← Book details Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 79

Sashe 58

Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka yi ma juna. Bara na dafa miki indomie in." A'a karki damu Abba zai aiko min da shi. sai ta sake musu sallama ta fita tabar Aunty Rumasa'u na ta masifa. A babban parlourn ta iske su tsatstsaye sai faman jijjiga suke yi, za su iya rantse wa da Allah babu wacce ta ta a musu irin rashin Mutumci kamar Aunty Rumasa'u. Hmmm na ga zallar rashin wayonku..........No wonder Mom take yawan cewa na fiki aiki da hankali, ku sani nuna mata iyayya tun farko shi zai ta mu rushe duk wani target in mu akanta. Fauza kenan, ai na rantse da Allah ko daidai da wayar zarra ba zan nuna ina sonta ba." Cewan Basma tana nufan stairs. Gaba aya sai idanunsu suka koma kan main door da ake shigowa. Abba ne ri e da wata leda ya shigo yana murmushi, yana ganinsu ya ara fa a murmushin. Fauza kira min Auntyn ku." Da haka ya zauna yana cire hular kansa. Bassey gyara tsayuwa ta yi, sai Marwa ta isa kusa da ita ta tsaya. Fauza umarninsa ta bi, inda ta shiga wancan part in ta kira Aunty Najlah. Fauza ta fito sai ta shiga Kitchen Dan aukan abinci. A hankali aka bu ofar, hakan yasa Abba mai da hankalinsa kan ofar, lumshe ido ya yi ganin Najlah ta fito tana tafiya a natse, ga wani kunya da take ji sai ya ara mata yau. Da sauri Abba ya mi e ya isa gabanta, hannunta ya ri e yana taimaka mata ta zauna. Kunya na miki yau. ya fa a yana zama gefanta amma ba dab ba. Sai rufe fuskarta da tafukan hannayenta wanda suka ta she Ya Salam, wannan hannun ai sai ya sa zuciyata ta buga. ya fa a yana kallon hannun nata. Ga abinci, ki cinye duka dan Allah, zan wuce inda zan kwanta. fuskar ta bu e sai ta amsa ledar. Uhmmm yanzu tafiya za ka yi?." Ya aga mata kai. Kina son wani abu ne Ammeen Basma." Basma ta an zaro jin abinda ya ce, sai ta rage murya ta ce. Hmmm daga gani na girma wannan........wai wani she ain in ne ya ba Abba shawarar auran yarinya hmmmmm harna tausaya mata, sai wani kunya take ji bayan ta gama......... maganar take ya tsaya mata a ma oshi dan kuwa idanunta sun nuna mata wani mugun abu. Abba sallama ya yi mata ya fara tafiya, Amma shegiyar ta kira sunansa a tausashe, bayan ya tsaya ya juyo, ta nufesa da gudu ta rungumesa ba ta tsaya a nan ba, har kumatunsa ta sumbata sannan ta ruga da gudu ta shige part in Abba. Abba kuma cikin jin da i ya shafa suman kansa ya fita yana murmushi. Zama Basma ta yi a asa tana rintse ido, Fauza ita ma ta ga komai murmushi ta yi tana cewa. ar hannu ce, shi be ta a ta ba amma ita ta rungumesa, hmmmm ina da tabbacin nan da 9 month za'a yi ma Basma anwa......." Ai gudu ta fara yi Basma ta fuma mata, Marwa kuma ya sauke ajiyan zuciya tana bin bayansu. *Washegari* Ta kama Saturday duk suna gida, babu wacce ta fito babban parlour har tana ta yi, jiya ba su kwanta da wuri ba hakan yasa suka kasa tashi, sai da yunwa ya tashe su tukun suka tashi. Wanka suka yi, kowacce ta sanya kayan da ya yi mata sannan suka fito a jere suna an hira, amma duk wanda ya kallesu yasan suna cikin damuwa. Dining area suka zazzauna, already an gama shirya komai, abincin suka fara ci suna yi suna dallama ofar part in Abba harara, inda suke ta jiyo surutai. Bayan sun gama suka zazzauna, a lokacin 11:45am. Wai nikam ina Al-hussain ne? Kwana biyu ina so na tambaye ki, gana aya kun dena wannan wahalalliyar soyayya, na ga sau aya kuke waya shima baku jimawa, ya dena zuwa, ke tsakani da Allah hakan ba ya fi ba?. Marwa ta kalla Basma, murmushi ta yi dan kuwa text kawai Al-hussain ke tura mata duk safiya da yammaci, da Al-hassan suke waya wanda suke yaudarar kansu da sunan gaisawa suke, amma a oye kowannen su aunar juna ya kamasu, sai dai sun kasa gane hakan. Murmushi Marwa ta sake yi tana lumshe ido sannan ta ce. Uhmm yana lafiya kawai ayyuka ne da suka sha mai kai. kafin Basma ta sake magana sai ga wa'inda suka kwana a angaren amarya sun fito kowa a shirye tsaf. A haka suka fito suna ta rarrashin Najlha dake cikinsu tana da hawaye, haka Rukky itama hawayen take yi. Aunty Rumasa'u ta kalla su Basma ta girgiza kai, sannan ta fice, haka duk suka fita babu wacce ta kulasu, suma haka. yar Najlah ta iya daurewa tana kallon motocinsu sukar gidan, hawaye ta share sannan ta gyara zaman hijabin jikinta ta juya zuwa ciki. Tana shiga ta nufa part in Abba, sai dai jin kalaman Basma yasa ta tsaya cak. Ke Najlah zo nan. a cikin ran Najlah ta maimaita kalman Zo nan. sai ta yi wani murmushin gefan baki, take kuma ta marairaice fuska tana mai nufan cikin Parlourn. Kujerar da babu kowa nan Najlah ta zauna tana mai kallon asa ala ita uwar ladabi. Munga zallar iskanci, muna sama tana sama, hmmmm lallai kam. da sauri Najlah ta sauka zuwa asa, tana jiran ta ji mai uwar mulkin za ta ce, dan ta gama gane Basma ita ce shugabar tantiran gida. Kwanda ki shiga hankalinki dan kuwa, yanzu babu kowa a gidan nan, tsab zamu kama ki mu kashe ki, kuma mun kashe banza." Cikin sha iyanci Najlah ta bu e baki kamar mai rawar le e ta ce. Na sani.....kuyi ari idan ma na muku wani abu........... Marwa ta katse da sauri. Shshshshshsh, idan muna magana karki kuskura ki dinga sa baki sai mun baki dama, tambayarki zamu yi munafuka. Ai kuwa munafuka tunda ta kasa kallon mu sai asa, kina jinmu." Cewan Basma, da sauri Najlah ta aga musu kai. Tambayar farko wani Bokan ne ya yi miki akan Abba? Kuma shi bokan be fa a miki auren Abba daidai yake da kin burne kanki da kanki ba...............ke nake saurare." Ba boka ba Malam, daga Allah ne soyayyar Abba, a kallon farko muka fara son junan mu. zabura Marwa ta yu za ta duke ta, da sauri Basma ta ri e ta tana girgiza mata. Najlah kuwa ta lumshe ido, za ta yi duk yarda za ta yi a yau ba za su fara rigima ba, za ta musu biyayya kafin ta nuna musu ainiyin launinta idan suka kai gaci, da dai hannun Marwa ya ta a ta da yau hankali kowa sai ya tashi. Da kin bari na durje bakinta, idan ba asiri ba uban me kika mai, nasan kuma saboda ku in Abba ne kika aurensa, amma me za ki yi da tsoho, to wallahi ki tanada hawayen ki dan kin tari babban masifa da bala'i a gidan nan, ke da samun da in aure sai a lahira, kuma ko a can in ne ma ba da Abba ba." Marwa ta kai nan tana wuci, Basma ta dasa. Hmmmm azaba iri-iri mun tanadar miki su, naso a yanzu da kike zaune, na watsa miki acid, anjima danginki su zo su kwashe ki, sai kuma na yi wani tunani, gwanda mu nakasani tukum, shegiya mai kama da Mayu. Dan Allah kuyi shuru, matar Abba ce fa, Ni bana son irin haka." Cewan Fauza tana tsugunnawa kusa da Najlah dake ta share ido kaman tana kuka. Haka ta rarrasheta, sannan ta raka ta part in Abba. Tana dawowa ta zauna tana cewa. Yarinyar ma ba ta da hayaniya, wallahi na tausaya mata, tana da rauni sosai, dan haka zan sassauta mata salon hu ubana. murmushi suka yi dukkansu. Tasan tana da tsoro shi yasa ta kasa magana, amma kalla kwanaki da muka yi waya da ita sai na ji muryarta a tsaitsaye. murmushi suka yi dan gani suke wannan aramar alhaki ce a wajensu. Najlah na shiga part din Abba ta murza key, dariya ta yi tana girgiza kai, Hijab in jikinta ta cire, sai kuma kewan an uwanta suka kamata, lumshe ido ta yi tana tunanin kalam na arshe. Najlah aure ya wuce duk yarda kike tunani, a kowani aure Akwai addararsa, akwai da i akwai rashin da i, babban makamin dake cikin aure shine *Ha uri* , da an fa a kalmar nan sai wasu su yi dariya akan kalmar, suna tunanin auren soyayya daban yake baya bu atar ha uri.......hmmm kowani aure yana bu atar ha uri sosai, sannan *biyayya* duk abinda ya ce ki yi, to ki yi, idan ya hanaki kar kiyi, Alhamdulillah na saki islamiyya, kuma iya gwargwado kinsan hukunce-hukuncen aure....... yata ki kula, dan Allah, ki zauna da mijinki da yaransa lafiya. Hawaye ta share sannnan ta yi murmushi tana cewa. Tabbas ba zan baki kunya ba Mamie, sai dai yaran nan zan kowa musu zama, har ga Allah sun min ka an, ina so na yi rigimar da gidan nan sai ya mana ka an wajen dambe." *Abinda ba ta sani shine, zuwan Abuja shine mafarin babban addarar da za ta iska, duk da tasani amma ba ta san hatsarin addarar ya kai haka ba...................* **************** Da misalin arfe 7:20pm na dare, motarsa ta yi parking a bakin get in su Marwa, wayarsa ya auka ya kira ta, bugu uku ta auka. Surpriseeeee ina waje." Da haka ya katse kiran, shuru ya yi yana sauraran wa ar dake tashi a cikin motar. asa da mintina 10 sai aka bu e get, yana juyawa idanunsa suka kalla fuskarta dake auke da murmushi. Motar ta bu e, sannan ta shiga da sallama, amsawa ya yi yana are mata kallo. Abaya ne jikinta sai vail da ta yafa, rabin gashinta yana waje ya kwanta luf-luf. Kinyi yau sosai." Ya fa a yana lumshe ido. Na gode sosai." Da haka suka yi shuru na dogon lokaci, amma zuciyoyinsu cike suke da jin da in kasancewa a tare. Lokaci zuwa lokaci sai su dinga saton kallon juna, da sun ha a ido sai suyi saurin kauda kai. Ita ce ta yi ta maza ta yi gyaran murya
Chapter 58 · 0% Book details