Sashe 21
Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
komai amma baya kuwa, akwai su masu tudu da cika ido. Sai Basma ta ce. Ke fara ke ce mai girki, daga Kitchen sai akin kwanan ku, ke kuma ba ar ke za ki dinga jerawa a falon nan, sannan sanya hijabi har asa wajeeb ne, zan sa a din o muku Hijab da kayan aiki, sannna idan wani abu ya ha aku da Abba, na ku bin umarni ne kawai, bance kowacce ta mai magana ba, ku zama kamar bebaye idan yana nan, bansan wasa da aiki, in mutum na son ya jima da mu, to tabbas ya bi doka ya zauna lafiya. Abu na arshe kuma ba wai na baku aiki bane, sai na ga yanayin aikin naku, ku kasance masu tsafta da iya girki, ku shiga da kayanku wancan akin, sauran bayanai kuma zan ara sa muku." Ta kai nan tana nuna musu angaren su, godiya suka hau sosai sannan suka nufa in da ta nuna musu. Kin iya za e, dan kuwa tun da na kallesu a biyun nan na fi ba da za ki za sai ta kalla Marwa ta yi murmushi. Allah yasa karsu ba da matsala, dan a halitta sunyi, saura a aiki. Kema ina fatan sun miki?. ta yi tambayar tana mai da idanunta kan Fauza wacce ba ta jima da saukowa ba. Kai ta aga tana cewa. Zan sa ido akan tsaftarsu in ya yi shike nan. Ok, bara na sallame wa'incan ti a-ti an Mutanen." Da haka ta mi a ta fita, Fauza kuma ta mi e ta kunna t.v tana aukan remote.......... Abba yana shiga room insa, sai ya murza ma ofar bedroom insa key, abin da be ta a yi ba. Zama ya yi gefan bed sannan ya auki wayarsa ya yi copying number sannan ya shiga contact ya yi pesting number ya danna kira, yana fara ringing ya ji wani sanyi ya mamaye mai zuciya, ya lumshe ido, ya auki pillow ya rungume tana ta murmushi dai, wayar ya katse sannan ya sake kira yana jero addu'a akan Allah yasa ta auka, kiran har ya kusa katsewa sai aka yi picking. Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya jinjina da gadon yana mai yin sallama cikin tausasa murya. Assalamu Alaikum warahmatullah." A natse kuma cikin shigar sha a wanda Abba ya ji tasirin har cikin zuciyarta ta amsa. Wassalamu alaikum warahmatullah." Sai ta yi shuru, shi kuma ya yi gyaran murya sannan ya kuma cewa. Ya jikin Najlahh?." Alhamdullah, wake magana dan ban gane muryan ba." Sai ya shafa suman kansa sannan ya ce. Abokin kine, a wajen General na samu number ta ki. ............. angaren Najlah kuwa, tana kwance ne take amsa wayar, jin abin da ya ce yasa ta zaro manyan idanunta ta ce. Laaa kaine?, Ya na ji muryanka ya ara za i." Ta fa a tana murmushi, shima murmushi ya yi. Kin iya zolaya wallahi, muryan tawa da yake kama da dukan durom shine akwai da Hmm sosai yana da shi, fiye da yarda kake zato. sai ya yi dariya. To ya jikin an ce kunsha dambe, kuma har kin barshi a kwance. An fa a maka Ni ta wasa ce? Ai ka an ma ya gani, sai ma na koma next week, zan je na fama ciwukan da suka fara warkewa. Kai Najlah, mugunta babu yau, ya kamata ki dinga jin tausayi mana." Aboki kenan, sam banda tausayin azzalumai, kasan Allah saboda haka nake kallon fina-finan Korea da Chinese." Sai ya murmusa. India fa?. Ina kallo sosai shima, dan sun iya soyayya mai shiga rai. Sai Abba ya gyara zama sannan ya ce. Kina soyayya kenan?. ya tambaya yana jin gabansa yana sauya duka. Soyayya, uhmmm ban fara ba saboda har yanzu ban samu wanda ya min ba. tana jin sautin da ya sauke. To wani irin saurayi kike so?." Sai ta yi dariya mai sanyi. Zan fa a maka amma ba yau ba, amma me yasa ka nema numberta kuma ka kira?." Yana jin tambayar sai ya rintse idanunsa sannna ya bu Ban iya oye- oye ba sam, tun a ranar da idanuna suka sauka a kanki na rasa natsuwa ta gaba aya, hakan yasa washegari na kuma zuwa dan ganinki, cikin ikon Allah na samu damar da muka yi magana mai tsayi, sa'anan yau na kira General da ya ha ani da ke a waya...........bansan ya zan kira yanayin da nake ji ba, amma ina son na dinga ganinki a kusa da ni, kallonki na sanyi nisha i fiye da misali........sai dai Ni tsoho ne, nasan na yi miki tsufa. ya kai maganar cikin wani irin yanayi. Najlah mamakin maganarsa ta yi duk da kuwa a iya firarsu ta fahimci yana sonta ne. Uhmmm matarka fa to?. ta tambaya tana lumshe ido. Matata ta jima da rasuwa, a alla za ta kai shekara 8-9 haka, sannan ina da yara mata uku, kuma sun girma, a kodayaushe suna iya aure su barni, wallahi Najlah zan kula da ke kamar wai, zan tarairayeki har zuwa mutuwata, ba zan miki dole ba, saboda nasan Ni ba sa'an aurenki bane. Uhmmm na ji, amma sai dai na baka ha uri gaskiya, bazan iya aurenka ba, duk da kuwa bani da burin da ya wuci na auri babban mutum mai cikar kamala kamar dai kai.........sai dai har ga Allah ba zan iya aurenka ba. ta kai arshen maganar cikin sanyi, shi kuma ya ji gaba aya duniyar ta yi mai zafi. Me....meya.....meyasa to?. ya fa a har bakinsa na rawa, sai da ta yi shuru na tsawon lokaci sannan ta ce. Ka ce za ka kula dani.........ka za tarairayeni..........sannan za ka ban farin ciki har arshen rayuwarka, gaskiya idan dai shike nan to ba zan iya aurenka ba........." Da sauri ya katse ta. To me kike so kuma?. *RIGIMA* , bani da burin da ya wuci na aura mijin wata, shi yasa nake son auren Babban mutum, kaima na za ci tana raye ne, amma da ko magana ma ba zan yi da kai ba, yarda baka iya oye- oye ba, haka nima ban iya ba, hmmmmm ka yi rayuwa wajen da ake rigima shima wani abu ne, ina so na ga tsantsar kishin wacce zan aurar wa miji a fili, kai na aureshi na zauna mata a gida, ta yi haukan kishi Ni kuma na biye mata mu hargitsa gida.........kasan Allah ko yayane Ina son rayuwa a gidan da zanyi rigima ko yayane, kawai ka ha ura gaskiya." Ta kai nan tana jin sautin dariyarsa, sai na tashi daga bed in ta nufa wajen mirror ta tsaya. akwai mace irin haka? Wake aure dan neman abokiyar rigima?. Ni, hmmm ko da nake yarinya, idan ina kallon Film in da ake zuba kishi na bala'i, sai na ji aunar gidan ya kamani, haka nake son irin gidan, da zarar Abbu ya dawo daga wajen aiki zan tambaye sa *Yaushe za ka yi ma Mamie Kishiya*, sai ya yi dariya kawai, Mamie kuna ta kamani da dukka, haka washegari zan kuma tambaya, da na ishe su Abbu, sai ya tsambayeni. Me yasa kike son a yi ma Mamie Kishiya?. Ba kunya zan ce Saboda a dinga rigima ina kallo. sai Abbu ya aya min kai, daga wannan lokacin ya dinga min aryan wai an kusa bikin, ko da na girma ban dena tambaya ba amma ba'a kusa da Mamie ba, haka dai har Allah ya ji ansa be mana kishiya ba.. ta fa a cike da kewan Abbu. Allah ya ji ansa." Ameen Nagode, to ga bazan yarda na aura mara mata ba. sai ya yi gyaran murya sannan ya ce. Kin kawo kuka gidan mutuwa, tabbas banda mata, amma ina da yara mata, wanda suka yi gadon kishin mahaifiyarsu, sai na su ma ya ara na uwar................ daga nan ya shiga ba ta labarin damar da yake sha idan ya auko aure, hatta mace be isa ya yi mu'amula da ita ba, labari ya ci gaba da ba ta Najlah kuwa sai dariya take yi, sai a arshe ya ce. To kinga ina da jarabbun a, balle ma Basma. Wayyo cikina, wai dama akwai yara irin haka? Ikon Allah, gaskiya yaranka sun burgeni, zan yi tunani a kai." Take farin ciki ya cika Abba, besan lokacin da ya fara gode Allah ba, Najlah kuma ta yi dariya tana cewa. An jima zan baka amsa, yanzu zan yi wanka. ba dan ya so ba ya ce. Shike nan, zan jira kiran na ki dan bansan na takura miki. murmushi ta yi sannan suka yi sallama. Tana aje wayar ta tashi dan sake watsa ruwa. Abba kuwa tsabar farin ciki rungume pillow yana an dariya asa- asa, yarda kasan an mai bushara da gidan Aljanna haka yake ji. Tashi ya yi ya koma kusa da mudubi fuskarsa ya ke kalla, sai ya ga kaman ya fi ko yaushe yau, kalmar da ta furta mai ranar nan shi ya tuna *Zu en saurayi.* Sai ya lumshe ido, a hankali ya furta. Allah yasa ta amince da ni. da haka ya tashi ya shiga restroom dan watsa ruwa.................. ************** Babban hotone da ya cinye kusan bango aya, Al-hassan da Al-hussain suka tsura ma mahaifiyar ido, suna kallonta kowa da abin da yake sa awa, Al-hassan kallonta yake kawai, daban yana farin ciki da kasancewar a matsayin mahaifiyar su, sai dai babu yarda ya isa, ita ce dole in sa, ko ya so ko a'a. Wani abu ya tuna akanta hakan yasa ya juya yabar akin da sauri. Al-hussain kuwa da idanunsa suka sauya launi saboda tunanin mahaifiyar ta su, sai ya bi bayan Al-hassan da kallo, yana tuna kalaman mahaifiyarsu na arshe. _Flash back_ A wani lokaci a can baya, Mom tana kwance a gadon asibiti, cikin mawiyacin hali, a haka ta umarci doctor da ya kira mata yaranta, ba musu ya fita ya kira su, su uku, a lokacin Tween suna da shekara 17, ita kuma Merry tana da shekara 13, suna shiga suka nufa Momy da sauri, hannunta duk suka ri e suna hawaye. Momy ta kalla Al-hassan, ha e fuska ta yi tana cewa. Al-hassan kira min Abbeey." Sai ya aga kai, da sauri kuma ya fita, yana rufe ofa idanunta suka sauka kan Al-hussain da Merry.