← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 106

Sashe 5

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mama kingani ba kwallo akaci ba Baba ne ya saimin waya" da mamaki mama ke kallon wayar Hannuna sannan tajuya tadubi Baba tace.

"A'ina kasamu kudi kasai mata waya Alhaji? Dan Allah saboda karatun yarinyarnan kada ka sanya kanka cikin damuwa da waya da babu waya zatayi karatunta" Murmusawa yayi sannan yace.

"Shekarun Baya kenan ai yanzu lokaci ya canja idan babu wayar bazata samu damar yin karatun ba"

"Amma!" Baba ya daga mata hannu sannan yace.

"Nasan zaki tambayi yanda nasamu kudi daya dga cikin gonakina nadauka na bada hayarta ta shekara biyar daganan harsu gama karatunsu zan sami kudinda zanna biya musu hankali kwance"

Jikina yayi sanyi matuka jin cewa saida ya jinginarda gonarsa kafin yasamu kudinda zai biya mana karatu. Toh wannan Bawan Allahn dame zamu saka masa?

Komawa nayi na zauna jiki a sanyaye nace.

"Baba Allah ya saka maka da dumbin alkhairai masu yawa Allah yabiya maka bukatunka yasaka maka da aljanna"

"Amin" ya amsa cikeda jin dadi. Mama dake tanason korata a wajan tace.

"Kinfasa zuwa karatun da kikace zakije ne?" Kai na girgiza mata dasauri nace.

"Banfasa ba"

"Toh naji baki tambayi Babannaku ba" Baba yace.

"Karatu Zataje ta?"

"Eh itada kawarta amma naji batayi maganarba"

"Shikenan tajeta Allah yabasu sa'a" na amsa da "Amin" sannan nafice. Ina shiga daki na É—auki wayar Mama na kira Maryam tace Zatzo ta daukeni. Minti talatin ta iso nayi musu sallma muka fice karatun 2hours kawai mukayi Maryam ta matsa sai mun wuce gidansu dake ban tambaya naki amma danaga tayi fushi tana faÉ—in.

"Tunda muke dake baki taɓa zuwa gidanmu ba amma ni naje gidanku sau babu iyaka Allah har indai yau bakije gidanmu ba toh bankara zuwa naku gidan"

"Duk mai yayi zafi haka? muje amma bazan daÉ—e ba tunda kinga ban fadawa Baba ba"

Murna sosai Maryam tayi dake dama driver yana jira kai tsaye muka wuce gidansu dake unguwar fadaman mada anan garin bauchi,

Gidansu ya haÉ—u sosai gidane Babba tsararre mai hawa biyu tun daga wajan gidanma abun kallo ne bare awuce zuwa ciki, a yanda maryam take mu'amala faram-faram da mutane baza'a taba dauka dukiyarsu har takai hakaba sai dai dama daga yanayinta zaka gane sunada hali.

Mai gadi ya bude mana gate muka shigr bayan minfito a motar kai tsaye É—akin mamansu muka fara shiga muka gaidata, tanada fara'a sosai cikeda Murna take faÉ—in.

"Yau wace rana Mamee tazo gidanmu kullum saijin labarin Mamee amma ban taɓa ganinta ba" dariya kawai nayi muka wuce ciki ta falonda muka ratsa zamu wuce muka riski wani Saurayi zaune yana danne-danne a laptop ta company apple dake gabansa,

batareda ya juyo ba Yace.

"Harkinyi karatun kenan?"

"Eh mungama shine muka taho gida"
Murmushi yayi mai sauti wanda yasanyani satan kallonsa iya gefen fuskarsa nake kallo amma hakan bai hanani gane kamanninsa ba, kyakkyawane sosai na karshe duk yanda nake kallon kyawun Maryam nasa ya zarce nan fatarsa har wani tarr tayi sai sheki takeyi kamar madara gashi yanda yake tafiyarda laptop na gabansa cikin tsari da nutsuwa gwanin ban sha'awa saukarda idona kasa nayi na tattaro nutsuwata da sanyayyar murya nace.

"Ina wuni" batareda ya dago ya kalleni ba ya amsa maryam taja hannuna mukabar wajan, É—akinta muka shiga shima da É—an karamin palour da saitin kujeru sai kuma uwar dakin da saitin gado kamar dakin amarya kayanda aka zuba mata adakin amaryarma idanba yar masu hali ba bazata samu kamarsa ba.

kwanciya nayi kan bed É—in ina maida numfashi maryam ta kalleni tana faÉ—in.

"Sannu" ita a tunaninta gajiya nayi yansa nake maida numfashin abunda bata saniba shine tunda nayi arba da Yayanta bugun zuciyata ta sauwa."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab  m Bawa JAIZ BANK shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance  zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️Ote
Comment
Follow
share

To be cintinued

Zaynab Alabura

*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023

*بسم الله الرحمن الرحيم*

BY
    ZAYNAB BAWA

PAGE 5

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝

Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid 200
*ƘADDARAR RAYUWA*

****

Ajiyar zuciya na sauke ta kalleni tace.

"ina zuwa" É—an karamin fridge dayake dakin ta nufa tadaukomin ruwa da lemo ta ajiye gefen gadon tace.

"Tashi kisha ruwa" banbi takan ruwanda takawo ba
na miƙe zaune wayarda Baba ya siyomin na ciro ajaka na mika mata dama already nafaɗa mata Baba ya siyamin wayar ina mika mata ta jonata a chargy tafaramin setting dinta,

Instagram da whatsapp ta budemin tadaura pic ɗin data daukeni mai nikab akai. Mikamin tayi tace nayi following wanɗanda nakeso ina karɓa nafara following ƴan wasan kwallon kafa (footballers) Da mamaki maryam take kallona duka takaimin tana faɗin.

"Ke ana folllowing mutanen arziki ke kina shirme" mtsww naja tsaki sannan nace.

"nikuma kinga ai mutanen tsiya nayi" karban wayan tayi tafara searching abubuwa tana nunamin tana faÉ—in.

"Kingani irin waÉ—annan ake following kina mace menene ya haÉ—aki da É—an wasan kwallo kuma?" Fauce wayata nayi nace.

"Yan wasan kwallon dai su nayi niyya kuma su zanbi. naga wayata ce ba taki ba? Æ´an wasan kwallon kaff sunmafi kowa yawan followers"

Bata sake kulani ba nikuwa naci gaba da dannawa pictures dinsu likes, aÉ—akin ta É—auko mana abinci takawo mukaci tafita da kwanukan sai wajan Yamma kafin muka tashi tafiya muka fito dan yiwa umminsu Sallama a falon da muka barshi muka taras dashi sai dai da alamu ya tashi danya canja kaya. Munzo daff zamu fita muka tsinci muryarsa yana faÉ—in.

"Kujirani zan kaiku" toh kawai maryam ta amsa amma abin yabata mamaki dan datsu babu yanda batayi ba yace bazai kaitaba tunda shi ba driver dinta bane amma yanzu bata tambaya ba yana fadin tajirashi yakaita.

Wajan Umminsu Maryam muka wuce danyi mata Sallama Kudi taɗauka tabani naki karba babu yanda batayi na karɓa ba naki bayan hakama ban faɗa agida zanje gidansu naryam ba kuma mama idan taga kudin sai tayimin faɗa, Umminsu Maryam bataji daɗin yanda naki karban kuɗin ba amma nima babu yanda na iya saboda yanayin gidanmu,
Muna zaune a falon munajiransa yashigo Bai kalli yanda muke yace.

"Muje" Nan danan zuciyata tafara bugawa da sauri-sauri  jin muryarsa danayi a hankali na daga kaina na kalli fuskarsa farine sol kyakkyawa yanada dogon hanci da manyan idanuwa kana kallonsa kaga sakk bafulatani kamarsa ɗaya sak da Umminsu, Yanada tsayi kuma siririne, Cikin harshen fulatanci naji yana yiwa Umminsu magana itama ta maida masa da harshen fullancin amma naji ta ambaci sunansa Abubakar abunda na iya ganewa kenan acikin abunda suka faɗa bayan sun gama maganar Ummi ta juyo ta dubeni tace.

"ki gaishe da Mamanku" na amsa sannan mukayi mata sallama muka fice. Kafin mu karaso harya isa gaban motarsa yashiga mu kadai yake jira. Maryam ta bude min bayan motar nashiga tarufe sannna ta shiga gaba, tunda muka fara tafiya baice komaiba tuƙinsa kawai yakeyi cikin nutsuwa ganin yanda maryam ta nutsu duk kuwa da rawar kanta ya tabbatarmin da cewa bayason hayaniya saida muka hau titi sannan naji yace.

   "ina zamuyi?" yayi maganar ne batareda ya kalli ko daya daga cikinmu ba.

"Kobi" Maryam tafaɗa sannan tayi masa bayani yanda zai gane. tunda muka fara tafiya nake satar kallonsa amma shi gabaki ɗaya hankalinsa ba'a kanmu yakeba. Yanda kikasan bai sanda mutane acikin motar ba. Sa'i-Sa'i maryam take jiyowa tanamin magana ina bata amsa. A dai-dai ƙofar gidanda ta faɗa masa yayi parking motarsa,

Muna isa nayi masa godiya da kayi kawai ya amsa na fice. Inajiyo maryam tana cemasa zataje ta gaida mamana juyawa nayi naga ko ita zai bata amsa sai naga itanma da kayin yabata amsa fitowa tayi muka wuce ciki tareda ita suka gaisa da Mama sanin yana jiranta yasa bata daÉ—e ba tafito suka wuce."

2YEARS LATER (Bayan shekara biyu)

Sanye nake da farin Uniform ɗina. ɗinkine wanda aka yishi na zamani yayi matukar zaunawa yamin kyau sosai yasha guga dagani har uniform ɗin sheƙi mukeyi. a shekara biyunnan da suka wuce nayi matukar kyau nayi cika har tsayi saida naƙara izuwa yanzu na cika ƴan mata wacce za'a kalla akirata da ƴan mata, baƙar jakace schoolbag maƙale a bayana duk wasu takadduna suna cikinta, muna sanya ƙafarmu cikin school ɗin wayata tayi ƙara. Inajin ƙarar shigowar Saƙo wayata saida gabana yafaɗi. Maryam ta dubeni tace.

"Saƙon koh?" Kai kawai na gyaɗa mata cike da damuwa nace.

"Wallh Babe Yanzu har banaso wayata tayi ƙara har indai nashigo school saina tsinci kaina da faɗuwar gaba" Maryam tace.
"ni abunda yake damuna mun kasa gane waye mai wannan saƙon mai kuma saƙon yake nufi" Nisawa nayi cikeda tabbacin abunda zan faɗa nace.
Chapter 5 · 0% Book details