← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 106

Sashe 105

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh tabbas kinyi auki sosai wallh amma kinsan wani abu nifa yanda na lura Hamma harda rashin tausayi fa yanzu ta'iya yiwuwa harda soyayyarki datayi masa kamu yana jin tausayin shiyasa yake ragar miki, Ni kinga Hammood ko yaya na nuna banaso ƙyaleni yake yaushema yasamu kaina dawuri nabarshi da shan lime da lemon kullum?" Aysha tace"Lallai Marmeeyy bakida kirki wallh Allah ya shiryeki na amsa da"Amin" Anty fadeelah tana jinmu ita dai tayi shiru tana tunanin kowa da tasa abincin wani gubar wani, ita nata mijinma kwata-kwata bata gane yanayi mu'amalarsa batasan ko Dan tana sabon shiga wa lamarin bane yasa. Amma itama idan ankwana biyu tagama gane komai bataji canji ba zata ajiye girma agefe ta nemi shawarata. Wuni mukayi ranar gidan da farin ciki Baba ma kan ganinsa zakasan yana cikin farin ciki dama yanaji aransa wata rana nice wacce zan haɗa masa kan farin cikin gidansa gabaki ɗaya."

Muda Hammood muka fara gaba saboda a cikinsu akwai wanda Visa ɗinsa bata samu ba, Kuma Hammood yanada match da zai buga a wannan time ɗin. tun isarmu kuwait naga ina yiwa Hammood magana yana shashsareni ban kulashi ba saboda isar safe mukayi saida dare yashigo kwanciya sannan na sameshi, "Masoyi me nayi maka kake shareni? Idan laifi nayi maka saika sanar dani bawai kazauna kana fushi dani ba" kallona yayi baice komaiba zaiyi hanyar toilet nasha gabansa na langwaɓar dakai, "Please mana masoyi zaka sakani cikin damuwa fa" ya kamo Hannuna muka zauna, "Kema fa shareni kikayi Rouhi tunda mukaje nigeria ko neman yanda nake bakyayi gabaki ɗaya kin fita harkata gashi natashi ramawa wuni guda kin susucemin kiyi tunanin yanda naji a kwanakinnana anya bazaki daina zuwa nigeria ba kuwa?" na zaro ido, "Rufamin asiri masoyi wallh ba haka bane naga hankalinka gabaki ɗaya yanakan abunda yakaika canne banaso na takura maka amma idanna shareka nasa kaina a'ina" kawarda kansa gefe yayi yanason yimin sakalci na juyo da kansa ya kalleni zaiyi magana caraff na haɗe bakina da nasa. Saida Hammood yasan yau na shirya faranta masa dan ba ƙaramar gara ya ɗeba ba, tare muka shiga wankan a wajan wankan ma saida aka ƙara ruwa ɗaya. Washe gari kuwa sassafe na matsa masa cewa saiya kaini naga mahaifin Babanmu. Yakaini naga tarairaya a wajansu ya sake aure yanada yara guda biyu Abun mamaki suma murnar ganinmu suke, a ƙasar Hammood yabarni yatafi buga match ɗinsa zuwa lokacin gabaki ɗaya Visan su yazama ready. Baba Hajiya Alhaji Habibu Ya Ahamd da ƙanwar Baba ɗaya akazo dama ɗayar tarasu. A familynsu kamar wanda ake biki haka aka taru ashe family ne suke dashi masu yawa. Saboda gudun kokonto a azuciyar mutane Babansa kam shi ya yarda da Baba ɗansa ne a bugun farko, akaje akayi DNA test ya fito 99.9% su Baba basu daɗe acanba aka sake jaddada aurensa da Hajiya sannan suka koma harda itama." bayan angama wannan Hammood ya ɗaukeni muka koma gida.

Inada Ciki 3month amma ni bansan dashi ba shima Hammood baisan dashi ba ko yawu bantaɓa tofarwa da sunan ciki ba, Sai ƙirjina da suka ciko naɗauka yana tafiya da sahun ƙibar danayi, sai wata jaraba dagani har Hammood muka ƙara wanda shi kansa yana Mamakin abun, sai cin dabino kuma sosai ina zaune saina tashi da box guda dama tunda Abie ya fahimci inaso koda yaushe store ɗinmu a cike yake dashi, saida abunda yake cikina yafara motsi kafin nasan da zamansa ranar ihu na dinga yi gashi Hammood baya gida a tsorace ma'aikata suka kirashi ya dawo shima dana sanar masa ya masifar razama likita aka kira aka fara gwaje-gwaje harda scanning nan ya gano abunda yake cikin tun daga nan Hammood yadaina fita gabaki ɗaya kullum yananan yana kula dani kamar wata ƙwai. Shida kansa yakira Mum da Abie harda Baba ya sanar musu, kusan kullum daga gidansu Har namu cikin kira ake aji lafiyata data abunda yake cikina, Aysha ta haihu ta haifi mace aka saka mata sunan Mama. ana haka aka saka bikin Maryam da Yaya Habibu tunda aka sanar dani na ɗaura niyyar zuwa lokacin cikina yashiga 7month Sai da lokaci yayi Hammood Ya hanani zuwa kuka na dingayi amma ya ƙeƙeshe idanuwansa yace bani zuwa. Nayi fushi nadaina masa magana amma yanakan bakarsa na bani zuwa Ko zama yanda yake na daina ina kallonsa sai naji zuciya tana hantsiloni wani lokaci har zama nake nayi kuka tunda nake bantaɓa tunanin akwai ranarda Hammood zance masa ga abunda nakeso yace a'a ba, ban taɓa tunanin a irin sonda Hammood yakemin akwai lokacinda zaiso wani abu fiye dani tunma abun baizo duniya ba. shi dai ya zubamin idanuwa kawai nayi borina nagama ganin borina bayida lokacin ƙarewa, banida niyyar sauƙowa daga fushina yasa yaje Neman sulhu Ina zaune a ɗaki yashigo natashi zanbar wajan ya kamo Hannuna raina a ɓace ina kallon gefe sai hura hanci nake, ganin yanda nake hura hanci dakuma titsetsen cikina yasa shi yin dariya, gabaki ɗaya haushi ya cikani ina fushi shikuma yanamun dariya. A hankali ya jawoni zuwa cinyarsa bai damu da nauyin da nayi ba.

"Rouhi har me yayi zafi haka? Me yayi zafi da zakiyi fushi har haka da Hammood ɗinki? wannan hukuncin yayiwa Hammood tsauri dayawa Tsawon kwana uku ba kenan bakya kulani ko nayi miki magana shareni kike" na lula tunani wai dama 3days nayi ina fushi dashi? A tunanina nayi zaton nakai 1week ana abu ɗaya inaga ni nama fishi jin jiki da fushin tunda lokacin tsayi yayimin shikuwa harya riƙe kwanakin da nayi ina fushi dashi, "Rouhi ki yafeni amma bazan iya barinki kiyi tafiya ba bayan aiki tuƙuru danayi kafin samun cikin nan, bazanma iya barinki ki tafi ba inaso kamar yanda nafara rainon cikina na ƙare abina" yana fara bani haƙuri na sauƙo saboda ni kaina naji jiki. A ranar dana shiga hannunsa saida ya kusan tayarmun da haihuwar cikin wata bakwai dan wuni nayi da ciwon mara, dama tunda cikina yafara girma Hammood yake ɗagamun ƙafa bai cika kusantata ba sai sa'i-sa'i. Cikina yana wata takwas aka fara shirye-shiryen buga worldcup tare muka tafi dashi kwanamu 2 a can saiga Aysha da Hamma Maryam da Yaya Habibu ya Ahmad Hammood yaje biya yasamu yabiya nasa shida matarsa shiyasa zuwansu baiyi ɗaya ba. Suma bayan ƙwana 1suka iso gabaki ɗaya tunda aka fara worldcup ɗinnan cikin farin ciki nake daga na ƴan uwana kusa dani yaya Habibu da Maryam anashan soyayya kamar babu gobe kuma still soyayya suke da Nawrah duk da ta girme masa, zaga maryam suke yafice itama tafice suje hira saisu dawo daban-daban kamar kowanne da tafiyarsa, wannan karon Mum da Abie sukazo tare kallon match sai dai Ba hotel ɗaya muka sauƙa dasu ba. Ana gobe za'a fara match Hammood yace nafaɗa masa abunda zan bashi wannan karon idan yaci cup kamar wancan karon nace masa duk wani abunda yakeso. Aka fara match cikin sa'a har aka kai final. Baifi saura 1hour afara buga final ba naƙuda ta tasomun banfi 30minute ba gabaki ɗaya da haihuwa da naƙudar kuma ban wani wahala ba na haifo yarinyata kyakkyar gaske itaba bahaushiya ba itakuma ba balarabiya ba ana ganinta anga ruwa biyu dagani harshi tafimu kyau, Hammood saida yaje asibitin yaganni nida Baby ya tabbatar muna lafiya kafin ya nufi filin buga match a faɗinsa nabashi kyauta tun kafinma yaci cup ɗin zaiyi iya bakin ƙoƙarinsa yaci cup. Cikeda sa'a da nasara suga buga wasa bai wani tsaya celebration ba yataho asibiti suma sauran duka asibitin suka nufo ko'ina acike yake wani Babban ɗaki aka sakani mai haɗeda kujeru da komai ciki da palour duk a asibitin. Gabaki ɗaya ƴan uwana danasa suna cikin ɗakin kowanne fuska ɗauke da fara'a ana ganinsu za'a fahimci suna cikin farin ciki, Hammood shima yashugo ciki kai tsaye wajena yawuto saida yasake tabbatarwa lafiyata ƙalau yayimin peck a gefen lips ɗina yayi wajan abie ya amshi babyn. Bakinsa kamar gonar auduga fara'a kawai yake. Tako'ina sumbatar yarinyar yake ina binsu da kallo cikeda sha'awa. Saida na ƙwana asibitin kafin aka sallemu da Hammood muka kwana duk da babu masu zaman jinya amma bazai iya kwana a wani wjaanba. Bayan kammala komai a garin kai tsaye kuwait muka wuce ƴan uwan Baba sunata zuwa kallon Baby, kusan kaff gidanmu aka taho suna harda Ummi Mama daƙayr tazo sai dai bata yarda tazauna agidansu Hammood ba dayawansu Ma gidansu Baban babanmu suka sauƙa sai dai abie ya nuna rashin jin daɗinsa yana ganin barema wanda bai sansu ba bai taɓa ganinsu ba yabasu muhalli a cikin duniyar gidansa bare ƴan uwana wanda yanzu suma suna masa matsayin ƴan uwa tunda jini yahaɗa.

Babu yanda banyi Hammood yabarni na tafi da ƴan uwana ba amma yaƙi. Su Mummy kanma ganin irin kulawarda ake bani yasa basuyi maganar tafiya ba. Har Mum ɗinsa yanzu sona take tunda taji nice dalilin dawowarta rayuwa cikin yaranta."

Hutu Hammood yaɗauka yadawo gida gabaki ɗaya yana kula damu tunda nake bantaɓa ganin soyayya irin wacce Hammood ke yiwa yarinyar dana haifa ba. Bayan 5month da haihuwata Hammood yafara zancen na sake samun ciki shareshi nayi kamar banji yayi zancen ba baisan nikanma planning nake namu na gargajiya yanda bazai gane ba. Saida yarinyarshi tayi 6month kafin yabarni naje gida Baba yasake sabob gini ƙatoton gida kai girman gaske kowa da shashinsa kuma komai equal yayi musu ya ɗaukawa kowacce mai aikin da zata dinga yimata hidima ya ginawa hajiyarsa ma shashinta wanda yafi na kowacce mace girma tunda mahaifin Baba yana zuwa lokaci-lokaci. Sai a wannan zuwan nawa Baba yabani sadakina ƙin amsa nayi nace mishi nabar masa ya fara business dashi, shawara suka zauna sukayi da Yaya Ahmad akan business ɗin da zasu fara dake zuwana naje musu da morethan 20 cartons na dabinon campanyn Abie nabawa Baba shawara adinga shigo masa dashi ya buɗe ƙaton store ana jibgesu da ƙananun shaguna na sayarwa hakan akayi kafin lokacin tafiyata yayi an tsara komai yazama shine Distributor na ƙasa baki ɗaya, sannan Baba suka haɗa business da mahaifinsa yana aiko masa kayyyaki daga wajansa suma aka buɗe musu shaguna manya-manya. 2weeks Hammood ya ishemu da ƙulafuci nadawo."
Chapter 105 · 0% Book details