Sashe 43
Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wannan ita kaɗai tasani tunda ga yanda all'amari ya kasance" mood ya ɓata rai sosai ya buga table ɗin dake gabansa yace.
"Duk kasanda haka mai yasa baka sanarda niba kabari naje mata ahaka?" P.A ya kunshe dariyarsa kawai dan yaga yanda Mood yabi duk ya kiÉ—ime kamar wanda yayi wani abun ba dai-dai ba.
"yanzu yaya za'ayi?"
"Yanda za'ayi shine gaba ka gyara karka ƙara zuwa mata ba'a Hammood ɗinda tasani ba be confident karka tsorata ka zama namiji itafa yanzu matarka ce kanada kowacce irin halastacciyar dama akanta. Kaje mata a matsayinka inada tabbacin zata amsheka, ita soyayya ba'a haka akeyinta ba, mace ba'a zuwa mata ahaka. Inada yaƙinin soyayyar da take maka matsayinka na celebrity datake so zaisa tasoka a matsayin miji bazaka taɓa samun soyayyarta ahaka ba zata ɗaukeka matsayin wanda ka takurawa rayuwarta kabarta na wani lokaci kafin ka dawo mata a matsayinka na Hammood ba'a matsayin ɓoyeyyen masoyi ba. Mood yayi shieru yana nazarin maganganun P.A tabbas abunda yafaɗa gaskiyane sai yanzu yake ganin wautarsa kuma ga dukkan alamu ta tsorata sai dai ya lura tanada ƙarfin zuciya dahar ta iya tsayawa ta saurareshi tayi ƙarfin halin tsayawa tayi masa tambayoyi akansa lumshe idanuwa yayi yanajin muryarta a kunnuwansa mai daɗi data sake sauƙar masa da nutsuwa yanajin sonta yana ƙaruwa acikin zuciyarsa komai nata yana burgeshi dai-dai da sauƙar numfashinta, yana tuno lokacin da ya rufe mata baki alokacin dataso yimasa ihu alokacin yashiga yanayinda tunda yake bai taɓa tsintar kansa a makamancin yanayi kamar wannan ba. Wannan lokaci ya tsaya masa arai yaƙi tafiya sai sake zuwa yakeyi a idanuwansa kamar a lokacin abun yafaru har P.A yagama magana ya tsaya yana kallonsa baisanma yagama ba gaanin haka ya sanya ya tashi yafice saboda yasan halin Mood fiyeda kowa.
Muna komawa gida bamu jira kowacce a cikinsu ba muka shiga domin kwanciya. Tun lokacinda ya manna jikinsa da nawa nakejin ƙamshin turarensa ya baibaiye gabaki ɗaya jikina dan haka ina zuwa wanka nashiga na daɗe a toilet ina dirza gabaki ɗaya illahirin jikina danji nakeyi gabaki ɗaya ƙamshin ya gama kamani tako ina amma ƙamshin bai fitaba haka na haƙura nafito.
Ina fitowa nasamu Maryam tana zaune tana jirana ganin nafito itama tashige bayan tagama tafito tashirya tazo ta kwanta sannan take cewa.
"babe Naji ƙamshin turare mai daɗi a jikinki ko toilet da kikayi wanka saida naji ƙamshin yanzu haka inajin ƙamshin wani irin masifaffen ƙamshine mai sauƙarda nutsuwa da kasala a lokaci ɗaya a'ina kima samu wannan turaren?" na dibirbirce nakasa cewa komai tacigaba da faɗin.
"Tun muna Hall nakejin ƙamshin banyi zaton a jikinki bane sai bayan nadawo daga wajan Yaya habeeb nakejin ƙamshin a jikinki a'ina kika samu wannan turaren?" nayi mata banza kamar banjita dan banda amsar bata saida tasake magana nace mata.
"Keh nima bansaniba Ya Ahmad ya aikeni motarsa na ɗauko masa aika sai... Sai maganar ta ƙaƙaremin nakasa ƙarasawa bansan wani irin kallo zatayimin babidan nace mata mutuminda bansanshi bane ya haɗa jikina danasa anan nasamu wannan ƙamshin Ajiyar zuciya nasauƙe.
"May be abokin yaya Ahmad ke amfani dashi amma gaskiya turaren yahaɗu" ahakan kawai nabita saboda inaso maganar da ƙare ahaka amma abun ya tsayamin arai sam yaƙi barina nasamu sukuni ganin haka ya sanya na ɗaga waya nakira Hamma Bugu biyu ya ɗauka kamar wanda yake jiran kirannawa yana amsawa nace.
"Amincin Allah ya tabbata agareka Hammana" daga cikin wayar naji sautin murmushinsa mai É—auke da farin ciki.
"Amin babyn Hamma yau Hammanaki harya cire rai dajin muryar babynsa gani ina kwance amma bacci yaƙi ɗaukana"
"Hamma nima ai kasan bazan iya baccinba koda na kwanta shiyasa nakiraka dukda dare yayi kuma ina tunanin kayi bacci"
"Bazan iya bacci ba baby. Kwana biyu da bakya É—aukan wayata bana iya bacci nashiga wani hali please bby karki sake yimin horo da rashin jin muryarki"
"In sha Allahu bazan sakeba Hammana kayi haƙuri" haka muka daɗe muna hira sannan mukayi sallama lokacin Maryam harta daɗe dayin bacci. Nima ban ɗauki wani lokaci ba na ƙwanta baccin zuciya cikeda soyayyar Hamma."
Asubahi jirginsu Mood yabar ƙasar zuwa Abu-dhabi
Ji yayi kamar yazauna yasake kwanaki ko zai samu yasake kallonta yasamu kansa a yanyinda yasamu a jiya da daddare tun baibar ƙasar ba yake missing ɗinta irin abunda yakeji akanta bai taɓajin makamancinsa ba. Wani lokacin yakan zauna yana tunani har indai haka kowane masoya sukeji akan abunda sukeso wasunsuma suzo basu samu soyayyar ba abun tausayawane shi kansa yanzu daya mallaki abunda yakeso yanajin fargaba taradadi da faɗuwar gbaa.
Bayan muntashi munyi sallar asubahi muka koma saida muka kai 10:00am bamu tashi ba saboda wajanmu babu hayaniya sau 2 mummy tana zuwa dubamu ko munfarka."
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Baba tunda yakoma gida bai sanrda su Mama yabda sukayi da Mummy ba yafiso sai sun tsayarda magana dan har lokacin Mummy bata sanr dashi lokacin dawowarta ba. Yasan halinta sarai da iya canja ra'ayi dukda wannan karon bayaji zata canja ra'ayi dan yaga danasani da tsananin son ta koma ɗakinta a tattare da ita tacire duk wani girman kai jijjida kai isa da gadara ta tsaya sunyi Sulhu su fahimci junansu yaga abunda bai taɓa kallo ba atattare da ita yana saka ran ta canja kenan yana fata kar wani abun yataso abaya. Shi ba wannan bane yafi damunsa kamar yanda akayi auren Ɗiyar Mama (Marmeeyy) batareda sanintabba yana ganin kamar baiyiwa baiwar Allah mai hakuri da kawaici adalci ba . Kawai dan mahaifinta shine wanda ya ƙarfafa akan kada ya sanarda ita harya samu gwarin guiwa amma zuciyarsa takasa nutsuwa yasan idantaji koda daga baya zata fahinceshi tayi kasa uzuri kamar yanda tasaba amma bayaso taji babu daɗi aranta yasan babu wata mace da zataso ace an aurarda ɗiyarta batareda saninta ba dukda kuwa burin kowacce mace shine ta aurarda ɗiyarta. Zaibi umarnin mahaifinta tunda shima mahaifi yake a wajansa bazai sanarda itaba har lokacinda ya kamata tasani Amma har zuwa lokacin zuciyarsa zata kasance cikin rashin daɗi."
Saida Muka tashi muka shirya sannan muka nufi palour. Mummy na zaune da su anty fadeelah muka shiga muka gaidata ta amsa cikeda farin ciki tana faÉ—in.
"Marmeeyy antashi kenan nashiga dubaku keda maryam gabaki ɗaya kuna bacci kutashi kuje kuyi breaskfast gashican an anshirya" muka miƙe muka nufi wajan breakfast muna gamawa muka dawo. Aysha tasha murr bansan mena mataba tun jiya nake ganin tana shamin ƙamshi nima na ɗebeta na watsar. wunin ranar haka nayishi hankalin nakan wayata gashi banda Maryam babu wanda yasanda zancen ɓatar wayar dan itama cemata kawai nayi ta ɓata amma jikina yana bani shine ya ɗauki wayar dan kaf cikin wajannan babu wanda wayar zatayi masa wani abun.
Da Yamma akayi buÉ—ar kan Yaya Ahamd da amaryarsa a harabar tsakar gidan sunyi kyau sosai bayan isha'i kuma za'ayi suya night(barbecue) tun Da yamma aka fara shirye-shirye mukuma bayan isha'i muka shirya cikin Abaya tawa data maryam iri É—aya Babu makeup a fuskarmu amma munyi kyau.
Bbu wani african time 8. Aka fita wajan babu masu kida zallan photographers ne sai ƴan uwa da abokan arziki anata hira ana raha anajin daɗi an zazzauna da gashashun raguna a banƙare duk da sauran kayan marmari da drinks serve your self duk wani abunda kake buƙata dakanka zakaje kaɗauka. Harsu Mummh sunfita wajan yayinda akayi hira dasu da da sauran Ƴan uwa nikam naja gefe ina waya da Hamma sai sani nishaɗi yakeyi ana cikin event Ya Ahmad leƙa yaga baiganniba tun jiya yakeso ya fahinci abunda yafaru bayan fitata amma naƙi bada ƙofa yanzu haka rashin ganina sai yakeji kamar gameda abunda yafaru jiyane yasa banzauna cikin mutane ba dan haka yatashi yafara nemana nikam baisan Hammana harya gogemin duk wani abinda yafaru a kwakwalwata da soyayyarsa banyi auneba naji zamam mutum a gefena dasauri na ɗauke wayar a kunnema shikuma baima lurada wayarda nakeyi na datse wayar haɗeda ajiyeta a gefena, na sakar masa murmushi haɗeda faɗin.
"Yaya angama kataho nan?" ya girgiza kai sannan yace.
"A'a naduba kine naga banganki ba akwai wata matsalace gabaki É—aya yau naganki wani daban" naÉ—anyi murmushi sannan nace.
"Subhanallahi Yaushe faruwar hakan kenan?"
"Jiya da dare wajan diner"
"Karki damu zan saya miki badai waya ba?" Na jijjaga kai sannan nace.
"Nagode yaya Allah yasaka da alkhairi" Amin ya amsa.
"muje ciki koh?" Yafaɗa yana ƙoƙarin tashi nace.
"Uhmm Yaya" na'am yafaÉ—i sannan yakoma yazauna yana saurarena dan yaga alamun magana zanyi. Abunda ya daÉ—e yana damuna wanda kullum nake burin sani yau zan daure na tambayeshi.
"Yaya menene atsakaninka da Anty naga gabaki ɗaya ka tsaneta ko gaisuwarta baka amsawa wanda kuma a zahiri ba haka kake ba kai mutumne mai sauƙin kai da saurin fahimta, wannan tsanarda kayi mata yawuge ace kawai dan Baba ya aureta kodan ta dalilinta Mummy da Baba sun samu matsala jikina yana bani akwai wani abun aƙasa koda Baba yabani labarin abunda yafaru a gidanmu nayita neman dalilin tsanar acikin labarin na rasa" murmushi yayi yafara magana.
"Marmeeyy meyasa bakya jin tsorin ciro maganane bakyajin shakkan tambaya kowace irice" Na ƙyaɓe fuska sannan nace.
"Yaya duk wani abunda yake faruwa a gidanmu nakeso naga yadaina komainya gyaru"
"Kin ɗauki hanya Habiba budurwatace" yafaɗa kai tsaye na tsaro ido haɗe dayin fiƙi-fiƙi na kalleshi amma babu alamun wasa bansan dariya ta kwacemin ba saida nayi mai isata shima ganin bazan tsayaba yasa ya tayani har muka tsagaita saida muka gama dariyar kuma sai yace.
"wato ke dariya ma nabaki marmeyy dagaske nake Habiba budurwa tace" nasake darawa ni tunda nakema ban taɓaji yakira sunan anty ba sai yau.