← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 106

Sashe 73

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baba wallh ba laifin marmeeyy bane. Marmeeyy nazaune da kowa zuciya ɗaya ƴan uwanta duk so ɗaya take musu kuma bata ƙullatar kowa a cikinmu Baba tun kafin ka aurawa Aysha Hamma take sonsa dukda tasan cewa Hamma saurayin Marmeeyy ne danni nagani da idona hawa kafat sata zumunta takeyi tana ɗauko pictures ɗinsa. Kuma naan Marmeeyy ta fahinci hakan amma bata taɓa nuna mata tasani ba. Akazo aka juya aurenta kan Hamma wallh Baba naje na samu marmeeyy akan mu sameka mu roƙeka taƙi kuma tayi hakanne danta fahimci aysha tana sonsa tun alokacin tabar mata shi ko bata faɗa ba actions ɗinta ya nuna tunda taƙi taɓuka komai da zaisa su kasance tare da Hamma. tunda aka saka auren Hamma da Aysha marmeeyy tadawo abun dariya da zolaya a idon Aysha da ƙawayenta har habaici suke yaɓa mata duk da Mummy tayi musu faɗa tun a abuja wannan dalilin ya ƙarawa Marmeeyy damuwa aranta sannan kuma tadaina zaman cikin mutane dan idan Aysha tanana saita yaɓa mata magana. Duk wani abubda yafaru abaya wanda Baba ya kamata yasani saida fadeela tafaɗa sannan ta ɗaura. Ko yanzu Baba Marmeeyy batayi niyyar kulata ba amma cin fuskar yayi yawa idan bata tanka mata abun zaiyi tsamari cewa take wai boka yasa Hammood ya auri Marmeeyy. Toh yanzu dan Allah Baba idan bata faɗa nata baƙa itama ko sau ɗaya ba ina zataji daɗi aranta? Wallh marmaeeyy nada zuciya mai kyau ita dai Aysha da tasawa ranta jin ɗacin Marmeeyy babu gaira babu dalili wai Mummu tafison Marmeeyy akanmu kuma Mummy ita kanta tafaɗa yanda Marmeeyy ta ɗauketa mu data haifa ba haka muka ɗauketa ba. Kulawarda Marmeeyy tabata bamu bata ba. Ni bawai kare Marmeeyy nakeyi ba Baba ban kuma ce wai yanzu sam batason Hamma ba amma tun a baya batasan tanada Hammood ba ta ɗauki ɗamarar cireshi aranta bare yanzu data san Hammood tun ana ajiyewa ta ajiye Hamma wallh Baba ka ɗauki mataki kan aysha dan bataji sam zata raba maka gida". Kaf cikin wajan shieu akayi ana sauraron Anty fadeelah bayan tagama Baba yayi salati kawai yana jinjina girman zancen a ƙwaƙwalwarsa haka tana faruwa agidansa amma babu wanda ya sanr dashi?.

Yayi musu faɗa sosai wanda ko wannensu saida yaji tsoro dan bai taɓa irin hakan ba sannan ya dawo nasiha jikinsu sanyi matuƙa. Sannan yabawa kowannenesu haƙuri yace karya sake ji ko wani abun makamancin haka yasake faruwa Anty fadeela tazo ta faɗa masa zai ɗauki mataki. Aysha tunda take a rayuwarta bata taɓajin anyi mata shari'a nai adalci ba irin na yau dan Baba bai goyi bayan kowacce ba kuma yayiwa kowwcce faɗa dai-dai da lafinsa sannan yace kuma shi yaransa gabaki ɗaya yana sonsu babu wanda yace yafiso aciki sannan yace idan kuna tunanin anfi nunawa wasu kulawa a cikinsu ku kasance kamar yanda wancan yake ta iya yiwuwa sai anfi nuna muku kulawa akan wanda kuke tunani sannan yace su iyaye tsere ake a yayin kyautata musu bawai nuna fushi akan wanda ya kyautata ba. Kaff babu wanda jikinsa baiyi sanyi a cikinsu ba har iyayensu mata maganganun Baba sun ratsa su sannan ya roƙesu suyi zaman lafiya. Yakuma soke maganar zuwan Marmeeyy gidan Aysha dan jiya yafara tunanin barinta tatafi amma yau magana tatashi."

Su duka suka fita Zuwa ɗakinsu mukuma mukaje muka ƙarasa aikin abinci. Bayan mungama su Anty zasu shiga kasuwa na bisu.

Saida nafara checking balance a bankin dake kusada kasuwar Zeros É—inne ban ganeba na cire kawai dan bazan tsaya irgawa ba muka shiga kasuwa kuÉ—inda Baba ya bada nace Anty ta ajiye muyi amfani da na hannuna. Wajan mai shimkafa mukaje zai auna mana nace.

"Anty tsaya kiga muyi amfani da wannan akwai kuɗi dayawa a ciki bansan ko nawa bane karmu auni shinkafar kawai mu sayai buhu" amincewa kawai anty tayi mukace abamu thailand buhu guda na miƙa masa Atm ya cire nace dubamin balance yaduba.

"Nawane aciki?

"Wallh hajiya toh dai ga kuɗin naki nan Bansan nawa bane ya kama ciki dan bantaɓa cin karo da zerorin kamar haka ba. Na kalleshi da alamu bawani dogon karatu yayi ba naɗauka ƴan kasuwa ai lissafinsu akai yake. nima danayi karatun ban tsaya lissafa zeron ba bare shi.

"Toh wama yadamu da zeron? Cire kuɗin buhu biyar nafaɗi" Anty ta kalleni ke Marmeeyy har buhu biyar?" shikuwa bai tsaya wata-wata ba ya danna kuɗin biyar ya miƙomin na amsa zansaka pin alokacinda nake hawa Anty amsa

"Anty ai shinkafa bata ɓaci idan takama goma saimu saya goman ma" Mai shagon ya washe baki.

"aikuwa kinga idan gomanne me zaifi a lissafe tubda kinga ko zero ta biyar bata motsa ba"

"Toh saka goman amma karka lissfa saimun haɗa da sauran kayayyaki" anty ta hanani haka naƙi haka kawai ina kallon mahaifina yana aunar abinci sa'i-s'i ace nasamu halin da zan hanashi auna ban hanashi ba. Komai dana tashi saya a na hauka na saya har gishiri muka gama lissafi ya cire kuɗinsa yabamu reciept da zummar zasu aika mana gida da kayan a abbar mota dan motar da mukazo da ita bazata ɗeba ba tun kafin mubar wajan mukaji kai shago yafice yaja bawa maƙwanta labari yana nunoni. Muka wuce wajan wasu abubun duk abunda na saya saida na sayawa maryam da Anty fadeelah sai ɗai-ɗaiku da baza'a rasa ba. Anty ma taɗauki abunda takeso muka gama muka fito Yaya habibu yaja muka koma gida.

Ina shiga na cirewa Anty Fadeelah nata na bar nawa dana maryam. Mama tayita yimin faÉ—a akan kashe kuÉ—in danayi tana faÉ—in.

"Dan shirme daga yabaki ATM saiki kama ki kashe kuÉ—in ciki marmeeyy babu ko dan kawaici idan yaga kuÉ—inda kike kashewa fa?"

"Bazai gani ba Mama komai da layina ya saitashi" kuma dagasken bazia gani É—inba domin komai da nata ya saida babu abunda zai shugo wayarsa.

"Dukda haka Marmeeyy wannan sayayyar tayi yawa"

"Hmm ai bakiga komai ba sai kayanda tayi sayyaya ya iso"

"Bayan wannan akwai wasu kayan kenan?"

"Suna hanya dan tun kafin mu taso anfara É—aurasu a mota"

"Allah yakyauta" kawai Mama tace

Sai bayan kusan 2hours lokacin ana kiran la'asar kafin kayan ya iso. Mama batace komai ba amma abun yabata mamaki sai dai bazatace nayi laifi ba tunda mahaifina na taimaka.

Aysha takira Hamma akan yazo sutafi amma marmeeyy bazata jeba. Data tambayi dalili tace sai yazo zata faɗa masa. Muna zaune mukaji shigowar Maryam tacewa Aysha ta shirya yana ƙofar gida su tafi. bayan aysha tashiga ɗauko kayanta maryam ta dubeni.

"Babe kinsan wai mutumin zuwa yayi wajan Abba ai abasu ni su tafi dani? Sai kace wata Æ´ar tsana wallh nima gara Yaya habib yafito muyi aurenan muhuta bayan muntafi ki faÉ—awa Mama dan Allah.

"Kafin kitafi zan faÉ—a mata dai maras kunya"

"No dan Allah ki rufamin asiri ki bari saina tafi" naja tsaki nayi ɗaki kayanda na siya mana na ɗebo nata a bags guda biyu na miƙa mata.

"Menene wannan?"

"Idan kikaje kika buÉ—e zamuyi waya amma yanzu kije suna jiranki" amsa tayi tamusu sallama suka tafi. Tana shiga Hamma ya nuna mata É—akin da zata zauna tashiga ta ajiye kayanta. Aysha taso su zauna É—aki É—aya da ita.

Anan tafara duba kayayyakin dana bata. Kayan sunyi mata kyau sosai tana gama buÉ—ewa ta kirani.

Na ɗauka muna magana kenan Hamma yashigo fahintar cewa dani take waya ya sanyashi ƙarɓan wayan ya kara a kunne."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab  m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance  zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Bai bata damar da zata faɗamin ya amshi wayar ba ya karɓe yakara a kunnensa. nikuma a lokacin magana kawai nake banjira amsarta ba.

"Mama ai tanata faɗa wai naje na kashe kuɗi kumafa shi bayani yace nayi amfani dashi duk abunda zanyi nayi dashi komai nakeso karna tambayi Baba kinga ai dama yanzu duk wani hakkina yana wuyansa Kuma Baba yana buƙatar hutu" harna ƙarashe magana nayi shiru batace komai ba. Shikuma yatsaya yana auna maganata a ma'auni yana nazarori akan maganata.

"Babe kina jina?"

"Bata jinki Da Abubakar kike magana. karki kashemin waya ki tsaya muyi magana" YafaÉ—a bayan ya tabbatar zan iya kashewa É—in. gabana yafaÉ—i damm jin muryar Hamma mai zaiyimin daya amshi wayar? Wai meyasa Hamma baya kaucewa abubuwanda zasu jawo hatsaniya a tsakani? Mai yasa yakeyin wasu abubuwan da zasu shiga tsakanina da Æ´ar uwata?.

"Marmeeyy waye shi wannan da kika magana akansa?" batareda wata tsoro ba nabashi Amsa.

"Hammood ne?"

"Menene haÉ—inki da Hammood?" bansan dalilin dayaaa yake yimin tambayoyi ba dan dai nasan babu abunda zasu amfaneshi dashi amma yazama dole na tsaya nayi masa bayani dan naga alama Aysha bata sanar dashi komai gameda aurena ba, toh ko tanajin kunya tace masa Hammood ne mijina?"

"Mijinane shine dalilin fasa aurena dakai a yanda aka faÉ—amin an daÉ—e da É—aura aurena dashi a lokacin da akazo neman aurena Baba yayi musu bayani shine suka nemi a maida auren akan Aysha. Kuma Aysha Æ´ar uwata ce duk wani dalili da zaisa ka soni Aysha tana dasu" ban kaiga gama maganataba ya katseni.

"Kina sonsa kenan?"

"Eh" nabashi amsa kai tsaye" saida yaji zufa sun keto masa dan baiyi tunanin zan iya faÉ—awa soyayya lokaci guda haka bayan rabuwata dashi ba.

"Marmeeyy kai tsaye kika amsamin kina son wani namiji baniba bakisan hakan zai cutar dani ba?" dama duk soyayyar da mukayi ƙaryace kenan tunda har zaki iya faɗawa soyayya a ƙaramin lokaci bayan rabuwata dake." na girgiza kai kamar wanda yake kallona.
Chapter 73 · 0% Book details