← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 106

Sashe 96

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa mukeyi a wajan mai cikeda daɗi tun daga wannan lokaci bansake ƙoƙarin hana Hammood hakkinsa ba. Koda wahala nasha a wurinsa da zarar nayi niyyar hanawa idan natuno halinda yashiga wancan lokacin sai naga i have no other way than to miƙa masa kaina yayi yanda yaso amma a zahirin gaskiya lokuta dayawa inashan wahala a hannunsa sai dai babu yanda na iya akwana atashi harna fara sabo da yanayin yanda yakebi dani. Shikansa sau dayawa yana ɗagamun ƙafa hawai dan bayada buƙata ba sai dan yanajin tausayina. Yanayin wajan ya amsheni sosai nayi wanj iron haske dau sai kace wacce nayi allurar fari, shikansa har mamakin hasken da nakeyi kwana biyu yakeyi, dan dai kawai yanayin haskenmu ya bambamta ne da sai ace nima nakusa dawowa Balarabiyar.

Rayuwa tsaftacecciya mai cikeda Kulawa da soyayya muke gudanarwa a zamanmu a wannan Waje yanzu gabaki ɗayama mun daina zama a ɗaki dare kawai ke dawo damu ciki Mutane ne kala-kala masu al'adu kala-kala suke shaƙatawa a wajan shiga kuwa babu irin wacce bama gani amma duk da haka ko sau ɗaya Hammood bai taɓa barina na saka kayan daya fitar fa shape ɗin jikina ba bare nasaka kaya mai rabi da rabi koda yaushe jikina yana suturce ko'ina zamuje. Duk yanda mukaje kuwa da zarar an gane cewa Hammood ne a wajan shikenan za'a ɗaga mana hankali sai dai mu sake waje canma idan aka gane hakanne take faruwa lokaci guda kusan labari ya zaga tako'ina da kowa da yake wajan cewa akwai Hammood da matarsa sunzo cin amarci a wannan wajan shiyasa idan muka fita an dinga mana Videos da pictures kenan pictures da Vidoes ɗinmu suka zama viral a kowace kafar sata zumunta gabaki ɗaya month ɗin topic ɗinmu ke yawo a kowace kafa. Bahaka Hammood yaso ba dan baitaɓa son Pictures ɗina du zaga kafar sada zumunta ba amma babu yanda zaiyi amma yana ganin abunda mutane suke masa kamar wuce gona da iri shi bai ɗaura pics ɗin matarsa ba thats meas bayaso aɗaura masa rufin asirinsa guda ɗaya kowane picture da zaiyi yawo jikina yana suturce idan ya tuna hakan sai hankalinsa yaɗan ƙwanta shiyasa yasake ƙaurara tsaro wajan shigar da nakeyi dan sakarcin mutane bazai hanashi samun farin ciki da iyalansa ba. Babu irin maganganun da ba'a faɗa gameda ni da Hammood ya aura ba kashi 70% cikin ɗari suna ganin bandace da zamowa matar Hammood ba yayinda kashi 30% suke ganin shi so baya duban cancanta. Hammood idan yaga Posting ɗin mutane wani lokaci dariya kawai yakeyi idan yaga post makamancin cewa Tayaya akayi na shawo hankalinsa har yafara kulani nasamu soyayyarsa? Yakanyi dariya idan ya tuna shine wanda yake neman soyayya gareni ba niba wani lokacin yakanyi dariya ne idan yaga har izuwa yanzu idan ƴan borina suka tashi nakanyi masa koda ta rana guda ce. Ya lura mutane yanzu suna amfani da abunda idonsu yaganine kawai ba wanda yake a zahiri ba. Lokaci ɗaya Yaya Habibu ya shata ya ɗaura videon da yayi mana ranarda Hammood yaci worldcup inata zuba masa rigimi shikuma yana bani haƙuri fuskata bata fito ba baya nane kawai ya fito a lokacin kuma hakanma ya rumgume a jikinaa gabaki ɗaya. A cikin Comment section Hammood yayi comment da Drama Queen da fuska mai nina tsantsar soyayya abun yaja hankalin mutanen media kowa da abunda yake faɗa yayinda wasu suke ganinma kamar ba niɗin bace tayaya namiji kamr Hammood zai tsaya yana rarrashin duk da basusan akan abunda yake rarrashin ba, a zahiri za'aga kamar yaya Habib ne ya saci lokaci kawai a ɗaura amma a baɗini ba hakan bane domin Hammood ya sakashi."

Idan nayi kewar ƴan gidanmu nakan ɓata lokaci muna waya dasu Shima Wasu lokuta inajinsa sa'i-sa'i suna waya da mahaifinsa da Mum harda Nawrah amma ko sau ɗaya bai taɓa bani mungaisa ba nima bantaɓa tambaya ba amma inaso wata rana yakaini wajan mahaifinsa sai dai shi bansam yanda zai karɓeni ba ba ban taɓa yi masa zancen inason ganin mahaifinsa ba amma zancen yana raina ina jirar ranarda ta dace sai nayi.

Yau saida magrib ta kusan riskarmu awaje muna muka gabatarda sallah saboda kafin mu isa magrib ta rigada tayi. Aka kawo mana abinci yanzu ya samamun abincin da zan rigaci hankali ƙwance, naci iya yanda zan iya nabarshi yana aikinci na jawo jaka naɗauki biscuit nafara ci.

"Masoyi" na faÉ—i kamar yanda nake kiransa yanzu, ya kalleni yanacin abincinsa batareda ya amsa ba yana jira nafaÉ—i abunda zan faÉ—a.

"Yaushe zamuje gaida Abie? Kullum inaji kuna waya dashi inaso naganshi amma bantaɓa kallonsa ba gidansu ɗaya da mum ne? Nayi tunanin zaizo lokacin da kake buga worldcup amma baizoba, baiyi magana ba har ya ƙarasa cin abincinsa nima ban damuba saboda nasan halinsa lokuta dayawa haka yake sai an daɗe dayi masa magana kafin yabada amsa. Saida yagama cin abincin yatashi yashiga toilet yagyara bakinsa sannan yafito ya zauna harna manta da nayi masa tambaya saiya miƙomin Hannu alamun nazo babu musu na isa gareshi na zauna kusa dashi kamar zan shige jikinsa ya sanya hannu yayi crossing ɗina ya mannai sosai munajin ɗumin jikin juna kafin yafara magana.

"Zamuje muga Abbie soon in sha Allah, Kuma abbie ba gidansu ɗaya da Mum ba bama ƙasarsu ɗaya ba abbie yana Kuwait Mum tana UK, Mum ƴar ƙasar England ne Abie kuma asalin balaraben Ƙasar kuwait ne, My Mum is christian and Abie musulmi ne sun haɗu a school suka fara soyayya har takaiga maganan aure familyn abbie sun basu ciwon kai amma familyn Mum tashi ɗaya suka amince da auren (itama familynta sun amincene saboda a ashekarun baya familyn Abbie is super rich and suna among the richest family in the world wanda shi Hammood ba lallai yasan hakanba amma Ku makaranta yakamata ku sani) daga baya familyn abbie suka amince amma da sharaɗin zai sake auren musulma bayan aurensu saboda yanason Mum yanaso ya aureta ya amince amma abbie bai sanarwa Mum yanda sukayi da family ɗinsa ba, saida yagama karatu yazama ciekkken soja sannan aka taso da maganar aure bayan wasu lokuta da aurensu suka haifeni dake Mum tasan familynsu Abbie sunfisu ƙarfi sosai yasa batayi maganar addini akaina ba sai bayan 5years tasake haifan Nawrah sannan ta nemi Abbie yabata dama Nawrah ta tashi a christian abbie yaƙi tunda tun farko basuyi haka ba yace kada tasake tada wannan zancen har wanima yaji saboda family ɗinsa zasu iya tuno da zancen baya na ƙara aure, Mum batajiba ta tada zance zancenda ya jawowa Abbie ƙara aure kenan daga family ɗinsa mum tayi fushi tatafi Dad yabita taƙi amincewa sai dai ya rabuda matarda ya aura sannan Nawrah tabi addininta Dad yace bazai iya ko guda ɗaya ba, daga ƙarshe familyn Mum suka nemi saki da cewar Abbie yabasu 70% of his dukiya saboda ta haifa masa yara biyu a tunaninsu zai saka Abbie yayi abunda sukeso idan kuma baiyiba yabasu kuɗin toh hakan gaba takaisu. Abbie babu ɓata lokaci yabasu kamar yanda sukayi demanding su suna murna suna ganin cewa sun gama tagayyara abbie Not knowing that abbie yanada dukiya may be za'a iya cewa 10% kawai suka sanda ita toh acikin wannan 10% ɗin yabasu 7 so ko'a jikinsa. Tun daga lokacin ko hutu abbie bai barni nida Nawrah munje wajan Mum ba har muka girma a tunaninsa zata iya canja mana tunani zuwa addininta Mum ma bata nemeni ba har saida na girma na sanu a duniya tukunna sai alokacin muka fara zuwa wajanta harda Nawrah. har yanzu Mum bata sake aure ba bansan dalili ba tunda bantaɓa tambayarta ba Abbie yanda mata biyu,
Abbie ba kamar Mum bane dan Abbie nasonki sosai alokacin dana shaida masa ina sonki shine yafara bani ƙwarin guiwa gameda soyayyarki. kuma shi yataka ya nemamin auranki har wajan Baba yanzu ina cikin hutu zan kaiki wajansa" nayi luff a jikinsa nagama sauraron abunda yake faɗi. Sai yabani tausayi tabbas Hammood abun tausayine ace uwa da uba kowa addininsa daban? To amma yaya zaiyi? Yanda ubangiji ya rubutawa rayuwarsa kenan. Cikin tausayawa nace.

"Kanaso Mum ta koma gidan Abbie sucigaba da zama matsayin ma'aurata? Ban bari yayi maanaba nacigana da magana. Dalilin da yasa Mum bata sake aure ba shine tanason Abbie har yanzu kuma ayanda na fahimci zancenka Familyn Mum dukiyar abbie sukeso yayinda Mum abbie takeso amma batada zaɓi face tabi abunda danginta sukace. Mum ba shahararka takeso ba kamar yanda kake tunani Abbie bai bata damar da zata kasance daku ba na tsawon girmanku sannan kuma hakan da yayi bawak laifi bane saboda yanayin bambamcin addini dake tsakani dama koda bata nemeku ba ku zaku nemeta sannan Mum kusanci kawai take nema daki tanaso ka ɗauketa matsayin uwa kamar yanda kowane ɗaa yake ɗaukar mahaifiyarsa. Tanaso da samu kulawa da soyayya ta uwa a wajanka" kadaina pushing mum away from you Masoyi Allah zai tambayeka baka yiwa Mum biyayya kana mata magana yanda kaso saboda kaga tana ƙaunarka sosai kamata yayi ace ƙaunarka tafi tata yawa tunda kaine yanzu wanda tafi kowa kusanci dashi dan Allah kayiwa Mum biyayya ko zata samu sauƙi daga wajanka koda kai ɗayane, kada bambamcin addinin dake tsakaninku yasa ka saɓawa mahaifiyarka ko kana mata kallon bata isaba shi musulumci babu ruwansa da wannan sai kaga Allah ya tambayeka akan hakan sannan idanma kanaso ta canja zuwa addininka haka yakamata ka tarɓeta? Yaushe har zataji sha'awar ta zama kamarka? Dan Allah masoyi ka gyara idan kanson muma yaranmu suyi mana biyayya" Idanuwansa sun canja launi baice komaiba amma shi kaɗai yasan zafinda akeji idan addinin iyaye ya bambamta kuma kana kallonsu Babu yanda ka iya dasu. Tallafo fuskarshi nayi da hannuna ina kallon yanda ta canja gabaki ɗaya tayi wani jaaa da alamu yana tafasa ta ciki.
Chapter 96 · 0% Book details