← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 106

Sashe 104

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hammood ya dubi Abie"Abie tanason magana dakai akwai abunda zata faɗa maka" da mamaki na kalli Hammood ya ɓata rai yaƙi kallon yanda nake. Abie yayi murmushi "Me kukeson faɗamin?" Hammod yace"Takeson faɗa maka dai abie gata ga tambayeta" Sai kallonsa nake inason ya kalleni yaƙi na mintineshi ta ƙasan dining yace "Auchh abie kaga ta mintsineni kuma ita tace tanason magan dakai" Abie dai dariya yakeyi nayi shiru nayi ƙasa dakai nakasa cewa komai, "Zaynab Habibty" Abie yakira sunana a hankali na ɗago na kalleshi sai yau na ƙare masa kallo kamarsu ɗaya sakk da Hammood sai dai shi akwai girma a jikinsa nayi ƙasa da kaina, "Me kikeson sanar dani? Please tell me zanyi farin ciki sosai kuma in sha Allah ko menene zan yi miki" nayi ƙasa da kaina ina tunanin ta yanda zan fara maganar saboda inaso ya fahimceni sosai "Abie bani nakeson magana dakai ba shine yakeson magana dakai amma ya juyo dashi kaina inaga bazai iya faɗa bane amma zaifi kyau da zai faɗa daga bakinsa" Abie ya nutsu sosai saboda ganin tawa nutsuwar "Karki damu Habibty Faɗa daga bakinki can ɗaukeshi kanar shine yafaɗa" kaina yana ƙasa nace, "Mum, Mum yakeso tadawo tacigaba da zama a matsayin matarka a gidannan yanason neman alfarma a wajanka kayi masa wannan alfarmar har indai hakan bazai zama takura a rayuwarka ba, koda Mum tayi maka laifi yana nema mata yafiya a wajanka matsayinsa na ɗanta, nima ina neman alfarma Abie dan Allah kayi hakuri ka maida Mum tunda kaga har yanzu batayi aure ba ta iya yiwuwa bata buƙatar wani yashugo rayuwarta ta'iya yiwuwa tsawon lokacinnan kai kawai take jira, ta'iya yiwuwa Hannu kawai take jira ka miƙa mata ta riƙe" Abie ya kalli Hammood wanda yake pretending kamar hankalinsa na wani wajan ba akanmu yake ba, "Habibty kinsan Mum ɗinku wane irin addini takeyi?" dasauri na gyaɗa kai "Nasani Abie kuma nasan hakan bazai hanaka sake zama da itaba saboda abaya kazauna da ita kuma ahakan, idanma kanaso tadawo musulunci Abie ka jawota kusa dakai ka kyautata mata iyakar kyautatawa ka nuna mata halaye masu kyau da ɗabi'u na kwarai na tabbata waɗannan kawai sun isa suja ra'ayinta" Abie ya jijjiga kai yakai kallonsa wajan Nawrah ga mamakinsa kuka takeyi hawaye wani banin wani akan kumatunta jikinsa ya ƙara sanyi sosai ya kalli Hammood, "Tun yaushe kake da wannan saƙon gareni?" sai alokacin Hammood ya kalleshi "Tun ranarda Mum tasa ƙafa tabar gidannan" "Meyasa kaɗauki tsawon lokaci baka sanar dani ba? Da ace ka taɓa faɗamin abunda yake ranka koda sau ɗaya da Mum ɗinku bata ɗauki tsawon lokaci bata gidannan ba da bakuyi rayuwa Babu itaba" Nawrah wacce kuka yakeson cin ƙarfinta tace.

"A kullum ƙoƙarinka abie shine kabamu rayuwarda zamu manta da mahaufiyarmu baka taɓa tambayarmu ko munason sake rayuwa da itaba ko A'a ko yaya mahaifiyarmu take tayaya zamu ƙi son rayuwa da ita? tsawon Shekarun na rayu da kewarta abie kuma har yanzu inason sake rayuwa da ita anan gidan amma bazan takura maka ba kuma bazan roƙeka ba abie idan kaji kanason sake rayuwa da Mum kayi, idan bakaso kada ka takura kanka karka damu tsawon shekaru bamu rayu da itaba yanzu ma zamu iya ƙarasa rayuwarmu ahaka" tana gama faɗin haka ta miƙe tabar wajan. abie ya sauƙe ajiyar zuciya ya kalleni "Nagode Habibty Allah ya miki albarka idanba ace keba bazan san abunda yake ran yarana ba in sha Allah zan dawo musu da Mahifiayarsu suci gaba da rayuwa da ita" Nima Godiya nayi masa Hammood ma yayi masa godiya mukayi masa sallama muka wuce ciki, muna shiga na zabga masa Harara"Amma ai bahaka mukayi dakaiba cewa kayi zaka masa magana menene zakace masa nine nakeson yin magana dashi?" ya jawoni jikinsa "Sorry Rouhi nasan zaki fahimtar dashi fiyeda yanda ni zanyi shiyasa naso ki fahimtar dashi da kanki" na ɓata rai sosai, "Shikenan ai" "Sorry kimin afuwa Gobe in sha Allah nayi alƙawarin fita dake yawo" jin zamuje yawo yasani nasake ina walwala. Godiya kawai yakeyi kamar ba Hammood daya nuna da zamansu tare da akasin haka duk bai dameshi ba."

Washe gari ni dashi zallah ya É—aukemu fita amma yarufe fuskarsa da Face-mask zaga wajaje mukeyi dama tunda mukazo bamu fita ba, wani mutumi mukaci karo dashi mai kamada Baba sakk a cikin shago da mukaje sai dai shi ya manyanta sosai na nunawa Hammood shi shima kansa yayi mamakin kamannin muka saya abunda yakaimu muka wuce.

Satinmu Biyu a gidan Abbie kafin muka ɗauki haramar tafiya daƙyar na lallasheshi muka wuce wajan Mum. Wannan karon Babu yabo babu fallasa bata dai shiga harkata amma idanna gaisheta tana amsawa gabaki ɗaya Hammood a takure yake a zamanmu wajanta saima ni nafishi sakewa, Muna wajanta Abie yazo neman aurenta ranar taci kuka kamar zatayi yaya dakyar tayi shiru Babu ɓata lokaci ta amince masa saboda itama batason ɓata rayuwarta a zama ita kaɗai, mun baro wajan Mum cikeda Murna dakuma ɗaukin abunda yake faruwa.

Shaf namanta da zancen wannan mutumin da muka gani saida ranar muna waya da Baba na tuna.

"Baba nikam ranar naga wani mai kama daki sosai a kuwait wallh Baba sakk amma shi ya manyanta sosai a wani shago da mukaje nida Hammood" nan da nana naga damuwa akan fuskarsa dake video call mukeyi yace yana zuwa yatashi ya ɗauko wani hoto ya nunamin" A tsorace nace Shine Baba wallh wannan mutumin sai dai kawai ya manyanta yanzu amma shine kamarku ɗaya sakk dashi Baba yace."Ina Hammood? Bani shi muyi magana" natashi nafito dasauri na nufi wajansa saboda naga hankalin Baba atashe yake, na miƙa masa wayar ya amsa ganin Baba yasa ya zauna suka gaisa. Basu waje nayi bansan abunda suka tattauna ba.

Bayan kamar 2weeks dayin wayarmu da Hammood yacemin zamuje Nigeria Murna kamar zanyi Yaya. A satin muka shirya tafiya amma nasha wahala bantaɓa tafiya da nasha wahala irinta ba muna sauƙa sai zazzaɓi hakan yasa Hammood yakaini gida kawai, dake shi hidimarsa Da Baba kawai yazo yi suka gama bincikensu akan abunda ya kawosu. Bayan kwana 2 Muna zaune ɗaki zazzaɓin ya sauƙa banmaje asibiti ba Baba ya aiko yana neman kowa nanda 2hours har anty fadeelah da Aysha sunzo da Yaya Ahmad dukanmu sai da muka haɗu har hassan da hussain koda kuwa ƙananune saida Baba yace aje hardasu. Harda Hammood cikin palourn Baba da Hajiya da ƙannen Baba da Alhaji Habibu, duk da Hammood bazai fahimci abunda za'ace aciki ba amma kasancewar yasan komai da za'a faɗa a wajan Baba yace yazauna ayi dashi. An gaisa Alhaji Habibu yafara magana.

"Nasan zakuyi mamakin abunda yasa aka taraku anan kamar yanda kuka sani mahaifin Babanku abokina ne na tsawon lokaci sai dai Rana ɗaya aka nemeshi aka rasa kamar yanada rana ɗaya dama yazo, ina nufin kakanku ba daga nan yake ba rana ɗaya kawai aka tsince shi kasancewar mutanen daa can da karamci wanda suka sameshi suka riƙeshi kamar sune mahaifansa idan bawak sun faɗa ba baza'a taɓa sanin cewa basu suka haufeshi ba sai dai kuma kalar fata data bambamta. lokacin baifi ɗan shekara goma sha ba a lokacin da aka tsinceshi baisan kansa koshi waye ba baisan daga yanda yake ba, anguwarmu ɗaya kuma lokacin muna kusan sa'anni yasa muka tashi atare bamu damu da farar fatarsa data zarce iyaka ba tunda munji da hausa yake magana tsawon wannan lokaci babu yanda zai kawo mana cewa ba daganan yake ba, kuma babu wanda yazo nemansa, aka sanya masa suna Muhammad aka sakashi a makaranta Bayan wasu shekaru sai Allah ya haɗasu da Hajiya gatanan akayi aure, aurensu gabaki ɗaya bai ɗauki tsawon lokaci ba bayan haihuwar yara uku aka nemeshi aka rasa ya ɓata ɓat kamar zuwansa babu bincike da ba'ayiba amma ko labarinsa babu shekaru kusan arba'in sai kawai ranar Marmeeyy taje can garinsu mijinta taga mai kama da mahaifinta sakk ta nunawa mijinta kamar ta manta da zancen saita yiwa mahaifinta magana yayiwa mijin magana bincike yayi bincike aka gane cewa mahaifin Babanku ne wnda ya ɓace tsawon lokaci shima bayan an tuntuɓeshi tabbaci ya nuna yayi zama A nijeria tun yana yaro kuma mahaifinsa ma'aikacin lafiya ne da yake zaune anan da iyalansa tun a wancan lokacin bayida lafiya yasamu taɓin ƙwaƙwalwa Rana ɗaya suka nemeshi suka rasa kamar yanda rana ɗaya yadawo garesu bazai iya tuna yayi aure kokuwa baiyiba amma shi kansa dayaga mahaifinku kamanninsu bai musa cewa babanku ɗansa bane mun shirya in sha Allah zamuje gareshi nida Mahaifinku da Ahmad mijin Marmeeyy ya shirya mana tafiya idanma takama muje harda matarsa zamu tafi da ita haka ubagiji yake lamarinsa wata rabuwar idanya ƙaddara tahar abada ce wata kuma sai dai aɗauki shekaru amma za'a sake haɗuwa. Allah ya ƙaddari zamu sake ganin mahaifinku Allah ya sada fuskokinmu da alkhairi su duka suka Amsa da Amin. Sukayiwa Hammood Godiya sosai."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Bayan mun fito gabaki ɗaya kowa mamaki yake al'amari irinna ubangiji. Bayan munsamu keɓewa muna zaune nida Aysha da Anty fadeelah aysha da dubeni.

"Marmeeyy wallh Shawarwarinki sunyi amfani kinga yanzu Hamma ya rage sosai bakiga har nayi auki ba?"
Chapter 104 · 0% Book details