← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 106

Sashe 38

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sama-Sama suka gaisa sannan yace akawo masa ruwa mai sanyi yasha. Mu muna can gefe muna zaune muna jira su gama mutafi Mummy ta kirani tace nakakawowa Ya Ahmad ruwa. Namiƙe ina faɗin Ya Ahmad ina kashiga tun safe ana nemanka. Batareda najira amsarsa ba nawuce na ɗauko masa ruwa da drinks na yi wajanda suke zaune. Tun kafin na ƙarasa idanuwan abokanansa yake kaina kamar zasu cinyeni ɗanya. Yaa Ahmad ya kalleni idanuwansa suka kai kan kayanda yake jikina. Ya ɓata rai sosai yace.

"Marmeeyy wannna wani irin kayane a jikinki?" na kalli jikina na turo baki nace.

"Me yayi" yaya habibu yace.

"ƙaniyarki yayi maras kunya"

"Yaya tailor É—inne yarage measurement da nabashi shine kayan ya matse" yajijjiya kai yace.

" toh amma dai badasu zakije wajan event ba koh" nayi narai-narai da idanuwa nace.

"Yaya toh damai zanje"

"Marmeeyy ki rufa mana asiri kicire wwannna kayan idan bazaki cire ba rashin zuwanki shi yafi mana alkhairi" yafaÉ—a gabaki É—aya nida Mummy muka zuba masa idanuwa. Cikeda tuhuma Mummy tace.

"Wai meyasa kasawa yarinyar nan idanuwa? Haka jiya taƙi zuwa wajan event saboda tsoronka a dama haka kake mata yanzu bikin naka ma bazaka barta ta sake ba?" da mamaki yake kallon Mummy yanda take backing Marmeey ya tabbata kosu Aysha yake yiwa faɗa bazata saka baki ba amma ta hayayyaƙo masa akan marmeyy. Shikuma ya faaɗi hakanne saboda yasan irin sonda Hammood yake mata kuma ya tabbata idonsa yana kan duk wani abunda take yi. Yasan yanda larabawa soyayyarsu take tafiya da masifaffen kishi barinma so irin na Hammood daya fita daban. Allah kaɗai yasan abunda zai iya aikatawa akan soyayyarta. Amma ganin Mummy nason ta fahimci wani abun yasa yace.

"Ina sauran suke kuma ku taso naga kayanda kuka saka. Dukansu suka taso yace.

" kingani koh marmeeyy duk cikinsu Babu wanda kayansu yakama kamar naki. Kije ki canja kokuma na hanaki zuwa bikin gabaki ɗaya har agama event dan dai bazaki fita ahaka ba" Na ɓata fuska sosai nace.

"Yaya kainefa farkon aure agidanmu yanzu dan Allah idan banje wajan bikinka ba bikinwa zanje"

"Ni bani bane farkon aure kije ki saka gyale" ban fahimci abunda yake nufi ba dan haka ban kai hankalina wajan ba. maryam ta ƙunshe dariyarta dan ta hango yanda kayan zaiyi da gyale. Idanuwana suka cika da ƙwalla bawai nasaka gyalen dayace nayi ba sai dariyarta naga sunamin. Ina shirin fashewa da kuka nace.

"Yaya kaga dariya sukemin" yace.

"Dukanku ku É—aura gyale akan kayanku kokuma bazaku jeba. Kuma sauran kayanku dake wajan tailor gara ku kirashi tun yanzu karya muku irin wannan É—inkunan ko bazaku saka su ba" Mummy tace.

"Kinga Marmeeyy rabu dasu karki ɓata ƙwalliyarki" muje anemi gyalenda zaki saka" nayi wajanta muka shiga ciki dama tana business na gyalluluka da takalma harda jakankuna acan na nemi gyale da takalminda suka shiga harda ƴar ƙaramar jaka. Saima hakan danayi yafi ƙyau. Nafito dukansu Mummy suma ta fitar musu da nasu. Ina fita Ya Ahamda yace.

"Bakiga kinfi kyau ahaka ba?" naturo baki nidai bance komai ba. Yaciro dabino a wani ɗan kwali daga aljihunsa ya miƙamin na amsa da murnata baiyimin wani bayani akaiba na jefashi ƴar ƙaramar jakata. Saida Ya Ahamd yayi wanka ya shirya sannan muka fita dan tafiya a motar abokanan ya Ahamd muka tafi. Daga nan muka wuce gidan amarya muka ɗauketa tukunna muka wuce wajan event. Matar Ya Ahamda kyakkyawa ce sosai. Kuma tanada son mutane Anyi event lafiya angama muka dawo gida. Dake mungaji sosai acan yasa muna dawowa sallah kawai mukayi muka ƙwanta. Dan munci abinci wajan event.

Dake munƙwanta da wuri sassafe muka tashi dan gidan yafara cika.

Yauma anyi event angama lpy lau event yayi daÉ—i sosai. Mummy ce tabamu kuÉ—inda Zamuyi masa manni.
Biki yana buguwa kuma yana daÉ—i sosai.

Wani labarine wanda gabaki ɗaya ya hargitse kowacce ƙasa wanda har yanzu aka kasa samun sahihancin labarin.

Tun jiya Mood ya canja bio É—insa na social media da wani tambari wanda acikin celebrities masu aurene kawao suke amfani da wannan tambarin duk wani celebrity da akaga yasaka wannan toh tabbas yana da aure lamarin yaja hankalin Al'umma lokaci guda aka buga a gidajen jaridu tareda tambayoyi masu tari yawa. Gidajen TV da radio da sauran kafafen yaÉ—a labarai. Duk wannan budirin da akeyi bansamu labari ba har saida nahau instagram kowane page na duba maganar kenan amma babu wata gamshesshiyar amsa dm É—insa kamar zai fashe da messages ko masu kulada social media É—insa basuda lokacin bin waÉ—annan messages bare shi da saiya samu lokaci yake dubawa.

Gabaki ɗaya Hammood yaja yayi buru da al'amarin kamar wanda bashi dakansa yaɗaura abunba. Ya ɗaura yaja gefe ya nutsu waje ɗaya yabar masoyansa da kace nace. Wasu daga cikin masu haukar sonsa harsun fara rikici saƙon barka da taya murna kuwa a lokacin baisan adadin shigowarsu ba. Koda zai ɗauki tsawon wata biyu yana replying saƙo batare da hutawa ba bazasu iya maida saƙon da suka samu duka a wannan lokaci ba. Su kansu masu handling social media nasa basusa takamammen bayani akan abunda yake faruwa sudai kawai sunga yahau yayi uploading abu Kuma basuda tacewa ko damar tambaya su dai kawai suna aikinda aka ɗaukosu suyine."

ZAYNAB BAWA

Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Ajiyar zuciya nasauƙe alokacinda na gaji da duba lamarin dayake faruwa. Nasauƙe wayar ina faɗin.

"Wata tayi wuff da wannan aljanin"

"Waye kuma aljani?" maryam ta tambaya.

"Hammood mana ɗan wasan ƙwallo wanda ranar muke hiransa. Kinmanta har nake cewa Su dama ƴan wasan ƙwallo basu cika auren sanannu ba sukayimin musu firr bagashi ba"

"Toh yanzu waya aura?" ta tambaya.

"ni ina nasanine? Ai bai faÉ—a ba"

"kun haɗa kanku da aiki" cewar Aysha dan ita tatsani wasan ƙwallo. Muna hirar Mummy tasauƙo tace muje part ɗin Hajiya akwai abincin da akayi order ankawo mu kaiwa su Ya Ahamd. Duka muka miƙe muka fice saida mukabi wajan Hajiya muka ɗauko abincin sannan nufi wajansu. mukayi sallama suka bamu izinin shiga sannan muka shige dukansu suna zaune a palour muka ajiye suma inajinsu zancen Hammood sukeyi. Ya Ahmad yace su Aysha suje su ɗauko musu cups da plates mukuma mu zuba musu wanda zai iya ciyiwa acikin takeawaye ɗin.
Box na Snacks na buÉ—e na fara jera musu akan a box É—aya Babba akan carfet. Ya Ahamd ne yasake dawo da hirar Hammood da sukeyi yace.

"amma hammood É—innan yanada nutsuwa koh? Dannaga kaman cikin footballers É—innan yanayinsa yafita daban. yanyinsa yanuna yanada nutsuwa" ÆŠaya daga cikin abokanansa ne ya amsa yace.

"Eh sosai ma yanada nutsuwa kasanfa shi ba irin rayuwar celebraties yakeyi ba. Da ace wanine yasamu wannan ɗaukaka daya samu aida ba haka ba dan yanzu haka ina tunani kaff celebrities na duniya yafisu yawan mabiya a zahiri da kafar sada zumunta. Duk wannan ɗaukaka da Allah yabashi at his young age amma rayuwarsa a nutse yake yinta gwanin sha'awa bayida wani mummunan hali" Ya Ahmada ya sauƙo kan carfet ɗin yaja box ɗin gabansa sannan yafara faɗin.

"Kunsan na taɓa haɗuwa fa dashi nayi noticing hakan nida kaina komai nasa a nutse da tsari ko maganarsama a tsari yake yinta kuma da alamunsa bai cika magaba ba" Kamar wanda aka tsomo bakina aciki nace.

"Ya Ahamd dan Allah dagaske kuma kunyi magana dashi? Meyasa baku É—auki photo ba?" Bai amsa tambayata ba yace.

"kinaso ki ganshi ne?" dasauri na gyaa masa kai yace.

"kibari idanya sake zuwa ƙasarnan zan kaiki ki ganshi" cikeda murna nace nagode. su kansu Friends ɗinsa sunyi mamaki da Yaa Ahmad yace ya ganshi. nan suka fara zolayarsa shima yazama celebraty. Duk wanda ya Haɗuda Hammood shima abun kallo ne. ɗaya daga cikinsu ne yace.

"Mutumina daga nemi autograph na mutuminnan da kasha ƙwana" kana zaune zakaji daga wata ƙasa wani hamashaƙin masoyinsa mai kuɗi yasiya a kuɗin tashin hankali. Dariya kawai Ya Ahmad yayi musu. Shikansa a lokacin daya fara haɗuwa da Hammood yaɗauka irin shirmen mafarki ne. Saida akwa ƙwana aka tashi yayarda ba mafarki bane. Har yanzu wani lokacin yana tsoron kada yafarka yaga ashe duk tsawon lokacin da aka ɗauka mafarkine. Alokacinda Baba yake faɗa masa zancenda Hammood yazo dashi ya daɗe sarewa rayuwar duniya. Ya tabbata rayuwa cike take da abun al'ajabi kuma yasan wannan ba komai bane sai wani ikon ubangiji. Shi kaɗai ya isa ya aikata wannan lamari ya sanya soyayyar marmeeyy acikin zuciyar mutum kamar Hammood. Su maryam suka dawo da plates ɗin da cups harda spoons muka serving ɗinsu sannan muka fice.

Bayan munfita abokin Ya Ahamda wanda yaketa shigemin yacewa ya Ahmad

"Yaahhh Dani nifa ina ciki da wannan ƙanwar taka yaya za'ayi dan Allah kabani ita wallhi aurenta zanyi. Ahmad yace.

"Ka makara"

"Kunyi mata miji kenan?" Kai tsaye yace masa Eh" Yaya habib yana jinsu baice komai ba amma shi baisan anyi mata mijiba. Yana tunanin Ya Ahamd dai kawai bayaso yabawa abokinsa ne. Baici abinci ba ya faki idanuwa ya sulale yatafi wajan Maryam.
Itama muna shiga tafice wajansa nikuma na shiga ɗaki saida muka wuce 11pm muna waya da Hamma sannan mukayi sallama. Har lokacin Maryam bata dawo ba dan haka nafice zuwa ɗakin Mummy nasami tana cire kayan da zata saka tana waresu kowanne da sarƙoƙinsu da gyalesnu na zauna na na tayata muka cire wasuma saita sanyasu na canja nace yafi dacewa da ɗayan dariya kawai takeyi idan nayi hakan. Har wajan 12:am ina wajanta. Muna hira sai dariha takeyi nace.

"Mummy" tace

"Na'am marmeeyy"

"Mummy kinada kirki"tayi murmushi da alamu taji daÉ—i sosai tace.

"Marmeeyy abakinki na farajin wannan kalamr kowa cewa yake banda kirki ko ba'a faÉ—amin hakan a idona ba yanayi ya nunamin. Har Æ´aÆ´an cikina kuwa"

"Allah dagaske nake Mummy kinada kirki amma tunda kowa yana cewa baki dashi ni kaÉ—ai kawai nagani ta iya yiwuwa na fuskanceki ta wata fuskar ce. kokuma yanda kika mua'amalanceni daban da yanda su kike musu Mai zai hana sauran ma ki canja mu'amala dasu? Ta'iya yiwuwa ma sai sunfi ganin kirkinki akan ni yanda nake gani" ta kalleni kawai batace komai ba. Nasake cewa.
Chapter 38 · 0% Book details