← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 106

Sashe 49

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Marmeeyy naji abunda yafaru kuma banyi bakin cikin hakan ba saboda inada tabbacin Baba bazai canja miki masoyiba face ya samo miki wanda ya ninkashi. Sannan kuma na tambayeki watannin baya nace miki kina soyayya kika cemin A'a meyasa?" Dakin sanar dani tun wancan lokacin da abun baizo ya kwabe hakaba. Munason farin cikinki kamar yanda kike kokarin faranta mana amma yanzu Bakin alkalami ya rigada ya bushe Marmeeyy kiyi hakuri inada tabbacin akwai alkhairai masu yawa a gaba" na sunkuyarda kaina kawai inata kokarin hana hawaye sakkowa kan kumatuna. Na dago bayan naci galaba akan hawayen na sakala murmushin karfin hali.

"Ya Ahmad kaifa kacemin Duk wani hukuncin da Baba zai yanke a kaina natsaya na fahimceshi. Tayaya zanki jin maganarka? Karka damu na fahimceshi na zubawa sarautar Allah idanu kasan dai kawai lamarinne bazai goge araina ta dadi ba sai a hankali. Na tabbata anayin aurensu zan dainajin komai inada yakinin bazanji komai akan mijin yar uwata ba" Murmushi Ya Ahmad yayi dama yasan za'ayi hakan dam Marmeeyy batada matsala.

"Allah yamiki albarka yadawo miki da ninkin farin cikin da kike tunanin kin rasa" cikin raina ma Amsa da Amin. Bamu zauna gidanba muna gama aiki ya maidamu gida.

Ankama azumi cikin yarjewar ubangiji wannan ayayinda nikuma ma dukufa Addu'a ina gayawa Allah damuwata a kankanin lokaci nafara jin saukin abunda nakeji."

Anata shirye shiryen Sallah nikam nazuba musu idanuwa akan duk wani abunda sukayi dai-dai duk wani abunda akeyi bandani iyakaci idan aka kawomin nayi godiya nakarba. Mama, Baba da duk sauran wanda sukasan yanayin mu'amalata da mutane abaya yanzu suna cikin damuwa danko hira nadaina zama anayi dani bawai dan bazan iya zama cikinsu ko akwai abunda yake damuna yasa nake haka ba duk yanda na zauna Sai Aysha tazauna itama ta yabamun maganganu bana kulata yawanci Anty fadeelah ke amshe maganar ta yaba mata maganganu itama harda gori take mata tace saurayin da take haukar akansa ko lamabr wayarta bayi da ita bare asaka ran wata rana zai kirata.

Akayi sallah angama Lpy daga nan aka shiga hidimar biki daga gidanmu har nasu Hamma bawani shiri akeyi ba ita kanta Ummi batason auren amma babu yanda ta iya saboda zancen daga sama yake. Maryam tabata labarin irin Abubuwanda Aysha ta dinga yiwa Marmeeyy a Abuja sam taji yarinyar bata kwanta mata araiba. Koda tajewa Abba da maganar yanuna mata shima babu abunda zai iya tunda shima mahaifinsa ya yanke wannan hukuncin.

Mama dafarko kamar bazata fara wani shiri ba sai taga rashin dacewar hakan ranta bayaso haka ta zage tafara hidima. Duk wani abu kafin Baba yayi saiya shawarce ta. Ya Ahmad ne yayi mata furnitures shida ita sukaje suka zaba. Dan rashin kunya tazo akan mu rakata zaben furnitures tayi hakanne danta cusa mana haushi arai. Nikam dama tasan ba zuwa zanyiba Anty fadeelah ma taki zuwa daga ita sai Mama da matar Ya Ahmad suka tafi. Dama Baba yabawa Mama kudin kayan Kitchen da Sauran wasu abubuwan. Daga wajan sayayya gidanta kai tsaye aka wuce dashi dan angama komai aka zubasu sai biki saura 1week za'ayi jere.

Idan nace banshiga tashin hankali da karatowar wannan lokaci ba nayi karya. Kawai tafiya nake ina rayuwa amma hankalina baya jikina ido nakebin mutane dashi ina kallon ikon Allah wai Hamma Wanda nashirya rayuwata dashi shine wanda zai auri yar uwata duk yadda naso daurewa haka nake zama nayi kuka wasu lokutan bana iya shiga mutane da lokacin bikin ya karato nadaina zama agida. A school nake wuni zubur ko banda lactures haka Maryam take jirana har sai lokacin da natashi tafiya kafin itama tatafi. Kullum cikin tausayamin take bata taba yarda ta sanar dani halinda Hamma yake ciki dan tasan Babu alfanun hakan zata dada dagamin hankaline kawai. Tunda aka soma maganar har rana mai kamar tayau Hamma bai taba kiran Aysha ba bai nemi yasanta ba sam danko kamanninta bai sanib. Gashi Maryam ta dada hura masa wuta a zuciya data sanar dashi irin Abubuwanda take yiwa Marmeeyy.

Ranar naje makaranta ban dawo ba sai yamma ina shigowa naga manya manyan motoci ima shiga nasamu Su Mummy ne suka iso. A shahshin Baba suka sauka itada wasu yayinda sauran yamn uwan suka sauka a gidn mahaifinsu dake bauchi. Nashiga na gaisheta tanata murnar ganina amma ni sai taga walwalata ba kamar yanda na sababa jikinta yayi sanyi alokacin tasaka Hakuri saida ta tambaya nakasa cewa komai banda murmushi danakeyi na karfin hali. Anty fadeelah ce tafara yimata bayani natashi nafice dasauri. Mummy tamike rai bace tayi dakin Mama tana fadin hakanma bamai faruwa bace."

ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin

Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba

Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔

Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo

Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍

Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝

------

Sallama tayi sannan ta kutsa kanta cikin dakin. Mama wacce ke daki tanajin sallamarta ta nufo palour fuskar Mummy babu annuri hakan yasa Mama taja jinin jikinta batasan abunda Mummy tazo dashi ba ko wani rikicinne kuma? Tanata saƙe-saƙe acikin zuciyarta. Jiki a saɓule tasaka murmushi akan fuskarta haɗeda faɗaɗa fara'arta tace.

"Sannu da zuwa Mummy kece da kanki dakin zauna ai kin huta idan wani abunne saina shigo" Mummy ta girgiza kai.

"A'a mamansu wannan ba maganar jira bace tafaÉ—a tana zama akan kujera"

"Toh Allah yasa dai lpy"

"Ba lafiya ba gaskiya ashe wannan yaron da Aysha zata aura saurayin Marmeeyy ne? Wane irin abune haka tayaya za'ayi wannan lamari ace saurayin ƙanwarta meya faru da za'a canja mata masoyi zuwa kan ƴar uwarta? Wannan bama mai yiwuwa bace dole azo a canja zuwa kan
Masoyiyarsa ta asali. Ko menene dalilin wannan sauyinma tukunna?"

"Babansu kawai yasan dalili danshi ya canja kuma bai sanarwa kowa komai ba. Amma ita Marmeeyy taceta hakura abar zancen kawai Sam bataso atada lamarin"

"A'a wannan ai bazata yiwu ba kinsan halin Marmeeyy ai saboda ke kika haifeta bazata taɓa damuwa ba har indai akan ƴan uwanta ne yanzu muje wajan Babansu idan bazaki masa magana ba kiyimin iso ni zan masa magana" Mama ta ɗaga da mamaki tana kallonta wai itane Mummy takeso tayi mata iso wajan Baba Mummy mai nuna isa da gadara wajan kowa. wane iso take bukata bayan kai tsaye ma shashinsa suka sauka itada baƙinta. Kodan tundaa ya kasance anan ɗakinta yake tun kafin tabar gidan. Saida tasake maimaitawa sannan Mama ta miƙe tayi gaba Mummy tana binta suka shiga har wajan Baba dake da mutane a ciki yabar musu Babban palournsa dayake zama yakoma palournda yake kusada main ɗakinsa. Da sallama mama ta shiga Mummy na biye da Ita. A palourn ta zauna ta jira Mama tayi masa magana suka fito tare. Mama tayi hanyar fita. Mummy tace.

"Kidawo kizauna a gabanki yakamata ayi zancen ai. Ganin Baba ya tsura mata idanuwa yasa tadawo ta zauna ba'ason ranta ba. Mummy Tajira Baba yazauna sannan tafara karanto masa ƙorafinta. Saida tagama sannan yace.

"Bantari nunfashinki ba Mummy amma akwai babban dalili dayasa akayi hakan wanda yin hakan kawai shine mafita. Banyi hakan dan banason Marmeeyy ko inason fifita Aysha ba.
Aysha da Mummy dukansu Ƴaƴanane kowacce inason farin cikinta babu wacce zan tauye acikinsu dan ƴar uwarta taji daɗi"

"Mummy kibar zancennnan kawai har indai Marmeeyy ce ta fahinci kowa da komai bata ɗauki abun da zafi fa kawai dai ranta baya mata daɗi ne kuma bata fushi da hukuncin" Mama tana gama faɗin haka ta miƙe tana tace"

"Bari naje zamu kasuwa da Aysha akwai kayan kitchen da bamu gama sayayyya ba yanzu zamu shiga mu sayo" har takai bakin ƙofa Baba yakira sunanta. Ta tsaya cakk dan Baba ya kwana biyu bai kirata dasunanta ba bata juyo ba Har saida yacigaba da Magana.

"Ko sau É—aya bazaki tambayeni dalilin dayasa najuya auren Marmeeyy kan Aysha ba? Da zaki tambayeni da zan zauna nayi miki bayanin komai tun daga farko yanda zaki fahinci lamarin. Baba (Alhaji Habibu) shine ya hanani faÉ—a miki komai amma har indai zakici gaba da shareni banaji zan iya bin umarninsa zan zauna nayi miki bayani ki fahimta anyi abunne batareda son zuciya ba" sai alokacin ta juyo tayi murmushi.

"Tunda Har Baba ya hana ka gayamin toh sanina baida amfani dan yasan dalilin dayasa yace kada ka gayamin ina bayan hukuncinsa. Sannan niba shareka nakeyi ba kawai yanayin da Marmeeyy ke shiga ke jefani wani yanayi da banajin daÉ—insa amma da zarar angama biki nasan komai zai dawo dai-dai" Bata sake magana ba tafice Baba ya sauke ajiyar zuciya yabita da kallo yanajin babu daÉ—i acikin ransa."

Dake wannan semetern bawani tsayi zatayi ba har munci rabi abubuwa sun fara zafi exam baifi saura 1month ba hakan yasa sam bana zama agidan kuma naji daÉ—in hakan dan nasamu damar kaucewa abunda banason gani.

ƴan uwan Mummy suka haɗa event Mummy bataso hakaba dan itama auren ya fice mata arai. Mamakin yanda Aysha take rawar kai takeyi tana ganin wautarta zata auri mijinda baya sonta take wannan abun wanda takasa gane dalili yin hakan son saurayin dama takeyi ko tanayine danta ƙuntatawa ƴar uwarta kamar yanda fadeelah tafaɗa mata.

Nadawo daga makaranta nawuce É—akinmu kai tsaya dukda yanzu bancika zama a ciki sosai ba nafi zama É—akin Mama dan banason zama waje É—aya da Aysha. ÆŠakin nasamu acike da Æ´an mata Æ´an uwansu Aysha waÉ—annan masu masifar jida kansu. Ina ganinsu najuya dasauri zanbar É—akin dan danasan suna ciki bazan shigaba bansan da isowarsu ba.
Chapter 49 · 0% Book details