Sashe 13
Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Marwa* Zaune take kan sopa tana waya da Al-hussain, wanda tun safe suke tare har yamma, sannan tun azu suka fara waya da shi, a natse cikin wannan muryan nasa dake sa ta ara narkewa a cikin soyayyarsa ya ce da ita. Gobe ki wuce school, a can zamu ha u, Al-hassan zai zo ku gaisa." Sai ta yi murmushi. Gaskiya na ji da i sosai, kullum na ce ka nuna min hotonsa sai ka nuna min naka, ko naka wanda aka yi double jikinka, finally dai zan gansa." Tana ji ya an yi dariya sannan ya ce. Hmmmm ki tabbar kin dawo ruwa dan za ki iya suma saboda mamamki." Haba dai, ba yau na fara ganin identical twins ba, balleku kallo aya zan gane ku, kaine fa masoyina. sai ya yi murmushi. Da haka suka sauya hira, har sai da barci ya ci arfin Marwa sannan ta mai sallama tana shiga bedroom Dan wanciya. Gado uku ne kowa da nasa, Fauza tuni ta yi barci akan takaddu, sai Basma dake latsa system akan na ta gadon. Marwa ta kwanta tana addu'ar barci tare da kallon Basma tana aukan wayarta dake ringing. Baki ga kirana bane? Ko barci kika yi?. cewan na cikin wayar dake handfree. Na gani kawai ban auka bane. Basma ta fa a cikin ko in kula. Kamar ya kina gani? Wato 7 missed called duk kina gani?. Eh." Sai ta ji ya yi wafa yana cewa. Basma hulakanci babu yau, dan na ce ina sonki ba shine zai sa na auki komai daga gareki ba...... an dakata Malam, karka aga min murya dan ba zan auka ba mtwwssss. Ni kike ma tsaki?. An yi maka in, na ji duka mtwwssss. ta kuma jan dogon tsaki. Marwa ta girgiza kai tana gyara kwanciya, dan ta gaji da magana akan abu aya, haka Basma take, ba ta yarda saurayi ya aga mata murya, gashi ba tasan menene biyayyan soyayya ba, ba ta kiran saurayi kuma in an kirata sai ta gamada take auka, sannan kai tsaye za ta fa a kawai ba ta son magana ne, daga nan su yi fa a ta yi blocking number mutum, shike nan sun rabu sai ta kuma wani, gaba aya samari ba su wuce sati aya da ita saboda halinta. Ke wai dan kin samu ana sonki ma shine za ki hulakantani." Ya fa a cikin masifa, ai da wani irin zafin nama Basma ta aje system in tana aukan wayar take da cewa. Kan bala'i......lallamai Shamsu ashe baka da hankali, wato Ni kake so ma, irin na rasa samari in nan....wallahi dan rage ma kaina lokaci yasa nake waya da kai, ka kalla kansa a mudubi za ka fahimci haka, mtwwssss....... Allah na gode ma da ka nuna min Basma ba matar aure ba ce, Allah na gode maka, banza kawai, ki arata da kanki" Ya fa a tare da kashe kiran gaba aya. Wani abu ta ji ya tokare mata zuciya, sai ta cillar da wayan tana tashi daga kan gadon, idan ranta ya yi dubu to ya aci, har wani tiriri take yi na masifa. Banza......Ni ce banza Shamsu, ka shiga uku, wallahi sai ka yi nadama, kan bala'i." Ta fa a tana fita ta zauna akan kujera. Yarda ta zauna a haka gari ya waye dan yarda take ji ko barci ba za ta iya ba saboda tsabar acin rai. Idanunta sun ka an sunyi ja, amma ba hawaye, kalma aya take tunawa, *Banza* Wanka ta yi tare da sallar asuba, sannan ta shirya cikin wani doguwar riga na atamfa, tashin su Fauza ta yi tana arasa shiryawa. Cikin barci Fauza ta kalleta sannan ta ce. Ina zuwa ne kike shiri ko 7am be yi ba?. Police station." Ta fa a tana aukan jakkarta sannan ta nufa hanyar fita. Basma. sai ta tsaya cak tana sannan ta juyo ta kalla Marwa dake shirin shiga toilet. Please ki ci wani abun kafin ki fita. sai ta aga mata kai sannan ya fita. Ya Marwa me za ta je yi a police station?." Hmmm kinsan Basma, maybe rigima ta yi da wani za ta sa a kamashi." Sai Fauza ta girgiza kai tana jin babu da i, haka Basma take abu ka an za ta kai ka staion, da yake D.P.O in yana sonta, kuma kaman yaron Abba ne, shi yasa take zuwa ya yi ma duk wanda ya so rashin mutumci. Basma na sauka ta nufa Kitchen dan jin motsi a ciki, kofar ta bu e tana kallon sabuwar mai aikin nasu, babbar macece wacce ba za ta wuce 32yrs ba, ba a ce amma a tana da jiki sosai, ga wani hips Masha Allah, take wani abu ya tsaya mata a wuya, duk da kuwa doguwar riga ce jikin Matar. Matar jin an shigo ta yi sauri ta jiyo tana gyara zaman gyalenta tare gaishe da Basma cikin ladabi kamar yarda aka ce ta dinga musu. Basma kuwa are mata kallo take yi, tana yau sosai, ga manyan Breast wand zai auki hankali, ita jiya sam ba ta lura da yanayin matar ba. Hannu Basma ta sa ta auki glass cup sannan ta sake shi ya fa i kasa. Idan na dawo zamu yi magana muddin kina son aiki a gidan nan dole ki bi kowani dokana. Insha Allah zan bi komai." Cewan matar cikin biyayya. Kwashe wannan." Ta fa a tana an ja baya. Ai cikin sauri matar ta mi e jikinta har rawa yake kar-kar, ta auko faka da tsintsiya, ta hau kwashewa, ko ina na jikinta sai rawa yake yi. Basma ta ja tsaki sannan ta fita, dan akwai aikin dake gaban tane da zama za ta yi ta kora ma matar warning, yanzu da Abba ne ya shiga cikin in fa?, da shi ne take ta ma rawar jiki haka fa?. Sai Basma ta girgiza kai tana shiga mota tare da cewa. Inaaaaa.......wallahi da sake." Da haka ta figa mota sai station. Da yake safiya ce ba yawaitan motoci, hakan yasa ta dinga sharara gudu, a ofan station din ta tsaya *Central Command Station* sannan ta fito daga motar ta shiga ciki. Akwai jami'ai sosai, suka dinga gaisheta dan sun san wacece, direct office in D.P.O ta nufa, wanda sukai waya akan ya shigo da wuri. Tana shiga ta iske sa, zaune yana duba wasu files, yana ganinta ya mi e da sauri, jikinsa ya fara rawa yana mata murmushi, shi har ga Allah yake son Basma, Amma ta kasa bashi dama, kuma kullum cikin faranta mata. Babban mutum ne dan yana da mata da yara biyu, amma Allah ya aura mai soyayyar Basma sosai. Ina kwana Divisional Police Officer D.P.O." sai ya yi murmushi yana cewa. Lafiya lau Basma, ai da kin turo min information na yaron har gida za ku kawo miki shi." Sai ta sauke ajiyan zuciya ta ce. Karka damu nan nake so a kawo shi, daga nan ka batar da shi na sati aya, bayan ya ci wiya sai a dawo da shi, ina so yasan saboda zagina da ya yi shine aka mai haka." Shike nan Basma, yanzu ki ban address in sa ki koma gida, zuwa anjima sai ki dawo, ai ko wani irin sharri za mu la a na mai." Sai ya ta mai murmushi. Latsa wayarta ta yi sannan ta ce. Sai na dawo in." Sai ya kalla wayarsa da sa o biyu suka shigo, aya information akan yaron na biyu kuma alert in 50k. Take ya hau mata godiya sannan ya rakata har bakin mota, ta shiga ta bar wajen, tana jin da i a ranta. Shamsu sorry for yourself." Ta fa a tana kunna wa ar larabci a cikin motar sannan ta nufa school........ *Marwa* A natse ta aje wayar dake hannunta zuwa kan jikinta, ta kalla filin makarantar na su, in da mutane ke fa zirga-zirga, murmushi ta yi dan yanzu ta yi waya da Al-hussain ya ce ta zauna a wajen, kuma ta tabbatar tana ri e da ruwa, hakan yasa ta yi murmushi tana jin ta osa su iso. Tana daga zaune motar Al-hussain ta shigo school in, sannan direct wajenta ya nufo, sai ta gyara zama tana zuba ma motar ido, bakinta auke da murmushi. Parking aka yi, sannan aka auki minti biyu kafin aka bu angaren Driver. Baby Love ki kulle idanunki." Ta ji Al-hussain ya fada, sai ta rufe tana cewa. Na kulle. A hankali Al-hussain ya fara fitowa daga mazauninsa, sanye yake da manyan kaya, Men Less coffee brown ya ji aiki sai walwal yake, ga wani arnen hula dake kansa, yana fitowa ya kulle motar sannan aya angaren shima aka bu e, sai irin takalmin dake afar Al-hussain ya fara fitowa. Kafin gaba aya gangan jikinsa ya bayyana, shigarsu dai sak iri aya, murmushi ne kwance akan fuskokinsu, sai Al-hussan ya zagayo kusa Al-hussain, hatta tsayuwar ma iri aya suka yi. Mutane ne masu wucewa suka fara tsayawa ganin an biyu masu masifaffen kama, kowa mamaki ya amshi saboda irin makar ta yi yawa, take aka fara musu hotuna sannan wasu suka hau kiran friends in su su zo suga abu. e." Ta ji an fada, a hankali ta bu e idanunta tana ganin mutane sun zagayesu, sai a hankali ta fara kallon afafunsu da takalmin su iri aya, a hankali ta fara binsu da ido, har zuwa fuskokin su, wani an zabura ta yi tana rufe ido tare da ara bu e wa, sai dai yarda suke tsaye sun zura mata ido suna murmushi iri aya sak, a razane ta mi e tsaye tana shirin gasgata abin da idanunta suke gani, dan kuwa Al-hussain in ta ta ga ya koma guda biyu, Rufaida bottle water ta bu e sannan ta wanke fuskarta, sai ta kallesu da yau, tana jin kaman ta isa gabansu amma afarta ta yi mata nauyi. A lokacin aya suka bu e baki tare da yin magana iri aya kuma cikin sauke nunfashi aya, al'amarin da ya ara burge gaba aya mutanen wajan. ara so, sannan ki cinka abokin rayuwarki. kanta ta dafe dan jin muryansa ma iri aya sak. Ya Allah, wai da gaske abin da nake gani haka ne. sai suka aga mata kai. Zufan dake fuskarta