← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 106

Sashe 83

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"wannan bashi bane dalilin. Dalilin shine saboda ka saka a ranka tun dama can zakaji daÉ—in rayuwa dani da zaka bawa sauran mutane irin damar daka bani na gane wane ne kai lokaci guda da zakasha mamakin yanda zakaji daÉ—in zama da mutane. Ni inajin daÉ—in zama da Æ´an uwana yanda idan bana cikinsu nakanji kamar duniya bazatayi daÉ—i ba nadawo wajanka da saka ran samun farin ciki wajan naka Æ´an uwan amma meh?" kai baka sakewa da Æ´an uwanka a tunanina idan ka É—aukeni ka kawoni nan Æ´an uwanka zasu zama nawa har naji daÉ—in rayuwa nima. Amma Bahaka ba kaima kanka baka samu sakewa da Æ´an uwanka ba bare ni danazo daga baya kawai zanyita zama cikim kaÉ—aici ne" nafaÉ—i hakan hawaye na gangara akan fuskata. Hannunsa yasa yana sharemin hawayen fuskata. Allah yagani yawan kukana yana damunsa danko yana farin ciki yakanji É—aci aransa yarasa abunda zaiyi nadaina kukannan.

"Kina tunanin samun kusanci da Æ´an uwana da zanyi shi zai basu kusanck dake?" na jijjiga kaina.

"Toh idan hakane zan samu kusanci dasu sosai yanda zakiji kaman kina gida, dan Allah ki taimaki rayuwata kidaina kuka idan kika sake zubda hawaye kinamin nuni da bakison nayi winning cup É—innan. Hawayenki are my weakness" dasauri na share hawayen dan banaso naji yayi zancen rashin winning cup É—innan.

Yana zaune a wajan ya turawa kitchen saƙon abunda yakeson su dafamin muna zaune har aka gama suka sanar dashi muka fita sai yana zune harna gama cin abincin na shirya Nawrah ta saƙƙo. Yayimin sallah ma akan akwai abunda zai fita yi nayi masa sallama na haura sama. Wajan Nwrah yabi tana zaune.

"مرحبًا Mood حبيي" Da murmushi ɗauke A fuskarsa ya shafo kanta.

"حبيتي Zan fita for wani lokaci take care okay?" ta gyada kai tana mamakin Mood da yakan tafi yabarta a gida sai dai idan tagaji da zama takoma gida. Har yakai ƙofa tace.

"Mum Will be here by 7pm"

"Okay I'll be home by then in sha Allah" mamaki ya kashe Nawrah dan tasan halin Hammood haka kawai idan yasan mahaufiyarsu zatazo yakan ƙi dawowa dan gangan wani lokacin kuma yadawo sai ɗaya idan yafita bazata sake ganinsa ba har sai tagaji dan kanta takoma kuma sam bayaso tazo yanda yake. Amma yanzu wai shine yake cewa zai dawo gida kafin isowarta ma bayan yasan yamata laifi dole zasu ƙwashi ƴan kallo." Hammood yafara canjawa dam da sam bahaka yake ba baisa sake wai ahakanma itace suke shiri dan babu yanda ya iya ta ita ko sun ɓata sai sun shirya."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Bayan Magrib Mood ya dawo gida yasamu Mum bata iso ba. Bayan ya shiga ɗakinsa yayi wanka ya shirya sannan ya fito zuwa ɗakina dan yasan ina zaman dana saba da iya yiwuwa tun fitarsa ban leƙo ba.

Kashe AC ɗakin nayi bayan ɗakin ya ɗauki Sanyi kamar yanda nasaba dai doguwar riga ce a ajikina kaina babu ɗankwali na kama gashin dake yanada cika sosai ina shirin cire rigar jikina na zauna da ƙananun kaya naji shigowarsa godiya nayi ga Allah da ban kaiga cire rigar ba Shi haka kawai sai yana shiga ɗaki batareda ya nemi izinin shiga ba

ƙananun kayane a jikinsa farar T-shirt da Short trouser bai ƙarasa guiwa ba farar tafarsa sai sheƙi da yalli take kamar wanda aka yita da dutsen lu'u-lu'u yayi matuƙar kyau sosai sai dai tunda na kalleshi sau ɗaya na kawarda kaina wata irin kunya ta rufeni nasaba yimasa kallo a yanayin dayafi haka ma tunda ina kallonsa da gajeren wanda na ƙwallo A TV banyi tunanin haka zanji idan naganshi a fili ba.

lumshe idanuwa na nayi a lokacin daya ƙaraso ya zauna kusa dani a kullum ƙamshin turarensa sabunta yakeyi a hancina nakanji kamar alokacin nafara shaƙarsa kuma akoda yaushe naji sai ya sauƙarmun da nutsuwa duk da ya kasance a halin yanzu nima irin ƙamshin da nakeyi kenan amma nasa danakeji a jikinsa yafimin daɗi. Sauƙar ɗumin hannunsa danaji akan wuyana ya sanyani buɗe idanuwa Na sauƙesu akan kyakkywar fuskarsa saida na Shaƙi numfashi Izuwa cikin cikine a raina nake yiwa Allah godiya daya mallakamin Hammood a matsayin miji ko a mafarki bantaɓa tunanin mallakar mutum kamarsa ba sai gashi baga wayona ba ba dabara ba Allah yabani shi kuma yayi ikonsa akansa ya sanya yakeyimin soyayyar da ni kaina bana tunanin ina yiwa kaina. Fuskata tana kan tasa ina ƙarewa kyakkyawar fuskarsa kallo nakasa cewa komai.

"هل اشتقت الي"
(kinyi kewa tane) naji zazzaƙar muryarsa a cikin kunnena, na lumshe idanuwa na nasake buɗewa akansa sanna ajiayr zuciya ta biyo baya. Sai asannan na ɗauke idona daga gareshi bawai dan idanuwana sun gaji da kallon fuskarsa ba.
Rumgumeni yayi ajikinsa tsam dan atunanina kewarsa nayi yasa nake masa irin wannan kallon kuma tunanin bai bashi ƙarya ba. Luff nayi a faffaɗan ƙirjinsa ina shaƙar ƙamshin turarensa tsabar daɗi sai nakeji kamar wanda bacci zai ɗaukeni. A kunnena naji kuryarsa.

"I missed you More Rouhii, I whish Babu wani abunda nakeyi na zauna dake nabaki farin ciki" Na raba jikina da nasa na kalleshi. A fili nace.

"Kai kaÉ—aine ke kalaman soyayya batareda murmushi akan fuskarka ba kuma kalmar ta ratsa mai sauraro sannan su zauna a mazauninsu" Baisan abunda na faÉ—a ba kawai yana bina da kallo akwai wani abu guda É—aya daya lura dashi game dani. Akoda yaushe yayimin wata kalma ta soyayya wacce bazan iya bashi amsa ba nakanyi da yaransa bazaiji ba. Koda a zahiri bai fahimci abunda nafaÉ—a ba jikinsa yakan bashi abu mai kyawu na faÉ—a.

"My mum will be here soon. Inason ku gaisa idan bazaki takura ba Will you please?" na kalleshi da mamaki. Maman nashine yake roƙona mu gaisa? Lallai Hammood shi wani irin mutum ne? Wace irin alaƙa ke tsakaninsa da mahaifiyarsa? Ko baki bai kaiga furtawa alamu ya nuna babu alaƙa mai ƙarfi da kyau tsakaninsu. Ban bashi amsa ba dan banga abunda zance ba shima bai sake cemin komai ba.

"Zan sauƙa May be ta iso" kai ja gyada masa kawai ya miƙe yayimin peck a goshi ya fice. Yana sauƙa kuwa yasamu ta iso. Da murmushi kwance a kyakkaywar fuskarsa wanda hakan ba sabonsa bane. Dan Hammood shi sam bama abocin dariya bane amma idan yayita takan fitarda duk wani sirrintaccen kyawunsa ta'iya yiwuwa ya lura da hakan shi yasa bayayinta. Akoda yaushe idan suka haɗu Mum ita ke ƙarasawa gareshi tayi hugging ɗinsa amma a wannan karon shine ya isa gareta da mamaki yayi hugging ɗinta yana mata barka da zuwa. Ita dai Hammood ya cikata da mamaki matuƙa ga wani yalwataccen murmushi dake kan fuskarsa. Kodan yasan Nawrah ta faɗa mata zancen Matarsa bayaso tayi masa faɗa ko yaya zaiyi saita masa faɗa dan zaizo ya maida yarinyar yanda ya ɗaukota shiyasa bata taho Hannu haka ba tazo masa da wacce takeso ya aura idanna zata bar masa ita anan saita barta daga baya aɗaura aure duk kuwa da sanin halayansa da tayi a wannan karon ya zama dole Hammood ya biyeta ba iya ta biyeshi kamar yanda aka saba ba. Yaro shine mai bin Mahaifiya amma ita itace kebin Hammood a duk abunda yakeso Amma banda wannan karon. Ta rafa cikinsa da nata fuska babu Annuri tace.

"Where is She?" Ya HaÉ—e rai sosai yadawo Hammood É—insa datafi sanin dan yagane wacce take tambaya.

"Who? Ya tambaya cikeda rainin hankali" caraf Nawrah ta kama.

"Your wife"

"Ki huta yanzu zamuyi magana yafaÉ—a fuska a haÉ—e yabarsu a palourn"

Har akayi isha'i bai shigo gidanba yana neman hanyar da zai ɓullowa Mum ɗinsa.

Nikuwa yana barin É—akin nayi wanka na fito É—aure da alwala dake naji kiran Isha'i saida nayi sallah sannan na shirya cikin doguwar riga mai kyawun gaske
Lipgloss kawai na shafa na gyara fuskata na saka hula ina zaune zaman jira shigowarsa. Saida Kyawawan Awa biyu suka shuÉ—e sannan naji shugowarsa É—akin yanda na ganshi nayi tunani ya shigone yayimin sallama zaije kwanciya.

Ƙarasowa yayi ya zauna fuskarsa Babu walwala ina game a wayata na ɗago na kalleshi zama yayi ƙasa kusa dani.

"Wai zaman É—aki baya damunki" na gyada masa kai.

"Meyasa kikeson saka manyan kaya? Suna miki kyai amma kina takura kanki" na girgiza masa kai alamun ni basa takurani.

"Kinajin kunya nane?" ban bashi amsa ba tunda yasani ai bai kamata ya tambaya.

"Thi is Your Home kina saka kaya the way you want kidaina saka manyan kaya idan ba fita zamuyi ba" Nanma kai na gyada masa.

"Zaki ƙwana ɗakina?" naji tambaya asam da sauri na kalleshi ni yake kallo Babu murmushi ko alamun wasa a fuskarsa. Girgiza kai nayi.

"No zanfi jin daÉ—i anan"

"Mum ta iso I'm sorry Amma bansan yaya zata ɗauki lamarinba. nafiso Ki zauna kusa dani Hankalina zaifi kwanciya" Alamun damuwa ƙarara da bayyana akan fuskarsa.

"Muje mu gaisheta"

"No idan bakyaso karkije kiyi zamanki"

"Inaso shiyasa nace muje"

"Ya Rouhi nace miki bansan Yaya Mum zata É—auki maganar aurenmu ba"

"Koma Yaya zata É—auka ai ita uwace tanada ikone yasa hakan Kabarta ta gudanarda ikonta aynda taso"

"Banason abunda zai ɓata miki rai domin na tsamoki daga cikin danginki na taho dake ƙasarda ba taki ba da saka ran zan baki farin ciki banason alƙawarina ya fara karyewa daga yanzu"

"Ni nace baka bani farin ciki ba? idan nace haka ban zamto daga cikin mata masu karamci ba. Na lura tun zuwana babu wani abunda kakeyi sai ƙoƙarin farantamin"
Chapter 83 · 0% Book details