Sashe 34
Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kiran tana dafe kanta. Basma kuwa wayarta ta auka ta rubutu wasu number. Kallo minti biyu na yi ma number na haddace ta, haddar da bana tsammanin zai goge a cikin kaina. Number ar iskan ce?. Eh Marwa." Marwa ta goge hawayenta tana kallon wayar, sai dai kira biyar suka yi wayar na kashe. Shegiya ta taro match dole ta kashe wayarta." Cewan Basma tana sake kira. Hmmm ko kuma shi Abba ya ce ta kashe ba........Abba ya cuce mu wallahi, harda wani cewa saboda mu........ da sauri Basma ta rufe ma Marwa baki. Ya isa, idan tasan wata ai ba tasan wata ba, number zan tura a bincike ta tsaf, a tura min bayanan, daga nan zan kwasa an sanda mu tafi da su, wallahi dukka an gidan zan sa a kwashe, ko sun kai nawa ne kuwa. Nijla take Nihlah ma?. Najla ya ce, wai Abba da budurwar..... kai ahayye akwai abu gobe wallahi. da haka Basma ta shige bedroom ranta fes, Fauza ta sake maimaita sunan tana zama. Najlah." Sai ta yi wafa, Marwa kuwa mayafi ta auka ta yi waje dan a part in Abba ta bar hularta. A Compound ta iske Al-hussain yana ta safa da marwa, murmushi ta yi dan kuwa Basma ta ara musu warin gwiwa. Yana ganinta ya nufota da sauri yana arin rungumarta, sai ta ma e kafa a tana turo bakinta, hankali a tashe ya ce. Me kike ma kuka?." Uhmm kawai abune ya shiga min ido." Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauke yana dafe zuciyarsa. Kinsa irjina dukan uku-uku. murmushi ta yi tana kama kunnuwanta. I'm sorry Mijin Marwa. sai ya yi murmushin. osa ki kammala karatun nan muyi aure, duk da ma iyaye sunyi magana. Very soon zan mu gama ko in ce zan gama, dan kai rakiyata kawai kake." To na zauna a gida wani ya yi wuff da ke, wai dana mutu kuwa." Ganin dare ya yi sai basu ja hirar ba, suka yi sallama ya wuce, da nisha i ta shiga ciki, har ga Allah ta ji da in ha uwar Abbeey da Abba akan aurensu, kuma an tsaida Ranar da za ta yi sign-out ranar za'a aura musu aure. Ko da ta shiga ciki, Fauza ta yi barci, Basma na wanka, sai ta cire rigar jikinta ta sanya na barci, jin wayarta na ringing ta duba, ganin Number yasa ta jirkinta auka. Bayan ta auka kuma aka yi shuru, har sai da aka ba ta haushi ta fara magana, amma bayan maganar da ta yi aka ba ta amsa yasa ta ji zuciyarta ta harba, balle da ya tabbatar da shi Al-hassan ne, ga kuma kalansa da suka tsaya mata a rai. Wayar tabi da kallo bayan katse kiran, tana jin wani irin yanayi akan Al-hassan wanda sam ba ta ji tare da Al-hussain, gasu dai iri aya sak, ba su da banbanci amma tana jin Al-hussain a cikin ranta, Al-hassan a cikin tunaninta. A haka kuma ta kwana da kalamansa da suke sanyata nisha Washegari ta kama Saturday, duk suna gida dan haka ba su fito breakfast ba sai 9:30am, Dining room suka nufa kowacce ta nema waje ta zauna, suna an hira kaman babu wani abu dake cin zuciyarsa. Kowa ya fara cin abinda yake bu ata. Wai ke Al-hussain in nan baya hawa miki kai? Haba ki ta soyayya sai kace Romio, waya kodayaushe, Chart, zuwa fira, kai Marwa Rayuwar ki da gyara." Ta kai nan tana kai bread bakinta wanda ya ji butter, Marwa da take shan tea da yam ball ta yi dariya tana cewa. Hmmm ke da kike son rayuwa a haka ki yi ta yi, har yanzu ba kisan da i da gardin soyayya ba shi yasa, a soyayya babu takura, babu matsi, ke duk bayanin da zanyi ba za ki gane ba, Allah daga lokacin da kika fara ainiyin soyayya za ki fahimci haka." Allah ya tsare Ni da irin soyayyar nan, wallahi da Ni ce, shatamai layi zanyi, na bashi idojin hira, waya sau biyu, zuwa hira duk sati sai aya, Ni fa na tsana abinda zai ta kurani." Haka suka dinga hira wani suyi dariya wani su harara juna. Fauza dai binsu take da ido tana shan lemon tea, dariya ta yi jin abin da Marwa tace. Sai kin zurma da yawa ma, ya i kiranki ke kuma tun safe ki dinga nemansa ya auka, haka za ki haukace mana, ki kasa cin abinci." Ita kanta Bama dariya ta yi, sannan ta zagaye kanta ta hannu kafin ta ha e yatsunta suka bada ara. God for bit....Marwa ki kiyayeni wallahi." Suka kwashe da dariya dukkansu, take kuma duk suka ha e rai kaman hadari ganin Abba ya iso inda suke, yaja kujera yana sakar musu murmushi, ganin suna cikin walwala. Basma ta fara mi e ba tare da ta gama ba, ta goge bakinta, ta bar wajen, take Marwa ta au na ta Plate in sannan ta kalla Abba, ta girgiza kai ta bar wajen itama, be ce musu komai ba yasan hakan za ta faru ai. I.....Ina.....ina kwana." Cewan Fauza itama tana arin tashi. Zauna ki gama cin abincin ki." oshi." Ta fa a tana tashi daga wajen dama ba ta cin abinci da safe, sai dai abu mai ruwa zalla sai rana ta yi take cin abinci. Da ido ya bi ta har ta ace mai, sai ya shafa suman kasan yana jin babu da i, ji yake kaman be yauta musu ba, kamar ya ci amanar Karima, kaman dai Allah zai kamashi dan alkawari ya yi mata ba zai yi mata kishiya ba, da sauri zuciyarsa ta ce. Ai ka cika alkawari dan kuwa ba ka kula kowacce mace ba sai da ta bar duniya, yanzu ba ta raye, auren Babu Najlah ba laifi bane. sai ya lumshe ido yana tuno abin aunarsa, mura in ransa, uwar ansa, Ammeen Basma mai Capacity a zuciyar Abba...... Haka Abba ya gama ya koma akinsa, yana da aikace-aikace da yawa a gida, dan haka be zauna a part in sa ba babban parlour ya zawo ya zauna da kayan aikinsa. Abin mamakin haka ya wuni a Parlourn babu wacce ya sake ganin ko inuwarta, har aka yi zurh aka yi la'asar, babu wacce ta sauko. Bayan da ya dawo sallar la'asar ne ya hangi mai aiki na nufan part in su da abinci, hakan yasa ya ji dama-dama, gaba aya ka aici ya ishesa, duk da tun asuba suke waya da Najlah har gari ya waye, yasan su da waya kuma sai dare. angaren yaransa kuwa, da sanensu suka i fitowa, kowa ta yi harkan gabanta, saboda ba sason su fita haka Marwa ta hana Al-hussain zuwa zance, sai suka sha V.D. Ai Abba sai ya yi nadaman fara kula macen, dan gaba aya za mu ja jikinmu daga garesa har sai ya janye kalmansa. Marwa ko ya fasa, sai mun nema yarinyar munci ubanta." Ya Basma me Shamo ya ce akan number?. sai Basma ta kalla Fauza. Tun jiya na tura mai number, to Ni ma yau nai ta kira baya shiga har na fara tunanin ko mistake na yi, amma azu ya kirani wai sim din an yi amfani da shi da safe, be gama samun bayanan mai number ba aka rufe sim in, dole sai an sake bu e wa zai bani bayanai gaba aya." Hmmmm na osa na ga wata Bazawara ce ta yi ganganci tsayuwa da Abba, sai na yi mata rashin mutumcin mai wassali." Fa in Marwa tana sanya yatsa a baki ta ciza, sai Marwa ta ce. A asibiti zan auko acid na watsa mata. Da gaske za ki iya watsa ma wata acid?." Me ze haka Fauza, ai duk macen da ta ra a Abba dole na azabtar da ita. dariya Marwa ta yi. Sai da ke anwata mai kamar Mom, daga kaman har zuciyar ba ki auki na kowa ba sai na ta." Shi yasa na zama ma'aikaciyar jinya irinta, kunsa muna da imani amma bamu da tausayi." Tare suka yi dariyar har da tafawa dan duniyar yana musu da i.......... *********** *Merry* Ba ta farka da wuri ba sai wajen 11am, tasan yau ba za ta fita ba shi yasa tasha barcin ta, bayan ta farka ta yi wanka sannan ta fito dan yin breakfast. Bayan ta ci abinci, ta dawo main parlour ta zauna, news take kallo, tana sha fruit salad. A natse ta mai da idanunta kan Tweeny aya da ya fito cikin shigar ananun kaya, Jean's ash da dark blue shirt, ga gashin kanan nasa ya sha gyara sosai sai yalli yake, ba warya Tweeny ma urar yaune. Murmushi ta yi dan kuwa ta gane Al-hassan ne saboda saman girarsa an sa mai plaster alamun yaje an mai dressing, da i ta ji, tana fatan wajen ya yi tabo wanda za ta dinga ganesu. Zama ya yi a kan kujera yana latsa waya. Good Morning Brother." Morning my sister." Na ce, ka tura min taswiran zanen Bello, zan gyara wasu wajen sai mu yi amfani da shi wajen aikin, zai fi sauri." Ta fa a tana kallonsa, sai ya ago kai ya kalleta. Ki bari Al-hassan ya fito, yana ciki." Kallon ka rainamin wayau ka yi ta yi mai tana ara kallonsa. Bangane ba!? Al-hassan ka ce yana aki?. ya aga mata kai alaman tabbatarwa. Please stop joking, ka turomin a yau zanyi aiki, gobe sai a fara aiki. kallonta ya yi da yau. Na ce ki bari ya fito, bashi bane." Da haka ya mi e ya nufa Kitchen, ita kuma ta harara bayansa dan gani take ya raina mata tunani, ba yarda za'a yi hakan ta kasance, dan kuwa Al-hussain shine ya fita a jiya, Al-hassan ta yi ma yankan nan, gashi Al-hussan in yana ce mata bashi bane. wafa ta yi, da sauri kuma ta juya tana kallon wanda ya iso cikin Parlour yana mata magana. Merry na tura miki zanen Bello, make sure ki gama aikinsa yau." Ganin yarda ta mi e tana kallonsa, yasa ya tsaya yana mata kallon mamaki. Mamaki da zallar sar iya take gani, a hankali ta fara takawa zuwa gabansa, ta kai hannu ta ta a ciwon dake saman girarsa, be ce komai