← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 106

Sashe 18

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da saninta ta hana mahaifi ta sama masa aiki saboda tana gani da zarar ya kafu da ƙafafunsa toh tabbas wata rana zaiyi maganar aure gara ta su zamana dimun da'iman duk wani abinda sukeso ana tanada musu shima kansa ta hutar dashi basai yasha wahalar aikiba sannan bazaisa wahalar nema wajan sana'a ba yana kwance ake tanada masa komai.

Daya gaji da irin wannan zamanda yakeyi sai kawai ya yanke shawarar nemawa kansa aiki haka yayitabi bai sami aikiba sai wata rana kawai school ɗinda yagama suka bashi appointment na lacturing a wajan yadawo gida da murnarsa ya shaida mata sam batayi murna da aikin daya samu ba. Kwanaki kaɗan da faruwar hakan akayi terminating appointment ɗinsa. Baisan daliliba haka ya haƙura daga baya yazo yagane cewa matarsa ce sila sai yabar zancen aiki yashiga neman sana'a ranarda tasan yana sana'a kuka ta sanyashi gaba tanayi tana faɗin dame ta rageshi bayan babu wani abunda ya nema yarasa yau abun kunyane ace anga mijinta wajan sana'a sirikin senate president, har mahaifinta saida yashiga maganar akan shima bai yardaba zai zubar masa da kima duk abunda yakeso ya sanar dashi zai bashi.

Wannan dalilin yasa ya zauna gabaki ɗaya ya daina taɓuka komai sai dai kawai akawo yakashe."

ana cikin haka kwatsam saiga ciki nan rikici yatashi tace itakam bata shirya haihuwa yanzu ba sai dai azubar da cikin. Rikici har gaban iyayenta wannan karon kam basu bata gaskiya ba dan haka dole tabar cikin amma anyi differing karatunta saboda tana laulayi sosai."

ZAYAB ALABURA
*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*

Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

PAGE 15

   Haka da sukaci gaba da zama amma gabaki ɗaya yanda al'amura suke tafiya a rayuwarsu. Ina nufin mu'amalar rayuwa banda abubuwan more rayuwa.

  Ko faɗa sukayi idan zasuyi sati guda bai bata hakuri ba bazata taɓa kulashi ba bazata sauƙo ba tunda sukayi aure bata taɓa fara sauƙowa alokacinda suka samu saɓani ba.

Hajiya Zaynab tacigaba da samun kula wajan mijinta da mahaifinta har Allah yasa tasauƙa aka samu mace. Mahaifanta da muhammad sunyi matuƙar murna aransa yaso saka sunan mahaifiyarsa amma yanda ta nuna tanason yasakamata sunan mahaifiyarta ya sanya bai fito danasa burin fili ba ya cika mata nata burin.

   Dukda taimakon da masu aiki suke yimata wajan raino amma hakan tana complain akan shan wahala kuma yarinyar babu abunda yake kawota wajanta sai idan zata shayarda ita. Hakan yasa batayi gigin komawa makaranta ba wata shekara data zagayo sai aka sakeyin differing.  Shekara ɗaya da haihuwarta tasake samun wani cikin batareda ta saniba babu wani laulayi sai dai ƴar ƙiba datayi alokacinda tagane cewa tanada ciki sai rikici yatashi wannan karon iyayenta sun goyi bayan azubar da cikin haka babu yanda ya iya dole ya amince ana zuwa  asibiti aka gwada cikin yana 15weeks har yashiga 4month likita ya nuna musu hatsarin dake tattara da zubarda cikin daya shiga Second  trimester jin haka yasa mahaifinta ya haƙura itama yashiga lallaminta  akan idan ta haihu sai ɗauki mataki dawuri.

  Awannan lokaci aka ɗaga bikin ƙanwarsa wacce kebi masa Halima abokin mahaifinsa Alhaji habibu shine yayi komai a wannan lokaci dan awajansa take. Itakam zaynab dake tana famada cikinta bata halarci bikinba sai dai tayi musu kyauta ta bajinta."

Cikin yana 7month taje asibiti aka cire mata shi dan acewarta tagaji. Wannan karonma sunan mahaifinta aka saka masa yaro yaga bajinta sosai wajan iyayenta. Tun batayi arba'in ba tabi majors na kariya daga sake samun wani cikin.

Shikuwa muhammad ganin irin rayuwarda matarsa da mahaifanta sukeson yayi na zama zauna gari banza ba aiki ba sana'a yasa yafara tanada kuɗin dayake samu daga wajanta dana mahaifanta. Ya buɗe shaguna da kuɗin nan da nan Kasuwancins aya haɓaka Allah yasaka masa albarka aciki duk wannan abin batasan yaan faruwa ba data daƙile tunda wuri.
saida ta shekara biyar cis bata sake haihuwa haihuwa ba  awannan shekara biyar ɗin Allah yasaka masa albarka a kasuwancinsa na bam mamaki komai haɓaka kawai yakeyi. 
    
   
  
Ahaka yatara kuɗi mai yawa yasaya fili mai masifar girma sai bayan yasaya yake sanarda ita data tambaya yanda yasamu kuɗi yace mata kuɗinda mahaifinta yake bashi yatara tunda yana samun na amfani a wajanta tayi murna sosai nan ta nemi kuɗi a wajan mahaifinta masu yawa domin fara gina filin mahaifinta batareda ya tambayeta abinda zatayi dashi ba ya bata fiyeda yanda ta buƙata. Nan da nan aka fara ginawa amma a hankali tsararren gini nagaske shima yana saka kuɗinsa acikin ginin amma nata yafi yawa ahaka aka gama tsara gida mai kyau alokacin  gidajen da suke sakyawun wannan gida a garin gabaki ɗayansu basufi a irga suba yanda aka tsara gidan ko nan zuwa shekara ashirin gaba design ɗinsa bazai taɓa fita ayayi ba Shashinsa da nata a haɗe suke a waje ɗaya babban palour da 4bed rooms funitures ɗin da tsarin ginin yazo sai extra 2room and living room (palour) da bathrom guda uku, da zallan bedroom guda biyu sai ɗakunan ƴan aiki dana sauƙar baki akwai babban fili a gaban gidan yanda aka cikashi da  flowers da ɓarin mai gadi sai wajan kiwon dabbobi acan gefe da wajan shaƙatawa da aka buga masa canopy mai rufin china ana gama tsara ginin suka koma gidansu da yaransu guda biyu."

Mahaifiyarce tafara yimasa zancen Auren ɗiyar abokin babansa da yayi alƙawari dama abun yana ransa ganin bata daɗe dafara karatu ba yasa bai tada zancen ba amma dayake tayi zancen akan gaɓa kawai saiya tashi yasamu mahaifinta Yabada sadaki mahaifinta yace bayan sadaki baya buƙatar komai dan haka aduk lokacinda ya shirya aure yasameshi kai tsaye zaisaka rana ayi biki.

A shekara na shida tasamu ciki ta haifo ɗiyarta mace  aka sanya mata fadeelah mahaifiyarsa ne yasa aka saka mata.

     A shekarar zancen aurensa tatashi dake maganar duniya bata ɓuya ya sanya kai tsaye abun yake kunneta ta birkita sosai jiransa kawai takeyi ya iso taji daga bakinsa. Yana shigowa daya ganta yasha jinin jikinsa yaranta suna zaune a falo ko takansu bata biba bare tace sutashi su basu waje tafara bala'i tana faɗin.

"Yau ni zakaci amana duk wani abunda nake maka a  duniya da kyautatawarda nake maka nasake maka kuɗi duk abinda kake buƙata shi nake Maka amma da abinda zaka sakamin kenan? Sakamakon kyautatawar da nake maka kenan?"  jin tana masifa yasa second born ɗinta Ahmad yace.

"Mummy mai dady yayi kike masa masifa?" dady kabata haƙuri kaga ran mumy ya ɓaci" dake dama sun saba duk lokacin wani saɓani yashiga tsakaninsu shike bata haƙuri ko agaban yaran yasanya suka ɗauka Dadynsu yana tsoron Mummynsu ne kaman yazama dole komai yafaru yabata haƙuri. isawa yayi sannan yace.

    "Wani irin sakamako nayi miki tun kafin na aureki na sanar dake auren yarinyar kuma ke kika amince zaki aureni ahaka ni ayanzu banida wani abunda zan iya cewa sai dai kiyi haƙuri dannasan dole zakiji zafi"
jin yabata haƙuri yasanya tafara sauƙa tace.

"Shikenan naji zan haƙura amma yanzu yazama dole ka janye zancen aurennan  kamar na faɗa maka har yanzu ba'a haifi macenda zan iya haɗa miji da itaba" girgiza kai yayi yace.

"Bazai yiwba zancen aurena babu fashi tunda kinada masaniya akansa bare kice na ha'inceki bazan iya karya wannan alƙawarinba" Yafaɗi hakan har cikin ransa saboda koda abaya baida niyyar auren nan kusa yanzu dole tasa zaiyi. Yanasp shima yafito a

  Kuka sosai tasaka tayi ciki takira mahaifinta ta shaida masa yace ta tattara tataho haka ta kwashe yaranta tatafi can bayan yatafi da sati suka nemeshi yaje yayiwa mahaifinta bayanin komai tun kafin zancen aure yashiga tsakaninsu har lokacin data amince zata aureshi bayan aurensu kuma zai ƙara aure. Mahaifinta yanajin haka yace tunda da amincewarta dole ta haƙura yayi aurensa yayita lallashinta sannan yace tabi mijinta su koma.

  Yasakata agaba da yaransa suka koma dukda hakan bawani ƙwanciyar hankali rikici na yau daban na gobe daban duk wata hanya da tasan zatabi yafasa auren tabi amma hakan baiyiwuba."

----
  Dake mahaifinta yace kada yayi komain na auren hakan yasa shima yace zaiyi funitures acikin 2bedroom da lving rooms ya zaɓa mata guda ɗaya wanda yake nasa da nasu shida Hajjaju."

Haka ta tada rikici bazai saka amaryar agidanba sai dai ya nemi wani wajan ya sakata daƙyar ta haƙura yashawo kanta tabari ta zauna agidan."

   Akayi aure yasamu amarya beyond expectation nasa saboda biyayya take masa da girmamwa duk wata kyautatawa tanayi masa alokacinnne yasamu damar da zaice ayi sannan ayi kuma yace abari, abari.

  Amarya na cikin wahala wulaƙanci na duniya babu irin wanda ba'a mata ga gori kullum acikinsa take ko sau ɗaya bata taɓa tankawa ba kuma bata taɓaji ta tankaba saboda mijinta ya hanata kuma tasan ko tankawar tayi batada riba tunda taga mijinda take aure wanda yake bata umarni shima bashi umarnin akeyi.  tacigaba da karatunta tana zuwa makaranta amma a ɓoye mijin yake ɗaukar ɗawainiyarta wata rana ma idan Mummynta bushi iska takance ita takeso tayi aiki dan haka bazata makarantarba, haka take haƙura da zuwa makarantar ta zauna tayi mata aiki, ganin hakan bai hanata karatunba ya sanya Mummy ta tashi rikici akan dole sai dai tabar karatun baza'a ɗauki nauyin karatun wata da dukiyar mahaifinta ba, shikuwa yace bazatabar karatu ba dan itama Mahaifinta yanada rufin asirinsa danshima ɗan kasuwane yanzu har takai takawo daga ƙasar waje yake shigoda kayyaki a wannan lokaci kuwa masu shigowa da kaya daga ƙasar waje sai mai ƙarfeffen jari ba kamar wannan lokaci bane da shigoda kaya daga ƙasar waje ya yawaita ba. Amma duk arzikinsa not to compare with baban Hajiya zaynab yayi masa fintinkau ya wuceshi fuu da aniya. ya gwada mata mahaifinta shi yafara ɗaukan nauyim karatunta kuma shi yake ɗauka har yanzu dan haka baida right ɗin hanata karatu tunda ya aminta da karatunta tun farko, itama idan tanada ra'ayi bazai hanata ba takoma. Tace ita bazata koma karatu ba tunda a yanzu babu abunda zata nema a duniya bata samuba. Ahakaz zancen ya mutu bata sake ɗagashi ba."
Chapter 18 · 0% Book details