Sashe 47
Budurwar Abban Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
uhmmm ki dai yi nazari." Da haka ta mi e tsaye tana sake isa gaban mirrow in ta kunna wa a ta ci gaba da rawarta. Rukky ta yi shuru tana tunani, tabbas maganar Najlah dai-dai ne, dan kuwa Tahir ba wuci 21yrs ba, kawai tana sonsa ne sosai, ga kuma wannan maganar, tasan waye Ustaz, mutumin da ko tunanin haka bata ta a yi ba, mutumin da mata suke mamarin tsayuwa da shi, malami mai tarin baiwar Alqur'ani, lumshe ido ta yi ta bu Najlah sha a zo mana. ta kira ta da sunna da an ajinsu suke kirarta. Murmushi Najlah ta yi ta juyo ta dawo wajen da ta tashi, ta kalla Rukky tana turo baki tare da lumlumshe ido tana yin alamun za ta yi kuka. Bansan iskanci, ba Alhaji Mubarak bane, ki kirasa ki in kin gama mai sha ar ma yi maganar." Da mamakin Rukky ta ga Najlah ta au wayarta ta fara kiran sunan da aka yi saving da LOML Menene LOML? cewan Rukky sai Najlah ta yi murmushi ta ce. Love of My Life. zaro ido ta an yi kafin ta kuma magana Abba ya katse kiran ya kira, auka ta yi take Najlah ta fashe mai da kukan iskanci tana bubbuga afafunta a asa, Rukky ta zaro ido tana kallon ikon Allah. A hankali muryar Abba ta fito ciki tashin hankali. Innalillah waya ta a minke? Menene Jaririya ta...........dan Allah ki yi min bayani.......ko kina so na zo ne?." Ya kai nan yana fatan ta yi shuru da kukan na ta. A....Abba.....A.......abba. sai ta sake fashewa da wani kukan, Rukky dai zuba mata ido ta yi. Na'am Ammeen Basma, menene?. sai ta yi shuru tana ma Rukky walo, cike da zallar sha a ta ce. Uhmmmm Ba uhmmmmm ba Rukky ba ce take min ihu, kuma bana sooooo. Subuhanallah, ba Ni ita na mata fa a....." Uhmmmmm A'a duka nake so a yi mata." To Jaririyata, tana kusa ne?." Uhmmm ga ta." Ta mi a ma Rukky wayar tana mi ewa, gaban mudubin ta koma tana kallon kanta tana fari da ido. Alhajin Allah, Ango Ango mijin Jaririya." Ta fa a tana dariya, shima dariya ya yi yana cewa. Ya fama da rigimarta?. Wallahi kullum aruwa yake, mun kusa fara ha a mata da duka." Da sauri Abba ya ce. Ku rufamin asiri dan Allah, ku dai lalla a min ita, kunsan kamar wai take. Hmmm na ga alama ai, amma tana cika mana ciki sosai." ara ha uri, bansan ko kallon banza ana mata kunsan yarinya ce. sai ga aga ido ta kalla Najlah, tsaye take tana an karka a jikinta, ta baya uban mazaunanta suna ta rawa. Ahhhh ba shakka Jaririya ce anyan goyo." Dariya suka yi sannan ta isa wajen Najlah tana ba ta wayar. Baki ta tura tana narkewa, shima sai ya rage murya cikin sanyi. Abban Basma." Na'am Ammeen basma. Uhmmm kana office ne?. Eh Shalele." To idan ka koma gida zamu yi waya. Shike nan, ki kula kinji Amarya." To Angona. Ina sonki." Ina sonka." Da haka ya mata sweet kiss yana katse wayar, murmushi ta yi ta kalla Rukky. Har kin fa a min maganar banza, ga sha ar na miki ai. Kinfi arfina, ai wanda mu aurar da ke, kut haka kike dama." Najlah ta yi mata fari tana cewa. Na fi haka, ki bari an jima ya kira, za ki sha kallo, kinsan yarda kaza ke zama wai haka wai yake zama Kaza." Allah ya tsare Ni, ni kaza, ba zan ji abinda zai do emin kunnuwa ba. Kinma kanki ai, ki koya cost kema ki dinga ma Ustaz Umar, nan da nan za ki narkar da shi a soyayyarki. murmushi suka yi sannan suka sauya wata hirar suna yi suna dariya, wani kuma su fara rigima....... ************** Mutane ne sosai a wajen ga sojoji ga an sanda, harda an jaridu masu aukan rahoto, gefe guda gawan wa'inda aka kashe ne daren jiya, mutane 13, aka ma yankan rago, kuma ba'a san suwaye suka aikata haka ba, hakan yasa hankalin kowa ya tashi, aka cika unguwar, ana ta bincike, mutanen gari kuwa kowa ya shiga damuwa da wannan labarin. an uwan wa'inda aka kashe suna ta kuka gwanin tausayi, an jaridu kuma sai aukan komai sune suna watsawa a duniya. an sanda suna ta kai da komo, ga manyan likitoci da suke bincike akan gawarwakin. Gaba aya wajen ya hargitse sosai, a daidai lokacin manyan motoci guda biyar suka faka a gefe ka an da wajen, Range Rover guda biyu duka Black sai Lamborghini ash guda aya da kuma Ferrari fari Take hankalin kowa ya koma kan motocin, jami'an da suke Range Rover suka fito da sauri suna bu e Ferrari dake tsakiya. Take shugaban jam'iyyar PRM wato Senator Tum a ya fito rai a ace, yarda yake tafiyar ma ya isa ka gane hankalinsa ba a natse yake ba, mutane suna ganinsa suka fara jin da i dan kuwa kowa yasa Senator Tum a, Mutumin kirkine, ga taimakon mutane, ko kwana biyu ba'a yi ba da ya yi rabon abinci, kuma ya hana a ya a al'amarin sai dai mutane suka fito suna ta nuna godiyansu akan yautatawarsa. Da shugaban masu binciken ya fara, in da suke nesa, amma ana ina hango yarda yake magana cikin tashin hankali da fa Da haka ya nufa mutanen da suka rasa nasu, ya dinga basu ha uri harda hawaye dan tausaya musu. Take kuma ya umarci a basu 1-1M, da haka ya tashi ya nufa motarsa yana share hawaye, mutane suka hau fata mai suna mai fatan alheri, an jaridu kuma suka yi kansa da gudu suna son mai tambayoyi. Tsayawa ya yi yana kallonsu a natse. Yalla a mutane suna ta nuna jin da insu akan abubuwan da kake yi kwana biyun nan? Sai dai wasu suna tunanin campaign kake ma kanka kafin lokacin za e, amma me za ka ce akan haka?." Cewan wani an jarida, sai ya yi murmushi. Wannan maganar haka muke ji kullum, Ni a yanzu ba mulki ne gabana, mutane sune damuwata, ba zan fasa taimako ba, ina jin ra in abubuwan dake faruwa domin a asata komai ke faruwa, dole hankalina ya tashi." Sir, me za ka ce aka masu wannan anyen aiki?. Ina musu garga i karsu bari mu kamasu, dan wallahi sai mun yi musu abinda ko dabba aka ba namansu ba za su ci ba." Ya kai nan yana nunfasawa sannan ya ci gaba. Kisa, fyade, garkuwa da mutane, ku sani masu wannan laifin Allah yana kwallon su, ko ku tuba ko ku ha u da fushin Allah, da in abun gidan biyu ne, amma ya kuke so talakawa sune yi dan ......dan Allah." Sai ga hawaye shar daga idanunsa, nan ya fara kuka yana girgiza kai, securities insa suka shiga da shi mota tare da sallamar mutane. Yana shiga motar ya tuntsire da dariya yana kallon abokin aikinsa David John. Aiki na yau, yanzu dole ka ara shiga ran jama'a." Hakane David John, yanzu mu koma office zan kira *BLACK DRAGON* akan ya shiga angaren kasuwa, ko huta a sanya ma wasu shagunan, kafin nan a kwashe komai ta yarda za mu dawo ma kowa da ku insa kuma mu samu girmamawa. Dariya suka yi, sai dai jin abinda wani ke cewa yasa suka mai da hankalinsu kan an jaridar, da yake window in be gama rufewa ba. Jama'a be kamata muna zagin shugaban asar mu ba Alhaji Muhammad Babangida Shamaki ba, yana iya arinsa akan mu, kawai mugayene suka mai zayage suna neman rushesa, amma mutumin kirkine" ya fa a yana kallon wata tsohuwa dake magana. arya kake, babu abinda shugaban kasa yake yi, waya sani ko dashi ake bin mu ana cutar mu........." Sai ta fashe da kuka tana ci gaba da magana. Yarana uku aka sace, aka nema ku in fansa mai yawa, sau nawa ina zuwa wajen shuwagabannin mu, sai dai babu wanda ya bi ta kaina, ga mu cikin talauci, haka na yi tattaki har zuwa wajen hasken al'umma *Senator Tum a* a ranar ya kira mutanen da suka yi garkuwa, ya ji nawa suke bu ata, shi ya biya aka dawo min da yara maza biyu ar macen sun kasheta, babu abinda zan ce akan Senator Tum a sai dai Allah yasa ya gama da duniya lafiya, ya kuma nuna mana lokacin da zai yi mulkin asar nan. take aka fara mai kirari. Yana mota ya yi murmushi sannan ya kalla an jaridar dake girgiza kansa. Uhm, David John wancan an jaridar, a kauda shi daga wannan duniyar. Ita kuma waccan matar, a sake tura mata sa on ku aikinta ya yi yau sosai. Ok sir she really made it look real. Good. Let s move to the office ll contact Black Dragon regarding the children he abducted. da haka wanon motocin suka bar wajen. ******** Fararen yatsunsa suna ri e da coffee mug, a hankali kuma ya kai baki ya an zu a, komai dake faruwa a wajen yana kallo a tv, be yi mamakin ganin Senator Tum a ba, saboda neman mulki yake ido rufe, yasan har ga Allah yana iya arin wajen ba ma Nigeria tsaro wanda ko a yanzu ya mutu yasan ya yi ayyuka na gari, mutane kawai da ba su gani, ko yace wa'inda suke asansa suke rushe komai. Gashin kansa ya shafa yana bu e baki hankali ya ce. Lokaci.....ya yi, ina da ya inin zan rusa mugayen asar nan, ya Allah ka taimaka kungiyar *BLACK SHADOW* kaba wannan ungiyar daman gano waye *BLACK DRAGON* da masu goyon bayansa akan rushe mana asarmu. (ameen) ya lumshe ido yana nazarin abubuwan da suke faruwa a an lokacin nan.. *********** A bakin get ta yi parking, sannan ta danna horn, aka bu e ta shiga da motar har cikin gidan, Anas ya ha iye wani kakkaurar miyau yana bin gidan da kallo. Bayan ta yi parking ta kalla Anas. Me kake so?. lumshe ido yayi sannan ya bu Ke nake so Basma, ina sonki sosai. Nima ina sonka sosai. sai ya yi murmushi. Za ki iya bani ranki?." Wallahi zan iya komai akan ka." Ta fa a cikin gaskatarwa Ina so ki mari