← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 106

Sashe 19

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suke rayuwa harta samu juna biyu Mummy batasan da zancen cikinba Har saida yafito itama lokacin tanada nata cikin had yafi na Amarya girma. Amma ita nata kowa yasan dashi itakuma amarya babu wansa yasani dake ba laulayi takeyi ba.

  Ganin tanada juna biyu ya sanya Mummy ta sassauta mata gabaki ɗaya tadaina shifa sabgarta. Hakan ya sama mata sauƙi ba kaɗan ba tasamu ta ƙarasa rainon cikinta cikin salama gashi dama ya haɗu matada karatu. mummy tafara haihuwa aka sanya mata Aysha.

daga baya itama amarya ta sauƙa aka sanya sunan mahaifinta Habibu.  ya hanata yin tsarin iyali saboda yanason yara itama Mummy adole takeyi bada son ransa ba. Watanta  biyar da haihuwa tasake samun juna biyi shima saida yafito kafin aka gane dan ita sam bata laulayi wannan karon mace ta haifa Aka sanya mata sunan Mummy yayi hakane dan kawai ya faranta ran Mummy ko zata sauƙo suyi zaman lpy da Mama hakan kuwa yayi aiki dan tayi matuƙar jin daɗi kuma tayi mamaki dan har tana tambayarsa.

"Kuma mahaifiyarta ta yarda kasaka sunana?" yace.

"Ta yarda sosai ma kuwa itace ta daɗa ƙarfafamin guiwa akan nasaka sunanki ai tana ganin girmanki sosai" wannan abun yasanya Mummy ta watsarda kaff makaman yaƙinfa akan Mama  tana nunawa yarinyar soyayya matuƙa wanda tayi mata laƙani da marmee tace tunda ita Mummy yabita ko wannan marmee ce haka ake  gaya mata kowa marmee yake cemata.

    Saida Mama tayi shekara taƙwas gaba bata sake haihuwa ba bayan haihuwar Marmee itakam Mummy dama ta sayarda haihuwarta kuma tunda ta haifi Aysha ta aika da Babbar ƴarta da fadeela Abuja wajan mahaifanta Ahmad kam mahaifinsa ya roƙi tabar masa shi anan, hakan yasa  gabaki ɗaya yaran basusam junansu ba. Ahmad anan yake karatu yana ajin ƙarshe a secondary alokacin Mama ta haifi sadik. A wannan lokaci ana zaman lafiya matuƙa agidan Saboda Mama nayiwa Mummy biyayya itama Mummy darajar Marmee yasa ta sauƙo ta maida Mama ƴar uwa amma har lokacin jiji dakanta da gadara sunanan dan akomai saita nunasu."

Suna cikin wannan sama mai cikeda Daɗi Baba yazo musu da maganar ƙara aure zai auri yarinyar abokinsa. Abokin baida lafiya ya roƙeshi ya auri ƴarsa saboda mahaifiyarta tarasu bayaso yamutu yabarta batareda yasan tana hannu na gari ba alokacin yarinyar gabaki ɗaya bazata wuce sa'ar Ahmad b sunanta Habiba. Dafarko Baba yaso yaƙi zancem saboda first born ɗinsama ta girmeta bazata wuce shekara sha takwas ba amma ganin kamar itace alfarma guda ɗaya da zai iya yiwa mahaifinta yasa yayarda.  Yaga tashin hankali matuƙa kan auren yarinyarnan dan wanda yagani abaya wajan auren anty ba komai bane wannan karon gashi yaransa sun girma hat Ahmad durƙusa ƙafarsa yayi yana kuka yana roƙon mahaifinsa Akan kar ya auri wannan yarinyar idan auren yakeso yacanja dawata yarinyar haka dai ya shafawa idonsa toka yacigaba da zancen auren tunda dama mutane dayawa sunce masa dole sai yayi haƙuri da irin abubuwanda zai gani yarufe idanuwansa kafin yiyuwar wannan lamarin.

Ahmad ganin mahaifinsa baida niyyar janyewa akan zancensa yasa  ya yanke shawarar barin garin rana ɗaya ya tattara yakom abuja wajan mahaifan Mamarsa."

    Ranar ɗaurin aure bayan anɗaura ƙanwar Baba Halima tarasu wajan haihuwa wannan mutuwa da girgiza shi shiyasa koda akayi auren amaryar bata gane kansa ba har zuwa lokacinda mutuwar ta sakeshi ya fawwala komai ga Allah, itama anata wajan anyi auren bada daɗewa ba mahaifinta ya cika kowa yaje mata ta'aziyya amma banda Mummy babu yanda bai roƙeta ba taƙi zuwa hakan yasa ya ɗauki fushi da ita bai taɓa yimata hakaba sai da yayi wannan auren shikuma yayi hakanne danta gane kuskurenda tayi."

Dafarko amaryar tashigo ta feleƙe ganin itace Yarinya acikinsu sam taƙi takuwa awajan Mummy kamar yanda ake taka kowa. Gani takeyi tunda gidan mijinta ne itama dole tayi abunda takeso batasan dawar garinba.

   Mummy na matuƙar jin Haushin Habiba dan haka tafara fito mata da halaye shikuma anasa wajan tausayin Habiba yakeyi kasancewarta babu Uwa babu uba kuma ƙaramar yarinya.

   Itadai Mama nata ido kawai tana kallon abubuwanda yake faruwa tana daga gefe shikansa yasan kaff cikin matanda babu maiyi masa biyayya da jin maganarsa kamar Mama hakan yasa takeda wani matsayi aransa ya lura ita kaɗaice ke tausayinsa da gudun ɓacin ransa."

    Ya lura itama Habiba sam batajin Magana duk wani abinda ya hanata saita aikata kuma idan Mummy tayi abu saita tanka hakan yasa zaman lafiya yafara ƙauracewa gidan a ƙanƙanin lokaci yafara danasanin ƙaea aure.

     Anyi hutu dan haka Baba ya buƙaci da akawo masa yaransa suyi hutu awajansa kowa yayarda zai taho hutu banda Ahmad. tsanarda yake yiwa aurenda mahaifinsa yayi tayi yawa wanda shi kaɗai yasan dalilin hakan.

A hanyarsu ta zuwa sukayi accident Babbar ƴarsu ta rasu Mummy kamar zatayi  hauka saboda ta rasa ɗiyarta. A garin aka ƙaraso da gawar aka wanketa aka kaita makwanci har akayi wannan abun Habiba bata fitoba, kowa hankalinsa yana tashe dan haka babu wanda ya lurada ita sai bayan an kaita andawo Har akayi ƙwana uku batayiwa Mummy ta'aziya ba Baba ma mutuwar tashiga jikinsa matuƙa dan har rama yayi. Yana lurada cewa Habiba bata fitowa wajan kraɓan gaisuwa da yaje ya sameta cewa tayi itama ramawa tayi  abun yabashi mamaki aiko batayi ta'aziyya dan Mummy ba zatayi danshi mahaifin yarinyar yayi mata faɗa sosai kuma yace taje tasamu Mummy tayi mata gaisuwa.
Itakuma taƙi zuwa tace itama lokacinda mahaifinta yarasu batayi mata gaisuwa ba ganin ana zaman makoki ya sanya Baba bai tada zancenba.

Ana gama zaman makoki Mummy tace sai dai Baba yazaɓa ko ita ko Habiba dan idan zata zauna agidan Habiba bazata zauna mata agida ba idan kuma Habiba zata zauna toya tabbatar ita zatabar gidan kuma da yaranta karya saka ran zata dawo har sai Habiba tabar gidan, wannan zancen yazo agaɓa da bayyanar cikin dayake jikin  Habiba dan haka Baba yakasa yanke shawarin abunda zaiyi kamar da wasa rana ɗaya Mummy ta tattare yaranta da duk wani mallakinta tabar gidan kuma ta tabbatarwa Baba da cewa kar yazp nemanta har ranarda Habiba tabar gidan idan kuma ya nemeta batareda Habiba tabar gidanba toh ko yaƙi ko yaso aranar sayya yanke igiyar aurensu gabaki ɗaya"  Wannan lamari ya girgiza Baba dayasa jininsa yahau ya kwanta jinya kusan abunda ya mallaka saida ya ƙare a jinyarsa a hankali yafara samun lafiya wannan jinya ta sanya Habiba tashiga hankalinta danta tsorata sosai gani takeyi kamar wanda zai mutu idan ya mutu kuwa itace asirinta ya tonu dan haka tayi mugun sanyi tun daga wannan lokacin yasa sam ba'ason ɓacin ransa. Mummy kuma ganin Baba bai nemeta ba ya sanya ta ɗauka ya zaɓi Habiba akanta dan haka ta ɗauki tsanar duniya ya ɗaurawa Habiba.

Bayan Habiba ta haifi wannan cikin dayake jikinta haihuwa ɗaya tasake yi wanda haifi ƴan biyu Mama ma haihuwa ɗayia ta ƙarayi. Sau dayawa mahaifin Mama ke taimaka musu da wasu abubuwan.

Wannan dalilin yasa gidan suka taso basusan juna ba kuma kansu arabe.

  Back to cikin labari.

ZAYNAB ALABURA.

Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Jikina yayi masifar sanyi jin wanann labarin koda wasa babu wanda yataɓa bamu labarin abunda yafaru agidanmu sai yanzu Baba shida kansa dayaji zai bada kuma ya bada tausayinsa ya kamani sosai amma tabbas akwai kuskurensa acikin faruwar wannan lamarin dukda nima a sanina bantaɓa kallon mutum mai sanyin rai irinnasa ba. Na ɗaga idanuwana na kalleshi na sakar masa murmushi tabbas ko a yanzu da mahaifina yake cikin shekaru na hamsin da wani abun yanada matuƙar kyawunda kallo ɗaya ya ishi bayyana kyawunsa ko mu cikin ƴaƴansa babu wanda ya ɗauko kamanninsa sak Yayana Habibu ne ma yake kamanni dashi sosai amma mu duka sai dai ace gawani abunda muka ɗauko nasa kama da mahaifiyarsa yakeyi sakk hakan zamuce tunda mu bamusan mahaifinsa ba. Cikeda ladabi nadubi Baba nace.

"Baba har indai bazanyi laifi ba zan iya yimaka gyara akan abubuwanda suka faru?" saida ya murmusa sannan yace.

"Nasan nayi kuskure akwai abubuwanda da hannun agogo zai juya baya dana gyarasu amma yanzu lokaci yawuce bana tunanin akwai Abunda zai iya gyara lamarinan amma ina jinki bazanƙi taki ba ta iya yiwuwa akwaita hanyarda zakibi ki gyara" ina jinki.
Nisawa nayi sannan nace.

"Baba komai zai iya dawowa dai-dai ya zauna a muhallinsa amma ba irin yanda daa can yakeba saboda abaya abubuwa basa zaune a muhallinsu ba Baba koma wacece Mummy koma waye mahaifinta bai kamata kabata damar daka bataba komai ta mallaka kaine mijin itace matarka bana tunanin akwai wani yanayi daya kamata ace ya canja hakan. Akoda yaushe kazama kaine mai iko da gidanka ba mace ba aduk lokacinda akace macece ke iko da gida toh tabbas za'a samu matsala. Koda sau ɗaya daka fito ka gwada mata kaine kake aurenta bazaka ɗauki abubuwanda takeyiba nasan tana sonka dole zata risina amma kawaicinda kakeyi mata ya sanya take ganin kamar tazama maka dole zata juyaka ta yanda taso kuma ka bita har wasu suke kallon tsoronta kakeji. Ni banaso naga mahaifina a matsayin matsoraci inaso naga mahaifina a matsayin mai iko da faɗa aji wanda ya isa da gidan da ƴaƴansa da matansa gabaki ɗaya ko Dabba kake kiwo Baba yakamata ace data ganka tasan kaine mai gidan bare matanda Allah ya rigada ɗauraka akansu Allah da kansa yabaku daraja acikin suratul baƙara Allah yace.
Chapter 19 · 0% Book details