← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 106

Sashe 99

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"I missed you Rouhii" banyi magana ha har lokacin idona kawai yana rufe sakarmin nauyinsa yayi saida nayi ƙara Yaƙi ɗagani banfara ƙoƙarin ƙwacewa ba dan nasan bazan iyaba yace.

"Nace nayi missing É—inki bakiji ba?"

"Naji menene yafaru?"

"bakice nima kinyi missing É—ina ba toh"

"Ai banyiba nikuma ban iya ƙaryaba shiyasa bance komaiba" yaja hancina ya miƙe zaune yana faɗin.

"Ba yanzu zaki gane bakiyi Missing É—ina ba kibari idan nazo garrki bakiyi sumbatu ba zan yarda" narai-narai nayi da idanuwana ina shirin yin kuka yafiya zolaya abu kaÉ—an sai yaÉ—auko wani abunda nayi ko nafaÉ—a a lokacin da muka kasance a tare muna farantawa juna yana tsokanata na juyarda kaina gefe.

" idan kasamu nabaka haÉ—in kai ba saika samu abun faÉ—a"

"Rouhi wane mutum waya isa ya Hanani shiga Gonata" Natashi ina cire Hijabin jikina.

"Mutum kuwa shi ya'isa ai koh kasan kuma zan rina ba?" ya jijjiga kai.

"No bazaki iyaba Rouhi" na isa zuwa wajanda muka aka ajiye kaya na ɗauki rigar bacci na ajiye a gefen gado nashiga wanka ban daɗe ba nafito ɗaure da towel a jikina na isa nagyara jikina na shafa mai na jawo rigar nasaka ina gaban madubi arazane nake kallon rigar dake jikina Babu abunda ha'a kallo sunanta Fam ɗarinka tsirara wannan rigar ina yawan saka irinta dan kusan yawanci kayan baccin daya zubamin mukayi tafiya dasu irinta ne bantaɓa tunanim haka takeba saida na kalleta yau a madubi kuma haka nake sakata nayita yawo a gabansa ban damuba ashe shi ganta sarai yake kallona, jiki a sanyaye na tako zuwa bakin gado na shige bargo duk abunda nakeyi yana kallona baice komaiba yagano abunda nagani dama yasan hansan haka rigar takeba da bazan sakaba yanzu damuwarsa karnace zan daina saka irinsu suna sanyashi nishaɗi kuma.

Dama shi yayi shirin ƙwanciyarsa tun kafin nazo shima yabi bayana ya ƙwanta ya rumgumoni a jikinsa Har muka fara shirin bacci banji yana shirin laluɓata ba na ɗauki Hannunshi na ɗaura akan ƙirjina da wayo sai naga ya kauda hannun cire kunya nayi na juyo muna facing juna.

"Masoyi wai yau baza'ayi komai bane? Yayi shiru kamar baijini ba na harzuƙa nakaiwa cikinsa duka"

"ina maka magana?"

"Banyi missing ɗinki bane shiyasa banyi komaiba da kika tambaya kuma bana ƙarya shiyasa nayi shiru" nagano so yake ya rainamin hankali da maganata ta ɗazu.

"Kafara shafani mana kaji zaka gane kayi missing É—ina ko bakayiba"

"A'a wane mutum" yafaɗi shima nagane kawai yana mayarmun ma maganganunane na raba jikina danasa naje can gefe na ƙwanta. Can naji yana faɗin.

"Rouhi zo kiji" yi nayi kamar banjishi ba na share amma a zuciyata inata Allah-Allah yasake magana wuf zan wuce natafi" ya sanya hannu ya jawoni zuwa jikinsa yafara magana a kunnena.

"Bake kikace bakiyi missing É—ina ba? Nima ramawa nayi shiyasa kinsan kuma wasa nake amma kikaji babu daÉ—i toh nifa danasan da gaske kikeyi?" na sake shigewa jikinsa.

"Nima ai wasa nakeyi na isa nace banyi missing ɗinka ba? Kai kasan irin sonda nake maka ai idan wasune ma suka faɗa yakamata ka ƙaryatasu"

"Yeah i know kina sona amma bai kai ƙwatankwacin wanda nake miki ba.

"Masoyi" na kirashi.

"Na'amm Rouhii" Masoyi kace duk ranarda nacika maka alƙawarinka zaka faɗamin yanda kaganni kafara sona amma baka sanar dani ba kuma nacika maka alƙawarinka"

"No rouhi alƙawari bai cika ba akwai yara 10agaba"

"Masoyi waida gaske kake? Wacece zata iya haifan yara 10 awannan zamanin? Kawai kabar wannan zancen idanma kuma hakane yara 10 aina mai nisan kwanane yafaɗamin yanda zan bawa yaranmu labarin yanda mahaifinsu yaga mahaifiyars.... Maganarce ta tsayamin a maƙoshi naja wani dogon numfashi na sauƙe sanadiyyar Harshensa daya zura cikin kunnena kuka kawai nasaka masa saboda daɗin abunda yakemin ya rigada yagama gano loggo na idan yanaso ya fitar dani hayyaci lokaci guda ban ankara ba sai dai naji harshensa cikin kunnena sauƙe komai mukayia a gefe saida muka faranta ran junanmu tukunna ya samu ƙwarin guiwar sanr dani yanda ya ganni.

"Rouhi kinason sanin yanda na fara ganinki har nakamu da soyayyarki?" na gyaÉ—a masa kai alamun eh inaso.

"Okay listen."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Bayan nagama buga worldcup kamar wannan lokaci ina hutawa naɗauki hutun lokaci, kamar yanda kika gani mafi akasarin lokuta bani nake gudanarda account's ɗina na social media ba ke kinsan komai akwai masu tafiyar dashi amma lokaci zuwa lokaci idan naji ina cikin kaɗaici kuma ina zaune babu abunda nakeyi Nakan ɗauki wayata nayi logging accounts ɗina aranar ma ina zaune naji sha'awar hakan ashe da rabon zan haɗu da Sanyin idaniyata wank ɗumbin alkhairi krmin maraba ina cikin Instagram notification ya shugomin kamar Haka Marmeeyy and 95677 others started following you ban kulaba ban duba ba duk da sunan marmeeyy yaɗauki hankali na, ina samun Likes babu adadi kowani seconds amma bantaɓa damuwa dana duba wanda suke bani saƙonni da likes ba Tsawon wasu minutes da shigowar notification saiga notification na likes sun fara shigowa picture dake jikin profile shiya ɗauki Hankali na amma ban dubaba na ajiye wayar bayan wani lokaci hankalina yakasa kwanciya na tsinci kaina dason shiga Wannant account ɗin danaga an rubuta Marmeeyy na daure banshiga ba aranar amma sam nakasa samun nutsuwa saida na shiga account na duba, Uniform ne ajikinki da niqab an ɗauki picture ɗin zallan kwayar idonki kawai yake waje Bansan dalili ba kika hanani kwanciyar hankali kika ɗauke min duk wata nutsuwa ta nidai kawai abunda zan iya cewa shine wannan wani lamarine daga wajan ubangiji wanda shi kaɗai yasan abunda ya tsara a kanmu shi kaɗai yasan irin albarkar daya shiryawa rayuwarmu har takaiga ya haɗamu haɗuwarda ba'a taɓa zatonta ba Allah kaɗai yasan me zamu haifa a duniya may be ma sai mun haifi sama da 10 ɗin danake faɗa" duka nakai masa ina faɗin.

"Masoyi kaifa sai ana labari saika canja ka ɗauƙo wani ka ƙarasamun abunda kafara please"

"Okay toh kina jina? Bayan ƙwana biyu naɗauki abun kamar wasa ban ɗauka soyayya bace ta kamani ashe itace nayita daure zuciyata ina tausar kaina amma bansamu sauƙi ba Ganin tana neman zautani yasa Na shiga neman ko wacece ke kinsan samunki bazai yimun wahala ba lokaci guda nasa aka nemaminke a lokaci na farko da aka kawomin picture ɗinki cikin kayan school na ganki a tunanina Zanji soyayyar taragu amma batayiba saima ta ƙaru toh ƙwayar idanuwanki kawai ta sanya na afka soyayyarki barega naganki gabaki ɗaya tun dana fahimci sone nake miki wanda abune mai wahala nasake yiwa wata mace irinsa saina sakawa raina bazanyi haƙuri dake ba lokaci guda na ɗaura niyyar mallakarki na sakawa raina bazan sarara ba har sai ranarda kika zama mallaki agareni ni bana cikin mutanen da suke ƙwallafa rai sai sun samu komai da sukeso na rayuwa ba amma akanki na sake ilimin rayuwa har indai zan so abu kuma inada Hali da ikon da zan mallakeshi yazamamin kamar dole saina mallakeshi. Abu nafarko dana farayi shine na Sayi layin wayarki gabaki ɗaya karkice duk wani saƙo da zai shigo wayarki tawa yake fara shigowa Naga rashin dacewar hakan saboda kamar ina buɗa miki sirrin Kine duk da kusan duk yarinta ce aka cikata a wayar" harara na wulla masa a lokacin nafara aika miki da saƙo kullim saboda inason kisan da kasantuwata, campanyn layinki dakansu suke alerting ɗina aduk sanda sƙon soyayya yashiga ko baƙuwar lamba data kasance kuma na mijine wanda bakuda dangantaka dashi karkiga laifina ina sonki ina da kishi sosai hatta da idan kina gida kaɗai Hankalina ke kwanciya idan kika fita har kidawo baja samin kwanciyar hankali hakan yasa na nemi wanda suke bibiyar rayuwarki nasan alokacin zakice wannan mutumin BIBIYATA YAKEYI kuma WAYE SHI, amma baki samu amsaba kin saka ayi miki bincike akan layina nikuma saina saka aka rufe campanyn layin gabaki ɗaya bawai dan ina tsoron ki gane ba saboda nasan cewa bazaki gano ni waye ba har abada idanba nine na nuna miki kaina ba kosu gidan layin basusan ni waye ba saboda akwai hannun danabi ya tsaya a matsayina. alokacin da kika sauƙe Qur'ani na aiko miki da saƙo wannan zoben ya daga hannuna yana nunamin, banyi tunanin zaki saka ba da kika saka nasamu ƙwarin guiwa sosai nasake samun kaimi wajan bibiyar rayuwarki ranar da kika ɗaura pictures ɗinki Jinayi kamar zuciyata zata fashe shiyasa nasa aka sauƙesu A lokacin bayan wasu A lokacina shirya bayyana miki kaina kuma nayi ƙoƙari wajan yin hakan sai dai nakasa kawai na fata tunkarar baba, nasan Baba bazai kasa sanar dake yanda lamarin ya kasance ba bayan wannan nafara fahimtar akwai wani abu tsakaninki da Brothern frnd ɗinki amma wannan abaya kenan ban nemi rabaki dashi ba sai kawai naƙara kaimi wajan mallakarki nasan banyi miki dai-dai ba saboda ban fara neman soyayya agareki ba amma nasakawa raina idan na aureki zan yi iya ƙoƙarina na sanyaki ki soni saboda kuma it works a ƙaramin lokaci kika fara sona duk wani abu a rayuwarki da kikaji kamar akwai Hannuna afaruwar hakan Yes akwai school ɗinku da komai nasan komaj a kanki Rouhi ina nufin everything" Na jijjiga kai.

"Kai kaÉ—ai ka isa aikata haka masoyi kuma naji daÉ—i daya kasance baka barniba saida ka mallakeni ka koyar dani soyayyarka kuma ka fahimtar cewa ina sonka, ina sonka sosai"

"Nima inasonKi Rouhi kiyi bacci kinji?"
Chapter 99 · 0% Book details