Sashe 67
Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Babyna zuwa yamma zan shigo." Kamar yana ganinta ta aga mai kai, sannan ta dasa hirar soyayya. Ajere motocin suka fita kan titi, Marwa ta yi hagu, Abba da Najlah suka yi dama, ta Najlah na gaba shi kuma yana bayanta, tafiya ka an suka yi Najlah ta yi kwana bayan ta danna mai horn sau biyar a jere, shima ya yi mata. A gefan titi ta yi parking, Fauza ta yi mata godiya sannan ta fita, tana tsaye har ta shiga *Event intranational school* sannan ta ara gaba. *Primecare Hospital* A jiya sai da aka ha a mutane da jami'ai kafin wasu suka bar asibitin amma wasu a Premises in suka kwana. Sannan zuwa safiyar yau ma an cika sosai. 8:34am na safe motar Dr. Ashraf ta yi parking a haraban asibitin, ya fito cikin wani gezna launin asa, daga sama har asa ya yi marching sosai, hannunsa ri e da I.pad da kuma waya. Mutane suka yi kansa suna mai Barka da zuwa, ya amsa ya musu murmushi. Yasan duk saboda Senator Tum a suke dan haka yana shiga asibitin shi ya fara dubawa, har lokacin be farka ba amma yana numfashi da kanshi. Farin ciki ya yi dan an samu ci gaba, ya sanar ma jama'a da an samu ci gaba, addu'a ta karbu. Take mutane suka farin ciki suna nuna jin da in su a fili. *RED ZONE COMMAND*