← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 106

Sashe 89

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran maryam Yayi suka fara waya tana kallon abunda yake faruwa. Cikin ƙwraancewa da salo haɗeda son burgeni Hammood yake buga wasa. Wannan wasan da zaiyi yasan zai sake taka muhimmiyar rawa a jawo hankalina gareshi. Duk wani salonda yasan idan yayi a wasan zai burgeni shi yakeyi. Shi awajansa hakanma rahama ne tunda Allah ya bashi baiwa sannan yasaka baiwar tazama abunda matarsa takeso da muradin gani a rayuwarta a ganinsa wannan wata dama ce da ubangiji yabashi tun kafin atafi Fisrt half Hammood yaci ball ɗaya celebaration muka fara anata murna da ihu. A idona Nawrah Da yaya habibu suka rungume juna da alamu basusan sunyi hakan bama saida suka ankara da abunda suka aiakata sannan ya saketa su duka sauka shiga taytayinsu. Ni kaɗai na lura da abunda yafaru Maryam kuwa baiwar Allah anjuya camerarta zuwa fili can kawai take kallo batasan wata na shirin iskantar mata da masoyi ba. Sa'i-Sa'i suke kallon juna sai suyi murmushi duk ina ankare dasu. Ana dawowa daga first half suka rama cin da Hammood yayi musu baƙin ciki raina kamar nayi kuka har wani ɗaci nakeji. Ana cikin wasa team ɗin su Hammood suka ƙara ɗaya. Angama wasa Su Hammood sunada 2 sukuma 1 aka tashi wasa akayi declaring su Hammood winners. munkoma gida batare dasu ba sai wajan 12yashugo idona biyu dan dawowata daga wajansu Ya Ahmad kenan.

Inajin buɗe ƙofarsa da gudu na tashi na nufi ƙofa yana kallona ya buɗemin hannu na ƙarasa na ɗaleshi gabaki ɗaya da.

"I made it Rouhi"
"Nasani I know You'll"
مبروك إليك أحسنت عملاً
(Natayaka murna Job weeldone)"

"Dagaske nayi?"

"Yes ka iya buga wasa sosai bantaɓa kallon ɗan wasan ƙallo kamarka a tarihin wasa gabaki ɗaya ba" murmushi yayi yaji daɗin maganata sosai. Sauƙa nayi daga jikinasa naja hannunsa har zuwa ciki. Saida yazauna sannan na kaleshi fuska cikeda murmushi da kuma zullimun abunda nakeson aikatawa nace.

"اسمح لي أن أهنيك"
(Let me offer you my congratulations). Yatsaya yana kallon abunda zan bashi. Murmushi nayi na sunkuyar dakai sai inajin bazan iya ba. Ya miƙe haɗeda riƙe hannuna yana kallon fuskata.

"Ina sauraronki Rouhi I'm eager naji abunda zai fito daga bakinki please say it" shi duk tunaninsa zan faɗa masa irin soyayyar da nake masa ne. Saida na runtse idanuwa na sannan na buɗesu akansa ƙara tsayina nayi yanda bakina zai iya sauƙa a dai-dai nasa saida na rufe ido sannan na sada Lips ɗina da nasa na kama lip ɗinsa na ƙasa nashiga tsosa rikicewa yayi dasauri ya mannani da jikinsa baiyi zaton abunda zanyi ba kenan. riƙe waist ɗina yayi ya ƙarfafamun tsayuwata yayinda ƙarfina yazama duk ajikinsa saboda akan yatsuna na tsaya yasan zan gaji. Sosai yake tayani muna kissing juna munji daɗinsa fiyeda wancan karo na baya dan wannna karo ana yinsa ne cikin shauki saboda duk rai sunason abunda suke aikatawa tsawon lokaci muka ɗauka a haka banja jiki ba har saida naji ni kaina ya isheni. Shikuwa maimaikon yaji yagaji saima wani kaimi dayake ƙara samu dukda nagaji amma ban daina bashi ƙwarin guiwa ba har yazare lips ɗins dakansa. yayi taking deep breath sannan ya sake manneni yana neman bakina zai sake mayarwa yatsuna nasaka akan lips ɗinsa ya tsaya yana kallona da kyawawan idanuwansa wanda suka fara canjawa. Saida na tsotse damshin dayake kan lips ɗina sannan nafara magana

"Is okay ya isa haka thats your reward dakayi wanning wannan match É—in. You only scored 1."
Yana rumgume dani batareda ya sakeni ba yace.

"Thank you thats a huge gift da na taɓa receiving alokacin danaci ball"

"أنت تستحق ذلك"
(You deserve it) nafaÉ—a ina sunna kaina.

"Nayi scroring 1 You kissed me sau 1 What if I scored 2 next time?" Da yatsuna nayi alamun 2 sannan nace.

"Then You'll have 2"

"dagaske" batareda na kalleshi ba na É—aga kai.
"Zan bakai mamaki next match"

"I'll be waiting" nafaɗa ina ɓoye kaina cikin jikinsa.

"kedai kawai Keep your Words kinyimin alƙawari dayawa remember?" na gyaɗa kai.

"Yeah ban mantaba"

"Muyi bacci koh? I'm tied amma kafin mu ƙwanta kinci abinci" kai na gyaɗa masa.

"Naci kaifa?"

"Ina jin yunwa amma ba abinci nakeson ci ba" shieu nayi kamar bansan abunda yace ba na raba jikina da nasa.

Kwanciya mukayi saboda shi kansa yace gajiye yake."

A match na biyu Hammood saida yayi scoring 3 each one yaci saiya É—ago hannunsa yayi kiss ajiki ya nunamin nafarko yatsa 1 yaÉ—aga na biyu ma haka. Haka na 3 mutane sai kallon al'ajabi suke dake akwai camera tako'ina kuma ansan matarsa ke wajan sai akayi tunanin kawai yana nunamin abunda yayi scoring ne ni dashi kawai muka san ma'anar kayanmu, wannan karonma haka aka gama cikeda nasara har yafi karon baya ma.

Yana wajan ɗan ƙaramin celebration da suka haɗa na winning match ɗinda sukayi amma gabaki ɗaya hankalinsa yana wajena Allah-Allah yakeyi ya dawo yasamu kyautar danayi alƙawarin bashi.

Muna zaune Da matar Ya Ahmad shikuma da yaya habibu sun fita ta dubeni.

"Marmeeyy kekam Allah yabaki wallh kinyi sa'ar miji mijinda kowace mace take fatan samu abun kamar wani mafarki Allah yabarku tare mijinki yana sonki sosai" na amsa da.

"Amin" sannan na É—aura da faÉ—in.

"Kema ai kinyi sa'a Ya Ahmad mutumin kirki ne" tayi murmushi.

"Sosai ma yayanki yanada kirki sosai. Yawwa kinga wannan Lina take koh Wallh kiyi hankali da ita hatsabibiya ce duk wata hanya da zataja hankalinsa na lura abunda takeyi kenan. Ranar mun fita da yayanki inaso naɗan taka ƙafata dake kinaan ai duk dare muna zaga waja koh? Tana tsaye ta sanya wasu mugayem kaya tana jiransa ya dawo mu munganta zaune ashe shugowarsa take jira. Yana zuwa ta miƙe da gudu ta rumgumeshi ƙoƙarinta ta haɗa bakinta da nasa wai adole tana masa murna. Dake shiɗin tsayayye ne kuma yana sonki yaraba jikinta da nasa bai bari tasanu nasarar abunda takeson yiba ya ɓata rai sosai yanayi mata magana akan bayson haka karta sake ƙoƙarin yimasa haka yanada mata kuma yanason matarsa baice mata yana neman komai a wajanta ba, ke dagani har Yayanki tsayawa mukayi muna kallon ikon Allah. Ba ita kaɗaiba kafin ya isa zuwa wajanmu mata nawa sun tsareshi? Kedai ki riƙe abunki Ki kalallameshi kinayin sake zakiji wuff irin wannan mazan ba ƙaramin riƙo akeyi musu ba Kiyi masa biyayya sosai yanda zaiji babu wata sai ke idan kikayi masa riƙon gaske shima zaiyi miki na gaske kinsan larabawa akwaisu akwai riƙon mata" murmushi kawai nakeyi amma araina inajin zafin cewa wai Lina na jiramsa yadawo. Banajin bacci amma nayi mata sallama na fita dan inaso naga marassa kunyan da suke taremin miji."

______________

Da sallama yashugo ɗakin ta amsa daga ƙwance yanda take. Ya zauna bakin gado.

"Sannu ko zamuje asibiti? Zazzaɓi tun jiya amma yaƙi sauƙa kekuma kinki muje asibitin banga mai son zama da ciwo ba sai ke" Turo baki tayi zatayi magana tunoda wanenne Hamma ya sanya tayi saurin maida bakinta.

"Hamma Nifa banason asibitin nan wallh koda yaushe cikin zuwansa muke daga wannan sai wannan gara kawai na ƙwanta har naji sauƙi" ɗan siririn tsaki yaja saboda wani lokaci taurin kan Aysha na damunsa"

"Bari naje nazo ki shirya Nima zanje na shirya idan kuma kin warke idan nazo saiki sanar dani zaki kama duk wata hidimar da take kanki saboda na ɗaga miki ƙafa ƙwana biyu bakida lafiya amma tunda kin gwadamin bazakije asibiti ba kin warke shikenan saiki cigaba da duk wani abunda yake kanki" Sarai Aysha tasan abunda yake nufi tayi ƙoƙari tamiƙe duk da zazaaɓin dayake jikinta.

"A'a Hamma bari na shirya kawai kaje ka shirya mutafi" saida yayi dariya ganin yanda tayi reacting lokaci guda.

"Okay Toh kona taimaka miki? Naga jikin babu ƙarfi"

"No kaje ka shirya kawai zn iya" miƙewa yayi yafice 10minute gabaki ɗaya sub shirya kashe abubuwan wutan gidan kawai yayi ya ɗauki wayoyinsu suka wuce asibiti. Bayan wasu ƴan gwaje-gwaje ya nuna tana ɗauke da ciki na sati 7. Dagashi har ita sunyu murna likitar tayita jan hankalinsu da bayani akan yanda zasu tafiyarda lafiyar ta sannan tace idanda hali ya ɗaga mata ƙafa har na wani lokaci zuwa cikin yayi ƙwari. Bayan ya biya kuɗin ganin likita dana test dana magani suka tafi gida. Yana zuwa ya kira Ummi akan Taturo masa maryam tazo Aysha babu lafiya Ummi ashe Likitar takira ta gaya mata tun bayan fitarsa toh kawai ta amsa masa sukayi sallama.

Bayan wajan 2hours dayin wayarsu sukaji sallamar Maryam hamma yatashi yaje ya buɗe ƙofa a tsaye yaga Ummi da Maryam Suna jiran abuɗe.

"Bismillahi Ummi kushigo ai bansan har dake za'azo ba Mun ɗagoku" ummi bata kulaba suja shuga palourn dake Aysha na palour basukai ga shiga ciki ba ta miƙe zata taryi Ummi.

"Aah aida kinyi zamanki jiki babu ƙwari zauna abinki zan ƙaraso har wajan" kanta yana ƙasa takoma ta zauna bayan sun gaisa Ummii ta tambayi ya jiki tana ƙare mata kallo duk da rame ta ƙara wani haske tayi fatt bayan jinya harda jarabar Hamma. Cikin tausayawa Ummij ta dubi Hamma.

"Haɗo mana kayanta tare zamu tafi idan cikin yayi ƙwari lokacin ta daina laulayi saita dawo"

"Ummii tafiya da ita kuma? Dan Allah da kin barta anan sai Maryam tazauna Ta kuka da ita"

"Maryam ai yarinyace bazata iya kula da mai laulayi ba haɗo kayanta ƙwana biyu kawai zatayi nadawo da ita" Hamma badon ransa yasoba yashiga ciki ya haɗo mata kaya itakuwa Aysha kamar ta goya Ummi dan daɗi zata samu sauƙi kenan farin ciki har a fuskarta saida ya nuna. Ummi dama duk halin da suke ciki yarinyar brother ɗinta tana sanar da ita dan itake duba Aysha tun kwanaki da tayi ɓari sau biyu tabada shawarar ta ɗauketa dama tana jira saita sake samun ciki saboda ta ɗauketa da Hujja."

PAID BOOK
Chapter 89 · 0% Book details