← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 106

Sashe 41

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"abunda ta faÉ—a gaskiyane ai dukanmu ya kamata kayiwa faÉ—a mu canja ba marmeeyy ita kaÉ—aiba. Hakan yana nuna matsayin marmeeyy daban yake da namu. Ko kafi sonta kokuma mu kafi sonmu shiyasa baka takuramu. Amma idan akayi duba da yanda marmeeyy ke mu'amalantar mutane zan iya cewa kafi sonta. Dannima anawa wajan hakanne"
Ya kalleta da tambayar me nata wajan hakan yake nufi. Bai kaiga samun cikekken tunani ba abokinsa yasake faÉ—in.

"Kabar amaryarka a tsaye ga dukkan alamu tagaji kabar yarannan abar musu mota É—aya su biyomu abaya" badan yasoba suka wuce suka barmu nida Maryam zallah dan Anty fadeelah tabisu
aysha kanma baisan yanda tayi ba.

   Sai da nayi iya ƙoƙarina wajan hana hawayena zuba dan tabbas zai ɓatamin ƙwalliyata. Ahaka maryam tashigo ta sameni ta ƙarasa kujerar da zauna tana faɗin.

"Babe kefa ake jira kokin fasa tafiya ne?"
Na kalleta da zan iya zuciya danace nafasa tafiyar amma bazan iyaba banida wannan ƙarfin halin.

  "Allah babe takurin ya Ahmad yakemin yayi yawa sai nakeji kamar nafasa zuwan kigafa kowa wajan babu mayafi amma  haka yamatsa wai saina saka mayafi ko matarsa bata dashi gasu anty fadeelah da aysha nanma duk babu ni kaɗai kawai zaice nasaka"

"Babe nifa gani nakeyi kamar yafi sonki ne akan sauran yasa yake haka kokuma kinfi jin maganarsa kinsan fa kowa yana gadara da abunda yake iko dashine ni aganina karki saka wannan aranki" nayi murmushi sannan nace.

"Duk da haka fa wannan ba hujja bane muduka ƙannensa ne sai yayi hukunci ma kowacce a cikinmu"

"Nidai babe tashi mutafi kinsanfa bazasu zauna jiranmu ba idan kuma kinaso ayi babu mu toh" namiƙe nace barina ɗauko mayafi.

"ki ɗauko mana tare" tafaɗa nashige ciki sannan nadawo hannuna ɗauke da mayafai ƴan ƙananu muka yafa muka fice. Ango da abokanansa gabaki ɗaya suntafi saura wancan motarda ya Ahamd yace mushiga ɗazu. Kai tsaye wajanta muka wuce. Kafin mu isa motar aka buɗe ƙofa dasauri ya buɗe mana ƙofar baya cikeda girmamawa. Batareda mun lurada kamannin wanda ya buɗe ɗinba muka shige muna shiga yarufe sannan yashiga driver ya tada muka tafi. CHIDA EVENT CENTER shine wajanda muka nufa wajene ƙayatacce mai kyawun gaske. Harabar wajan kamar ba dare ba saboda yanda hasken fitula ya haske ko'ina. Tun daga wajema abun kallo ne izuwa ciki yanda akayiwa wajan decoration mai masifar ɗaukan hankali. Kyawun wajan ya ƙarawa mutane wajan kyau duk da cewa kana kallon mutanneda suke wajan za'asan bikin ƴaƴan manya ne.

  kafin mu ƙaraso faɗa sosai Mummy taketa yiwa su anty fadeelah da aysha akan meyasa zasu tafi su barni bayan ni baƙuwace babu yanda nasani alokacin tasaka Anty fadeelah  kirani saboda ita batada contact ɗina. Dayake ina kallosu yasa ban amsa ba na ƙarasa wajan. Ina zuwa aysha taja tsaki tabar wajan banɗauka dani takeyi ba nasan dai muna yawan haurawa amma yanzu ai babu abunda ya haɗamu dan haka na wuce wajan Mummy.

"Hankalina yatashi marmeeyy anbarku agida can bayan bakusan waje ba Ahmad bansan wane irin abun yakeyi hakaba sa'arsa ɗaya kun iso yanzu da saina ƙarasa har gaban amaryarsan naci ƙaniyarsa. Murmushi kawai nayi ta miƙa mana bandir na kuɗi nawa daban ta miƙawa maryam nata daban tace muyiwa ango da amarya liƙi. Natsaya ina kallon ikon Allah ko Baba samun irin wannan kuɗi wahala yake masa amma nan gashi an damƙa mana shi wai muyi liƙi. Can gefe danaga su aysha suna zaune muka ƙarasa amma sai naga ta kauda kanta dama suna zaune da sauran ƴan matanne sa'anninmu suma kamar wanda tafaɗa musu wani abun sai naga sun kawarda kai harda masu jan tsaki. Haɗeda yimana wani kallon ƙasƙanci. yanayin shigarmu da tasu iri ɗaya ce ganin irin kallonda muke mana yasa naja hannun maryam muka bar wajan muka zauna gefe Daga yanda muke zaune muna iya kallon yanda ake wasa da kuɗi abun. Ashe duk wanda akayi abaya wasane yanzune ake liƙi abokanansa ma kamar wanda sukayi taru suka ajiye suna jiran zuwan lokacin bikin.

  Muna zaune aka kira ƙannen ango naga ƴan mata sun tattashi cikeda  masifar jida kansu suka isa aka fara liƙi bantashi ba hakama maryam har suka gama kwasar rawansu suka dawo. Kusan 30minute muna zaune a wajan hancina yafara jiyomin wannan ƙamshin turare mai masifaffen daɗi da sauƙarda nutsuwa wannan ƙamshin ya tsayamin araina da duk yanda najishi bana iya mantashi duk ɗaruruwan mutane masu aji da suke wajan cikeda ƙamshinsu saida wannan ƙamshi yafita daban. Ajiyar zuciya nasauƙe saboda yau naji mai irin ƙamshin hankalina ya ƙwanta. Ina zaune naji Mc yana kiran Hajiya marmeeyy yanason ganin Hajiya marmeeyy afili ban kawowa raina ni bace har saida yace ango yanason ganin ƙanwarsa Marmeeyy a fili. Kasa tashi nayi inata rabe raben idanuwa suka mutane sun zuba ido suna son ganin ta yanda zan fito. Saida maryam ta matsa sannan natashi amma ahakanma tareda ita babu yanda batayi nasake ta ba naki sai da mukazo daff shiga filin tajanye hannunta tayi baya da sauri. Najuya ina kallonta gashi  babu halin na fita tunda na rigada na fito har an haske  ni na ƙarasa har wajanda Ya Ahmad da amaryarsa suke tsaye ƙafata tana rawa saboda idon mutane dayake akaina. Ina shiga narasa abunda zanyi sai kawai nacire kuɗin nahau musu manni. Alokacin Mummy tafito itakuma tafaramin Manni fuskarta ɗauke da farin ciikin da ita kaɗai tasan ma'anarsa tun tafiyarsu Baba nake kallonta ahaka.
  Ya Ahmad ma yaciro kuɗi yanamin manni gabaki ɗaya sai mannin yadawo kaina. Mc yana faɗin.

"Uhmmm Hajiya marmeeyy ƴar gata autar Mummy. Allah yanuna mana naki auren kema musha biki za'ayi kallo ranar bikin auta" Aysha daga yanda take kamar zata fashe dan baƙin ciki. Sai take ganin kamar wanda suke abun da gayya. Ya Ahmad kanma datayi masa magana ko ajikinsa ya sake sai liƙi yake yiwa marmeeyy wato babu alamun zai gyara kenan dukda tasaka haƙuri magantu. Taja tsaki yafi a irga.
Mummy  takoma tazauna sannan ya Ahmad ya miƙamin key ɗin motarsa haɗeɗa faɗin.

ZAINAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

"Marmeeyy kuɗin wajena ya kusa ƙarewa kuma namanta sauran a mota amshi wannan key ɗin kifita harabar wajan ki danna key ɗin motar zatayi ƙara saiki buɗe ki ɗaukomin" yafaɗi haka bayan yamin kwtaancen yanda motar take. na amsa sannan Najuya nayi wajanda muka zaune banga maryam Ba. Nakira wayarta taƙi amsawa. Nasan tatafi wajan Yaya Habibu dan haka kawai na shareta dan koda zan mata kiran duniya bazata amsa ba. Da tafiya tsakanin Hall ɗin zuwa parking lot ɗin danshi yanda yayimin kwatance bama a ainihin main parking-lot ya ajiye motarba tayi ɗan gefe da wajan kaɗan. Kamar wanda aka share wajan babu kowa babu masu zirga-zirga. Bayan nafito ƙamshin ya sake bayyanamin ga dukkan alamu mai wannan ƙamshin ya gifta ta wajan alokacinda na isa wajan mota naji ƙamshin ya kusantoni dayawa dayawuce ace giftawa kawai akayi ta wajan. Da dukkan alamu mai ƙamshin yana zaune ne a wajan. Adaidai lokacin wutarda ke wajan ta ɗauke gabaki ɗaya tadawo dim haka na ciro wayata dasauri na kunna flash light ɗinta amma dake wayar taji jiki batama da haske sosai. Na isa gaban motar dasauri na buɗe aikuwa naga jakar kamar yanda yamin kwtance na ɗaukota dasauri dan nafara jin tsoro-tsoro. Jin alamun da mutum a kusa dani ya sanya nayi saurin jiyowa aikuwa nayi arba dashi a tsorace na cillar da wayar zan saka ƙara fahimtar hakan da yayi yasashi ƙarasowa da sauri banyi auneba sai ji nayi ya haɗeni da jikin motar haɗeda sanya tausassan hannunsa ya rufemin bakina ayayinda taushin hannunsa da ƙamshin jikinsa ya sanyani lumshe idanuwa sai inaji kamar wanda bacci zai ɗaukeni. A hankali na buɗe idanuwana akansa. Wajan akwai duhu sosai sai hasken farin wata daya hasko wajan amma ba sosai ba dake kamawar watan kenan baida haske sosai amma hakan hai hanani kallo cikin idanuwansa ba shima idon ya zubamin ina iya jiyo bugun zuciyarsa kamar yanda shima yake jiyo bugun nawa zuciyar gabaki ɗayanmu bamusan yanayinda muke ciki ba ni gabaki ɗaya natafi tunanine tunanin yanda nasan fuskar dukda duhu ya ɓoye kamannin amma sai inaji kamar na taɓa kallonsa. Abu ɗaya nakeda tabbaci shine mutuminda yake zuwa school ɗinmu amma fuskarsa a rufe da facemask a wancan lokacin. yanzu kuma akwai duhu sosai a wajan amma Koda ƙamshinsa zan ganeshi. Kuma ganinsa yanzu anan ya tabbatarmin da cewa shine baƙonda yake zuwa wajan Baba. Yanzu na yarda na tabbatarda shi kaɗaine mai wannan ƙamshin. Ko a wancan lokacin dana ganshi school ɗinmu jikina yabani da wata aƙasa amma ganin bai bani wata ƙofa dazan zargi wani abunba yasanya badan nasoba nasakawa raina wani abun daban ke kawoshi. ahankali na sanya hannuna nayi ƙoƙarin tureshi amma ko gizau baiyiba ganin haka yasa yaraba jikinsa da nawa yaɗanja baya kaɗan. Ajiyar zuciya mai sauti na sauƙe daya sakashi murmusawa dukda shima nasa numfashin yana bashi a wahala a wannan lokacin. Daƙyar na iya tattaro nutsuwata dasauri sauri nace.

"Waye kai? Bibiyata kakeyi nasani Danba wannan bane karo na farko dana ganka ba" duhune a wajan amma kallona yakeyi da rashin fahimta dan bai fahimci abunda nake faÉ—a ba. Iska ya furzar gabaki É—aya komai ya É—auke masa baisan abunda zaiyi ba. Dama shiyasa yake taraddadin haÉ—uwa da ita dan kalmarda zai furta mata ba baisanta ba. Ganin yatsaya yana kallona kamar statue yasa nima na tsaya ina kallonsa. Dafarko na tsorata amma yanzu sam tsoro yafice araina tunda nagane cewa shine mutumin can. Na tabbata baida niyyar cutar dani dan da yanada niyyar hakan daya daÉ—e da cutar dani.
Ganin ina kallonsa ya sanya yayi baya a hankali yasake shiga cikin duhu yanda alamun tsayuwars kawai zanna kallo dan yanada yaƙinin idan naganshi zan ganeshi, zan gane cewa Shine Hammood baisan kuma yanda ƙwaƙwalwata zata ɗauki lamarinba. Na gyara jinginuwata jikin Motar ina kallon ikon Allah abunma ni saiya fara bani dariya. saida naɗan dara kaɗan har lokacin kallona yakeyi baisan abunda yabani daeiya ba. Tsawon mintuna muna ahaka shiru naja ɗan siririn tsaki sannan nace.
Chapter 41 · 0% Book details