin su ya kaita, sai dai idan zai yi mata magana sai ya kirata da jauhar, sai dai hakan bai dameta ba, lambarsa kawai da ya bata, ya sanya ta din ga jin kamar ta ma riga ta aure shi an gama.
Tun safe jauhar ta shirya, ya din ga kiran wayar Walid da ta liti, amma ba ta shiga, tun tana saka ran za su zo, har ta fara sarewa, sai azahar walid ya zo, kamar ta yi masa kuka ta ce "Tun safe nake kiran wayarku, ina jiranka amma shiru ba ta shiga"
Walid ya ce "Ai wayar nan ta sa ma kawo ta zaki yi"
Cikin mamaki ta ce "Saboda me?"
"Akwai dalili, yanzu idan kin shirya ki zo mu je can wurin P.A É—in ki gaya masa, da mun je shiga zaki yi, mun gama magana da wani yaronsa" ta ce "To"
Suna tafe tana yi masa magiyar, dan Allah ya kaita ta ga master, amma ya ce "Shi fa ya ce kar a kuskura a kai ki, yanzu idan muka kai ki tijara zai yi mana".
Cikin damuwa ta ce "Haushina yake ji, ba ya son ganina ko?"
Ya ce "Gaskiya ba na ce ba, ya ce dai kar a kuskura a kai ki, kuma ranar Litinin zaku fara jarrabawa, ki je ki fara"
Mamaki ne ya kama ta, ya aka yi ya san lokacin da za su fara jarrabawa?
Tayi ajiyar zuciya ta ce "To yaya jikin sa ya warware?"
Walid ya ce "Eh ya warke"
"Ina nan ina É—an haÉ—a 'yan kayayyakin abinci, sai in baka ka kai masa"
"Kar dai ki takurawa kanki"
Jauhar ta ce "Ban takura kaina ba, amma dan Allah idan ka je ka ƙara bashi haƙuri, wallahi laifina ne ban gaya masa an kawo abun ba, kuma mantawa na yi"
Ya ce "Manta kawai, dama Allah ya riga ya ƙaddara faruwar hakan".
Suna zuwa ofishin, ba su wani sha wahala ba, aka shiga da Jauhar, ta gaishe shi ya amsa mata, ya ɗan ƙare mata kallo ya ce "Kamar na taɓa ganinki"
Jauhar ta ce "Eh, akwai ranar da na je wurin mijina, na tarar ka je kai da yaya walid an fito da shi a police station".
"Oh matar mai zamani ce, Viper?"
Ta jinjina masa kai ta ce "Eh nice"
Ya ce "Allah sarki, ya gida ya fama da rigimammen mijinki"
Tayi murmushi tana wasa da yatsun hannunta.
"Yaya aka yi?"
Jauhar ta sauke numfashi ta ce "Dama, mijin nawa aka kama, har an kai shi prison an ƙi sakinsa, shi ne na ce bari na zo wurinka dan Allah ko zaka yi wa honorable magana, ko za a fito da shi"
Ya girgiza kai ya ce "Al'amin ba zai canza hali ba, me kuma yayi a wannan karon?"
"Ba laifinsa bane, abu aka kawo aka ce na ajiye masa, ban san ko menene ba, kuma na manta ban gaya masa ba, jami'an tsaro suka zo suka yi bincike cikin dare, suka kama shi, wai sun ga hodar iblis a cikin kayan"
Cikin mamaki ya ce "Hodar iblis kuma? A ina ya sameta?"
"Ai ba shi ne ya kawo ba, ba ya ta'amalli da ita"
"Taɓɗijan, a wannan karon case ɗin babba ne, bari na kira honorable duk da ba ya gari".
Ya kira honorable Indabo, ya sakata a hansfree tana jin duk abun da suke faÉ—a, suka gaisa. P.A ya ce "Honorable, mutumin ka fa ya janyo babbar jagwal ga matarsa nan a gabana ta zo a taimaka mata a fito da shi"
"Wa kenan?"
"Ma dogon zamani mana"
Indabo ya ce "Kuma dai? Me kuma yayi?"
"To wai hodar iblis ce, aka kama shi da ita?"
"What! Coacine? Yaron nan yana da hankali kuwa, a ina ya samu coacine kuma?"