← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 106

Sashe 88

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Kuka? Meyasa? Ba nace miki banason kukanki ba? Akan abu kaÉ—an sai kifara zubda hawaye"

"Abu kaÉ—an koh? Cewa ba kayi babu komai acikin abunda tayi kuma kasan duk wannan abun tanayine kawai danta sameka shin zakace babu komai" ya mannani da jikinsa sosai yana shafa bayana sannan yafara rarrashi.

"Is Okay let her call me whatsoever she wants ai ba hakan yana nufin ta mallekeni nazama nata kenan bakoh? I'm yours naki ke kaÉ—ai, kidaina tada hankalinki akan Lina da ace Lina zataja hankalina ko ta mallakeni may be 5-7years backs ta mallakeni you don't need to worry about her Okay?" na gyada kaina.

"We're late yakamata mutafi yanzu" cikeda shagwaɓa nafara magana.

"Nifa bann shirya komai na tafiya ba nazo ina nemanka baka nan har zan fita shine ka shigo"

"Is okay Babu abunda zamu tafi dashi nasaka an shirya mana komai a masauƙinmu duk abunda kikeso ki saka ciki handbag ɗinki thats all you'll need" na raba jikina da nasa.

"Barina É—auko bag da phone É—ina"

"Rouhi" ya kirani na kalleshi. Yakai idonsa kan breast É—ina wanda suna cikin riga ne amma sunyi Tum-tum tunda ya rumgumeni yaji suna tokarinsa hankalinsa yatashi badai ahaka zan fita ba? Allah yagani shiko tudunsu bayaso agani saboda yanda yaga kyawunsu bayaso ko a cikin riga wani ya kalla har yayi la'akari da shape É—insu. Ganin ina kallonsa ina jiran abunda zaice yasa yafara magana.

"Change your Outfits Rouhi" na kalli kayan jikina babu abunda yayi na kalleshi yacigaba da magana.

"Ta fitarda shape fa tudun breast É—inki bazan iya jure wasu sh kalli abunda yake mallakina ba ko yayane duk da kuwa yasan suna killace amma ba irin wannan killacewar yakeso ba.

"Wait I'm coming yafaɗa haɗeda shigewa ciki phone ɗinsa kawai ya ɗauka da ya zura alijhu dubawa yayi duk wani abunda yakamata yayi plug-out yayi sannan muka fita, ɗakina muka fita kai tsaye dakansa ya buɗe ya ɗauka wata riga yabani Saida nabar wajan sannan na canja rigar bayan nasaka itama yace ba ita saida nasaka riguna morethan 10 duk basuyi ba daga ƙarshe Half Vest wanda tayi tighting jikina nasaka kan bra sannan na ƙara wata full vest akai dakyar a hakan yayarda amma hankalinsa bai gama ƙwanciya ba.

Munsamu Lina da Nawrah suna jiran fitowarmu Nawrah riga da wando tasaka sai wani mini veil datayi rolling. Lina kuwa kayan gadone a ajikinta wato iya cinya sai dai wannan karo cikinta a rufe yake. Na kalli kayanda suka saka na ƙara ko ajiki sa amma ni shine zai matsa saina kammala jikina waje ɗaya. Lallai Hammood rayuwarsa da gyara ai Nawrah ma yakamata yayi kishinta tunda ƙanwarsace akwai hakkinta a kansa wato shi yanda na lura dashi matarshi kaɗai yasani. Dagani harsu Babu wanda ya kula wani banbi takansu ba danaga nima batani sukeyi ba.

Mota ɗaya muka shiga da Hammood Nawrah da Lina suna mota ɗaya. A jirgi ma waje ɗaya muka zauna dashi Suma suna wajansu. Dake ƙasar sun snaarda lokacin isowarsa yasa airport ke cike da cincirin doma jama'a tako'ina hasken camera kawai nake kallo yau Sunga abunda suke nema wato masu labarai Matar Hammod yau A idonsu bayan lokaci daya ɗauka yana ɓoyeta.

lina da suna bayanmu amma saida dawo ɗaya gefenshi ta riƙe hannunsa sai zuba murmushi take ma nema labarai sun samu abun nema sai ɗauka kawai suke cikin mutane kawai yasa ban mata rashin mutumci ba dama inaji da haushin ɗatsu. Kallona yayi naci magani yasan za'a.

"Menene?" yayi magana a yanayin son shagwaɓa mutum. Idea ce mai mugun zafi ta faɗomin dan haka na kalli ƙafata shima kallon ƙfar yayi sannan ya dago gareni.

"Ya kama miki ƙafa? Dasauri na ɗaga kai,"Kina buƙatar na sassauta miki?" nanma kai na gyaɗa masa. Ya zare hannunsa cikin nata a wajan ya durƙusa Akan gauiwarsa guda ɗaya a gabana batareda damuwa da matsayi ko cincirindon mutane da suke wajanba. Hannuna yasa yafara gyaramun igiyar takamin. Wani irin rikitaccen ihune kawai yake tashi a wajan fans ɗinsa mata kuwa ji suke inama ace sune masu wannan sa'ar. Bayan yagama ta ɗaya ƙafar na miƙa masa ɗayarma ya gyara. A zahirin gaskiya fa babu wani kamani da takalmin yayi kawai dai inaso na nuna matsayina a wajansa ne. Ya miƙe haɗeda sakarmin murmushi nima murmushin nayi masa.

"Yayi miki? Na gyaɗa kai alamun yayi kuma fa ya ɗan yimin ruwa amma tunda buƙata tabiya komai yayi dai-dai. Shida kansa ya buɗemin ƙofar mota na zauna ya rufe kafin ya isa an buɗe masa yashugo muka tafi.

Wani tangamemen hotel ne wanda aka sauƙi palyers na team ɗinsu kusan gaba ɗayansu sun iso Hammood na ɗaya daga cikin wanda sukazo late. Kowane player apartment yake dashi shida family ɗinsa sannan duk wani expenses both nasa dana family ɗinsa an ɗauke. Su kansu naga alamun wajan ya burgesu bare ni wacce inbanda Abu dhabi danaje shima hakan ina ƙwance zazzaɓi banga ko'ina ba sai wannan ƙasar. Apartment ɗinmu yana ɗaya daga cikin apartment na musamman a gajiya muka ƙarasa ciki ni dashi Dama ɗaki ɗaya muka zauna Nwarh da Lina kowacce takama ɗakinta.

Ana gobe za'a fara buga worldcup washe garin ranarda mukaje kenan saiga Yaya Ahmad da Yaya habibu harda matan Ya Ahamd wacce cikinta ya fito sosai Bansan da zuwansu ba sai ganinsu kawai nayi babu wanda ya sanar dani ko Hammood bai faÉ—amin ba ashe shiya shirya tafiyar. Baisan Matar Ya Ahmad nada juna biyu ba ya haÉ—a harda ita da Mummy tace tazauna Baba yace tataho kawai duk wnai kula zata sameshi acan kusa da mijinta. Mum ma aranar ta iso ni ina wajansu Yaya Ahmad banmasan ta iso ba a wajansu na raba dare saboda Hammood bai dawoba kuma ya shaidamin ba lallai ya dawo ba zai iya kaiwa safiya."

Nagama exam Please kuyimin addu'ar fitowa da kyakkyawan sakamako."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Ranarda za'a fara buga worldcup bansaka Hammood a idona ba motocine sukazo har yanda muke É—aukanmu Sai alokacin naga Mum na gaisheta ko kallon yanda nake batayiba Gabaki É—aya muka shiga mota Ya Habibu ba mota É—aya mukaje dashiba bansan yaya akayi ba nidai naga bayan mun isa suna magana da Nawarh bansan ko É—an zamansu da baifi 30minute a mota bane har suka saba. Bata yanda kowa yakebi ba mukabi ta wani waje daban muka shiga ciki.

Fili yacika da ƴan kallo tamƙam da ƴan kallo amma sai da mu ba cikin wannan wajan muke ba wani wajene da ake kira da VIP suit daga cikin wajan kallon duk wani abunda yake gudana a cikin filin da glass aka rufe wajan sannan akwai set na Sopa a ciki da table na drink da komai a takaice dai wani ƙayataccen living room akayi a wajan. Nida Nawrah da Lina sa Ya Ahmad ta matarsa da Mum Da Yaya habibu. Wajan ya tsaru sosai banajin wannan wajan Hukumar worldcup ne suka ɗauki nauyin biyansa tunanina yafi karkata akan Hammood ne ya kama mana dakansa wanda suke cikin fili suna iya ganinsu da duk abunda mukeyi. Muna kallo ƴan wasa suka fara shigowa har suka gama idona yanakan Hammood yayi kyau sosai cikin kayan ball ɗin bayan angama duk wasu ɗabi'a da ake gudanarwa kafin fara ball Juyowa Hammood yayi ya kalli wajan da muke murmushi na sakar mas adake da wajanda muke babi wani nisa sosai shima ya maidomin.
Ana shirin fara wasa yaya habibu yamin magana cikin harshen hausa.

"Marmeeyy bani wayarki nakira Maryam tace nakirata video call da zarar anfara" miƙa masa wayar nayi ya ya amsa ya kirata mamaki da al'ajabi yagaza ɓoyuwa a fuskar Nawrah bata taɓa tunanin Yaya Habibu ɗan uwana bane sai a yanzu dataga munyi magana da yare ɗaya sannan ta ƙare mana kallo. Har ɗan kama mukeyi. Aranta tana faɗin aida nayi kama da Yaya habibu toda komai zaizo da sauƙi ko Mum ɗinsu zata ɗauki abun dasauki akan yanda ta ɗauka yanzu. Duk da Yaya habibu Bai kaisu haske ma amma tsakanin haskensa da nawa akwai bambamci sosai kuma suma a cikinsu ana iya samun masu madaidaicin haske kamar nasa Kuma gashi kyakyawa ni mace dayakamata ace nice nayi kyau sai shi namiji yayi kalar kyau sosai. Saida na ɗago na kamata tana kallonmu sannan ta kauda kanta mamaki yaƙi barin ranta Ba ita kaɗai ba ashe har Mum da Lina sunyi mamaki amma babu wanda yafito ya nuna mamakinsa a fili.
Chapter 88 · 0% Book details