Sashe 53
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Al'amin ya ce "Ita ce matar gidan fa"
"Kai haba maza, wannan É—in?"
"Yarinyar da ta suma, na ce ka saka a kaita Asibiti"
Walid ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maza ka sha kwana wallahi, dama ita ce, kaga rabo, wata 'yar caras beauty ka ji muryarta".
"Kai dalla malam, ka buga mata ƙofa, ka ce ta duba in da na tashi, na bar leda ta baka, ka tsaya shirme".
Walid ya ce "To meye na yi mini masifa kuma, na ga dai auren dole aka yi maka" katse wayar walid ya yi, yayi ashar ya ce "Ina da wannan, ai kan a ganni a ƙofar gida, sai an sha wuya, kai Aminu kamar ba biladam ba" yayi maganar yana bubbuga ƙofar gidan.
Kamar ba zata buÉ—e ba, ta sake buÉ—ewa cikin mamaki ta ce "Malam lafiya?"
"Ya ce ki duba in da ya tashi, ya manta leda ki bani"
"Shi wa?"
Cikin mamakin yadda take neman raina masa hankali ya ce "Maigidan"
"Dan Allah ka yi haƙuri, bai bar mini wannan sallahun ba"
Ya ce "Saboda bai bar miki sallahu ba, ba zaki bayar ba?"
Ta marairaice ta ce "Idan na baka ya dawo, ya ce mini ba shi ya aikoka ba, kaga bani da abun da zan ce masa".
Ya ce "Gaskiya ne, shikenan" ya juya ya tafi, ta mayar da ƙofar ta rufe.
Duk da kayan suna da nauyi, haka ta zage ƙarfinta a kan kayan nan, ta wanke su.
Sai a lokacin ta kalli window, ta ga mpn da ta É—aukko masa ta ce "Na shiga uku, da ya ganta fa me zan ce masa?" Ta É—auka ta mayar masa É—akinsa
Al'amin kuwa duk in da ya juya, sai dai ya yi gyatsa saboda yadda ya ƙoshi.
Walid ya je ya samu Al'amin, ya din ga yi masa mitar yadda jauhar fafur ta hana shi saƙon nan. Yayi ya gama, bai ce masa komai ba, sai sakace da yake yi, yana cigaba da jin ƙamshin miyar da ya ci a hannunsa.
"Yanzu mai zamani shikenan yau b za a sayar da kaya ba? Saboda ka yi aure 'yar yarinya ta hana aiki yau?"
Al'amin ya kalle shi ya ce "Ƙila"
Yayi tsaki ya ce "Yauwwa, na haÉ—a maka da mp É—ina a kayanka, ka kawo mini kayata kafin ita ma ta ce taka ce ba zata bayar ba"
Al'amin ya tuna ya ganta a kan window, kuma ya ga yadda ta gyara masa É—akin, ya tabattar É—auka tayi ta kunna.
A ransa ya ce 'Ashe ba tsoron ki ke da gaske ba'
"Malam magana nake yi maka, a kawo mini mp É—ina. Yunwa ma nake ji, ko zamu je cin garau-garau ne?".
Aminu ya miƙe ƙafa ya ce "Sai ka dawo"
Walid ya fice yana tunanin asarar da za su yi, na rashin sayar da kayan nan yau, ya san ko zasu dambace da Al'amin, ba zai koma gidan nan ya É—aukko kayan ba.
Ƙarfe tara na dare ya shiga cikin unguwar, tare da su liti, da Walid, sai dai ba su shiga cikin gidan ba, suka zauna a barandar kusa da gidan, suka din ga hira suna shaye-shaye.
Jauhar kuwa kamar a cikin falonta suke shaye-shayen, saboda yadda duk gidan ya gauraye da wari.
Yau da gari yayi haske ta fito, a falo ta tarar da shi, a kwance a kan doguwar kujera.
Ta durƙusa ta ce "Yaya ina kwana" waiwayowa yayi ya kalleta ya kawar da kansa, sai dai ba ta tashi ba.
Har ta fitar da ran zai amsa ya ce "Lafiya"
Ta miƙo masa leda ta ce "Ga abun da ka manta jiya, wani ya zo ya ce ka aiko shi, ni dai ban bashi ba. Na ga kamar ganyen shayi ne, ko na ɗiba na dafa mana tea?" Afujajan ya kalleta, tashi ya yi zaune ya ce "Da me zaki dafa tea ɗin?" Ta nuna masa ledar tana sunkuyar da kai ta ce "Naga kamar ganyen shayi ne, sai na dafa mana ko jallof ɗin taliya ce?"
"Wiwin zaki dafa a matsayin shayi, saboda mahaukaciya ce ke?"
Da sauri ta kalleshi ta saki ledar da sauri, sai dai ba ta ji daÉ—in mahaukaciya da ya kira ta da ita ba.
"Dan Allah ka yi haƙuri, ban sani bane".
"Jiya mai laya ya zo, ya ce miki yana neman mai dogon zamani, kin ce ke baki san shi ba, to ni ne mai dogon zamani, idan kuma jami'an tsaro ne suka ce miki Viper ni suke nema, idan ki ka cigaba da yi musu rashin kunya kuma, za su sassaraki ne a banza su bawa karnuka namanki"
Shagwaɓe fuska ta yi zata yi kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ka bashi haƙuri, ba zan sake ba, dama ban san me zai yi maka bane, shiyasa na ce masa ba kai bane ba shiyasa"
Ya saka hannu ya É—auki ledarsa ya tashi zai fita ta ce "To karin kumallon fa" ko waiwayowa bai yi ba, ya fita.
Bayan fitarsa, ta je ta kwaso kayansa da ta wanke, ta ninke su tsaf, ta shiga ɗakinsa, tana shirya masa kayan, ta fito masa da guda ɗaya da zai saka, ta ɗaukko bedsheet tana canzawa katifarsa, kawai ta yi karo da wata irin zabgegiyar wuƙa.
Gabanta ya faɗi wuƙar kawai abun tsoro ce.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, jikinta na rawa ta hau kuka, ta kai hannu za ta É—auka"
"Idan ta ji miki rauni, ke ki ka sani".
A razane ta É—ago jikinta na tsuma.
"Fita ki bar mini É—aki, bincike ki ke yi mini ko?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a wallahi, bedsheet zan canza maka na ganta, ba bincike nake yi maka ba"
"Fita to"
Ta ce "To, ga kaya na fito maka da su, wanda zaka saka".
Ya sake tsuke fuska ya ce "Ki fita na ce"
Ta zo fita, ta kasa saboda yana tsaye a wurin.
Yayi tsaki ya bata hanya, ta fita har da tuntuɓe, a tsakiyar falon ta ga ledar buredi, da sugar da madara da Lipton.
Ta lallaɓa ta fita ta kunna gas, ta ɗora shayi.
Buga gate ɗin gidan ake yi da ƙarfi, ba shiri ta tafi ta buɗe.
Wani matashin magidanci ta gani, a tsaye ya kima uwar hula, ya rufe kunnuwa.
Ta gaishe shi cikin ladabi, ya ce "Ina matar gidan?" Mamaki take yi, meyasa mutane suke neman matar gidan idan suka ganta.
"Lafiya?"
"Eh, megidan muke nema? Sunana malam lawan, ni ne mai wannan gidan na kusa da ke"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, baban su halimatu? Ai suna shigo mini".
"Eh, mai unguwa yana neman mijinki, ƙararsa muka kai"
Ta ce "Subhanallah, laifin me yayi muku?"
"Au jira zamu yi sai ya yi kan mu É—auki mataki, an ce mana mutumin banza ne, kuma da ya zo bai yi mana sallama ba, bamu san da wani irin mutum zamu zauna ba, jiya an hanamu sukunk da warin wiwi, ya tara mana 'yan iska a layi. An gaya mana gawurtaccen É—an daba ne da ya addabi in da yake, aka yi masa aure mu aka kawo mana bala'i. Gara aje a zauna da mai unguwa da 'yan sanda, ko ya tashi, ko ayi yarjejeniyar zaman lafiya da shi".
Jauhar ta ce "Haba malam, bai yi muku komai ba kuma sai a kai shi wurin 'yan sanda, ina laifin mai unguwar ma, in sha Allah ba zai sake sha muku komai a layi ba, kuma ba zai cutar da kowa ba ma. In sha Allah wataran sai labari zai daina".
"Ke rufe mini baki kan na kwaÉ—e ki, nasiha zaki yi mini, ba zamu zauna da mutumin banza da wofi ba wallahi, ya lalata mana yara haka kurum ba"
Motsi ta ji a bayanta, tana waiwayawa ta ganshi a tsaye, ashe duk ya ji abun da malam lawan ke faÉ—a.
Da sauri ta leƙa ta ce "Ka tafi kar ka bari ya ganka"ta waiwayo ta rufe gate ɗin tana kallonsa.
"Ya tafi kar ya bari na ganshi ko? To ke bari na yi miki abun da zan yi masa".
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Kafin ta yi wani yinƙuri, ya janyeta daga jikin gate ɗin, sai dai kasancewar ba ƙwari ne da ita ba a kansa, sai da ta kai ƙasa.
Ya buɗe ƙofar ya lelleƙa, bai ga kowa ba, tuni malam lawan ya ɓace.
Ya dawo ya kalleta, ta sunkuyar da kai, sai murza yatsan ƙafarta take yi, da yake yi mata zafi, saboda faɗuwar da ta yi.
Ƙwafa ya yi ya wuceta, ta lallaɓa ta tashi, ta shiga kitchen ta ɗora tea, ta ɗebi miyar nan da su Anty lubabatu suka kai mata, ta ƙara gyarata ta zuba ta kai masa falo.
Ya wani maze yana basarwa, nan kuwa jira yake yi, tayi ta kawo masa ya ci.
Sai dai yadda yake cin abinci ya goge mata a jikin kujera, ko carfet yana damunta, sai dai idan ya gama ya tashi ta goge.
Dan haka ta sayo toilet paper, take haɗo masa da ita, amma ko kallonta ba ya yi, idan Allah ya taimaketa ne, wani lokacin sai ya goge a jikin kayansa kamar wani ƙaramin yaro.
Da daddare kuwa kullum, sai ya cika gidan da warin sigari, wasu lokutan ba zai dawo ba, sai sha biyu na dare, ya shige É—akinsa yayi ta shaye-shaye, da safe kuma idan ta ajiye abinci zai ci, idan ba ta ajiye ba ba zai tambaya ba, kuma ba zai sayo ya kawo ba.
Idan za ta gyara masa ɗaki sau goma a rana kuwa, muddin ya shiga sai ya watsar da komai ya ɓata, yayi shaye-shayensa ya bar mata toka da sauran karan sigari duk a ɗakin.