← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 106

Sashe 46

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama nashiga na ajiye ruwan agabansa nashiga nazauna suma suka shigo saida suka zauna sannan na nuna masa Anty fadeela nace.

"Hamma ga anty fadeelah danake gaya maka wannan kuma Aysha itama sistanace" anty fadeelah da Aysha duka suka gsheshi ya amsa da fara'a Aysha ta ɗaga taklleshi kamar ance nakai idona kan Aysha naga tana ƙareshi da kallo banji daɗin kallonda take masaba dukda ban fahimci ma'anarsa ba shikam hankalinsa gabaki ɗaya yana kaina kamar yanda nake ganin yayimin Kyau haka shima yake ganin na ƙara masa kyawunda bayason ɗaga idonsa daga kaina. Bai wani daɗe sosai ba yatashi tafiya. Banso ba dan naso ya daɗe sosai tunda washe gari zaiyi tafiya zaije yajira isowar su Ummi har bakin motauka rakashi kamar yanda muka shigo dashi."

ZAYNAB ALABURA
"Kinga na sha'afa na manta da ruwan shyin. Babanku yaga shiru yakira" na mike ina fadin.

"Kiyi zamanki bari najr nakai masa. Nafada hadeda cire wayata a chargy nafice da ita saida nasake daura ruwan shayin akan wuta yayi zafi sannn na juya nanufi dkin Baba. Da sallama nashiga na sameshi zaune hannunsa dauke da casbi. Ya amsa sallamar na isa na ajiye akan center table na zuba acikin kananun cup sannan na nemi waje na zauna ina jira yadan huce na mika masa. Na zauna gefe ina fadin.

"Barka da hutawa Baba" ya amsa.

"Sannu Marmeeyy yaya gajiyar hanya?"

"Lafiya" kawai nace.

"Kunbar su mummyn naku lafiya?"

"Lpy kalau tama bada sako a baka yana wajan Mama"

"Toh madallah nagode" yafada sannan mukayi shru kamar wanda yake jira nafada masa wata aikar bayan wannann yaji shiru. Yayi yar gyaran murya.

"Marmeeyy bakuyi magana da Mummyki akan zancen dawowarta ba? Ko akwai abunda tace?"

"Batace komaiba Baba amma mai zai hana kairata ka tambayeta? May be jira takeyi ka tambaya shiyasa batace komaiba" jijjga kai kawai yayi yana mamakin halin marmeeyy da batajin kuiwar fadar magana koda tafi karfin shekarunta. Idan aka sanya maganganunta da shekarunta a mizani magnganun zasu rinjayi shekarun, bbu wanda zai yarda karamar yarinyace mai zaro maganganu haka. kuma gashi ta iya fahimtar mutannenda take tare dasu.

"Baba kaga wayarda Yaya Ahmad ya siyamin" na fada ina mika masa wayar. Ya rigada yasan zancen wayar Ya Ahmad ya gaya masa ammma saiya nuna baisani ba.

"Madallah Ahmad yayi kokari Allah yabiyashi"

"Amin Baba amma baka ganin wayar tayi tsada da yawa" ya jijjiga kai.

"Batayiba Allah yasaka masa da alkhairi" na amsa da amin sannann na tuna maganar wannan mutumin inaji kamar intambayi Baba ko yasanshi.
Nadade ina tunani Baba yana kallona kawai yasan akwai abunda nake nazari akai"

"Wani abunne Marmeeyy?"

"Uhmm dama Baba inaso na tambayeka akwai wani lokaci daka tabayin bakin kamar watannin baya wanda harn kasaka mukayi musu aiki. Daga ina suke Baba?" Yana kare min kallo yanason gano wani abun yabani amsa.

"Wani senate ne da mukyi school tare ya rako wani nrman alfarma wajena da izinin governor wani abunne?" Na zaro ido hadeda jijjiga kai.

"Babu komai kawai ma tambaya ne naga baka taba hirar ba. Lallai wannan Babbar alfrmace Baba governor fa kace kuma kayi musu?"

"Eh sosai Babba ce danshima da kansa ya kirani kuma yazo (governor). nayi musu alfarmar sboda naga dacewar hakn"

"Allah yataimaka"

"Amin" alokacin tunani yashiga raina abunda nake zato ashe n haka bane" Amma wace irin alfrma ce har governor zaizo dakansa?

Nayi masa sallma nafita dan nasan Hamma na jirana washe gari tashin sassafe zaiyi."

ZAINAB ALABURA
Wannan Littafin na kudine kibiya 300Naira ta asuusn bankina domin samun damar yin karatu cikin kwanciyar hankali. 0003075326 JAIZ BANK ZAINAB M BAWA

Bayan isata daki na iske Missed call dinsa guda biyu ban bata lokaci ba wajan maida masa da kira saida ta kuwa katsewa yadaga. Nayi sallama ya amsa sannan na daura da fadin.

"Sorry Hamma ina wajan Babane kakira bana kusa"

"Babu komai nima yanzu ina duba kayayyakin da zanyi tafiya dasu ne" mukaci gba da waya sai wajan 12:00am mukayi sallama washe gari sassafe ya dauki hanyar Abuja yana isa ya kirani kwanansa biyu acan yana jiran su ummi bayan saukowarsu ko kwana daya basu karaba suka kamo hanya cikin dare suka iso.

Washe gari sassafe Maryam ta shirya Babu yanda batayiba na shirya mutafi tare naki. Tun lokacin da wannan abun yafaru nayiwa kaina alkawarin bazan sake zuwa gidanba. Data matsa sai nace mata ni narigada nayi alkawari bazan sake zuwa gidanba sai amatsayin matar Hamma. Batayi fushi ba kamar yanda nayi tsammanin zatay ba itakuwa a wajanta dake zuwanmu wancan lokacin taso ta zargi wani abun yasa bata tsaurara akan sainaje ba. Baba shi da yaso yabari su Ummi suzo dakansu kamar yanda suka kawota kar suga kamar saurin maido musu da ita suke. Amma ganin yanda maryam ke daukin zuwa ganin iyayen nata yasa yace Mama tashirya ta kaita Mama ta shirya bayan ta shiryawa su Ummi abun trba wnda zata kai musu. Da Maryam zata tafi 2k Baba yabata yace su hau adaidaita.

Bada kayanta suka tafiba saboda adaidaita zasu hau shiyasa tace daga baya zatazo tadauka. Warmers dinda Mama ta shirya musu abinci kawai suk dauk sai jakar Hannu.

Sun samu Ummi na baccin gajiya sai bayan zuwansu tatashi. Kai tsaye maryam tawuce dakinta da murna ta tasota. Itama Ummi tayi murnar ganin yartata gashi tayi kyau ta sake murjewa da alamu tasamu kula mai kyau. Ummi ta karaso ta zauna damurnarta tana fadin.

"Ashe kuna tafe? datsu nagama fadin idanna gama baccin gajiya zanzo na tafi wajannaku"

"Ayya da gajikam sosai mu Yakamata muzo muyi muku bangajiya ai kinga Maryam ma ta kagu taga Umminta"

"Ita ta tasoku kenan ja'ira, mungde sosai mamansu Marmeeyy da Maryam Allah yasaka da alkhairi yaba zumunci zamuzo har gida nida abbansu muyi godiya"

"Ah haba babu komai yaro aina kowa ne" Ummi ta danyi waige-waige sannan ta juya ta dubi Maryma tace ina marmeeyy? Bata kaiga bata amsa ba Hamma yashigo parlourn da Sallama. Maryam bata damu da shigowar Hamma ba tafara fadin.

"Ummi ai yanzu wasan buya zakunayi da Marmeeyy Saboda suna soyayya da Hamma" saida Hamma yayi turus yakasa karasowa ciki Maryam tacigaba da magana.

"Babu yanda banyi da itaba wallh Ummi taki zuwa kunyarki takeji" daga Mama har Ummi baki bude suke kallon Maryam Hamma najin haka duk gwarin guiwarsa saida yaii kunya dasauri yajuya zai fita Ummi ta Kirashi yadawo sai sunna kai yakeyi.

"Gaskiya ne abunda Maryam take fada?" Ya sauke ajiyar zuciya.

"Eh Ummi dam ko Maryam bata fada ba kuna dawowa nayi niyyar samunku da Maganar"

"Toh madallah Alhamdulillhi abu yayi kyau dama abbanku ya fahimci wani abun tun ranarda zamu tafi ya fadamin inata addu'a Allah yasa zarginsa yazamo gaskiya nayi murna sosai Allah ya tabbatar muku da alkhairi. Kaji tsoron Allah ka rikemin diyata tsakani da Allah wallh nayi farin ciki nadade ina maka sha'awar auren Marmeeyy yarinyace mai hankali amma fahimtar hankalinku kamar baya kan juna yasa ban daga zancenba Allah yamuku albarka. Kansa akasa ya amsa da Amin cikin jin dadi.

"Bakice komai ba" Ummi tafada tana kallon Mama. Mama wacce ke murmushi tun lokacin da aka fara magana tasake fadada murmushin.

"Ai kince komai Ummi Allah ya tabbatar da Alkhairi yasa muna cikin rayayyu za'ayi" su duka suka amsa da Amin. Hamma ya saci kallon mama dukda wancan ranar bai daga ido ya kalleta yanda zai ganeta ba amma kamanninta daya kalla yau ya tabbatar masa da cewa itace mahaifiyar Marmeeyy duk da a haka baza'a taba zaton ta ajiye yarinya kamar Marmeeyy ba balle Yaya Habibu. Kamanni suke sosai da Marmeeyy kamar an tsaga kara. Yayi saurin mikewa ya fice dan baisan tana wajanba."

Mama tabawa Ummi warmers dinda tazo dasu Ummi nata godiya sannan tayi mata Sallama tafita.

Adaki tasameni nayi mata sannu da dawowa ta amsa sannan ta zauna fuskarta babu dadi.

"Marmeeyy zo zauna magana zamuyi" nazauna ganin babu fara'a afuskarta yasa nasha jinin jikina.

"Ashe akwai abunda Zaki boyemin matsayina na mahaifiyar ki Marmeeyy? Nadauka kowani hali kike ciki ni zaki fara sanarwa" kaina yadaure sosai narasa yanda maganar Mama ta dosa. Nayi tunani dayawa abubuwa dayawa sunzo raina amma banda zancena da Hamma.

"Ashe soyayya kuke da yayan Maryam ni uwarki sai dai naji agari? Haka kikag ya dace?" Na dukarda kaina kasa.

" Dan Allah Mama kiyi hakuri wallh bawai naki fada miki bane da wata namufa kawai banason asanine saboda kar manya su shiga zancen"

"Bakya son manya su shiga bakya sonsa ne?" Na girgiza kai da sauri.

"Kina sonsa kenan?" Nayi shiru ban bata amsaba tafahimci abunda nake nufi dan haka ta canja tambayar.

"Bangane abunda kikac bafa Marmeeyy mr kike nufi da bakyaso manya su shiga zancen?"

"Naga Baba baida kudi kar suzo suce zasu turo n sanyashi a wahala shiyasa"

"Wannan ba dalili bane da zakiki sanar dani wannan zancen. Nadauka kinada wayo da idan lamari irin haka tataso ni zaki fara tunkara ashe babu. Yanzu haka kin sakani a kokonto bansan abubuwa nawa kike boyemin ba ta iya yiwuwa akwai wani abun. Idan akwai gra ki sanar dani tun yanzu idanna sani daga baya abun bazaiyi mana kyau ba. akwai wani abun?" Nayi kasa da kaina ina wasa da yatsuna.

"Menenne ina jinki"

"Zan fada miki amma Mama dan Allah kimin alkawari bazakiyi fushi ba" saida ta karemin kallo sosai.

"Nayi ima jinki"

"Shekara biyu baya harda watanni akwai wata number da take damuna da message ko ankira bata shiga kuma ko nayi blocking zatayi unblock da kanta message yashigo. Sannan duk wani abunda layina yake ciki Whatsapp ko kira ko Instagram wannan lamba tanada masaniya akai. Ko pics na daura a Instagram saukesu akeyi ayi delete a page dina gabaki daya harna hakura na daina. Duk wani labarin daya kamata nabata gameda numbern saida na bta har zuwa da akyi ofishin layi suka kulle." Tsoro karara nagani a fuskar mama abunda banaso kenan yasa tun baya ban gaya mata ba.

"Mama dan Allah kiyi hakuri wallh ban fada muku bane saboda banaso na daga muku hankali" shafo fuskata tayi cikeda tausyawa.

"Marmeeyy duk ke kadai kika shanye wannan abun?daga yau karki sake haka duk wani halinda kike ciki ki fadawa mamanki. Kikace kina zargin ba Bahaushe bane?" Na jijjiga kai.
Chapter 46 · 0% Book details