← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 106

Sashe 45

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bagashi ba ta gayamin magana babu wanda yamata magana amma ni ina faÉ—a mata dukanku kunji haushina nice wacce muka fito ciki É—aya daku amma ita kukafiso" a hasale anty fadeelah tace.

"Banza kema ki gyara halayanki su dawo irin nata mana kiga ko baza'a soki ba" tana faɗin haka tatashi tabi bayana nikuwa ina komawa ɗaki harna fara kuka sai naga menene ma amfanin kukan da zanyi harme yafaru haka da zanyi kuka dan haka na share hawayena na zauna kawai ahaka tashigo ta sameni ganin bana kuka ko ƙoƙarin haɗa kayana da niyyar tafiya sai hankalinta ya kwanta tana zuwa ta zauna gefena tana rarrashi. Nace mata ni babu abunda yafaru tunda na rama daban rama abunda tamun bane shine zan zauna nayita jin zafi araina amma banda yanzu dana rama. Daga nan har muka fara hira muna dariya itadai tanata mamakin wani irin hali nake dashi haka da sam ban iya riƙo araina ba."

Mummy tashigo tasamu abunda yake faruwa dan ya Ahmad ya kirata tayiwa Aysha magana idan shine yace zaiyi mata magana yanaga zai fara karyata tukunna. Dataji abunda yafaru ranta yayi masifar ɓaci dan haka tasa aka kiramu nida anty fadeelah da sauran wanda suke wajan abun yafaru duka ta haɗamu. dake kusan kowa yana tsoronta har yayyunta maza shakkarta suke bare ƴaƴansu.
Saida tafara da faÉ—a sosai.

"Dan Ahmad ya siyawa marmeeyy waya shine kike tada jijiyar wuya kuɗinki ko nasa? Idan yaga dama ya cire kaff dukiyarsa yabata yanada damar yin hakan kuma babu wanda zai tuhumeshi tunda nasan kuma marmeyy ta cancanci fiyeda haka har zaki mata gorin gida wai tatafi. Toh kema zakizo kitafi tunda ba gidan ubanki bane sai ki koma gidan naki uban nan ni kaɗai nakeda iko nida ya kasance gidan ubana ba na ɗaya a cikinku ba" sannan kuma ta sauƙo tana faɗin.

"Nasan zakuga kamar nafison Marmeyy akanku ku yarana dana haifa a cikina ni kaina banida wannan amsar banta tabbacin da marmeeyy daku waye nafiso amma abu ɗaya nakeda tabbaci shine kaff cikinku babu wanda ya fahimceni kamar yanda marmeeyy ta fahimceni babu wanda yakemin uzuri kamar ynda takemin babu wanda yasan ciwona sai ita ban tsugunna na haifeta b aamma abunda yakamata wanda na tsugunna na haifa Yakamata suyi itace takeyi toh ina laifi dan na bata matsayin abunda na haifa? Tunda nabar gidan mahaifinku cikinku babu wanda yataɓa tunkarata da maganar ko maganar mahaifinku amma ita tayi ta fahimci ciwon aita kaɗaice ta kalleni ba irin kallonda duniya takemin ba. Ko ɗaya a cikinsu babu wanda yataɓa tarɓata da murmushi saboda kuna tsorona inada zafin hali amma ita kullum saita yimin murmushi a cewarta inada hali mai kyau. Dan haka idan damaijin haushi acikinku toh yaji amma acikinku da marmeeyy bansan wanda nafiso ba kuma karna sakejin wani abun yataso. gabaki ɗaya jikinsu yayi sanyi Muduka muka bata haƙuri ya Ahmad ya amshi wayata ya bani."

Banyi amfani da wayarba na sanyata a cikin akwatina kawai na ajiye.

Da Dare Kuwa nasamu Mummy da maganar tafiya hankalinta yatashi tana tunanin ko abunda yafaru ne ya sanya nakeson tafiya nace mata dama ana gama biki mukayi akan zamu koma. Saboda Maryam su Umminta sun kusa dawowa Tace toh zatayi shawara tasaka mana ranar tafiya saita sanar dani ahaka muka tsaya da maganar nakira Hamma na sanar masa yanda mukayi da ita. Yayi murna danya matsu yaganni bayaso muyi saɓani dan shima abujan zaizo week ɗinda zamu shiga saboda dawowar su Ummi kuma zai jirasu kaman na 2days anan. Bayida tabbacin ko yazo nan mu haɗu shiyasa yafiso nadawo kafin lokacin tafiyar.

ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

A gidansa yasamu Nawrah tana zaman jiransa Baiyi mamaki ba dan dama yayi zaton hakan. Baibi takanta ba ya wuce Shashinsa bata bishi ba dan taga alamun a ynzu bayason hayaniya kuma dama shi kaɗai keda access da part ɗinsa. Aranta ta ƙudirta cewa bazata tafi ba Dole idan yafito zaiyi mata ƙarin bayani akan abunda yake faruwa. Yana shiga ya dannawa wajan lock yanda ko knocking tayi bazai jiyota. Har yanzu bai shirya basu amsaba daga ita har mum ɗinsa ajiye wayarsa yayi yashiga wanka yana fitowa ya ƙwanta dama already yayi sallah tareda mutanensa kafin yakaiga shigowa ciki.
ransa fesss idan yatuna cewa Yanzu Zaynab tazama mallakinsa sai yasaki murmushi ahaka Har bacci ya ɗaukeshi. Bashi ya sauƙo daga part ɗinsa ba sai bayan wajan 11hours abunda baiyi zato ba shi ya taras mum ne agidansa ba kasafai tafiya zuwa wajanda yakeba kmar yanda bai wani damuda itaba hakama itama bata damu dashiba kodan rashin damuwar tasamo asaline daga wajanta tunda sam bata damu ba yaranba har saida yaronta yazama wani a duniya alokacin sannan tafito takeson nunawa duniya itace mahaifiyarsa wanda shikum yaƙi yabata damarda zata shiga jikinsa sosai itakuma saita ɗauki hakan ta alaƙantashi da bambamcin al'ada dakuma addini dake tsakaninsu atunaninta alaƙarda take tsakaninsu zata gyarune da Zarar ta aura masa wacce takeso daganan zai dawo jikinta alƙarda take tsakaninsu kuma taƙara girma anan zai dawo yanajin maganarta. Ko dangin mahaifinsa bazata yarda ya aura ba bare kuma baƙar fata wacce ita batayi musu kallon cikakkun mutane.

Bayan ganinta saida yasha jinin jikisa saboda halin mitarta Amma yajaa yadake dake dama shi namijin duniya ne abune mawuyaci gane yanayinda yake ciki ya ƙaraso yaɓoye duk wani mamakin ganinta ya isa yazaun a kujera fuska babu yabo ba fallasa yayi mata barka da zuwa ta Amsa sannan cikin tuhuma Tafara magana da harashen turanci.

"What is happening. Word is spreading that you are getting married Ko akwai ƙarin bayani da Zakamin gameda haka?" Murmushi kawai yayi baice komai ba mum tace.

"Mood Say something. Speak up"
Ajiyar zuciya yasauke yatashi ya nufi fridge yadauki ruwa mai sanyi ya ajiye agabanta haɗeda sakar mata murnushi. Tarasa gane wane irin murmushine mood yakeyi haka danshi ba ma'abocin murmushi bane bare ma ita wacce dama jininsu bai haɗuba. Batareda ya tsaya ya sauraresu ba yayi ficewarsa gabaki ɗaya yabar gidan kwananta biyu a ƙasar bata sake sanyashi a idanuwanta ba Mood ya bar ƙasar gabaki ɗaya saida tagaji dakanta takoma ƙasarta wayarsu kuwa kosun kira bata shiga kamar wanda aka datse layinsu gabaki ɗaya itada Nawrah a layinda zasuna kiransa dan sam baya shiga. Wannna abunda yayi yasake tabbatar musu da abunda sukaji gaskiyane dan Mood baya ƙarya duk rashin daɗin abu bazai iya cewa ba haka bane gara yayi shiru.
Mum bata bar ƙasar ba har saida ta tabbatar ta nunawa Nawrah hanyarda zata samo musu amsa wajan mahaifinsu.

Shim Nawrah tun kafin tazo nan tayi- tayi yafaɗa mata yaƙi danya kasance mutum mai riƙe amana tunda yayiwa mahafin Marmeeyy alƙawarin bazai sanarwa kowa ba tofa bazai faɗa ba danshi riƙon alƙawari yana ɗaya daga cikin sanannun halayansa. Duk wani abinda akace alƙawari toh angama tashi dan zai iya bada rayuwarsa akan hakan. Ko ita nawrah batada masaniya cewa mahaifinta yayi alƙawari dan da bazama tafara tunkararsa da cewar tanaon tasani ba danko kasheshi za'ayi bazai faɗa ba.

Itama Nawrah tagaji da zaman jiransa tatafi abunta dan batada tabbacin lokacin da zai dawo zai iya tafiya babu wanda yasan yanda yake his whereabout remain secret har sai randa yadawo dan kansa dagashi sai masu yimasa hidima yake tafiya.

_____

Bayan 2days dayiwa Mummy magana ta shirya mana tafiya da drivernda zai kaimu Ya Ahmad shi sai bayan 2weeks zai dawo yaso yakaimu amma Mummy tace yabarshi zata saka akaimu ransa baisoba amma babu yanda ya iya, yaso kamar yanda yaÉ—aukomu ya maidamu. Mummy tayi Mana hidima sosai wasu abubuwanma bamusan ta zuba mana suba.

Fitan Sassafe mukayi. Ƙarfe bakwak motatmu tatashi muka ɗauki hanya. Jefi-jefi ake hira a cikin motar amma nida Aysha zaman kurame mukayi idan ana hira ina saka baki take shiru nima danaga haka nadaina saka mata baki dukda ita bawani hiranma takeyi ba dan tun ranar bata sake sosai ba.
zuwa 12:00Pm Mun isa garin bauchi kai tsaye gidan Baba aka kaimu. Shi kansa Baba akwai aikanda mummy tayi masa driver da yaya Habibu suka fitarda Kayan suka shigar gida. Munyi murna sosai da ganinsu su Mama ma sunyi murna dan gidan yayi musu shiru da bamanan. Muka fitarwa kowa da tsarabarsa mula bashi bayan munshiga nake kiran Hamma a waya na sanar dashi isowarsmu ya sanar dani da magrib zaizo nayi missing ɗinsa sosai dan haka banyi masa musuba yazo kawai Zansan yanda zanyi dasu Mama. koma bahaka ba Yanzu ban tsoron asan tarayyata dashi na shirya tsaff dan sanarwa nunawa iyayenmu zaɓina.

Kafin Yamma saida nasake wanka na shirya cikin riga da skirt Amma nasaka Hijan ƙarfe biyar kuwa ya iso muka samu mama mukace mata yayan Maryam yazo ganinta Mama tace mushigo dashi palon anty tunda akwai mutane a falonta.

Nida maryam muka fita danyi masa iso a waje muka sameshi yana jingine jikin mota yana danna waya yayi kyau sosai cikin shadda ɗinkin jamfa yasaka hula tun daga nesa dana hangoshi fiskata ta yalawata da murmushi bana aune kawai sai naji na sakin murmushi. Kodan na kwana biyu ban ganshibane sai naga yayimin wani irin kyau mai cikeda ɗaukan hankali da sallama muka ƙarasa wajan sai alokacin yasan da zuwanmu ya ɗago yana kallonmu shima idanuwansa suna kaina ƙasa nayi na kaina ina murmushi nasake gaidashi ya amsa yana ƙaremin kallo. Nayi kyau sosai bayn gyaran jikk da mukasha ga lalle da yayiwa zara zaran yatsuna kyau ya sauƙarda idonsa ya kalli hannuna a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya amsa gaisuwar asannan maryam ta gaisheshi.

"Hamma mushiga daga ciki nafaÉ—a" yace.

"Okay muje" muka fara tafiya yana biye damu a baya har muka shiga ciki Saida yagaidasu Mama kafin muka shiga falon anty wacce tatafi tabarmana falon.

Hirarmu muka fara kamar bamusan da Maryam a ɗakinba saida muka taɓa hira sannan namiƙe na fice ɗakin Mama dan ɗebo masa abunsha. Dai-dai kunnen anty fadeelah naje na raɗa mata Hamma yazo kizo kugaisa saida tayi ƴar dariya sannan tamiƙe takamo hanun Aysha suka biyo bayana.
Chapter 45 · 0% Book details