← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 106

Sashe 63

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh ya isa kinji idanda wanda yakamat Hammood ya warewa lokaci toh kece idanda wanda ya cancanci lokacinsa toh kece. kinfi kowa kusanci dashi a ƙasarnan gabaki ɗaya. Nan gaba zaki samu kusanci dashi wanda aduniya babu wanda Allah yabawa damar samun wannan kusancin ke"

"Mummy ban ganeba fa"

"Bayan yana sonki babu abunda ya faÉ—a miki?" Har zan girgiza kai sai natuno wani abun.

"Uhmm yace wai nice wacce nafi kowace mace kyau a idonsa"

"Bayan wannan babu wani?" na girgiza kai.

"Na manta sai dai idanna tuna na sanar dake"

"Okay toh tashi kiyi wanka kici abinci. Saiku fito naji Babanku yace za'ayi aiki" kai na gyaÉ—a hawaye nabin fuskata.

"Menene kuma Marmeeyy"
"Mummy halan yanzu yanajin haushina saboda shirmenda nayi masa koh?"

"No bayajin haushinki Ta iya yiwuwa hakanma ya nishaɗantar dashi maza tashi kishirya" namiƙe jiki babu ƙwari.

Dukansu suka fice yazama saura Nida Anty fadeelah da maryam a ɗakin. Anty fadeelah ta miƙomin wayata.

"Kingani buɗemin na tura pics ɗinda kuka ɗauka" na amsa na buɗe na miƙa mata.

"Barina fita nafara nunawa mutanen waje tukunna" tafaÉ—a tana kama hanyar fita abubuwanda suka faru sunata dawomin na kalli Maryam wacce take kallona da mamaki É—auke a fuskarta.

"Babe Hammood fa shine mai turamin saƙonan"

"Nasani ai" Na zaro ido.

"Yaya akayi kika sani?"

"Ya Ahmad ya faɗamin jiya shine dalilin zamana da kana anan nakira Ummi na faɗa mata anan zan ƙwana bazan iya haƙuri zuwa gobe ba nabari kizo kibani labarin abunda yafaru kika dawo kika shareni daƙyar na iya bacci"

"Wato Ya Ahamd yasan Hammood shine ɓoyeyyen masoyi?"

"Iyi yasan yana bibiyarki amma baisan shine ɓoyeyyen masoyi ba"

"Lallak biri yayi kama da mutum" sai alokacin wasu abubuwanda ya Ahamd yakeyi suke dawomin har lokacinda yasaka na ɗebo masa kuɗi amota naje na haɗu da Hammood tabbas ko shakka babu mutuminda na haɗu dashi Hammood ne dan muryarsu ɗaya har yanayin jikinsu sannan a wancan lokacin yacemin sunansa Mood Acikin Hammood za'a cire Mood sannan kuma ƙamshin turaren ɗaya komai ɗaya ya tabbata Hammood ke bibiyar rayuwata. Amma duk soyayyata da Hammood meyasa wancan lokacin nakasa gane shine? To tayaya ma zan iya gane Hammood ne bayan ko ayanzu ƙwaƙwalwata daƙayr take ɗaukan lamarin. Ajiyar zuciya na sauƙe da sanyin jiki.

"Wai menene Babe? Ko wani abun yafaru ne? ÆŠatsu kina zancen bayan kunzo gida kuma yamiki sai kikayi shiru.

"Babu abunda yafaru" sake cemin yayi yana Sona.

"Nikam danaji kin ƙaƙare kin kasa faɗa saina ɗauka kiss yayi miki"

"Allah ya sauwaƙa"

"Allah ya sauwaƙa koh? Ai naga bashi kaɗai yafara ba Hamma ya rigashi. tunda ranar ina ganin wajan event ɗin dinner ɗinsa ƙoƙari kawai yake ya haɗe bakinku waje ɗaya. Kuma bana tunanin wannan shine karonsa na farko akwai lokacinda mukaje gida su Ummi na umra naga kinfito kinata kuka na tambayeki kikaƙi faɗamin Kukayi faɗa daga sai daga baya muna abuja kuka shirya. Harni yayita kira yana cewa nabaki waya naƙi saboda jikina yabani a akwai abunda yayi miki kika shiga tashin hankali. Aranar kwana kikayi bakiyi bacci ba sannan bakiyi karatu ba gashi atlast kinyi carrying course ɗin. Sai a abuja kuka shirya. Duk mai hankali dayake tsakaninku yaga abunda yafaru yasan akwai abunda yamiki bare nida nazauna dake nasan bakida fushi. Sannan idona yazo ya ganemin abunda yake shirin yi a wajan event na bikinsa dan rashin kirki"

"Ke yayankine fa kika faÉ—a masa haka"

"Aysha ƴar jaraba tashiga hannu madallah" tafaɗa tana dariya na ɓata rai.

"Kekam maryam kin iya wulaƙanci wallh"

"Menene na wulaƙanci aciki keba Allah ya fissheki ba? Da wannan kayan kunyar dake za'a ƙareta kiyi kwanan asibiti tun baki haihu ba kin farke an ɗinke"

"Hmm lalli Maryam bakisan itama Aysha dan baya sonta yasa baiji ciwon aikata hakan akanta ba yabi da ita batreda tausayi ba. Ai duk yanda soyayya take akwai tausayi"

"Nidai koma menene wallh naji dadi anyi maganinta"

" Toh bari kiji wallh ba'a dariya wa motar gawa kina hanya ke bamusam yaya zaki kasance ba"

"Ahirr wallh babu abunda zai kasance wannan abunda sukayi ai tonawa kai asiri ne Ummi fa ko haÉ—a ido bata iyayi da Hamma"

"Allah ya kyauta" shine kawai abunda nafaÉ—a.

"Wai meya farune lokaci guda kika sauƙo Marmeeyy? Saida nayi taraddadin faɗa miki wannan abun saboda nayi tunanin zaki shiga tashin hankali" na jijjiga kai.

"A'a ni hakanma shine yaƙara cireminshi araina saboda nasan yayi nisa agareni"

"Kinyi nisa a gareshi dai koh Marmeeyy? Kefa yanzu ta Hammood ce a duniya wanda zasu iya bige hammood su mallakeki basuda yawa"

"Hmm" nafaɗa namiƙe.

"Kinga bari nayi wanka na shirya muje muga wani aikine a waje. Gobe yazama dole muje makaranta tunda yanzu mu mundawo Æ´an duniya rabonmu da makaranta tun friday"

"Ai mubari sai wanj sati kawai gobe fa friday"

"Koma satuarday ne haka zamu shiga" nafaɗa nashige toilet. Nadaɗe a cikiin toilet ina tunanin abunda yake faruwa mai ƙarfinda ƙwaƙwalwa sai tasha wahala kafin ta iya ɗauka.

Na shirya cikin riga da zani acikin kayana nabawa Maryam tasaka dan batazo da kayaba muka fita wajan aikin. Babu kowa a cikin gida da alamu ba'a fara aikinba Maryam tatafi neman su Anty fadeelah nikuma na shige wajan Baba a palourn baba na samesu Mama da Baba sai Mummy ta anty yaciro kuÉ—i da alamu yana basu na wani abunda za'a saya ne.

Na gaisheda Baba shine wanda bamu haÉ—uda shiba dama ya amsa da fara'arsa.

Yaji daÉ—in ganina cikin walwala idanba idonsa ba sai yake ganin jiya da yau kaÉ—ai nafara fike ramarda nayi.

"Mummy amma kindawo kenan koh?" na tambaya alokacin da nake ƙoƙarin tashi nabar palourn danna basu sararin ƙarasa maganarsu.

"Nadawo kenan Marmeeyy bazan sake tafiya ba har indai masu gidan sun amince da dawowata kuma sunce na zauna karna tafi" Mama ta washe baki.

"Dagaske kike Mummy kai Alhamdulillhi dan Allah kizauna karki tafi. Wallh tunda bikin yazo ina taraddadin ranarda zakice zaki tafi saboda zamanmu yayi daɗi sosai fiyeda na wancan lokacin. Yanzu duk ahunda yafaru abaya a maidashi yawuce kawai girma kamamu yakeyi mu rungumi yaronmu mu ƙarasa rayuwarmu atare"

"Nima sai yanzu na fahimci hakan zaman yafi daÉ—i kodan yanzu kun saki jiki danine. Nima kuma nasake ziciyata? Zaman da mukayi abaya sam baida daÉ—i yanzune idan zamuyi zama zamuyishi cikin aminci"

"Allah ya zaunar damu lafiya gabaki É—aya ya kauda duk wata fitina da zata taso konan gaba" anty tafaÉ—a su duka suka amsa da Amin.

"Allah yayi muku albarka gabaki ɗaya ya ƙara haɗe kawunanku" Baba yafaɗa. mama ta kalleni ke tashi kitafo da Allah ana magana.

"A'a haba mamansu nifa dalilin Marmeeyy nadawo gidannan idan kikace zakina mata irin wannan hantarar sai nakoma yanda nafito"

"A'a haba dai itada zata tafi tabarmu kwannan gabaki É—aya" Cewar anty.

"Aiko tunda zata tafi can waje mai nisa sai ayita lallaɓata har murabu lafiya"

Mama tana jinsu batace komaiba Na miƙe nafice dan ban fahimci abunda suke nufi ba. A harabar gidanmu na samu su Anty fadeelah harda maryam Amma ita tana gefe da Yaya habibu da sauran cousins ɗinsu Anty fadeelah nayi sallama na zauna.

"Marmeey zonan" yaya habibu dasuke zaune da Maryam a kujerun gefe yafaÉ—i. Natashi na isa wajan ban kaiga zamaba yafara magana.

"Marmeeyy manya Jiya ai banyi bacci ba nace barina tsaya naga dawowarki saiga Hammood naganshi ido da ido ya kawoki ke kuma daga kawoki gida harda Wuce gona da iri? Naga abunda kukayi ai Shegiya Ba Hammood ba ko koma waye kika gani ai bai kamata ki biye masa har yakai hannu ya riƙoki ba daga ƙarshe ina kallo yayi miki peck a kumatu. Idansu al'adarsu kenan ta larabawa ke al'adarkice da tarbiyarki haka dan ubanki? kuma bani kaɗai ba Baba ma yaga abunda yafaru dan baiyi bacci ba sai da kuka dawo yaga shigarki cikin gida sannan yace na kulle ƙofa" nayi narai-nari da ido jin cewa Baba ma yaga abunda Hammood yayi.

"Ai bakiyi kuka bama wallh sai Baba ya kirani yace na dakeki tukunna zakiyi kuka da gaske"

"Eh Marmeeyy lallai wuyanki yayi ƙwari wato har ƴan rungume-rungume kukayi" cewar Maryam.

"Allah ya isa wallh Maryam ni nace miki haka?"

"Zakija Allah ya isa dakyau alokacinda na dakeki"

"Metayi za'a daketa?" Ya Ahamd ya tambaya wanda shigowarsa kenan yafito amota yaji yaya Habibu yana zai dakeni.

"Ya Ahamd bakasan abunda yarinyarnan tayi ba dagaka kaita wajan Hammood saita wuce gona da iri ta manta da tarbiyar da aka bata"

"Me tayi haka na mantawa da Tarbiya Habibu?"

Toh gashinan nabiya harda na jiya

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Hawayenda nake riƙewane suka zubomin.

"wallh Yaya Ahmad banyi komaiba kawai ya rakoni nan ban ankara sai naji.." nayi shiu nakasa ƙarasawa hawaye suna zarya akan fuskata.

"Riƙo hannunta fa yayi daya sake hannun kawai sai yayi mata peck a forehead nata, sa'arsa ɗaya Hammood ne da wanine ai tamolo zanyi dashi wallh kuma Baba mafa yagani"

"KaCe Baba yagni?"

"Eh dan inada tabbacin yaga shugowarsu bayan yatafi yace na rufe ƙofa"

"Toh Baba yagani Habibu baiyi magana ba ai kaima da kaja bakinka kawai kayi shiru koh?" kai kasan dole akwai dalilin dayasa Baba baiyi magana ba.

"Nima nayita tunani haka danna É—auka sassafe zai kirani nayita tamolo da ita"

"Toh taso nan kaji " yafaɗa yana riƙo kafaɗarsa suka bar wajan. Nazauna a gefen Maryam naƙi kulata.
Chapter 63 · 0% Book details