← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 106

Sashe 62

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saida safe" na faɗi da yaranda nafi iyawa kallona yakeyi batareda yayi ƙoƙarin tafiya ba dukda nasan dama baisan abunda nafaɗa ba.

"طاب مساؤك"
Na canja harshe nafaÉ—a. Da mamakina wannan karon É—inma kallon bai fahimci abunda nace yayimin.
"Goodnight Okay?" yanzu ga gane?" baice komaiba baiyi alamun yagane ba baiyi ƙoƙarin tafiya ba yatsaya yana kallona kamar maison gano wani abun a tattare dani sai dai alamunsa ya nunamin tun a yanzu yafara missing ɗina hakan ya bayyana akan fuskarsa. Ganin baida niyyar magana ya sanyani juyawa ina ƙoƙarin tafiya. Da sauri ganin zanbar wajan ya riƙo hannuna. Da sauri Baba yasaki labulen plaournsa dayake tsaye tun 11pm yana jiran dawowata jin alamun shugowarmu ya sanya ya ɗago labule yana kallonmu harya rakani zuwa ƙofar gidan har izuwa jiyowata da yanzu daya kamo hannuna. Ajiyar zuciya ya sauƙe ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerar palourn. Zuciyarsa tana faɗin masa.

"Menene na damuwa tun akaron farko bayan kasan tane tareda mijinta? Duk wani hakki yana dashi akanta tunda ta rigada tazama mallakinsa." Wannan tunanin ya sanyata masa rai yazauna yana jiran yaji fitarsa sai yakira Habibu yace ya kulle ƙofa.

Kallon hannun nayi sannan na kalleshi A hankali nake ƙoƙarin ƙwace hannuna batareda yayi gardama ba ya sakeni na ɓoye hannun a bayana waje ɗaya saboda tsorom karya sake kamamnin ganin abunda nayi yasashi sunkuyarda kai haɗeda sosa girarsa wacce take da yalwar gashi sannan kusanci dashi zaisa agane a haɗe girar take waje ɗaya.

Step ɗaya ya ƙara ya iso gareni Banyi auneba naji Sauƙan lips ɗinsa akan forehead ɗina. Lumshe idanuwa nayi alokacinda naji sauƙan lips ɗinsa a lokaci guda haɗeda ƙamshin turarensa.
Cikin muryarsa mai daÉ—in sauraro yace.

*تصبحين على خير حببتي أحبك*
(Goodnight habibty) I love you"
Kyabkyabta idanuwa na nakeyi akansa nakasa taɓuka komai na tsaya kawai ina jiran naga yanda Allah zaiyi dani.

واحلام سعيدة
Yasake faÉ—i.
jiki babu ƙwari na juya a zuciyata ina faɗin akwai mafarkinda zanyi daya wuce wannan daɗi?

Saida yaga shigata sannan ya juya yatafi yanajin wani daɗi mai Cikeda kewa acikin ransa. Yau gashi ga abun sonsa sun ɗauki tsawon lokaci a waje atare yana kallonta yanajin daɗi bai taɓa ɗauka wannan lokaci zaizo ba dukda kullum baida aiki sai tunanin ranarda zata zama a ƙarƙashin ikonsa gabaki ɗaya. Har indai zama kasancewa da ita na awanni zai bashi farin ciki marar misaltuwa kamar haka to yaya rayuwarsu atare zata kasance? He's looking foward to rayuwarsu tare. Bayida high expectation akan komai amma ganin irin yanda yake kasancewa idan yana tareda ita a zallan kallo minute ko hours toh he's expecting/wshing something with pleasure a rayuwarda zasuyi gaba.

Ina shiga ciki da Maryam nafara arba. Ta leƙo dataci takun takalma ganin konice na dawo. Da gudu tazo ta rumgumeni.

"Yeaahhh my babe is back" anajin ƙarar ihunta aka fiffito kusan kaff gidan basuyi bacci ba kowa jiran dawowata yakeyi. Ganin maryam a gidanmu 1am ya ciremin kokonto ko shakka babu mafarki nakeyi.

Wucewa nayi ɗakn mama ina shiga Maryam da Anty fadeelah Suka biyo bayana. na juya na dannawa ƙofar lock na ƙarasa na buɗe fridge abunda hannuna yakai kai shina ɗauka nafara cika cikina tukunna Maryam tanata surutu ban kulataba Anty fadeelah tace.

"Ƙyaleta maryama a gajiye take yanzu bazata iya cemiki komai ba zuwa gobe dukanmu zatayi mana bayani" Ban kulasu ba saida naji cikina ya ɗauka natashi nashiga ɗaki na cire kayana nahau gadon Mama. maryam ta biyoni itama kan gadon.

"Babe menene yafaru naga da kayanda kika tafi badashi kika dawo ba" juya mata bayana nayi na naja bargo na ƙwanta ina kwanciya kuwa sai bacci ya ɗaukeni Maryam badan tasoba itama ya kwanta.

Mama aɗakin Baba take Dan batamayi niyyar zuwaba saboda baƙinda suke wajan tunda aka fara biki matan suka ɗauke ƙafa a turakarsa saida ya kirata yace taje dan yanaso ya tausheta akan abunda yafaru.

Baba yanajin fitarsu Hammood yayiwa yaya habibu waya akan ya kulle ƙofa. A kwance yasamu Mama tana bacci ba kamar shida yakasa ba. Jin motsinsa ya farkarda ita.

"Ina kaje a daren nan?"
Ya zauna bakin gado sannan yafara magana. Naga ke hankalinki ƙwance ƴarki tana can wani waje har kin iya bacci nikam bazan iya bacci ba sai naji dawowarta"

"Kaji Baba da wani zance mai zai hanani bacci kuwa? Aini inaga tunda na haifi ƴa mace ma bantaɓa samun bacci mai daɗi irinna yauba wajan mijinta fa taje, tunda ka ɗaura musu aure kasan wata rana gabaki ɗaya zata tattare tabishi tun kafin zuwan wannan lokacin gara ga cirewa ranka dan mermeeyy ba'a kusa zata zauna ba. Tunda kacemin hankalinka ya ƙwanta da yaron kuma naga alamun Marmeeyy zata samu farin ciki tattare dashi nima sai hankalina ya ƙwanta Allah ya Sanya alkhairi yabasu zaman lpy ya kauda duk wata fitina da zatazo abaya"

"Amin" Baba ya amsa Takoma ta kwanta.

"Bacci kuma zaki koma? Tunda kin farka tashi muyi sallah muyiwa yarinyarnan addu'a. Mamam tamiƙe zaune tajira Baba yayi alwala sannan itama tashiga tayi alwala Saida tatashi tabarshi yaba kan sallaya shikam saida aka kira Asubahi kafinnan yatashi daga kan sallaya yafita zuwa masallaci.

Tunda na kwanta bacci nake mafarkin Hammood Abubuwanda suka faru A daren ranar suketa maimaituwamin acikin mafarkina. A kunnena naji kiran sallar amma ban iya tashi ba har saida aka fito a sallah. Na mike nashiga toilet nayi lokacin maryam bata É—akin. ina sallah nasake kwanciya ZumuÉ—i ya hana maryam komawa bacci tana kwance tana jirana natashi taji labari.

ƙarfe ga takwas na safe 8am na farka Da murmushi natashi ɗauke a fuskata dan nayi mafarki mai daɗinda tunda nake bantaɓa mafarki makamancinsa ba.

Anty fadeelah ce tashigo É—akin.

"Au ashema kintashi. Haba Marmeeyy sai kace mai baccin mutuwa? Mun jiraki mun jira habawa kinsan dukanmu fa jiranki mukeyi yaushe hankalinmu zai kwanta isan bakizo kin bamu labari ba.

"Anty fadeela wallh wani mafarki nayi mai masifar daÉ—i"

"Lallai ma marmeeyy an done kiyi mafarki mai daÉ—i" kwanciya nakoma nayi ina murmushi ina tuna mafarkin danayi.

"Marmeeyy bar baccin man please kitaso kizo muna jiranki idanba so kike ki fasa zuciyarmu ba" Alokacim Maryam tashigo ciki tana faÉ—in.

"Babe wallh yanzu kam dolema kitashi dan bazan sake jiraba kuma haba wannan wane irin baccine aike kamata yayi ace yau murna ya hanaki bacci" tana shigowa tayi arba dani ido buÉ—e. Dasauri ta haye gadon.

"Kai Alhamdulillhi naji daɗin tashinki haba bacci yaƙici yaƙi ƙarewa mu kanmu bamu iya bacci ha saboda ɗauki amma ke kin zauna baccinki kawai kikesha" Da mamaki nake kallonta.

"Ke kuma meya kawoki nan sassafe haka?"

"Bangane meya kawoni ba? Anan nakwana toh Kuma jiya da daddre har magana namiki tsabar baƙin hali kikaƙi kulani yanzu kinzo kina cewa meya kawoni kaji zancen shirme" Zaro ido nayi ina kallonta da sauri na fara neman wayata dan tabbatarda abunda take faɗi." akan dressing mirrow naganta dasauri na miƙe na ƙarasa wajan na ɗauka ina dubawa naga akashe take dasauri na danna switch na kunnata zuciya sai bugu take ina jira takawo sukuwa suka tsuramin ido kawai sun kasa cewa komai.

Wayar tana Kawowa nasaki ƙara na yarda gefe dan ganin pic ɗina dana Hammood a face ɗin wayar. Zaro ido nakeyi ina sauƙe numfashi kenan jiya dama ba mafarki nayi ba? Ya Ahmad yacika alƙawarinsa kenan yakaini wajan Hammood nikuma nayita masa shirme naɗauka mafarki nake na ƙarasa. Tunowa da shirmenda nayi ya sakani sakin ihu haɗeda sanya hannuwana bibbiyu ina dukan kaina. Wani irin haushin kaina da takaici nakeji. Nasan shima kansa yanajin haushina a shirmenda nayi jiya, kukan takaici nasaka dan baƙij cikin abunda nayi.

Maryam ta taso ta É—auki wayata dana wullar itama ganin fuskar wayar ya sanyata ihu anty fadeela ta amsa tagani nan danan suka cika É—akin da Ihu mutamenda suke cikin gida suka shigo.

"Menene yake faruwa?" suka haÉ—a baki wajan tambaya.

"Pic É—in Marmeeyy da Hammood wallh shine Hammood ne yeahhh" mama ta girgiza kai ta juya gareni da nake kuka.

"Ke kuma menene abun kuka?" ban bata amsaba Mummy tayi sallama tashigo tana ganina zube aƙasa ina kuka ta ƙaraso wajena da sauri.

"A'a marmeeyy mekuma yafaru?" na ƙara ƙarfin kukan nawa ina shure ƙafa"

"Ko kiyi shiru kifaɗa mana abunda yafaru kona makeki" mama tafaɗa aƙufule. Na share hawayen haɗeda rage karfin kukan sai jan zuciya kawai nakeyi"

"Menene faÉ—amin ko marmeeyy ta? Meya sameki wani abun yafaru dakene?" cikin muryar kuka nafara magana.

"Mummy kingani Ya Ahmad ne yamin alƙawari duk ranarda Hammood yadawo nigeria zai kaini naganshi toh ranar sai yacemin yanada surprise ai kuna wajanma toh ni bansan menene ba. Sai jiya ashe wajan Hammood yakaini. Nikuma ganin Hammood yasa na ɗauka mafarki nake tunda banyi tunanin cewa zansamu ganinsa cikin sauƙi haka ba kuma haɗuwarma mu biyu kacal wane muhimmanci nake dashi da Hammood zai waremin lokacina ni kaɗai bayan manyan mutane da suka cancanta su ganshi suna neman ganinsa basu samuba. Toh ni naɗauka mafarki nakeyi wallh Mummy shirme kawai nayita masa jiya har cewafa nayi ina sonsa atunania tunda da an tashi bacci shikenan komai yawuce. Dana shiga ruwa nayi wanka har wanka nayi a masauƙinsa na canja kayana da wanda ya kawomin wallh Mummy duk na ɗauka mafarkine har taɓashi saida nayi atunanina tunda mafarki nake ban aikata komaiba. Toh shine yace muɗauki hoto duk amafarkin yayi saving a walpaper na har yadawo dani gida aƙofar gidannan ma yam..." Shiru nayi nakasa ƙarasawa ina tunanin yanda zancewa iyayena Hammoood yamin peck a goshina bayan baya ɗaya daga cikin muharramaina."Toh tohh shine fa yanzu kawai ina farkawa naga maryam agidanmu kamar yanda naganta jiya da dare. Kuma ina duba wayata naga pic ɗinda muka ɗauka A jikin wayata gashinan hakan yana nuni da ba mafarki nakeyi ba kuma ga kayanda nasaka nazo dashi ajikina ma" ina ƙarasa faɗin haka na fashe da kuka.

"Yanzu ke shirme kikaje kikayi masa? Allah ya kyauta ya shiryeki Marmeeyy" ina cikin kukan nace.

"mama dan Allah tayaya zanyi tunanin ba mafarki bane harfa cewa yayi yana sona a a wajan" idanba mafarki ba mai zanyi tunani tayaya zanyi tunanin Hammood zaice yana sona" juyawa tayi tafice ta takaicin abunda nayi mummy cikin rarrashi tace.
Chapter 62 · 0% Book details