← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 106

Sashe 53

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari haka natashi fuskata a kumbure luhu-luhu kaina kuma yana ciwo da zarar natashi jiri kawai nakeji saboda kukan danasha hakan yasa ban fita koda palour ba Mummy data jini shiru dakanta ta biyo sawu tazo tasamu ina ƙwance itadai tunda aka fara bikinnan batada ƙwanciyar hankali yanayinda take ganina aciki yana ɗaga mata hankali ayanda tasanni da surutu tasan duk abunda zai maidani shiru-shiru toh ba ƙaramin abu bane. Koda bata zauna dani sosai ba amma tasan halina inada fara'a da surutu sannan ga tambaya idan mutum baida haƙuri tambayoyina saisun gundureshi. Duk wanda yasaba dani da wannan halayan nawa a wannan lokaci dole idan aka ganni aji babu daɗi.

Mummy da Mama duka suna zaune a gefena suna hira sama-sama mukaji sallamar Ya Ahmad Mama ce tabashi izinin shiga yayi sallama ya shigo yafara gaidasu sannan nima na gaisheshi ya amsa yana tambayar ko banajin daÉ—ine dan yaga fuskata ta canja Mama ce tabashi amsa da faÉ—in kaina yana ciwo.

"Subhanallahi Allah ya sauwake yabata lpy" shine abunda ya Ahamad yafaÉ—a mu dukanmu muka amsa da amin.

"Kinga kuwa nazo miki da wani albishiri kash ashe babu lafiya toh Allah ya sauwake yanzu zan koma da kayana har sai kin warke" Na kalleshi inaso ya sanar dani albishir É—inda yazo dashi yagane mai nake nufi yafara magana.

"Ƙwana biyu nasan baki buɗe TV bakoh?" na jijjiga masa kai.

"Okay toh madallah garada baki buÉ—e ba dan inaso yazama suprise dama tun É—atsu nakasa tdaida zuciyata waje É—aya na faÉ—a miki ko karna faÉ—a miki amma yanzu bazan faÉ—a É—inba kawai gara idanuwanki su gane miki.

"Dan Allah menene Yaya please ka faÉ—amin"

"No idanna faɗa yazama ba suprise ɗinba kenan kedai kisha maganin ciwon kannan yatafi dawuri dan nasan zaki girgiza dayawa sannan waɗannan luhu-luhun idanuwan kaff su saɓe" Nayi Shiru ina kallonsa kawai dan naga alamin bazai faɗaba tunda yafara haka.

"Amma zan iya kunna TV na kalla idan babu laifi danna ƙagu nasan abunda kakeson nunamin"

"Eh zaki iya amma ba lallai ki kalli abunda nake faÉ—a ba"

"Nidai zan buÉ—e idanma ban ganiba shikenan" mama da Mummy gabaki É—aya sunji daÉ—in yanda na sake ina magana da Ya Ahamad. Mummy ce ta amshe zancen.

"Haba Ahamad ka faÉ—a mata mana kaga tadamu dayawa tanason sani"

"Barta kawai Mummy sai nanda 2days hakanma saita ƙwantarda hankalinta nagani nanda 2days ɗinma idan hankalinta bai ƙwantaba toh babu yanda na iya ban isa nuna mata abunda nakeso na nuna ba"

"Kinji koh? Gara ki ƙwantarda hankalinki kijira kiga abunda zai nuna miki" cewar Mama. Na turo bakina batareda nace komai ba.

"Toh nidai barina tafi nabarku zamu kai gara kar yamma tayi" mama ta miƙe tana faɗa. Yaya Ahamad ma yamiƙe.

"Akwai wanda zan É—eba a cikinku saimu fita tare" mama da Ya Ahamd suka sanya kai suka fita akabar zallan nida Mummy aÉ—akin. Itama batabar É—akin ba saida ta tabbatar tasaani nayi wanka nasaka kayana dan yau ake wuni agidanmu.

Danayi wanka naji daɗin jikina kuma idanuwan nawa sun saɓe bakamar tashina da safiya ba haka nafita cikin gida muka ɗan yi hira nasake komawa ciki. Zuwa la'asar su Mama sun dawo daga kai gara kafin magrib saiga Maryam da Ummi sunzo dubani wai maryam ta faɗa mata banda lafiya. Gabaki ɗaya kunyar Ummi ne ta kamani nakasa haɗa idanuwa da ita sai haƙuri kawai take bani kamar wanda itace tayimin wani laifi. Sai bayan magrib suka bar gidan dukd bawasu mutane tabari agidanba amma tasan baza'a rasa masu zuwa ba dukda bata gayyaci mutane dayawa ba iyakacin ƴan uwanta na jikinta ne sukazo bikin kuma tun jiya suka gama bikinsukowa ya watse taso tun ajiyan akai amarya ɗakinta amma hakan baiyiwuba. sai yau ango zai ɗauki amarya yatafida kayarsa. Naji daɗin ganin Ummi danayi tazo dubani zuwa dare gabaki ɗaya na ware banajin komai sai zallan idanuwana da har yanzu nauyinsu bai gama sakewa ba."

---
Da magrib abokanan ango sukazo da kansu suka ɗauki amarya suka kaita ɗakinta saida suka rako ango kamar yanda aka saba a al'adance sannan suka ɗebi ƙawayen amarya aka tafi dasu akabar zallan ango da amarya. Ko ƴar kazarda ango yake sayawa amarya Hamma bai siya ba sai abokanansa suka saya aka sanya masa a mota baya tunanin zai iya kasancewa da wata ba Marmeeyy ba watanma yayar Marmeeyynsa dayakeso yake ƙauna hakan yafi cimasa rai akan komai tunda idan wata dabance zai saka ran samun marmeeyy ko nan gaba amma tayaya zai saka ran samunta bayan yayarta yake aure? Tunda yafita raka abokanansa kai tsaye ɗakinsa yawuce itama yazo ya sameta bata palour yanda yabarta wanka yashiga yayi harya ƙwanta yatuna yabar kazarda aka sayo a mota ko ɗaukosu baiyiba baisan ko tanajin yunwa ba tunda tun magrib aka kawota gidan kuma yasan babu wani abinci agidan tsaki yaja yatashi ya zura jallabiya akan gajeren wandon dake jikinsa. Yafita ya buɗe mota ya ɗaukosu kai tsaye ya nufi ɗakinta dan ajiye mata kazar. Ita kuma alokacin tafito daga wanka cikin sleeping wears ɗinta taɗauki wani riga mai gajeren wando tasaka tunda batayi tunanin shigowarsa ɗakinba. Babu abunda ba'a gani ta cikin kayan amma ita wacce tasaka batasan da hakanba dan dole saida tsaya a jikin madubi kafin tagane kayan transparent ne, yana shiga idanuwansa yasauƙa akanta saida gabansa yafaɗi daram idanuwa ya tsurawa ƙirjinta yayinda zuciyarsa take bugawa dasauri dasauri. Tunda yake a rayuwarsa ido da ido bai taɓa kallon mace a wannan shigar ba gabaki ɗaya tatafi da hankalinsa ta lurada hakan a hankali take tafiya harta ƙaraso wajanda yake har yanzu idanuwansa nakan ƙirjinta. Ita kanta tsoro takeji amma babu yanda ta iya wannan ce damar da take da ita da zata fara amfani da ita wajan jan hankalinsa gareta. Batasan ko samun kamar wannan damar zatayi mata wuya ba so gara tayi amfani da ita tuna tana iyawa. Saida tazo daff dashi sannan tace.

"Sannu da zuwa Hamma" sai alokacin ya ɗaga ya kalli fuskarta ta sakar masa murmushi" ya ɗan kalleta na wani lokaci ƙyayyawa ce sosai dan tafi marmeeyy kyau kuma tanada jiki mai ɗaukan hankali amma shi ba wannan bane damuwarsa shi zallan marmeeyy ita ɗindai ita yakeso.
Ganin ya tsura mata idanuwa yana kallonta kamar maison kissing ɗinda ya sanya ta ɗagalgale ƙafarta ta ƙara tsawo dan taimakawa lips ɗinsu yayi saurin haɗewa waje ɗaya. Amma ƙirjinta sai duka yakeyi. Saida tazo daff haɗe bakinsu waje ɗaya ya kauda kansa gefe. Wani irin kunya da takaicine ya lulluɓeta wannan wane irin wulaƙanci ne? Tafaɗa acikin ranta tayi ƙasa da kanta alamun jin kunya ya tabbata agareta jikinta yayi sanyi. Ganin hakan yasa shima jikinsa yayi sanyi ya tabbata bai ƙyauta mata ba cikin rashin jin daɗin abunda ya aikata yace.

"I'm sorry kiyi haƙuri. I dnt mean to embarrass u"
Chapter 53 · 0% Book details