← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 106

Sashe 77

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sun tafi already mun iso you were sleeping akwai zazzaɓi a jikinki naga kaman kinajin daɗin baccin shiyasa nasa suka fara gaba idan kintashi saimu tafi tare" Na kalleshi da mamaki kawai dan ina bacci shine bazai tayar dani ba? ni banmasan cewa tare muke tafe dashi ba dan 2days kenan banji daga fareshi ba ashe shi tun asuba ya wuce abuja yasauƙa a masauƙinsa sannan bayan isha'i yatafi filim jirgi shahsin daya zauna da muƙarrabansa sabanne yasa bamusan yana ciki ba. Ina ƙoƙarin miƙewa yace.

"Idan baki warware ba zaki iya baccin kawai ko kaɗanne ki ƙara na girgiza kai danni yanzu zanfi ganewa na ganni wajan Mummy. Tallafeni yayi a jikinsa muka sauƙo motoci suna jiranmu ya buɗe mota ya shigar dani a hankali sannan shima ya shiga ta wani gate daban mukabi na filin jirgin batraeda mun fito cikin mutane ba da dukkan alamu cincirindom mutane suna jiran sauƙowarsa shikuma bayason hakan hankalinsa gabaki ɗaya yana gareni gani yake duk ƙarancin hayaniya zata takuramin ne. Tafiya mai tsayi ce takaimu gidan da jami'an tsaro a zagaye da ko'ina. Ni dake a kwance nake idona suna lunshe ban lura da mutanen da suke jiran isowarsa ba ciki harda ƴan jaridu muna shiga aka rufe gate babu wanda zai iya hango cikin gidan. Nanma taimakamin yayi muka shiga har ciki yanayin tsaruwar gidan dakuma zazzaɓin dake jikina sai tasa naga kamar mafarki nakeyi. Kai tsaye ɗaki yawuce dani na ƙwanta ya zauna yana kallona nikuma bacci nema yake ƙoƙarin ƙara ɗaukata. Cikin barci naji yana bani hakuri dan yana ganin shine yayimin causing ciwon nan dayasan halinda zan shiga kenan daya danni zuciyarsa ya ƙaramin lokaci.

A lokacin yakira waya yace akawo su Mummy ɗakina dan yasan idan na farka zanji daɗi naganni kusa dasu. Yana ciki riƙe da hannuna suka shigo dake dama sun rigada sun gaisa yayi musu bayanin likita zaizo dubani sannan ya sunkuyarda kansa a gaban Mummy yayimin peck a goshi duk ina bacci bansan abunda yake faruwa ba.

Mummy bata damuwa ba dan tasan al'adarsu ce hakan bazaiji komai ba ko agaban mahaifinsa ko mahaifiyarsa zaiyi hakan. anty fadeela ce ta kalli gefe dan abun yabata kunya.

Bai daɗe da fita ba likita yazo dubani bayan ya dudduba ko magani bai bani ba yace zazzaɓin zai sauƙa saida yabi can yayi masa bayani dan yana cikin damuwa sannan yatafi da zumnar zai shugo nanda 2hours yasake dubawa ko zazzaɓin yasauƙa.

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Bai kai 2hours da tafiya ba nafarka zazzaɓin ya sauƙa zafin jikinma ba sosai ba mummy ta tashiga toilet ta haɗamin ruwan wanka mai zafi bath-mist tagani kala-kala cikin toile ɗin duk na mata da kayan wanka kala-kala wanda ga dukkan alamu dan wacce zatayi amfani da ɗakin aka haɗasu tayi amfani da bathmist data gani a cikin toilet ɗin wajan haɗa ruwan wankan dake nata wanda ta haɗomun daga can ba'a buɗe kayanba tukunna. Nan da nan banɗakin ya ɗauki ƙamshi bayan ta haɗa tafito tace nashiga nayi wanka. Namiƙe jikina babu ƙwari na nufi toilet ɗin tunda nashiga ƙamshin ya daki hancina irin ƙamshin turarensa ne sakk sai dai wnnan ƙamshin yafi wancan sanyi ma'ana wancan yayi ƙarfi sosai ba kamar wannan ba da dukkan alamu wanda yake amfani dashi anyishi ne dan maza wannan kuma na mata. ƙare toilet ɗin nake da kallo Nakeyi da badan Mummyn ba bansan yaya za'ayi na iya amfani da abubuwan cikin toilet ɗinba. Gabaki ɗaya na cire kayan jikina na shiga cikin ruwan na ƙwanta lumshe idanuwa na nayi dan naji daɗin ruwan sosai na daɗe ahaka a ciki amma zafin ruwan bai sauƙa ba ga dukkan alamu ta saita ruwan a dai-dai temperature ɗinne bazaiyi ƙasa ba kuma bazaiyi sama ba. Daɗin ruwan ya lulani tunanin dangina ina tunaninsu hawaye yanabin fuskata saida Mummy tayi knocking ganin na daɗe sannan natashi nayi amfani da Showergel dake wajan nayi wanka towel na ɗauka cikin jerinsu na ɗaura sannan nafito Sai alokacin na ƙarewa ɗakin kallo komai na ɗakin farine sall hatta da funitures babu sirkin kala ya tsaru sosai Gaban dressing mirror kuwa mayuka ne da turaruka acike rinkiss kala-kala amma gabaki ɗaya brand ɗinsu ɗaya. Mummy tace na ƙarasa na shafa mai babu nusu na ƙarasa wajan danni kaina wajan ya burgeni inataso na ƙarasa nazauna narasa wanne man zan shafa daƙyar na iya cankan wani na shafa sannan na taso Babu kayanda zan saka a ɗakin gabaki ɗaya kayanmu har yanzu ba'a buɗe suba bamusanma yanda yake ba gabaki ɗaya gashi babu wani alamun closet a ɗakin bare muyi tunanin akwai kaya a ciki. Gadon na koma na ƙwanta dake inajin sanyi kaɗan-kaɗan nashige cikin bargo. Mummy ce tafice bata daɗe ba sai gashi tadawo da wata ma'aikaciya balarabiya ce da uniform na aiki a jikknta doguwar rigace bata ƙarasa guiwa ba sannan kanta babu ɗankwali ta ɗaure gashin kanta a baya. wangalau nabita da kallo yanzu haka suke yawo a cikin gidan? Kuma shi Hammood ɗin yana kallonsu? Naja ɗan ƙaramin tsaki da babu wanda ya jini na koma na ƙwanta. Jikin wajan da muke tunani wall ne na ɗakin ta ƙarasa ta ɗauki remote dake ajiye a bedside drawer ta danna tashi ɗaya wall ɗin yabuɗe tun daga farkonsa har ƙarshensa ƙofar takoma tashige jikin wall ɗin gefe da gefe. Kamar wani ɗaki haka wajan yake dan girmashi yakai ɗaki guda Tun daga kan inners zuwa kayan bacci da kayan sawa jaka da takalma komai da Anyi amfani dashi akwai a cikin wajan. cikin girmamawa tayi mana sallama ta fice. Nida Anty fadeelah muka buɗe baki muna kallon ikon Allah wato a duniya idan baka mutu ba zaksha kallo. Wajan da muka ɗauka wall ne na ɗaki sai gashi a tangamemenn closet ne. Anty fadeelah tace.

"Mummy dan Allah É—auki remote ki sake rufewa ki buÉ—e zanyi video ne. Mummy tayi murmushi. Na taso daga zaunen da nake.

" Yawwa Anty fadeelah kiyi mana shooting dan Allah" Wani murmushin Mummy tasake yi.

"Ayi shooting kiyi me dashi Marmeeyy? Keda ɗakinki da kullum zaki kasance a cikinsa har sai kin gaji da kallonta, bar fadeelan dai tayi tunda bata gajiya tunda muka shigo gidannan aikin kenan" sai alokacin na tuna cewa nifa yanzu nadawo rayuwa anan kenan jikina yayi sanyi na koma Na ƙwanta nayi laƙwas.
mummy ta ƙarasa wajan da kanta ta ciremin kayan da zan saka doguwar riga ce ƴar yaloluwa sai ƙananun kaya na ciki.

"Tashi ki kirya Marmeeyy tunda naga zazzaɓin ya sakeki ki samu kici wani abun. Ta miƙomin Kayan saida na ƙarewa rigar kallo sannan na sheqe da dariya.

"Menene kuma abun dariyar"

"Mummy Kiga rigar fa kanar wata yaÉ—i gabaki É—aya kama jiki zatayi"

"Ke bansan aikin ƙauyanci Meye acikin wannan rigar da zakice bazaki saka ba" na turo baki.

"Allah Mummy ni wannan rigar tayi wani iri ki canjamin wata"

"Au Marmeeyy haka zamuyi dake? Toh aikwa zan koma gobennan zan juya har fadeela da Habibu zan É—auka mutafi saimu barki ke kaÉ—ai" na girgiza kai dasauri.

" A'a Mummy zan saka"

"Yawwa toh maza amsa kisa kiyi sauri dannasan yanzu Dr zaiso duba jikinki nasaka kamar yanda nake tunani duk yanda na motsa sai jikina ya kaÉ—a.

"Yawwa kinga ai tayi koh? Duk kayanda kika gani cikin nan kar kiji komai ki saka kayanki Bakiga Æ´an aikinki na yawo da riga iya cinya bane?"

"Ƴan aikina kuma Mummy?" nafaɗa ina juya maganar tata.

"Eh ko nawa ne?" na girgiza kai nakoma na ƙwanta ko gama lulluɓa banyi ba mukaji sallamar Hammood muka amsa sallamar amma ni ciki-ciki na amsa yanda bazai jiyoni ya ya shigo idanuwansa suna kaina nima shi nake kallo ya sakarmun murmushi daga yanda yake banyi komai ba kallonsa kawai nake ya juya yabawa likitan izinin shigowa yazo yayi ƴan dube-dube yace zazzaɓin yasauƙa shikenan tare suka fita bai daɗe ba yadawo. Ganin yadawo yasa su Mummy suka fita suka bamu waje. Ya ƙaraso gadon dai-dai yanda nake ya zauna Saida yasa hannu yaji zafin jikin nawa sannan ya sauƙe ajiyar zuciya ya tambayi jikin da head kawai na amsa masa ya sauƙe ajiyar zuciya. Ya riƙe hannuna a hankali yake murzawa nikuma yin hakan da yakeyi sai yanaso ya sakani bacci. A hankali nafara lumshe idanuwa ganin hakan yasa yabar abunda yakeyi na buɗe idanuwa akansa shima ni yake kallo. ganin yaƙi ɗauke idanuwa a kaina na kulle idanuwana gam ban sake buɗesu ba inajin sautin murmushinsa dayaga na kulle a idanuwan. A hankali kamar maiyin raɗa yafara magana.
Chapter 77 · 0% Book details