← Book details Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 79

Sashe 40

Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

karka gur ata mata tunani da soyayya. Yaya dukka za ta iya, ina da tabbacin haka, sannan ko wani irin buri kake da shi akanta, zan tsaya mata duk wiyarsa. Hmmm Mubarak auren Soja ba wani armashi, dan kuwa rayuwarta na Barack sannan ga yawan transfer daga nan zuwa nan, ba lalle ka samu kalawa ba. a lokacin murmushi ya yi. Yaya karka damu, Ni kawai so nake na ga na rayu da ita, ina so na ba ta kulawa sosai, ko da Ni bansamu kulawarta ba dan nasan tana aikin kula da unbin al'umma ne." Murmushi suka yi, da haka suka sauya hira, yamma na yi ya dawo Abuja ta flight. Babu kowa a parlourn Dan haka be zauna ba ya haura sama ya shiga part in sa, wanka ya yi sannan ya auro alwala, jin an fara kiran sallah yasa ya sauko da niyar fita. Sai suka ha u da Marwa, hanya ta bashi ya fice yana mata murmushi, ita kuma ta maimakon ta wuce part in su sai ta nufa na Abba bayan ta aje ledar da Al-hassan ya ba ta a parlour. Tana shiga parlourn Abba ta gansa clean kamar yarda masu aiki suka gyara, direct ta nufa bedroom in sa, wanda ta mance rabon da su shiga wajen. Tana shiga ta hangi wayarsa dake kan mirrow, sai wata jakka da ya shigo da ita. Hannunta har rawa yake ta auki wayar, ta rubuta *Najlah* take wayar ya bu Shegiya tsinanna." Ta fa a tana fara duba cikin wayar, sai dai duk iya bincikenta ba ta iya samun komai ba, babu a whatsApp, babu call logs, haka babu pics na wata, tsaki ta ja, kamar za ta aje wayar sai kuwa hannunta suka latsa wajen sms. Gabanta ya fa i, ta dafe irji tana kallon sa on dake sama na *01IMH* da sauri ta latsa sa on da aka bu e amma ba'a yi reply ba. Abinda ke asa kawai ta bu e tana jin fargaban abin da za ta karanta. (Babyna ina fatan ka koma gida lafiya, ka mi a min gaisuwa wajen Yarana, kaga wasan da muka yi azu sai da na buge a afa yanzu yana min zafi, arouund 12pm zan kunna wayana karka yi barci ka barni kaji.) Marwa ta karanta kaman sau biyar, sannan ta aje wayar tana maimaita. Wasa........Wasa......wani wasa Abba yake yi da wata? Innalillah." Ta fa a tana fita ta bar part in gaba aya. Ko da ta shiga part in su, zama ta yi kan sopa tana tunanin menene abin yi, da sauri kuma ta mi e ta shiga bedroom. Gobe zan shigo asibitin shike nan, okay." Cewan Basma tana kashe wayarta sannan ta aje gefe guda. Marwa na isa kusa da ita ta ce. arfe sha-biyun dare za ta kunna wayarta, amma me yasa take haka? Ko ba ta gaskiya ne?. cikin arin bayani Basma ta ce. Akan wa kike magana?. Karuwar Abba, yanzu na fito daga part in sa, na duba wayarsa, kinga sa onnin da take mai na rashin a'a, hmmmm." Da gaske an jima za ta kunna wayarta?." Eh haka ta turo mai, har da cewa wai ya gaishe mata da yaranta." Basma ta yi dariya tana cewa. Muna amsa gaisuwa da yau da yau, za mu kira muma mu gaisa. da haka suka au alwashin kiran number Najlah arfe 12pm. **************** Zaune yake a mota yana duba wayarsa, ganin lokacin be wani ja ba, yasa ya lumshe ido yana jin ya kauda babban abun da ke gabansa. Sanye yake da suit black Riga da wando, yayi wani masifaffen yau na bugawa a jarida, dan kuwa kayan sun arbesa, sauti wayarsa ya fara dan haka ya auka, sai dai ba wannan wayar ba ce, ayan wayar ne dake pocket in sa, auka ya yi yana duba wanda ke kiransa da wannan layin. Bayan ya auka aka yi magana da wata irin murya mai cika kunne. Sir, komai ya yi dai-dai, wayarka kawai muke jira sai dai shuru gashi lokacin na tafiya kuma akwai aiki mai yawan gaske." Le ansa ya an ciza. Zan kira ku." Ya fa a yana katse kiran, take kuma ya katse wayar yana lumshe ido sannan ya bu e, sai ya yi murmushi mai cike da ma'anoni daban-daban. Merry ce ta bu e motar ta shiga tana cin snack. Muje Al-hussain." Da Haka ya kunna motar suka au hanyar gida. Biki ya yi albarka, na za ci ko na 1h za je hotel da Amar..... hararar da ya watsa mata ne yasa ta ha iye sauran maganar tana fiskewa. uri za ta yi na an lokaci." Hmmm ango kasha yau, anya muka koma gida a haka Al-hassan ba zai tuhume ka ba." Sai ya lasa le ansa kafin ya ce. Karki damu nasan me zance mai." Sai ta aga mai kai tana duba wayarta. Yaushe za ka fara aiki?. be kalleta ya ce. Tuntuni nake da aikin yi, sannan a yau ma an aramin matsayi, matsayi mafi girma na wajen aikin. da mamaki ta kallesa. Bangane kana da aiki ba?." Eh, kallonku kawai nake yi, amma da aikinsa." Uhmm." Ta fa a tana mai da hankalinta kan wayarta, dan tasan wasa yake mata, mutumin da kullum yana gida, sannan duk abinda yake bu ata daga al-jiwun Al-hassan yake fita. Murmushi ya yi yana shareta shima, ba yason damuwa gaba aya, so yake ya samu ya kwanta ya yi barci ko walwarsa za ta huta... ********* Abba ko da ya dawo be lura an shiga part in sa ba, Dan haka harkokin gabansa ya ci gaba da yi, 12:10pm ya au wayarsa ya kira number Najlah, sai dai tana waya, da haka ya tura mata sa Idan kin gama ki kirani. da haka ya ci gaba da aikin da yake a system. Abinda be sani ba shine, 12:00pm daidai Basma ta kira number Najlah, wacce kunna wayar na ta kenan, suna can angarensu suna rikici kamar za su cirota ta cikin wayar su kasheta. Su uku suke zaune a can carpet sun sanya wayar Basma a tsakiya suna kallon yarda take ringing Amma ba'a auka ba, tun sha-biyu saura suke kira a kashe sai yanzu da sha-biyun ya ha e shine wayar ke ringing. Har sun fidda rai za'a auka sai aka auka, ba su yi gaggawan fara magana ba, dan haka suka jiyo muryar Najlah tana magana a hankali kamar mai ra Baby Mubeee na ya na ga sabuwar number?. an Mubeee ne. cewan Marwa tana jin ranta yana zafi. Ku bari da safe ma yi waya yanzu muryan Babu nake son ji." Malama in za ki saki muryanki ki sake, ki dena sha e mana dan ba hula ne akan mu ba. ta kai nan harda wafa dan kuwa a tunaninta sha e murya Najlah take yi.............. ********************* Malama in za ki saki muryanki ki sake, ki dena sha e mana dan ba hula ne akan mu ba. ta kai nan harda wafa dan kuwa a tunaninta sha e murya Najlah take yi.................. Numfashi Najlah ta ja mai ara ta sauke a natse sannan ta ce. Bazan kasance aya daga cikin matan Uban da suke hayaniya da yaran kishiya ba, never mu dinga fa a a waya, ku bari na shigo gidan, daga lokacin za su fahimci komai." Mtwwwssss kuma dena tunanin auren Abba, kima dena dan kuwa an mu kasheki abu mai sau cewan Marwa, sai Fauza da yanzu ta fara magana a cikinsu. Ina tausaya miki Najlah, ki kama kanki, ki rabu da Abba ta hanya mai sau i, sannan ki koma wajen Bokan ki ta rushe aikin nan dan daga ke har shi mun tanadar muku hu uba mai tsanani. hatta Marwa da Basma sai da suka sake kallon Fauza saboda yarda ta yi maganar, Najlah cikin sha iyanci tace. Banga laifin ku ba, dole kuyi kishin Abba sosai dan Guyen ya ha u wallahi. Ke wai wata irin ar duniya ce, yanzu tsakani da Allah Abba ne Gaye? Ki ji tsoron Allah, ki rabu dashi ki zauna lafiya. in Marwa hawaye na zuba daga idanunta, sai dai jin kalaman Basma ba aramin ru ata ta yi ba. Da gaske Ina son Abba kuma za ki auresa?. warai da gaske, aure kaman anyi nema. Shike nan, ki ci gaba da shirin auren, ki yi party ki yi walima, daga yanzu daga Ni har su babu mai sake damuwa da aurenki. mamakine ya kamasu amma sun kasa magana saboda Basma ta musu alaman suyi shuru, dariya Najlah ta yi harda Allah dai ya muku albarka yaran nan, ya baku majaje na gari kaman My Mubee. da Haka ta kashe kiran. Da sauri Marwa ta fara magana tana dafa Basma. Kina hauka ne za ki ce da ita haka? Kinsan me kika furta. murmushin mugunta Basma ta yi, ta mi e tsaye ta yi taku uku sannan ta ce. Daga gani aikin asiri ke cin Abba, ko mu so ko mu i sai ya aureta, dan haka mu bari ya yi auren, mu bari ta tako afarta cikin gidan nan, daga nan wasan zai soma. ta kai nan tana lumshe ido. Kina nufin mu bari wata ta shigo gidan nan?. Eh Fauza, sai dai ba za ta ko yi kwana aya ba, zamu yi mata wula ancin da ko kare aka bawa namarta ba zai ci ba. Hmmmm shike nan, wannan shawarar ta yi, amma ya zamu nuna ma Abba?." Sai Basma ta juya ta kalla Marwa. Ai shi ba za mu nuna mai muna so ba haka ba zamu nuna mai bamu so ba, daga yanzu mu sanya mai ido, daga gaisuwa sai gaisuwa, kunsan dai yarda ya kamata. jinjina kai suka yi kowa yana sakar zuci. Da haka kowacce ta nema waje ta kwanta tana tuna irin mugunta da za ta yi ma Najlah dake gigin auren Abba. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a cikin gidan Abba, idan sun ha u da shi iya gaisuwa ne kawai, daga nan suke kama kansu, shi kuwa tun yana jin babu da i har shima ya fita sabagarsa, balle ma hankalinsa gaba aya ya koma kan Najlah, sannan babu abin da ya fi mai da i irin zaman da danginsa suka yi dana Najlah, a kuma
Chapter 40 · 0% Book details