← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 106

Sashe 24

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shikenan Baba zan zauna anan É—in in sha Allahu" Baba yace Allah yayarda yayi maka albarka. Ya amsa da amin."

""""""""

Sati ɗaya yayi kullum sai Baba yayi baƙi wannan ƙamshin ya zauna dimun da'imun acikin gidanmu."

ZAYNAB ALABURA

*BIBIYATA YAKEYI*
              *(WAYE SHI?)*

Ya daɗe acikin toilet yana wanka yayinda yayi amfani da duk wani bath-mist dayasan yana amfani dashi nan da nan ƙamshi ya karaɗe gabaki ɗaya floor na illahirin hotel ɗin. Yayin beard ɗin fuskarsa ya ƙwanta luff-luff sai sheƙi yakeyi Cike da nutsuwa ya fito daga wanka. Ya isa gaba mirror da aka jera mayuƙan da yake amfani dasu cikin nutsuwa ya shafe jikinsa da mayukan wanda ƙamshinsu ma wata duniyar ce. Ya isa jikin Cloth cupboard ya tura murfin yayi gefe ya tsaya yana kallon ciki kusan 5minute kafin yaciro sabuwar jallbiya wacce take cikin ƙwalinta da singlet itama sabuwa dall acikin ƙwalinta sai boxer shima yana cikin ƙwalinsa da 3quater jeans gabaki ɗaya singlet da Boxer stamp na sunansa ne ajiki ga dukkan alamu daga company ake buga masa tasa daban ko shine mamallakin kamfanin gabaki ɗaya. Ya shirya cikin farar jallabiya yayi matuƙar kyau sosai ya tsaya kallon madubi yafi 10minute gaban madubi duk wannan abunda yakeyi yana yine cikeda nishaɗi amma wani ɓangaren akwai tsoro cike aransa. Ya shafo sajen dake ƙwance a fuskarsa sannan ya sauƙe ajiyar zuciya ya fara tafiya zuwa gaban wani bell ya danna 3minute saiga P.A ɗinsa yashigo ganinsa a shirya yasa yace.

"Mood sir harka shirya zan iya sanarda tafiyarka yanzu?" yayi ajiyar zuciya kana kallonsa zaka tabbatar akwai abunda yake damunsa.

"كيف ابدو
(How do i look)"
yayi magana out of fear saida P.A yayi murmushi sannan yace.

"Kayi kyau sosai you
انت دائما تبدو وسيم
(always look Handsome)" ajiyar zuciya ya sauƙe yasake komawa ya kalli madubi sannan yadawo yadubi P.A yace.

"هل أنت متأكد؟"(are you sure)"
tun yana mamakin yanda boss nasa ya nutsewa soyayya harya dawo yadawo yadaina amma sanin waye Hammood dakuma matsayinsa yasa dole wasu abubuwan suke saka bashi mamaki gabaki ɗaya ya canja Akan ƙaramar yarinya yarinyarda bawani kyau ko kuɗi ko suna gareta cikin celebraties na duniya baki ɗaya yana daga cikin wanda yafi sanuwa babu yanda zaije bai samu macenda yakeso ba kowace irin mace a halin yanzu sai dai ya sauƙe class ɗinsa ya aureta amma bawai danta kai ba aganinsu saboda status ɗinsa yawuce tsarar kowace mace amma sai gashi yabasu mamaki mamakinda basu kaɗai ba da duniya da zatasan da wannan lamari ita kanta zata jijjiga tashiha firgici numfashi ya furzar sannan sannan yace. g

"أنا متأكد جدا"
(am very sure)" Ajiyar zuciya ya sauƙe ya ɗauki facemask yasaka ya ɗauki glass yasaka sannan ya ɗauko Facing caff ya rufe fuskarsa gabaki ɗaya yanda babu wanda zai ganeshi.

Ƙarasawa yayi ya ɗebi wayoyinsa sannan ya ƙarasa yabuɗe masa ƙofa yafita gabaki ɗaya ɗakunan floor ɗin dayake an kamasu morethan 50rooms gabaki ɗaya aka kamesu saboda tsaro dakuma rashin son hayaniya. Harya fita cikin harabar mutane babu wanda ya ganeshi ya ƙarasa wajan motanda ake jiransa motoci biyune kacal wanda shi ya buƙaci hakan gabaki ɗayama ba'asanda shigowarsa garinba kusan kowa ya ɗauka yana abuja dayake dai kods yaushe idan zuwa abujan takama yakanje yadawo har ila yau babu wanda yasan dalilin daya kawoshi sai ƴan tsirarrun mutane gidan tv da jaridu sunyi tambaya harsun gaji har yau babu wanda yasamo musu amsa. Kuma abunda yake kan bawa mutane mamaki shine daɗewar dayayi aƙasar da bai taɓa yi awata ƙasa haka kawai bawani aikine yakaishi ba.
Atarihinsa ma gabaki ɗaya bai taɓa zuwa ƙasarba baida friends a ƙasar nigeria sai zallan fans da yake dasu wanda shi kansa yaji mamakin ganinsuba lokacinda ya sauƙa a ƙasar ya kasance yanada masoya masu tarin yawa haka a ƙasar.

Yanayin yanda motocin suke tafiya baza'a taɓa zaton tafiyarsu ɗaya ba yanabin duk wata hanya da zaibi dan ganin babu wanda yasan da zamansa a garin."

Fitowarmu daga lactures kenan cikina sai ƙugi yakeyi danko karyawa banyiba dake sassafe na shiga school jan hannun Maryam nayi muka nufi wani eatery dake cikin school ɗin tunda muka doshi wajan hancina yake jiyomin saƙon kamshin da ƙwana biyu nasaba da jinsa. a tunanina inajin ƙamshinne saboda shaƙarsa danayi ƙwana biyu dayawa wanda yanzu haka ya gama kama gidanmu barinma shashin Baba tunanina ya canja a lokacinda nasaka ƙafata cikin wajan saboda yanda ƙamshin ya tunkareni gadan-gadan ko shakka babu akwai baƙon Baba acikin wannan wajan kokuma wani mai irin ƙamshinsa. Waige-waige nafarayi mutane daban-daban zaune cikin wajan can idona ya tsaya akan wani dake zaune can gefe gabaki ɗaya cikin wajan shine wanda yayi suiting wannan ƙamshin. sanye da fara jallabiya amma sai dai hula ta rufe fuskarsa bana iya kallowa na kai fuskata kan hannunsa saida gabana ya faɗi fari sol kaman a tsaga jini yafito abune mai matuƙar wahala samun mutum mai irin wannan hasken a nahiyarmu. Agogon dake ɗaure a hannunsa brand na Patek Philippe koda bansaniba nasan agogon mak masifar tsaɗa ne. Bansan kuma ko kwayun hannun bane ya ƙarawa watch ɗin kyau ba. Sai wani zobbe mai wani design wanda nakasa tunano yanda nasan zobben. danna waya yakeyi gabaki ɗaya hankalinsa ya karkata a kan wayar. Muryar maryam tadawo dani daga tunaninsa na wuntsila.

"Babe kije kiyi mana order nagaji wallh ga wani azabebben ƙamshi daya sauƙarmun da kasala tunda nake ban taɓa cin karo d ƙamshi makamancinsa ba"
Sai alokacin na tabbatar da cewa bani kaɗai kejin wannan ƙamshin ba. Ajiye bags ɗina nayi akan kujerarda da zan zauna. Ƙarasawa nayi wajan nayi making ordern daga yanda nake ina iya jiyo muryar wanda suke zaune tareda shi yana magana cikkn harshen labarci harna bar wajan nadawo na zauna banji yabashi amsaba.

Na zauna akan kujerar ina facing É—insu kauda kaina nayi daga garesu dan zuciyata tanata faÉ—amin something is off. Nadubi Maryam nace.

"Babe something is not right a cikin awajannan bakiji ƙamshinna ba? bantaɓa jinsa ba sai ƙwannan cikin gidanmu kuma yanzu najishi anan ina tunanin kamar mutum ɗayane da wanda yaje Wajan Bab. Maryam saida ta nisa tace.

"Naji mana babe ba yanzu nake miki magana ba? Nima bantaɓa jin irinsa ba amma kinsan turare dayawa a duniya bbu yanda za'ayi brand na turare su buga sample ɗaya idandai ba nawani celebrity bane sune suke amfani da turare su kaɗai so calm down. Mema zai kawo baƙin Baba nan? Nan fa school ce ɗai-ɗai ku wanda ba ƴan makaranta ba suke shigowa nan sai suma a irin waɗanda ke buƙatar wani snacks awajan ko wani abun" Nayi shiru kawai dannaga bazata fahimceni ba. Lokaci-lokaci nake kallon wajanda suke zaune ganin ko sau ɗaya bankamasu suna kallo naba yasa hankalina ya ƙwanta muka gama abunda zamuyi muka tashi na nufi wajan na biya kuɗin sannan nazo muka fice.

Bayan nafita ya dubeshi yace.

"Mood sir tafita ko zamu bita?" Ya girgiza kai da Mamaki P.A yace.

"Are you not going to talk to her?" ya sake girgiza kai yace.

"No. I love her even though i haven't met her. So whats the point of meeting her" P.A yace.

"Go met her express your feelings" murmushi yayi yace.

"it's a fantasy, hopes and a dream. It's sweet kuma it's a basics for actually wanting to meet her amma ba yanzu ba not now. Expressing feelings ga wanda gareta i am a totally stranger that would surely freak her out. if i met her bazan iya barin sonda nake mata ya ƙwanta cikin raina kamar yanda nayi alƙawari ba koda na seconds ne and Banason na fara rayuwa tareda ita batareda ta yarda dani da kanta ba. Yanzu abunda yake gabana what can i do to make her fall for me?" P.A yace.

" okay. Meet her first. Let her get to know you. Go on a few date. if things work out then it would be appropriate to express your feeling" Dariya yasaka kawai dan abun bai kama hankalin kansa ba ya miƙe yana shirin barin waje. P.A ybashi yana faɗin.

"Mood sir whats the problem?" Ya nuna masa hannunsa haÉ—eda faÉ—in.

"This. This is the problem. My skin colour. Yarena ƙasata everything about me is different from her shine kake tunanin muje date? How? Tayaya zata yarda da totally stranger sufita date"
P.A cikeda gundura da maganar yace.

"Mood sir whats the point of all this? She's already yo..... . Shshshhhhhh ya dakatar dashi alokacinda yayi arba da ita ta dawo cikin wajan. Saida ta kalli yanda suke wannan karon ita yake kallo amma bata kallon idonsa saboda yana cikin gilashi ta kauda kanta hankalinta na wani wajan ba tasu takeba dasauri ta ƙarasa wajanda suka zauna da ɗauki ƴar ƙaramar wayarta data bari haɗeda sauƙe ajiyar zuciya. Menene wannan Zuciyarsa ta tambaya a yayinda tayi arba da wayar hannunta. Nan ƙirjinsa ya fara bugawa dasauri me takeyi da wannan wayar? Badai waya takeyi da wani ba?" idanuwansa suka rufe nan da nan suka kaɗa bai ankaraba harta fice. Dasauri yabi bayanta shima yayi wajen."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab  m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance  zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

ZAYNAB ALABURA

*BIBIYATA YAKEYI*
              *(WAYE SHI?)*

       Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Ina isa dai-dai yanda maryam take na tsaya ina haki saboda saurin da nayi. Ta taɓe baki tace.

"Wannan wayar ko rayuwarki iyakaci kin waani bi kin rikice kawai dan kin duba baki ganta ba" na mika mata wayar haÉ—e faÉ—in.
Chapter 24 · 0% Book details