← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 106

Sashe 15

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"toh" sannan nafice ina tunanin wace irin maganace Baba yakeso muyi dashi da asubahi, Banbi É—akin Mama ba dayake fushi nakeyi da marinda tayimin nawuce É—akinmu banbi takansu ba nayi wajan wayata in dubawa naga missed call É—in Hamma dake dare yayi sosai banbi takan kiran ba na kwanta Bawani bacci nayi sosai ba saboda abubuwada suke cikin kaina asubahi tanayi natashi nayi sallah inajin dawowar Baba daga matsallaci natashi natafi É—akinsa sallama nayi yacemin na shigo na zauna bayan na gaisheshi ya amsa. A hankali nace.

"Baba" yace.
"Na'am Marmee akwai wani abunne?"

"Nisawa nayi nace Baba wata alfarma nake nema awajanka"

"Wace" irin alfarma kenan Marmee?"

"Baba bazan faÉ—a makaba saika yarda zakayimin" Baba yayi murmushi irin nasu na manya yace.

" Toh faɗuwa tazo dai-dai ta zama kenan nima inaso na roƙi wata alfarma a wajanki banaso na yanke huknci akanki kamar yanda nayi abaya yazo ya tarwatsamin gida gabaki ɗaya banaso na maimaita kuskuren danayi abaya"

"Baba kaifa ubane wace alfarma kuma bayan kai mai bani umarnine nawa bine kawai daga yanzu karkaji komai karkaji shakku akaina a duk lokacin dakaji zaka yanke hukunci akaina bakada buƙatar shawara dani kai tsaye kayanke saboda kanada cikekken iko akaina kuma zanyi maka biyayya ɗari bisa ɗari saboda inada yaƙinin bazaka yanke hukuncin da ba dai-dai ba akaina" Baba cikeda jin daɗi yace.

"naji daɗin wannan zancen Allah kuma yayi miki albarka kuma in sha Allahu bazan yanke hukuncin da zakiyi dana saniba. Yanzu ina jinki ki faɗamin wace alfarma ce kikace zaki nema a wajena nima nayi miki alƙawarin yimiki komenene faɗamin inaji" Na nisa kafin nace.

Baba kafin na faÉ—a maka abunda yake tafe dani ina neman alfarmar ka faÉ—amin ainihin abunda yafaru a gidannnan da dalilin daya janyo rabewar kan gidanmu gabaki É—aya. Wacece mummy kuma wani irin hali take dashi da kowa yakejin tsoronta harda kai kanka daya kamata ace kaine wanda kake bata umarni tanabi?" Baba yayi shiru kamar bazaiyi magana ba Harna cire rai da zaiyi magana sai kuma naji yace.

"SHEKARUN BAYA*

ZAINAB ALABURA

*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI)*
     

       Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

PAGE 12

     SHEKARUN BAYA  (bari mu tsunduma cikin labarin tsundum)

       kyakkyawan matashine wanda gabaki ɗaya illahirin makarantar Abubukar tafawa ɓalewa babu wanda yakaishi kyau sannan kuma yanada ilimi matuka da gaske a wannan lokaci anyi ittifaƙin kaff samarin makarantar babu mai kyawunsa a shekarun baya ɗalibanma gabaki ɗayansu basuda yawa so tantance irin wannan lamari abune mai sauƙi.
Ƙyawunsa yasa daga lacturers mata har ƴan makarantar basu ƙyaleshi kowwacce da taga fuska sai tayi Ƙokarin buɗe abunda yake zuciyarta. Har malamai mata sunsha bayyana masa ra'ayinsu akansa wasun sunzo da niyya mai kyau wasu kuma sun nemeshi da fasiƙanci agabaki ɗaya babu wanda yayi nasarar samun kansa, wata hanya ɗaya da Allah ya fissheshi yanada ƙoƙari sosai koda Malamai sun tunkareshi da wata mummunar niyya yaƙi tofa basuda damar da zasu kayardashi saboda makaranta ta shaida ƙwazonsa da zarar hukumar makaranta taga ya faɗi zatabi diddigi tayi bincike.  Matashi mai kamun kai da nutsuwa haƙuri da sanyin hali sannan ga girmama nagaba dashi hakan yajawo masa farin jini wajan malamai da dama kuma baida ƙuiwa wasu daga cikin malaman idan ayyuka sunyi musu yawa sukan kirashi su sakashi a ƙanƙanin lokaci yake gama musu aikin wannan matashi Ba kowa bane sai Muhammad Muhammad Dani.

    Muhammad Dani iyayensu su Huɗu kawai suka haifa a duniya Mahaifinsu babban manomine. shine Babba awajansu sai sauan ƙannesa Mata gabaki ɗayansu. mahaifinsu tun suna ƴan ƙanana aka nemeshi aka rasa Har ila yau ba'asan yanda yakeba.
Wasu daga cikin gonakin mahaifinsu aka sayar mahaifiyarsu takama kasuwanci take kulada yaran har karatunda zasu zai fara ma sayarda gobar akayi ana biyan Aka É—auki É—awaniyar karatunsa dashi har gashi yanzu yazo aji biyar."

*********
     motace ta tsaya ɗan gaba da yanda suke da abokanansa, cikeda izza da isa ta dubi wata ƙawarta dake zaune a gefenta tace.

"fita ki kiramun shi" ƙawayen gabaki ɗayansu suka saka shewa suna faɗin.

   "eh lallai yau Hajiya Zee an ɗauki shawara kenan tsawon lokaci guda ana abu ɗaya yau dai rana tayi" Ganin yanda ta kimtse fuska ya sanya su duka sukaja bakinsu sukayi shiru sanin halinta abune mai sauƙi yanzu ta disgasu a wajan. Wacce aka aika ta buɗe murfin motar tafita ta isa zuwa wajanda suke zaune tayi musu sallama sannan tace.

   "Hajiya zee na son ganinka" tafaɗa haɗeda yin pointing ɗin Muhammad.

"Ni" yafaÉ—a asanda yake nuna kansa da yatsarsa.

"Eh tana jiranka" tafaɗa haɗeda juyawa ransa yaɓaci amma sanyin halinsa yasa murmushi kawai yayi haɗeda girgiza kansa. Nan abokansa suka fara faɗin.

"haba mutumina kaje mana kasan wacece Ita kuwa? kaff gayun makarantarnan sun gwada sa'arsu akanta amma har yanzu babu wanda ta kula kaje kaji abunda tazo maka dashi"  bada son ransa ba sai dan yanda sukayi masa caaa yasa yatafi tana kallon ya iso wajan tadubi ƙawayenta sun gane abunda take nufi dan haka dukansu suka fice a motar. Tsayawa yayi abakin motar yayi mata knocking. Da yanayin maganarta yanda tasaba tace.

  "ƙofar motan a buɗene" kallonta yayi na seconds ganin batada niyyar fitowa yasa yabuɗe yashiga tunda shi baida zafin randa zai iya kaucewa yabar mata wajan.  hand bag ɗinta ta ɗauka taciro wani littafi ta miƙa masa kallonta ya tsayayi bai karɓaba dan bai gane abunda take nufi ba. Cikeda gadara tace.

"lissafi zaka koyamin test muke dashi kuma ban iya ba" ganin yanda take magana cikeda izza kamar wacce take bashi umarni ya sanya yayi murmushi mai cikeda takaici, takirashi zuwa motarta maimakom ta gaisheshi ko sannu tace batayiba saita fara da bashi umarnin ya koya mata lissafi. Cikeda mamaki yace.

   "Kinsanni? Koni nasanki?" yatsine fuska tayi tace. baka sanni nima bansanka ba kawai naji ance kana yiwa mutane tutorial akan abubuwanda basu ganeba nikuma bazan iya shiga cikin kowasu irin mutane na zaune  ba shiyasa na nemi kamin nawa ni kaɗai idan takama na biyaka ne zan biyaka ko nawa kakeso just name your price" yayi murmushi mai cikeda takaici yace.

  "idan kinaso na koya miki kije ki zauna cikin mutanenda bakyaso ɗin yau da ƙarfe huɗu shine zan iya haɗawa na koya muku tare"  yana faɗin haka yakama ƙofar zai buɗe tayi saurin dannawa ƙofar lock ya juyo da mamaki ya kalleta jin ta garƙame ƙofar. Yana mata kallon tuhuma dan haka ta haɗe rai kamar wanda akayi mata dole tafara faɗin."

  Honestly nifa bana ganewa ne idan bawai ni kaɗai akayimin dalla-dalla ba acikin mutane bana fahintar abunda ake koyarwa" Saida ya ƙare mata kallo itakuma ta kauda kanta gefe tana ciccin magani tace.

"kuma wannan abunda na faÉ—a maka babu wanda yasani sai kai kaÉ—ai dan haka ka koyamin kuma kar kowa yasani" jin yanda tayi magana cikeda umarni yasa yayi murmushi yace.

   "Okay maa" yanayin yanda yayi maganar saida ya sanyata takusan yin dariya amma saita dake hannu ya miƙa mata ta bashi littafin ya amsa ya fara nuna mata cikin lokaci ƙalilan tace tagane yace ta gwada masa tabi ta gwada masa kamar yanda yayi mata.
Zai tafi tace.

  "Toh yanzu idan inason ganinka ka sake koyamin a'ina zan sameka?"

"A'ina yau kika sameni? Kullun inanan idan bawai lactures nake dashiba ko wani abun" ta yatsine fuska sannan tace.

  "Ka sakamin phone number ɗinka inaga kaman zaifimin sauƙin nemanka"

   "Banida waya ya faɗa alokacinda yake ficewa" ta taɓe baki kawai saida ya isa wajan zamansa sannan ƙawayenta suka shigo motar ta tada sukayi gaba. Suna tafiya suka fara tambayarta yanda sukayi ta taɓe baki haɗeda farfara ido tace.

  "kuna tunanin kai tsaye zan fito na faɗa masa ina sonsa? Inaga you're mistaken nice fa Hajiya Zainab banajin kun manta halina sai dai ganganci shida kansa zan sashi ya faɗa sannan yazo da ƙafarsa ya faɗamin yana sona kuma hakanma saina garashi kafin na amshi soyayayrsa" ta faɗa fuskarta babu alamun wasa. Nan da nan suka fara wasa mata kai itakuma tanata hura hanci ita adole tafi ƙarfin tace  Masa tana sonsa."

   Shikuwa anasa wajan abokanansa sunajin wai karatu tazo ya koya mata sai murnarsu takoma ciki sunso ace tazo masa da soyayyace su samu abun bragging akai."

**********

  Tun daga wannan lokaci ya daina zaman wannan waje saboda ya lura rainin hankalin yarinyar yanada mugun yawa sai tazo tayita yimasa gadara akan abunda roƙonsa ya kamata tayi. Itakuma nata wajan yanzu tana neman mafita ne tunda baida waya a wannan lokaci bakowane yake iya affording waya ba ita gabaki ɗayanta ma wayar bata wadatu a hannun al'umma ba sai gidan wane da wane ko ɗan wane ko ƴar wane.

  Yau kam sanyawa tayi amata jiransa tun daga bakin gate ɗin makaranta da zarar anga yashigo asanar da ita hakan kuwa akayi mai achaba yana sauƙeshi a ƙofar school dake sun saba da masu tsaran gate ɗin yasa bai nuna IDcard ɗinsa ba yabisu suka gaisa kawai yashige. Tana tafiya yaji Horn abayasansa ya waiga kawai sai yaganta tana zuwa dai-dai shi ta tsaida motar tace.

" shigo" murmushi kawai yayi dan isarta ta kai akirata da isa.

"Barshi kawai nagode i can trek" yafaɗa hankalinsa yana gaba.  Cikeda gadara tace.

  "kashigo kai kayi alƙawarin koyamin lissafi and i look for you Everywhere. but you're no where to be found, you just vanished. Tayi maganar cikeda iyaye da ƙwainane Cikeda zolaye yace.

"did you look for each an every corner?"

"Yes i do tafaɗa tana ƙara jaddada masa"

"you look All over. the entire surface of everywhere"? YafaÉ—a ya tsaya kallonta yana jiran amsarta.

" ehem naa,,," sai kuma tayi shiru data fahimci zolayarta dakuma shan cikinta yakeyi." dariya ya saka itama saida ta murmusa yace. 

"dama inada muhimmanci har haka?  dakewa tayi tace.

  "Kashigo mutafi" batareda ƙara yin wata gardama ba yabuɗe yashiga, tace.

Kayimin alƙawarin zaka ringa koyamin karatu amma bana ganinka kuma lokacin exam yakusa yanzu haka muna tests"
Chapter 15 · 0% Book details