Sashe 37
Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka kawota gidan nan sai mun kasheta, kuma wannan marin bashi ne, akan ta zan rama. murmushi mai tarin ma'ana ya yi dan tunawa da wacece *Najlah* duk abinda ke awainiya da su to na ta ya dama na kowa ya shanye. Idan na kawota ku kashe ta in, amma aure kaman an yi ne. da haka ya shige ya barsu baki sake. Marwa ai tun maganar Abba na farko ta auke huta, numfashi kawai take amma jinta da hankalinta ba sa tare da ita, Fauza ma tuni take ta kuka. Najlah!!! NAJLAH!!!!!! Kin shiga uku, kin taro ma kanki masifa da bala'i, ku dena kuka, ita ce za ta yi kuka." Ta fa a tana share hawayen da suke zuba daga idanunta. Bassey ina da tabbacin ta asirce shi, marin ki ya yi, wai Abba ke aga mana murya. ta kai nan tana shafa gefan kumatun Bassey. Bashi ne, zan rama, yanzu dai gidansu za mu nema, ko ba'a Nigeria take ba sai munje har gidansu, muci mutuncinta harda na iyayenta. Sosai ma kuwa, wula ancin da ba za ta sake tsayawa da wani namiji ba. Saboda tsabar masifa na cinsu, a nan Parlourn suka zauna kowa na sa a da warwara a cikin ranta. A'isha mai aiki ce ta nufo cikin Parlourn hankalinta a tashe, ta ji duk abin da ke faruwa kuma ta tausaya musu ainun. Jiki na rawa ta zauna a asa kusa da Bassey, ta rage murya tana cewa. Dan Allah ku ya uri, ku dena damun kan...... gigitaccen mari Basma ta wanke ta da shi, sannan cikin tsawa ta ce. Tashi kibar wajen nan ko na miki illah, uban wa kiraki. ai da sauri A'isha ta bar wajen tana zubda hawaye. Mtwwsssssssss ba ar munafuka." Ta fa a tana sake ha e rai. Be kamata ki wuce akanta ba, ba ta da laifi, ta zo ta nuna kulawarta ne akan mu." Ya isa Marwa, haushin kowa nake ji, akan meye za ta tsugunna kusa da ni, bansan hauka wallahi mtwwwss." Da haka duk suka yi shuru, yarda cikin gidan ya au shuru, dan dare ya shiga. Fauza ce kawai ta yi barci, su kuwa yarda suka ga rana haka suka ga dare, suna zaune idanunsu sun bushe, haka zuciyoyinsu. Ana kiran sallar asuba, suka hanga part in Abba an kunna haske, da haka suka gyara zama. A natse ya bu ofa ya fito, tun daga sama suke jiyo dariyarsa kafin suka ji yana cewa. Zan tafi masallaci, kema ki samu ki yi sallar yanzu, an jima zamu yi maga...... ganisu yasa ya kasa arasa maganar, sai dai irin kallon da suke mai yasa ya katse wayar da yake yana nufan cikin Parlourn cike da mamaki. Subuhanallah kar dai ace anan ku ka kwana?." Hmmmmm Abba kana ban mamaki, amma nasan maganinku kai da karuwarka." Da haka ta mi e ta wuce. Sai ya kalla Marwa, kauda kanta ta yi gefe tana cika taba atsewa kamar mahaifiyarsa, sai ta yi mai kama da Hajiya Mama idan ta yi fushi, dama da shi take kama haka ita ma Marwan, yarda ta yi sai tuna mai da wani lokaci da Hajiya Mama take wannan kumburin kamar fulawar ta ji yis ta sha rana ta cika roba sukutum. Besan ya yi ar dariya ba yana shafa kansa, ai wannan dariyar yasa Marwa fashewa da kuka, ta mi e tsaye tana fara tafiya ta baya-baya tana girgiza kai. Abin dariya na zama? Dariya kake min Abba? Da...Dari...dariya fa?. Marwa ba haka bane, wani abu na tuna ne." Sai ta jinjina kai sannan ta haura sama tana share hawaye. Lumshe ido ya yi yana jin babu da i, kallon Fauza dake barci tana ta sauke ajiyan zuciya aya na bin aya, alamun ta sha kuka sosai dan har fuskarta ta yi ja, kai ya girgiza sannan ya yi waje................. ************* Please Tweeny, kawai zuwa za ki yi ku gaisa a matsayin Ni, ba za ta gane ba, zanje kallon wani match ne sannan na biya asibiti na kai taimako. Al-hussain ya kai nan cikin sanyi ta sigar ro Su biyu ne zaune kan sopa, suna kallon juna, kamar kullum kaya iri aya ne jikinsu, Orange in riga da Army green in wando. No Al-hussain, wannan ai haukane, ta ya zan je wajen budurwarka a matsayin kai, ka kirata kace ba za ka samu zuwa ba. sai Al-hussain ya ri e kunnuwansa. Please and please, I begging you, jiya banje na ganta ba, yau kuma wayarta na katse, a jikina nake jin babu lafiya amma akwai wajen da dole ne je shi yasa, shike nan tunda ba za ka min wannan alfarmar ba. da haka ya mi e ya juya baya. Hmmm Shikenan zani but in one condition. ya fa a yana jin gabansa yana fa i jin ya ce Kamar ba lafiya Marwa take ba. Al-hussain ya yi murmushi sannan ya juyo baya, zama ya yi inda ya tashi. a min me kake so?. Kamin al awarin za ka kula min da kanka duk inda kaje, Ni kuma zanje na duba maka lafiyar Marwa. rungumesa ya yi cikin farin ciki. Zan kula maka da kaina, kaima ka kula min da kanka. take hawaye suka zubo mai daga cikin fararen idanunsa, yana tsoron ranar da *Promise* zai bayyana, a wannan ranar yasan zai rushe duk soyayyar da Al-hassan ke mai, yana son an uwansa kuma yana son *Promise* saboda umarnin Momy ne. ara amesa ya yi yana jin kamar kar a rabasu, a yau zai yi aure, auren sirri, auren da ko an uwansa da suka rayu na tsawon wata goma a cikin Momy, suka fito a tare, suke rayuwa a tare, sai dai *Promise* ya rushe komai. Al-hassan jin irin ri on da an uwansa ya yi mai, yasa ya raba jikinsu yana kallon fuskar Al-hussain. Meke damunka?. Ba komai." Ban yarda ba, fa a min hankali ya tashi." Ya fa a yana share mai hawayen da suka gangaro daga idanunsa. Da gaske babu komai....... Ka fa a min ko na fasa zuwa duba Marwa. jin abinda ya ce yasa Al-hussain furta abinda dole Al-hassan zai bar maganan nan. Momymu na tuna. take Al-hassan ya ha e fuska, ya mi e da sauri. Okay, zan fita daga can zan biya, kaima ka fita da wuri karkayi dare." Be jira amsar Al-hussain ba ya yi waje yana sanya wayarsa a cikin pocket in sa. Al-hussain kuma ya bi bayansa da kallo yanajin babu da i gaba aya, da haka ya au wayarsa da kiran Merry ya shigo. Hello Ango Ango. ta fa a tana dariya. Waye Ango? Al-hussain yana wanka." Da sauri kuma a an rikice ta ce. Ah...Ah Al-hassan Wasa nake dama, uhmm tambayarsa zan yi, in ya fito ya kira. Dakata ke! Me yasa kika kirasa da Ango?." Ya ha e fuska amma kuma yana murmushi. Al-hassan dama ina kiransa da Angon Marwa, kuma ai very soon hakan za ta faru. ta fa a tana arin kare kanta. Hmmmm kina yanzu haka?. Ina aki kallo nake. yarda ta yi maganar yasa ya bushe da dariya yana cewa. anwar Ango ya da tsurewa, to Angon ne akan layi. take ta atse kiran tana wafa, ba za ta biye ma koma waye ba ya mai da ita mahaukaciya ba. Al-hussain kuwa aje wayar ya yi dama baya son damune shi yasa ya mata haka, sai ta shafa mai lafiya......... ************** Wani irin numfashi ta ja mai tsawo kafin ta f urzar, da wani irin azama ta fizge kanta daga wajen wata soja, baya-baya ta yi ta zube a asa tana ta tari, dan kuwa sojan nan sha eta ta yi, take idanunta suka koma launin ja, fuskar ta ha e, ta ciza le anta sannan ta buga asa da hannu ta, take ta yi wani juyi sai gata a tsaye, kamar ba ita ce yanzu aka lilkisata ba, take sojojin wajen suka hau mata tafi suna kiran sunanta. Murmushin mugunta ta yi tana kallon atuwar sojan da suke fa a, wiyarta ta lan wasa dama da hagu suka yi ara, sannan ta aga hannayenta ta yi mi a, jikinta suka fara Sai dai sojoji Mazan da suke wajen, da sauri wasu suka rintae ido, wasu kuma suka ara ware mata ido suna kallon yarda Breast in ta suka fito a cikin wannan rigar duk da yana da fa Najlah ba ta san ma suke yi ba, da haka ta nufa kan wannan sojan wacce take ma kallon kin shiga uku da Ni, yarda kasan Zakin da ya kwana hu u bega abinci ba, sai yau ya iske akuya a aure, haka Najlah ta yi mata, dukkanta kawai take, sannan ta i ba Sojan daman ramawa, haka ta gama lallasata har ta kai ga asa, take ta baje a sume. Nan fa aka ara tabbatar da Najlah ta wuce sa'a, mace ce mai kamar Maza, ar Sojo anwar soja, jinin jikinta gudana yake da jinin soja. Haka ta mi a tsaye duk ta yi du un-du un da asa, bakinta daya fashe ta goge da hannunta, sannan lokaci guda ta yi kan wani soja dake zaune, ta nufesa da gudu, gudun da wasu suka ga ta wuce makan wal iya, tana zuwa ta kifa masa mari, Marin da be yi tsammani ba dan ya shagala da kallonta, take ya fa i a kujerar yana mai dafe kuncinsa dan marin ya shigesa. Yanzu kusan kowa tsoronta yake ji, General kawai take shakka, yarda take wuci yasa mutane suka san akwai wani abu da ya yi mata. Ya Adam dake tsaye daga gefan wanda ta mara, ya agosa yana cewa. Najlah uban me ya miki za ki mai wanna marin?." Ba ta kallesa ba, ta yi wafa tana nuna mai dogon yatsanta manunuya. Wannan ya zama karo na farko dana arshe da za ka dinga kallona kana lashe baki kamar wani maye......ba shi ka ai ba duk wanda ya kuma min kallon da ban gamsu da shi ba, sai na ule ma mutum ido, na harbesa da bindiga." Ta fa a tana ciro bindiga daga ajiyun wandonta. Ai da sauri kowa ya fara silalewa, hatta Adam ya shafa kansa yana abokinsa suka bar wajen, yasan Najlah ba ta da hankali, tsaf za ta iya