← Book details Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 79

Sashe 68

Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da misalin arfe takwas da rabi na safe, motar Najlah ta yi parking a bakin babban gate na barrack in DSS Barracks, fitowa ta yi sannan ta nufa bakin babban get hannunta ri e da wannan jakkar. Jami an dake tsaro suka mi e cikin girmamawa bayan ganin ID card inta. Officer Hafsat Abdullahi?. aya daga cikinsu ya tambaya. Ta gyara tsayuwarta cikin alfahari da jin kanta a yau. Yes. Welcome to the barrack, Madam. suka sara mata, itama ta sara musu sannan suka bata hanya ta shiga ciki. Wow. shine kalmar da ta furta tana kallon ko ina na cikin Barack in, Komai yana da tsari kamar an zana shi da layi. Gidajen sojoji suna jerin gwanin tsari, babu hayaniya sai arar takun afafun jami ai da ke wucewa cikin gaggawa. A nesa, ana jin umarnin horo yana tashi sama na wasu tarin sojoji da suke parrade. Left! Right! Left! Right! Sojoji suna motsi cikin tsari, gumi na zuba a fuskokinsu amma babu wanda ke nuna rauni. Najlah ta sauke numfashi a hankali. Tasan cewa daga wannan rana, rayuwarta ta fara da wani sabon babi babin da babu ja da baya. A nutse ta aga kai sama a cikin ranta tana ara gode ma Allah bisa wannan baiwa da ya yi mata, daga nan ta kalla hanyar da za bi kafin ta ci gaba da tafiya. A natse take tafiya amma sautin takalmanta kawai ake ji a wajen saboda wajen interlock ne a malale kaf kaf abin da ya sa wasu jami ai dake wucewa suka juya suna kallonta. Wasu na mamakin kyawunta, wasu kuma na kallon nutsuwarta da yarda take tafiya sak soja a gaban shugabannin sa. Amma ita ko a jikinta, haka fuskarta cike take da confidence irin na gogaggun jami Da ta isa babban office in shugaban barrack, ta tsaya cak a bakin ofa, a jikin office din an yi wasu rubutu akai *General Barkono* shine a rubuce, da haka ta yi knocking sau biyu. Come in. wata kakkausar murya ta amsa daga ciki. A hankali ta shiga ta tsaya, sara mai ta yi, tana mai murmushi dan ba wannan bane ha uwar su ta farko. Officer Najlah reporting for duty, sir. Wannan mutumin mai cike da izza cikin uniform din da suka ara mai yau, ya aga kai yana kalleta na wasu da u kafin ya nuna mata kujera. Sit down, Officer Najlah A.B.D. ta zauna cikin nutsuwa, tana tunawa da mahaifinta General A.B.D. Sai Barkono ya mai da hankalinsa gaba aya kanta. A karo na farko da tawagar Black shadow suka nema a tura musu ke, suna bu atar ki a aikinsu.....kinyi sa'a sosai, dan kuwa jami'an sirrin hatta hukuma bata da information a kansu, suke da information din kowa, sannan umarni daga shugaban asa kawai suke samu, suna nan suna yawo kamar kowa sai dai babu wanda ya sansu, a haka suke aikinsu, shekara biyu da fara aikinsu, kuma kowani irin aiki suna kammala shi cikin an lokaci ka an........sun tabbatar da warewarki shi yasa suka za eki a cikin jerin sojoji dubu dari hu u da aka auka a gaba aya asar nan cikin wannan shekarar." Da haka ya nunfasa sannan ya dasa. Ni kaina zanyi alfahari idan har kika shiga wannan kurunin, su dan asa suke aiki ba dan wani abu ba, suna jefa kansu cikin hatsari domin ceton al'umma, nasan kin san komai akan aikin nan da kuma *Black shadow*." Kai ta aga tana sauke numfashin a natse. in da awa ke ar abokina ce General A.B.D, jarumin Namiji, shi kika Gada ai, naga videon traning na ku, gaskiya kin horu sosai." Murmushi ta yi tana sinne kai. Thank You Sir." You are welcome Dear. Da haka Barkono ya bu e drawer dake gefansa sannan ya fito da wani jan file mai auke da alamar *CLASSIFIED* ya ora file in a gabanta a hankali. Wannan shine aikin farko da aka baki tun zuwanki Abuja. Najlah ta an kalli file in kafin ta ago idanunta. Aiki ne mai ha ari? ya sake fa a a natse, murmushi ta an yi ka Tura file in gabanta ya yi. Target in ku shine *Black Dragon*, komai yana ciki, sannan shugabanki zai miki arin bayani. ta aga kai gana bu e file Sunan Black Dragon ka ai ya isa sanya manyan jami ai cikin fargaba, balle ace an baka aiki a kansa... amma ita, a hankalin a kwance ta bu e file in da hannunta, ta duba sannan ta mai da ciki. Thank You Sir." Ta fa a tana mi ewa tsaye. Yauwa, daga yanzu bake babu sanya wanna kayan har sai kunyi nasara, daga lokacin za'a bu e miki office inki, idan kuma kinfi bu atar zama cikin *Black shadow* shike nan. Ta jinjina kai sannan ta sara mai again. Sir an bani lasisin aiki da makaman da aka turo min gida, shin zan iya amfani da su wajen gyara arna.?" Murmushi ya yi. An baki, sai dai kowani irin aiki ne, ya zama baki bar hujja ba, aiki da basira shine aikin ku." Sake sara mai ta yi tana imagine ta kan Anas za ta fara aiki. Da haka ta nufa bakin ofa, hannunta yana kai handle ta ga an bu e, sannan wani matashi ya bayyana. Suna ha a ido, ya sara mata yana murmushi ganin kaman ta an tsorata. Al-hassan yarinyar A.B.D ce, a nan take aure." Cewan Abbeey yana kallon Al-hassan. Laaa ashe sister ta ce, wata rana za ki kawo mana ziyara har gida ko?. murmushi ta yi. Sosai ma kuwa." Da haka ta wuce, shi kuma ya arasa ciki yana sake gaishe da Abbeey. Zama ya yi yana shafa sunan kansa. Abbeey gani." Abbeey ya kallesa da yau sannan ya ce. Tambayarka zanyi akan Al-hussain, ina da tabbacin kai za kafi sanin komai kunfi kusa sosai. Abbeey kenan da daane zance haka ne amma banda yanzu da Ni kaina bana gane masa, kuma abinda Al-hussain in ya fa a gaskiya ne, wajen aiki biyu yake zuwa, duk na bincika ance yana zuwa, kawai lokacin neman ku in nasa ne ya zo, sai na shi ya zo da yawa." Murmushi Abbeey ya yi. Yanzu ka same shi a wajen?. kai ya girgiza. A'a amma yana wajen Marwa." Shike nan tafi aikinka. sallama da haka suka yi sannan Al-hassan ya wuce wajen aikin sa. *Marwa* A hankali afafunta suka shiga cikin ajinsu, idanunta na kan littafi hakan yasa ba ta an kara da mutumin dake gabanta ba, karo ta yi da kafa arsa hakan yasa ta yi baya littafin na fa asa, da sauri kuma ta kalla wanda ke gabanta jin amshin turaren Al-hussain. Cike da mamaki take kallonsa har tana yafta ido, ta rasa me za ta yi farin ciki ko akasin haka, dan ya shammaceta sosai. A..... Al-hussain." Ya aga mata yana bu e mata akan ta rungumesa kamar dai yarda ta saba. Matsawa ta yi tare da rungumarsa, duk kuwa da ajin cike yake da mutane sosai, Marwa tana shiga jikinta ta yi murmushi dan tunawa da Al-hassan, da shine da yanzu sanyi na ratsa jikinta. Al-hussain murmushi ya yi yana jin sanyi na ratsa duk argon dake jikinsa, karo na farko kenan da Marwa ta rungumesa, tabbas ya ji da in haka sosai. Dama yau ya ce zai mata surprise, shi yasa duk abinda ke gabansa ya aje dan zuwa wajenta. Ihun an ajine ya dawo dasu duniyar zahiri, dan kuwa kowanne su da tunanin da yake yi. Murmushi suka yi suna sakin juna, Marwa ta harara wacce ke musu video tana wa I need your love, I need your time....... Al-hussain ya ja hannun Marwa suka yi waje ana ta musu dariya. Sun au lokaci suna hira, kafin ya barta ta rubuta exam, ya mata sallama, tana komawa aji, ya kalla agogon hannunsa, da haka ya yi murmushi yana shiga mota. Be tsaya a ko ina sai *Primecare Hospital*, kallon asibitin ya yi sannan ya auki facemask ya sanya, da haka ya saba wannan jakkar ya shiga cikin asibitin bayan ya sa p-cap. Akwai mutane sosai, kuma duk saboda Senator Tum a ne, murmushi ya yi sannan ya ciro wani wu a a aljiwunsa, hannunta na hagu, ya daba, sai ga jini ya fara fita, da kansa ya kara girman ciwon sannan ya nade da wani farin yalle, take jikin gyallen ya fara ji ewa da jini. gefe-gefe ya dinga ra awa har ya kusa shiga ciki. Hannusa na dama ya dam e na hagu, ya shiga kiran Nurse's Dan su bashi kulawa, ai duk wanda ya ga wannan jinin sai ya ru Nurse's biyu suka yi kansa da gudu, sannan aka nufa wani waje da shi. Nurse's suka duba ciwon suka mai dressing, sannan bashi magunguna. Thank You." Ya fa a yana tashi a hankali, su kuma suka bishi da kallon tausayi. Yana fita maimakon ya yi asa, sai ya nufa Aminity word, yana ganin wani Nurse ya kirasa. Toilet zan shiga, ina so ka taimaka min, jiri nake ji ga wannan ciwon." Ya fa a yana nuna hannunsa, saurayin cikin tausayi ya dafa shi suka shiga toilet Second 1....2.....3.......zuwa minti 5, sai ga Al-hussain ya fito cikin kayan Nurse din nan, ya mai da faskmask insa, sannan ya ri e jakkarsa da ya mai dashi akwaiti yana ja, dan jakkar yana da tayoyi, tray in hannun wancan Nurse in, shi ya ri e a nasa hannun sannan ya yi wani shu'umin murmushi yana nufan akin da aka kwantar da Senator Tum a, duk da kuwa ga Sojoji biyu da suke bakin ofar ri e da bindigu........... Yana isa wajen jami'an sai ya yi arin shiga, suka dakatar da shi. Dr. Ashraf ne kawai mai iya shiga ciki." Cewan soja guda aya. Okay shi ya aikoni amma bara na kirasa." Da haka ya matsa gefe, da le ansa ya fara furta. 1,2,3,4,5. sai ya lumshe ido, yana bu e wa, sautin harbe-harbe suka fara tashi a cikin asibitin, nan fa asibiti ya ru e, da sauri Sojojin nan suka yi waje, suna barin wajen Al-hussain ya shiga akin sannan ya rufe. Mutanen da suke haraban asibitin suka ru e jin harbe-harbe, nan kowa ya fara neman wajen uya, amma a haka an harbe
Chapter 68 · 0% Book details