Sashe 23
Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
"kinsan halin Hamma ai bazai taɓa yarda ba yanzu hakama ya shirya ni yake jira" ni dama nagama shiryawa dan haka nazauna ina jiran zuwansu. Da suka iso ta kirani nayiwa Mama sallama na fice Maryan harta koma Baya kamar yanda tasaba yanzu banso na sameta a baya ba da bayan zan shige dan yau kunyar Hamma nakeji. Suluf-suluf nashige na gaisheshi yana kallona amma sam naƙi kallon yanda yake murmushi yayi daya gane kunyarsa nakeji sai dai baisan kunyar ta menene ɗaya ba, ta sakin layin da yayi jiyane kota cewa da nayi ina sonsa.
A bakin gate na school ya ajiyemu Maryam ta fita harna saka ƙafata waje na juyo na kalleshi. Shima ni yake kallo dan haka nayi saurin yida kaina ƙasa nace.
"Hamma nayiwa Antyna maganarka.
yanzu agidanmu akwai wanda yasanda tarayyarmu" yayi murmushi yace.
"naji daɗi sosai nagode ahaka har Baba zai sani wata rana. Dariya kawai nayi ina ƙoƙarin fita yace.
"Bakicemin kina sonaba zaki tafi" Nace.
"Ai kasan inayi" nafaɗa hakan alokacinda nake ƙarasa fita. Maryam tana tsaye tana jirana ina ƙarasowa tace.
"Kukam dai sai gyaran Allah abu ba kunya sam ba tsoron Allah kuyita kallon juna kuna sakin murmushi gaban mutane aiko wanda bai saniba daya ganku zaisan kuna soyayya" Nace.
"kefa bakida Hankali idan bamuji tsoron Allah ba kinaso muji tsoronki ne?"
"Ke dai Allah yayi banza tafaɗa haɗeda wuce nima nabita abaya har muka ƙarasa lacture hole."
Zaynab Alabura
*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
Lacture É—aya mukayi muka dawo gida kasancewar ranar friday ana tashi muka fita gate kawai kowacce tahau abun hawa batareda munjira anzo an É—aukemu kamar aka sababa.
Da motar Yaya Ahmad naci karo a harabar cikin gidan, aɗakin Mama na sameshi da alamun isowarsa kenan ko wajan Baba bai ƙarasa ba nashiga da fara'ata ina gaidashi yace.
"Marmee har andawo daga makarantar?"
"Eh yaya lacture É—aya mukayi yau Friday dama bamu cika daÉ—ewa ba" yace toh Allah yataimaka bari nashiga ciki naduba Baba. Mama tace.
"Babanku yafita ɗazu amma yace bazai jimaba saƙo yasamu na gaggawa ayanda ya sanar dani" Yaya Ahmad yace.
toh barin fita kafin yadawo nima zan dawo" Dasauri nace.
"Yaya dan Allah bari nazo ka ajiyeni gidan Hajiya (Maman Baba) rabona da gidanta na daÉ—e bazan iya tunawa ba" yatashi yana tafiya yace.
"kiyi sauri" mama tace sai kiyiwa ƴan uwanki magana ina tunani tunda suka dawo ko sau ɗaya basu taɓa zuwa ba" nace.
"Toh" namiƙe nayi ciki nayi musu magana dasaurinsu kowacce taɗauki mayafi dayake dama sun gaji da zama Jiya ko makaranta basu fita ba hakama yau saboda tsoron abunda Mummynsu zata iya aikatawa. kaya kawai na canja nasaka Hijabi Nafito Mama tabamu mai da sinƙin sabulai sai abincinda tayi ta zuba a cooler tace akai mata dama akai-akai ana kai mata abinci. acikin mota muka sameshi.
"Abakin ƙofa ya sauƙemu yace ku gaisheta" da Mamaki nace.
"Yaya bazaka shiga ba? Aikuwa bazataji daÉ—i ba saida ya kalleni kamar mai nazarin wani abun sai kuma yace.
"Nafi shekaru ban leƙata ba nasan yanzu idan naje sai tayita mita nikums banaso" nace.
"Yaya kabarta tayi mitarta na lokaci É—aya yashige gaba sai ka gyara kana zuwa ganinta akan lokaci. Amma yanke zumunci babu kyau" batareda wani tunani ba yace.
"muje toh" Daga baya Anty fadeela tace.
"Marmee hoo sarkin iya tsara zancen da magana kenan. idan kina zubo da zancennan na tabbata babu wanda bazai saurareki ba. Wannna bakin naki inaga babu wanda bazakicishi da zance ba zanso ki haÉ—u da Mummynmu naga ko bakinki zaiyi aiki akanta" Harararta Yaa Ahmad yayi yace.
"ke kifara haɗuwa da Mummyn kiga yanda zata kaya muku zaɓar rashin hankali ma a blacklist kuka sakata idan bazaku dawo ba kufito kuce mata bazaku
dawo ba mana amma yanzu mummy tana wuya daku yanzu haka ita ta turoni na tafi daku" Anty fadeelah taturo baki tace.
"wallh banzuwa ko'ina" yace.
"toh saiku gaya"
"Allah yaya dama mata dama ace idan mungaya mata zata yarda ta barmu ne saimu zauna yimata bayani" Aysha tace.
"Taɓ wallh ban binka. zama ka koma kamar yanda kazo kuma Babama yace ba yanda zamuje" yaja tsaki.
"mtswww uwar Æ´an tsiwa komai bazaki faÉ—eshi da ladabi kamarna Æ´ar uwarki ba" Aransa yana mamakin wai Babane zaice su bazasu koma ba sai Babandai yadawo zaiji kanun labarin. Suka fice dukansu suka shiga cikin gidan.
Hajiya tasake aure bayan shekaru da ɓatan Babansu Baba amma bata samu haihuwa ba. Sunyi shekaru da mijin kafinnan Allah ya ɗauki ransa bai daɗe da rasuwa ba. babu yanda Baba baiyi akan zai ɗaukota gidansa ba yaran mutumin suka hana. Sunce suma tazama mahaifiyarsu tunda anyi zaman mutumci yazama dole su riƙeta, tana zaune yaran duk abunda suka yiwa mahaifansu itama sunayi mata. Babban gidane sosai shashi-shashi kowacce sun zuba mata ƴan aiki. Da sallama muka shiga dake nice agaba nita fara hangowa tana kallona tafara faɗin.
"Idonki kenan ja'irar yarinya ɗazu da ubanki yazo gaisheni nagama yimasa akan rashin zuwanki. ta iya yiwuwa ma shi yayi miki magana kikazo. Habibu ɗan arzkiki daga dawowarsa sansa huɗu acikin gidannan" na ƙaraso ciki ina faɗin.
"mukuma Æ´aÆ´an tsiya koh?" tace.
"kyaji dashi ni dai bance ba ai fitinanniya" tana hango Yaya Ahmad wanda shi tagane tayi salati ta sanarwa ubangiji.
"Laha'ila ha illalahu Mahammadar rasulillhi Wa nake gani kamar amadu?" muka ƙarasa ciki Yaya Ahmad shidai murmushi kawai yakeyi" Tana kallonsu fadeela tace.
"waɗannan fa? Ƙannenka ne Ahmadu?" Yana amsa mata ta fashe da kuka tana faɗin bantaɓa tunanin zan sake ganinku kafin Allah yaɗauki raina ba. tana kuka tana faɗin.
"Amadu haka kukayi watsi damu kuka wulaƙanta zumunci. gara kaima idan anci sa'a ana ganinka amma banda waɗannan ta nunasu Anty fadeelah sukam sunbi uwarsu sunyi watsi da ubansu. Toh ingaya muku da uba ake ado zakuce na gaya muku sai an goranta muku rashin uba. Inbanda ku fitinannu waya ke ƙin ubansa uyumm. Uwarku ta hure muku kunne. Batayi muku huɗubar gaskiya. Idona idon uwarki saina faɗa mata Allah yayi mata abunda tayi mana a danginmu. Aysha data fara ƙuluwa tace.
"Ah ji matarnan" Yaya Ahmad yayi saurin taranta faÉ—in.
"ƙaniyarki Aysha, Hajiya kiyi haƙuri in sha Allahu zamu kiyaye" Hajiya tace.
"Kagani koh?" fitinianniyar yarinyar nan rashin kunya zatayimin" Natashi ina faÉ—in.
"kedai Hajiya idan kika kama mita bakyaji bakya gani. mu babanmu ba haka yake mana ba. Wallh kamanninki kawai ya É—auka banda Azabar masifarki"
"Allah na tuba daya ɗauko halina mace ta juyashi? badai halina ba wallh. Kitchen ɗinta na nufa batareda naji ƙarashin faɗanba dan bala'i kawai takeyi takasa sararawa sai haƙuri suke bata amma kamar wanda suke zugata. Na ɗauko coolern kwacokam datake zuba dambun namanta na fito dashi na zauna tana surfa bala'i ina ina gefe ina ci " Aysha ta dallah mata harara hajiya tace.
"uwarki kika harara" nace.
"Ya Ahmad tashi katafi abunka tunda bazata daina masifa ba" Tanajin haka tayi shiru nacigaba da faÉ—in wannan mitar kaÉ—ai Hajiya ta'isa ta hana zuwa wajanki kin sakasu gaba kinata faÉ—a. Sunzo kinyi faÉ—a basuzoba kice basu zoba kinyi faÉ—a wanne É—aya kikeso subi?" Hajiya tace.
" shikenan ai tunda baza'a faɗa muku gaskiya ba nidai nafaɗa yarage naku ku ɗauka uba ba abun yasarwa bane. Saiki kawo Muku kisaka muku agaba aiko tunda dai banaki bane natashi nashiga kitchen ina faɗin Hajiya basai kinmin gori ba akan dambun nama inaji tana magana amma bana iya jiyota na ɗauko ƙananun unbreakable bowls na fito aciki na zuba na maida coolern kitchen.
Muna zaune hira tayi nisa harmun manta da mitarta Yaya ya miƙe yace.
"Hajiya ni zan wuce" Hajiya ta ƙyaɓe baki tace.
"Sai kuma wace shekarar Amadu?" yace.
"Jimawa ma zan dawo zanzo na ɗaukesu" Hajiya tace toh Allah yasa. Saida akayi magrib kafin yaya Ahmad yazo ya ɗaukemu tare muka shiga cikin gidan dashi. Ƙamshin turarennan ne yafara muna barka hakan ya nuna yauma Baba yanada baƙi. tare muka ƙarasa har ɗakin Mama Yaya yace.
"Har yanzu Baba bai dawo ba? mama tace.
"Yadawo yana tareda baƙi"
"Toh nikam zanje saida safe na haÉ—u"
Mama tace.
"Allah ya tashemu ya amsa yafita"
"Mama baƙin jiyane suka dawo? " Na jefa mata tambaya.
"Eh dannaji Naji gidan gabaki ɗaya yaɗauki irin ƙamshin jiya" tabani amsa.
----------
Baba ya gyara zamansa dakyau yadubi Yaya Ahmad. Murmushi yayi sannan yace.
"Ahmad kenan A tunanina Uba ne yake sanarda ɗansa ranar auren yaro bayan yaje ya tattauna da mahaifan yarinya amma naji kai kake sanarmin lokacin aurenka. Bansan kodan banida komai bazan iya yimaka komai a wajan bikin bane yasa kayi haka amma ko yaya mahaifi yake Ahmad mahaifine kana tunanin zanji daɗin wannan maganar ne?" Jikin Yaya Ahmad yayi sanyi ayanda yasan Baba bai taɓa tunanin danya cemasa anje an tambaya masa aure harsun bada rana zai ɓata rai ba. Lallai Baba ya canja sosai. Jiki a sanyaye yace.
"kayi hakuri Baba banyi niyyar hakan ba da zarar na sanarwa Mummy saita tura gidansu yarinyar sukuma ana zuwa suka bada rana" Baba ya jijjiga kai kawai zuciyarsa tayi masa babu daÉ—i sakenda yayi agidansa yayi yawa dahar aka kai wanan stage É—in. jin Baba yayi shiru yasa Yaya Ahmad yace.
"Baba dan Allah kayi haƙuri" Baba yace.
"shikenan yawuce" amma idanda son rainane inaso ka zauna anan bazan tilasta maka ba amma idan zakabi umarnina inaso ka zauna anan garin kaida matarda zaka aura. Banason zamanka acan yakamata ace kaima yanzu kadawo cikin ƴan uwanka kayi rayuwa. Jiya da kukaje wajan Hajiya ta kirani tanata murna. Yakamata ka zauna anan bance dole ina nufin idanda umarnina zaiyi amfani. Yaya Ahmad ya sunkuyarda kansa Maganar gaskiya yanason garinnan amma akwai dalilin dayasa bayason zaman garin yanzu kuma ga Baba yanason ɗaureshi da jijiyoyin jikinsa yasan bazai iya kaucewa maganarsa kuma kamar yazama dolene ya faranta masa tunda yasan abunda akayi a neman aurensa ya taɓa masa kimarsa matsayinsa na uba, yasan ko dangin matar suma zasuyi mamaki ace Babu mahaifinsa a neman aurensa bayan yana raye. amma baisan yanda zasu kaya da Mummy ba idan taji" jiki babu laka yace.