← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 106

Sashe 76

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Shiru nayi ina sauraron abunda zaice dan ganin yayi murmushi ya ƙaramin ƙarfin guiwa.

"I know bakizo tafiya ba amma yaya za'ayi? You have to kamar yanda na faɗa miki abaya cewa duk ranarda nasaka ƙafata a ƙasarnan bazan tafi batare da keba and yanzu gashi nazo nasan za'ayi haka yasa na ƙara miki morerthan 1month akan lokacin gama school ɗinki yanzu tunda na saka idanuwana akanki bazan iya tafiya ni kaɗai ba, wannan dalilin yasa tunda natafi ban kiraki a waya ba dan ina tunanin da Zarar naji muryarki bazan iya yimiki adadcin ƙarin lokacin dana sanyawa raina zanyi ba, I'm sorry amma wannan karon yazama dole nutafi tare" kukan taɓara na fashe dashi dan dajin kalamansa suna fitowane daga zuciyarsa bazai iya barina na ƙara lokaci tare da ƴan uwana ba. Ya dawo wajanda nake a zaune cikin sanyayyar muryarsa yafara rarrashina yana mamakin yanda kuka bayamin wuya danasaan yanda kukana yake cutar dashi da bazan sake yarda ko drop na hawaye ya ɗiga a idona ba.

"Shhhh is okay Zaynab please لا تبكي (Dont cry) yanzu toh we're not leaving tomorrow sai Jibi" na maƙe kafaɗa nacigaba da kukana. Hannuwansa ya sanya ya kamoni gabaki ɗaya ya shigar dani jikinsa ya rumgume lokaci guda kukan ya tsaya batareda ya furta wata kalma ta rarrashi ba na rumtse idanuwana ina shaƙar ƙamshin jikinsa. Shima ya ɗaura kansa akan gashina yana shaƙar ƙamshin dayake fitowa daga ciki. Dama Mummy ta bada an haɗamin Humra masu masifar ƙamshi kusan kullum saina turara jikina dasu da turaren jiki dana gashi da kulaccam na jiki dana gashi. Mamakin irin ƙamshin dayaji a jikina yakeyi yaji ƙamshi kala-kala a duniya na turaruka brand masu masifar ƙamshi da tsada amma bai taɓa cin karo da makamancin ƙamshin dayakeji a jikina ba bakowani irin ƙamshi bane yake masa daɗi he's picky about turaruka shiyasa turarensa yake na daban amma yayi admitting wannan ƙamshin mai daɗine gashi yana sauƙarda nutsuwa shiru mukayi gabaki ɗayanmu kowanne da abunda yake saƙawa a cikin ransa. A hankali na raba jikina da nasa na sunkuyarda kaina dan banaso mu haɗa idanuwa murmushi yayi ganin kukan ya tsaya. Sai alokacin yasamu ƙarfin lallashi amma lokacin ina kukan rasa abunda zai faɗa wanda zai ƙwantarmin da hankali yayi dan gabaki ɗaya rikicewa yake idan yaga hawayen fuskata sai dai shi rikicewarsa ba'a iya ganeta dan sai dai kawai ya tsaya ya tsura ido batareda yasan abunyi ba.

"I'll إن شا اللله be good to you ki kwantar da hankalinki Ina Sonki sosai bazan cutar dake ba in sha Allah bazaki samu wani tashin hankali a gidana ba zan tsaya miki a komai a matsayina na mijinki and your protcetor bazan yimiki alƙawarin cewa bazakiyi kewar gida ba amma I'll be there na ɗebe miki kewar da kike tare da ita. kuma bazance zan kasance tare dake a kullum ba sai dai ke zaki iya kasancewa tare dani a kullum Idan kinso zaki bini duk yanda zan saka ƙafata muje tare dan banaso ki kasance cikin kaɗaici" nayi shiru ina sauraronsa wato dai barina a gidane bazaiyiba ya rantse sai mun tafi a wannan tafiyar. Baiyi dare sosai kamar yanda ya sababa baifi 1hour ba yatafi saboda akwai abubuwanda yake buƙatar yi kafin yabar ƙasar kai tsaye cikin gida na nufa dukaninsu suna harabar cikin gidan Har mummy dake shashinsu ɗaya da Baba kuma a palourn Baban muke zama shiyasa tafita tabamu waje. Na ƙarasa wajan da suke zaune ana kallona ansan naci kuka.

"Kuka kikaje kikayi masa kenan Marmeeyy? Kina tunanin kukanda zakiyi shi zaisa a fasa tafiyar?" mama ta faɗa cikin ɓacin rai.

"Toh dan tayi kuka shine tayi laifi? Waye baiyi kuka ba lokacin da zai bar gidansu? Kefa a gari ɗaya anguwa babu nisa haka kikayita zabga ihu har aka shigo dake cikin gidannan kina ihu amma bakiyi laifi ba sai ita wacce bama gari ba ƙasar za'a bari ta ita gabaki ɗaya idan tayi kuka tayi laifi?" Mama taja baki tayi shiru jin Mummy na shirin yimata tonon silili a cikin yara. Naje na zauna wajan Mummy na ƙwantar da kaina a kafaɗarta. Cikin muryar kuka nace.

"Mummy kijifa wai jibi zamu tafi dan Allah kiyiwa Baba magana yace masa yabari sai wani sati"

"Au jibi? Kinji tafiyar yanzu tadawo jibi ai Marmeeyy da gobe ne ma tafiyar ta iya yiwuwa yaji tausayinki ne ya ƙara kwana ɗaya akai kuma yanada abunyi ai a cikin satinnan naji Ahamd yana faɗa"

"Mummy toh yatafi mana sai mutafi abayansa ai ba sai lallai muntafi tare ba idan muka isa sai yasaka aje a É—aukomu"

"Kinga Marmeeyy ni ban is ada wannan zance ba bawan Allahn nan dai yayi ƙoƙari wallh aure yana neman shekara anata jaa masa lokaci saifa da akayi aurenku sannan akayi na Ahamd gashi matar Ahmad yanzu inaga cikinta yakai wata 6 shiyasama bazamuje tare dashi ba ko bikin Aysha yanzu wata 4 yake ciki ina muka isa muce masa yatafi wai sai bayan sati ɗaya? Sati ɗya da jibi ai duk ɗayane wajan ubangiji idan darai da lafiya" na fashe da kuka.

"Wallh Mummy nikam a wajena ba ɗaya bane ko ƙwana ɗayane idan zan ƙara cikin ƴan uwana zanji daɗi"

"Nidai wallh Marmeeyy bansan yaushe kika dawo haka ba gabaki É—aya kin dawo sakaliya wai akanki aka fara aure da zakiyita fitowa mutane da sababi kala-kala? Ba gashi zaku tafi da Fadeelah da Mummy ba harda Yayanki mafa waya samu irin gatan da kika samu? Kowa shi kaÉ—ai aka kaishi gidan miji amma banda ke wacce gata yayiwa yawa" mummy tayi dariya.

"Toh idan Mummy da fadeelah da Habibu sunanan Mama tana nanne? Ko akwai Baba? Babu anty babu ƙannenta Dan Allah ki saurarawa yarinyar nan taji da abu guda ɗaya." Mama taja baki tayi shiru sukaci gaba da rarrashina harda Anty.

Washe gari sassafe nida Anty fadeela mukaje gidan Aysha har azahar mukakai acan daga nan nawuce gidansu Maryam. Itama tun safe tamin waya akan zatazo nace mata gani gidan Aysha idan nagama zan biyo ta gidan. Kuka sosai mukayi nida Maryam Ummi tana aikin lallashi dama yanda muka shaƙu tasan dole idan akazo rabuwa da aiki. Daga ƙarshe tare muka tafi da ita agidanmu muka ƙwana. Da safe Haka mama tatashi ido jajazir da alamu taci kuka cikin dare amma sai fisfisgewa takeyi dan kar agane. Nima tunda natashi dasafe nake kuka maryam tana tayani mama ganin bazata iya rarrashi ba tabar mana ɗakin gabaki ɗaya. Tun safe nake zuwa ɗakin Baba a kulle gashi wayarsa bata shiga. Dana matsa da zuwa Mummy tacemin ai Baba tunda yafita sallar asubahi bai dawo ba dan dama haka yaƙwana baiyi bacci ba. mummy tace ko runtsawa baiyiba. 12am zamu tafi gashi har 10 Baba bai dawoba nazauna ina kuka ni bazan tafi ba sai naga Baba duk ƙarfin halin Mama saida ta zauna ta rarrasheni. Yaya habibu yafita neman Baba yaduba duk yanda ya kamata amma bai sameshi ba. Hamma ya kawo Aysha muyi sallama saiga Aysha tana kuka riras ganin yanda nake kuka kuma tasan tafiya zamuyi" tsabar kuka jikina har yayi laushi kukan yadaina fita da sauti sai zafin zuciya da nakeji 12 kuwa muka tashi tafiya alokacin danaga tafiya za'ayi nafara tijara babu wanda baiyi kuka ba kaff gidanmu. saida Mukabi gidan Hajiya da Gidan Baba (Alhaji habibu) mukayi masa sallama sukayitamin nasiha sannan muka kama hanyar airport. jirginmu ya sauƙa a abuja amma gidansu Mummy muka wuce sai nazamo kamar wata celebarity kowa son kallona yake ni ɗaki ma nawuce dan haushin mutane nakeji daƙayr mummy tasaka naci abinci ahakanma babu yawa ban fitoba sai bayan la'asar liss nasmau Mummy jibge da kayyayaki agaba da turaruka da abubuwa wanda bansan menene su ba jibgi guda ashe ananma tasa a haɗa mata wasu kayan wancan an rigada an gama dasu dan har sun hau jirgi waɗannan ne zamu tafi dasu. Har kayan sawa da Mummy ta ɗinkamin bansan adadinsu ba gasunan akwati set guda mai 4pcs. Munyi waya da Maryam daga zuwanmu kusan sau 5 kenan a lokacin na faɗa mata saƙonta dana bari awajen Mama. Har wayar Hannunama yanzu ƙarama ce nabar wancan a bata Baba har lokacin wayarsa a kashe take. Kuɗin wancan account ɗin kuwa tunda aka saka ranar tafiya kullum sai nayi tranfer wa Mama iya gejin Tranfer na account ɗin per day.

Bayan magrib jirginmu zai tashi kafin magrib zazzaɓi ya rufeni saboda kukan danasha. Mummy ta haɗamin ruwa nayi wanka tazo tabani magani nasha sai bacci ana kiran sallah naji a kunnena natashi nayi sallah ina zaune har akayi isha'i natashi na gabatar da sallah ban ida ba saiga Mummy tashigo akan nafito. Har lokacin jikina da ɗumi Mummy ta ƙaramin maganin dan bataso jikin yayi tsanani muka tafi airport kai tsaye. Ayanda naga alamun jirgin babu wasu mutane a cikinsa muka shiga aka kaimu wajan zamanmu muka zauna. Bamufi 30minute da zama ba jirgin ya ɗaga dake nasha magani lokaci guda bacci ya ɗaukeni ga zazzaɓi Sa'i-sa'i kawai nake farkawa ina komawa bansan awa nawa muka ɗauka muna tafiya ba dan inajin zazzaɓi sosai hakan yasa baccin yayi nauyi. A hankali nake buɗe idanuwa na Nayi miƙa haɗe dayin addu'a idona har sun kumbura saboda kuka har alokacin hucin zazzaɓi fita yake a jikina.

Idanuwana suka sauƙa akan Hammood wanda yake zauune cike da damuwa da alamu jira yake natashi dasauri na miƙe ina kallon gefe babu mummy da Anty fadeelah ko Yaya habi namiƙe a hankali zan zauna dan jiki a babu ƙwari ya taimakamin na tashi zaune ina kallon gefe yagane wanda nake nema.
Chapter 76 · 0% Book details